Daudar Gora Book 2 page 79

 


…..Bayan wucewar Doctor jagwaf Jasrah takai zaune idonta akan yar uwar tata. Abubuwane da yawa ke mata kaikawo, ga dunbin mamakinta da al'ajabin wai mike faruwa haka? Ko ita dake a cikin halin tashin hankalin hallayar mijinta batajin tana a rabin wannan yanayin. Amma ita da bata nema komai na rayuwa ta rasa ba tarasa mike faruwa da ita. A kwanakin nan fa har rama tayi, sannan zaka ganta jigum kamar mai tunani duk ta hargitse. Gaskiya ta fara ji a ranta lamarin ya fara zarce na kiyayyar Iffah kawai. Akwai dai abinda take boye musu da ya kamata ace sun sani, dan al'amarin ma kamar gaba- gaba yake. Jiba dai yanda ta hargitsa dakin yau gaba daya, ta fasa abubuwa masu daraja da tasan ko sanda suna yara bata bari su taba mata. Tashi tai da kanta ta gyara komai, dan kiran wata hadima ta gyara kamar yana nufin fitar zancen ne, dan hadimai da yawa dake akowane sashe zaka samu an leken asirin wasu ne. Musamman ma ita da girman ikonta yasa kowa kunnensa bude yake da son jin labarin wani al'amari ya bullo da ga gareta makamancin haka. Tana cikin gyarawar doctor ya kirata ya dawo, ajiye aikin tai taje ta amso magungunan ta daw sannan ta karasa gyara komai ya koma need.


   Gabannin asuba ta farka a wani irin firgicen da yafi wanda ma Doctor ya ce zata iya tsintar kanta a ciki. Yanda jikinta ke rawa haka gadon ke rawa, ta fasa wata irin gigitacciyar kara ganin halittun da suka firgitata a cikin barcinta zahiri muraran a cikin dakin. Gaba daya sunma gadon zobe ga wani kalar kuka da sukeyi mara dadin saurare a cikin kunne., Sotake ta ambaci sunan ALLAH koda sau daya ne amma bakinta ya gagara furtawa, sai rawar da lips dinta keyi kamar yanda jikin nata ke rawa. Duk da sanyin ac dake dakin ita a jike take sharkaf da zufa kai kace wanka tayi.


"Hahahaha!!!!"


  Uwa ta bayyana cikin mummunar dariyarta. Kamar koda yaushe a kan kujerar tata take cikin jajayen kayan nan. Mummunar fuskarta ta tsufa ta sake munancewa tsabar itama bata a cikin hayyacinta.Dariyar ta sake kyakyalewa da shi da fadin, "Kikace zaki ¡ya hahaha! Dama na fada miki ke karamar mara kunyace Bushirat, k! Karamar tsagerace!! Hahaha!!!!! Daga yanzu zuwa ranar cikar burina saina dandana miki azaba, kisa a ranki yanzune wasan zai fara na gaskiya. Kuma dole ne ki biya diyyar da jinin dan da mune mukai sanadin samuwarki garesa (Wa'iyazubillah🙏) da ga karshe zan tona miki asiri ta yanda jama'arki su zasu idasamin rayuwarki karamar yar iska kawai butulu. Hahahaha!!! Kuje gareta, ku sauyamun kamaninta". Ta fada cikin bada umarni ga munanan halittun nan ita kuma tana bacewa. Wata irin zabura sukai kanta, hakan yay dai-dai da bude kofar da Jasrah tayi a rikice, dan ta farka saboda kiran sallar asuba kawai ta dinga jin kamar dokuna na sukuwa a cikin masarautar, shine ta fito a zabure, amma maimakon jin da take duka masarautar ne sai taji kamar a dakin Malikat Bushirat din ne kawai, shine ta nufo nan a rikice. A take duk suka bace batare da taga komai ba, sai Malikat Bushirat da gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Sallallami ta dauka tare da haurawa gadon a rikice, bata kawo komai a ranta ba face maganar doctor da yace dama zata iya farkawa a rude, ita kuma ta koma daki ne dan taji yace zata iya kaiwa ma safiyar gobe bata farkaba saboda nauyin allurar da yay mata.


  Rikota tai ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu na tausayin yar uwar tata. Zuciyarta ta fara bata kodai asiri akai mata ne wai....






**..





Itama a gabanin asubar ta farka a razanen da ta saba a duk sanda tai mafarki mai nauyi irin haka. Ta dafe kanta dake sara mata tana mai karanto addu'a. Taja kusan minti biyar a haka kafin nutsuwa ta dan dawo jikinta. Hannunta ta janye da ga saman kanta tare da kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke getenta yana barcinsa hankali kwance. Fuskarsa ta tsurama ido kamar mai son karanto komai data gani a cikin mafarkinta kan fuskar. Ta jima batai mafarki mai sakata a rudani irin wannan ba. Itakam wadan nan abubuwa sun fara damunta, Shikenan da ga wannan sai wannan kullum babu hutu, da anyi maganin wannan sai was su sake ballowa wace irin rayuwace wannan. "Ya rabba ka kawo mana iyakar wadan nan

musibu". Ta fada a hankali tana sauke ajiyar zuciya. Yunkurawa tai zata sauka a gadon taji an rikota. Juyowa tai ta dubesa dan sam batai tunanin ya farka ba. Maidota yay ta hawo saman jikinsa, cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci ya kai hannu saman wuyanta da fadin,"Zazzabin ne?".


   Kai ta girgiza masa a hankali. Cikin yar damuwar mafarkinta da bai gama sakinta ba ta ce, "A'a na farka ne kawai asubama yay". Ajiyar zuciya kawai ya dan sauke batare da ya sake cewa komai ba. Itama sai ta sake yunkurawa ta mike....





    Tana idar da sallar asuba ta fito a dan harzance, dan so take taje ta dawo kafin ya dawo da ga massalaci. Sashen Malikat Bushirat ta nufa a yanayin badda kamar data fito. Kasancewar da dan sauran duhun asuba duk da ko'ina zagaye yake da haske babu wanda ya fahimci wanene a cikin tsirarun hadiman da suka fara ayyukansu. Koda ta shiga sashen ma tsirarune a hadiman suka fito fara shara. Cikin dabara ta dinga wucesu batare data yarda kowa ya ganta ba. Koda ta iso kofar dakin da zuciyarta yafi karkata da samunta sal data dan nutsu a kofar domin tabbatar da babu motsin komai sannan ta murda handle din a hankali ta shiga. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana bin dakin da kallo, babu kowa a ciki sai Malikat Bushirat din da ke zaune jingine da gado tana sallah a haka. Da alama bazata iya yi a tsaye ba. Key ta murzama kofar sannan ta karasa shigowa cikin dakin, dai-dai da ta idar. A dan yatsine Iffah ke mata kallon mamakin gain yanda tai wani irin zuru-zuru, duk rashin gane abubuwan mutum idan ya kalleta yasan akwai matsala a tattare da ita....


"Miya kawoki nan?".


Ta fada muryarta a shake sai dai cikin bacin rai. Baki Iffah ta labe itarna cikin tunzura ta bata amsa. "Kin san abinda ya kawo ni ai. Wai ke dan ALLAH bazaki dawo cikin hayyacinki ba. Inata nuna miki hanya, inata miki kanta farga amma kin kasa fahimta saboda son zuciya ya toshe tunaninki. Wai shin dole ne sai kin saka rayukan masoyanki cikin kunci da bakin ciki ne. Wlhy ki fadama bokanyarki ta fita a hanyata, danni nafi karfin ta da izinin UBANGIJI, hakama shi wanda kuke fadan a kansa yanzu duk da dank ne. Ta shiga hankalinta ta tsaya a iya kanki ke da kika gayyaceta a rayuwarki. Why duk randa ta sake gigin zuwa sashenmu sai kunyi nadama da ga ke har ita. Ni babu abinda ya shafeni da abinda zata miki matsalarkice wannan, tunda na nuna miki qujema irin wanna ranar tun kan tazo amma kika nun ban kai ba. Idan kuma ta cika cikakkiya dan ALLAH ta zo gareni a zahiri taga ikon ALLAH, wlhy sai na sauya mata kamannin halitta da tambarin da harta mutu bazai gogu a jikinta ba".


   Tana gama fada ta juya tal tafiyarta fuuuu ta fice tana bugo kofar. Da kallo kawai Malikat Bushirat ta iya binta, zuciyarta na.raya mata anya kuwa (wannan yarinyar mutum ce? Koma dai wanda aka kira uban nata bashi bane Aljanun Ammarah din ne suka mata cikinta).…... Fitowar Jasrah da ga bayi ya katse mata zancen zucin. Sai kuma yanda Jasrahn ke mata kallon tuhuma da rudani ya sata shan jinin jikinta, ita sai yanzu ne ma hankalinta ya dawo jikinta. Duk da abinda yarinyar nan ta fada kenan Jasrahn ta jisu tunda tana a cikin bathroom...


"Akia!".

 

Jasrah ta katse mata tunanin. Dan firgigit tai ta dubeta. Sai dai ta kasa amsa mata. Babu alamar wasa tattare da Jasrahn ta sake fadin, "Akia kamarfa maganar Zawjata-almilk naji, shin wane maganganu take fada miki haka masu rudarwa? Mike faruwa ne?".


Dauke idanunta tai da ga kan Jasrahn zuciyarta na wani irin gudu a kirjinta......


  "Hakan na nufin hasashena nakan gaskiya kenan,Akia akwai abinda kike boye mana tsakaninki da yarinyar nan? Taya kamarki da ke matsayin mahaifiyar mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin mijinta, shugabanta amma tazo tana datsa miki irin wadan nan maganganun cikin kaushin harshe amma ko tari bakiyi ba. Anya kuwa Akia.....


"Jasrah!!"


   Ta fada a zafafe cikin dakatar da ita, muryarta adan kausashe da bata fita. Shiru Jasrahn tayi sai dai ta kasa dauke idanunta da ga kanta. Babu abinda ke mata kai da kawo a zuciya sai kausasan kalaman Iffah masu nuni da akwai wata jikakkiya a kasa tsakaninsu. Sannan kalmar bokanyar nan ya matukar tsaya mata a kahon zuciya ya kasa fadawa...






**.





Koda ta koma ta iske ya dawo sai dai ya wuce Gym.Ajiyar zuciya ta dan sauke ta canja kayan jikinta ta nufi kitchen. Yau ma da kanta ta hada masa abincin breakfast din, suko masu girkin duk sun tsargu duk da tare da su take yi. Sai dai aikinsu kawai bani kaza yankamin kaza wanke mun kaza. Amma komai ita da kanta ta hada abunta. Ta kuma tsaya a kansu har sai da aka kawo komai dining room din.


    Ya fito da ga wanka kenan ta shigo da sallama hanunta dauke da tray mai dauke da kofin shayi da keta faman turiri. Ido ya dan tsira mata har ta iso gabansa ta ajiye. "Good morning ". Ta fada tana zuba zuma kadan a shayin. Cikin dan lumshe ido da budewa ya amsa mata da "How Are you".


"Alhamdullah".


Ta amsa masa itama tana mika masa kofin shayin.Amsa yay dan dama shi yake jira. ya ce, "Thanks". Kai kawai ta dan jinjina masa tana murmushi. Da ga haka ta wuce bathroom dan yin wanka. Kallo ya bita da shi kasa-kasa zuciyarsa na masa kaikawo.




  Lokacin da take fitowa har ya kammala shiryawa,dan haka ya taimaka mata itama ta shirya cike da tattali da kulawa. A tare suka fito cin abincin gwanin sha'awa. Duk abinda take kallonta kawai yake cike da so da kauna harta kammala hada musu komai. Bismillah ta masa tana masa nuni da abincin da ido ya make kafadarsa yana kauda kai gefe. Hannu ta kai ta dan ja masa kunne tana murmushi, sai hakan yay dai- dai da fitowar amintaccensa da basu san da shi ba da ga cikin karamin falonsa ya gyaro. Da wani masifar sauri ya juya har yana cin ban tuntube dan idonsa ras akan hanun Iffah da ta ja kunnen Shahan-shan din nasu. Itama idanu ta waro da sauri ta mike da sauri ta rungumesa. Dan harga ALLAH bata san bayan su akwai wani a wajen ba. Da kyar ya danne dariyar dake taso masa ya danna mata mintsini a gefen ciki shima, tako zabura gaba dayanta ta haye saman cinyarsa……✍️


No comments

Powered by Blogger.