Doctor Mansoor 15
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*DOCTOR MANSOOR*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
_Jiddah S Mapi_
*Chapter 15*
_Na kusa kawo karshen free page kuyi making payment domin samun ci gaba_
~Saida ta gana juye juye da wannan hannun nata wanda yake a yanke kafin ta janyo box ta fara wanke hannun, bayan ta wanke ta ɗaure da bandage, cire kayan tayi ta maidasu inda take ajiyewa, rigan bacci mara nauyi wanda yake bayyana duk wani sura da shatin jikinta shi ta sanya, rigan pink ne ya kara mata haske sosai, dayake ita ɗin chocolate color ce, kallon hips nata tayi wanda yacika rigan kamar zai fasa, murmushi tayi me kayatarwa a ranta tace "badai a gayamin diri ba saide kyaun hali, ko uban Man ne ya ganni a haka saiya girgiza balle Man da yake yaro matashi me ji da sabon jini, zama tayi tana kirkiran abinda zaisa Man ya ganta a haka, itafa bata ki suyi tarayya kafin aure ba, a kullum tada mata tsimi yake kuma saiya kyaleta, koda yaushe ta ganshi sai taji sauyi a jikinta, kallon breast nata tayi wanda ya ɗan taso kaɗan domin ɗazu ba karamin matsa yayi musu ba, lumshe ido tayi tana murmushi tace "ke duniya ina sonki kuma zan barki"
kamar daga sama taji karan faɗuwan cup haɗe da ihu, tasan za'ayi haka shiyasa tayi murmushin shu'umanci, itace tasa ɓera a cup din tea kuma tasan Noor da tsoron ɓera, a hankali ta fara takawa ta buɗe ɗakinta, saida ta iso kasa kafin taje da gudu alaman tsoro tana riko shaira wacce take zare ido, ɓeran kuma ya koma gefe ya gudu, Man ma cikin tsoro ya sauko yana tambayan meya faru? "shaira ce taga ɓera a cup shine ta tsorata"
dafe kai yayi "ya Allah meyasa nake yawan tsorata ne?"
hakuri ta basu ta wuce ɗakinta, da ɗan gudu Jahad ta haye matattakalar tana ɗan girgiza jiki, runtse ido yayi, yana ganin wannan yarinyar watarana saiya mutu, giftawa tayi zata wuce shi, ai da karfi yasa hannu a waist nata ya janyota, bai cire hannunshi ba sai janyota yake, yanajin wani nutsuwa a duk lokacin da yake tare da ita, zame hannunshi ta fara cikin shagwaɓa tace "sakeni mana"
kallon karamin bakinta yayi, bakinshi yakai kunnenta, saida ya ciza kaɗan kafin yace "bazan iya ba, you are too sexy"
cikin wasa ta fara kwace jikinta tana so ta gudu, a hankali tace "idan wani yazo ya ganmu fa?"
"sai nace ina tare da matar da zan aura"
kamar zatayi kuka ta rinƙa janye hannunshi, babu abinda yake sai kara matso da ita, juyata yayi ya rungumeta ta baya, shiru tayi jin yana manna bayanta da jikinshi, sajenshi ya fara shafa mata a gefen wuya zuwa fuskarta, lumshe ido tayi tana ture shi, hannunta ya damke yana kara matso da jikinshi zuwa nata, Jahad tasan irin halittan da Allah yayi mata, ba kowani namiji zai iya daurewa ba idan ya ganta a haka, a kunnenta ya raɗa mata cikin romantic voice "I love you so much Jahad"
"I love you too" ta faɗa tana janye jikinta, da kyar ya saketa ya rike hannayenta, kallonta yayi saida ya shagwaɓe fuska kamar zaiyi kuka shima kafin yace "to kiss me"
kanta a kasa tace "I can't"
"to idan ba zaki iya ba saide mu tsaya haka kuma idan naga mutane sai nayi hugging naki, matso da lip nata tayi a kumatunshi tayi mishi kiss, taɓe baki yayi tareda girgiza kai "banson wannan"
"to wanne kake so?"
"a baki nake so"
janye hannunta tayi kamar zata kamo kanshi sai kuma ta juya da gudu ta bar wurin, tsayawa yayi harda karya wuya yana kallonta, "Allah ka mallaka min wannan baiwar taka"
"Ameen" yaji muryan Ahmar, cikin harara yace "kai kuma daga ina?"
"daga sama"
hanyar tafiya ya kama, Ahmar yace "amma Man kai ɗan iska ne, ji yadda kake mannewa yarinyar nan, naji komai fa"
"to kaji mana ina ruwana"
yayi magana yana shirin barin wurin, domin shine me neman tsokanan Ahmar idan baida lafiya gashi yau shine a ruwa, dariya kawai ahmar yayi, ya tabbata Man yana son jahad, Allah ya nuna musu aurensu kafin Man ya tabka abin kunya.
tana shiga ɗaki ta rufe da karfi, zuciyarta kamar wuta,a duk lokacin da Man ya taɓa ta sai taji feeling Kuma sai taji ya fame mata ciwonta, yana fame inda ya jima yana mata ciwo, tana jin shauƙi idan yanayi mata irin wannan abin amma tafi jin zafi da raɗaɗi fiye da shaukin, da karfi ta buga kanta jikin kofan, a hankali ta sulale, janyo wuka tayi ta kuma yanka yatsan hannunta, a duk lokacin data kasance da Man saita yiwa kanta illa, idan jini bai fito a jikinta ba batajin daɗi, cizan leɓenta na kasa tayi tana runtse ido, da karfi tace "Maaaan.!!!!"
kwanciya tayi a wurin ta fara lumshe ido tana so bacci ya ɗauketa, kamar da wasa ta gagara baccin, saida ta ɓallo wasu kwaya tasha kafin bacci ya sace ta.
yana shiga ɗaki shima pills yasha domin haɗuwa da Jahad a wannan daren ba karamin ɗaga mishi hankali yayi ba, ada bai damu da mace bama yajin wannan feeling ɗin, amma yanzu daya haɗu da jahad kullum sai yasha pills yake iya bacci.
*International police station Gombe*
nan aka kawo Hamida, tunda suka shigo da ita ake mata azaba iri-iri, kuka harda majina saida tayi tana musu bayanin ba ruwanta batayi komai ba amma sunki kyaleta, daga baya kayan jikinta aka sata cirewa suka bata wani riga na ƴan cell tasa, hula aka bata tasa a kanta, tana kuka aka cire duk wani zobe da abin hannu akayi cajinta sosai, rikota akayi suka kaita can ta ɓangaren mata, tana kuka tana cewa "wallahi bani nayi ba" suka kulle wurin, juyawa tayi tana kallon matar datake gefenta, sai ido matar take aika mata, da sauri tayi baya tana salati da addu'a a cikin ranta, jingina da jikin karfen kofan tayi tana kiran sunan ummanta, bata taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba, matarce ta fara matsowa tana taɓa jikinta, a firgice taja da baya, farace matar da kiɓa sosai, kana ganinta kasan batada kunya, binta take ita kuma ta mike da gudu ta faɗa gefen wata wacce take a taƙure, wani irin dariyan mugunta matar tayi tana kallon Hamida tana lasan baki, da karfi ta riko hannun wacce ke gefenta cikin tashin hankali tace "ki taimakeni"
Matar ta riko hannunta tace "kada ki tsorata ƴar lesbian ce haka take, da taga mutum saita kura mishi ido, kada ki nuna jin tsoron ta a fili kinji?"
jijjiga kai tayi saide har yanzu a tsorace take, har dare bata motsa ba sai rawan jiki da ciwon kai, wani bushashen abinci aka kawo musu, karɓa tayi ta rinƙa cusawa tana ci, saida taji zatayi amai kafin ta bari, a gefen matar da take bata shawara ta kwanta domin zazzaɓi takeji sosai, da wani karamin mayafi ta rufa jikinta sauro yayi yawa a ɗakin, ganin bata tsira daga cizon sauron ba ta mike tana kallon kafarta, kuka ta saki tanajin kamar ta kashe kanta ko zata huta, da kyar ta samu ta kwanta bacci ya ɗauke ta, kanta har wani bugawa yake, hakika bazata taɓa yafewa Mr R ba domin shine silar kasancewarta cikin wannan halin, saide har yanzu Allah bai nuna mata shi ba, amma tasan idan kere na yawo zabo na yawo watarana dolene su haɗu.
"abba ya kirasu gaba ɗaya yace su taya Kabir da addu'a domin har yanzu Hamida bata faɗi bakinta ba, bata faɗi wanda yake sata aikata aikin ba, zasu ladabtar da ita har sai ta buɗe baki ta faɗi da suwa take aikin, cikin alhini kowa yayi shiru, Sabir har ya rame dan wannan damuwan, gara Ahmar yana iya daurewa, Shaira kullum tana karkashin Laila tana kuka, hakuri Abba yake basu yana cewa su daure watarana sa labari, Jahad ce a kitchen tana shirya kayan breakfast, rigan atamfa da da skirt tasa ruwan kasa, tayi kyau sosai kuma ta yafa ɗankwalin a kanta, Man ne ya shigo yayi shiri cikin kayan doctor domin Abba yayi magana an buɗe hospital nashi, hannu ya zuba cikin aljihu ya jingina da jikin kofa yana kallonta, a jikinta taji ana kallonta kuma tasan Man ne, a hankali ta juyo ta sakar mishi murmushi, karasowa yayi zai rungumeta ta kauce, shagwaɓe fuska yayi yace "nayi missing naki fa ki barni mana"
dariya kawai tayi, Shaira ce ta shigo tana cewa "yah Man?"
kallonta yayi yace "ya dai?"
gaisheshi tayi ya shafa fuskarta tareda cewa "an tashi lafiya?"
jijjiga kai tayi, tace "Yah Man Hamida taki magana anya babu wata a kasa? na fara zargin ba itace ke aikata abinnan ba"
da mamaki yace "miye shaidan ki?" waya ta ciro zata nuna mishi abu, wani mugun kallo Jahad ta aika mata ta kasan ido, da karfi tasa hannunta kan gas ɗin dake kunne a kitchen din, saida ta kone sosai kafin tayi ihu tana kiran sunan Man, barin Shaira yayi yaje wurinta yana cewa "meya faru Baby?"
hannunta da take yarfawa ya riko yana kallo, ganin yayi jaa a bakinshi yasa ya fara tsotsa lumshe ido tayi tana sakin ajiyan zuciya, ba karamin zafi takeji ba a hannunta, rikota yayi yace "muje na duba miki"
shaira na tsaye da waya tana kallonsu, sannu kawai take cewa, saida suka zo bakin kofa Jahad ta juyo, fuskarta na asalin Jahad ta nuna mata tana me aika mata kallon da zaiyi wuyan fassara, a palour ya zaunar da ita, yaje ya ɗau oitment ya dawo ya shafa mata, Shaira na tsaye jikinta yau duk a mace, sama ta haura taje wurin laila ta rungume ƴar uwarta sosai tana jin tausayinta a ranta, kissing ɗin goshinta tayi yana shafa fuskarta, bata son ganin laila a wannan halin na rashin tafiya ga kuma rashin magana, Ahmar ne ya turo kofar yai tsaye yana kallonsu, ganin tana sharan hawaye yaji shima idanunshi suna cika da kwalla, karasowa yayi ya riketa yana share mata hawayen "zaku fita da driver karɓan sako"
"To" ta faɗa tana jijiga kai, riga mara nauyi tasa kafin ta yafa mayafi, rungumar Laila tayi kafin suka fita tareda Ahmar, Abba ne yace kada su Ahmar da man su fita har sai an gano inda Kabir yake, amma ita Shaira ba kowane ya santa ba, Jahad tana zaune tana kallon Shaira har ta fita daga ɗakin, a hankali ta danna wayan dake gefenta alaman ta tura sako, fita shaira tayi suka ɗau hanyar karɓan maganin Laila, har sun karɓo ta kira Abba ta sanar mishi sun karɓa, yace Allah ya kare, ameen ta amsa, ci gaba sukayi da tafiya, har sun kusa gida motarsu ta tsaya, fita driver yayi yana duba matsalan motar, gyarawa ya fara Shaira na ciki tana zaune, bini-bini tana duba agogon wayarta, ganin rana yayi sosai ta sauke glass tace "driver kodai na samu adaidaita sahu ne?"
cikin zafin rana yace "eh to bari dai na duba na gani"
cigaba yayi da gyarawa, ganin zasu ɓata lokaci yace "fito mu kama miki napep Hajiya"
buɗe mata yayi ta fito tana kallon yadda garin yayi zafi, kamar daga sama taji anyi harbi, gabanta ne ya faɗi ta kalli driver tana zaro ido, hannu ya ɗaga mata alaman ta gudu, gudu suka fara mutanen suna binsu a baya, ta yadda mayafinta da jakan hannunta hadda maganin data karɓo, tayi iya bakin kokarinta da kyar suka kamata, babu ɓata lokaci suka fasa kanta da bindiga, jini ne ya fara zuba a hankali ta sulale ta faɗi a wurin, jikin driver ne ya fara ɓari, Abba ya kirashi a waya domin yaga sun jima ya amsa ta dalilin haka yake jinsu, nunashi sukayi da bindiga "ba kai muke nema ba"
barin wurin sukayi da gudu yaje yana kiran sunanta, ɗagata yayi sama ya kaita mota, sai a lokacin yaji muryan Abba yana cewa "meya sameta?"
"sun kasheta Alhaji"
zama Abba yayi akan kujera yana jin idan bai zauna ba zai iya faɗuwa, da gudu driver ya koma da gawanta gida, a hannunshi ya ɗagata tayi nauyi sosai, cikin palour na kasa ya kwantar da ita, Ammi har tuntuɓe take gurin taka stair, riketa Noor take cikin tashin hankali suka iso wurin, Abba ya gagara tashi yana zaune kawai ya zubawa gawan ido, Ahmar ya karaso da gudu yazo gabanta, sunanta ya fara kira a kiɗime, kallon Abba yayi wanda yake zaune "me mukayi musu? Abba me muka yiwa su Hamida?"
da ido kawai Abba yake binsu, Man dake asibiti yana settling na komai yaji wayarshi na ruri, ɗagawa yayi yana kallon sunan "Baby Jahad" yana yawo, ɗagawa yayi yace "Baby"
cikin kuka tace "an kashe Shaira"
sakin wayar yayi, salati ya farayi yana kiran sunan Allah, ba tareda ya shirya komai ba ya fita daga Office ɗin, bai tsaya ko ina ba sai cikin mota, da mugun gudu yabar asibitin, yana shiga gida yaga gawa kwance su kuma suna zaune kowa yayi tagumi, wannan karon kasa kuka yayi sai kallon Abba da yake, waya ya ciro ya kira wani layi, a handsfree yasa ana ɗagawa yace "ina Hamida?"
ɗayan ɓangaren akace "yau an samu matsala a station abinda ya faru bamu ga wasu daga cikin ƴan cell ba amma har yanzu muna dubawa"
cikin zafin rai yace "kuna barin criminals haka a gari? kunsan yanzu Hamida ta kuma yin wani kisan? na baku awa uku ku nemota, da hannuna zan kashe ta"
kashe wayan yayi yanaji kamar a kawo mishi ita ya daɓa mata wuka a ciki, babu abinda zai wanke mishi wannan ciwon sai ganin gawan wannan yarinyar a kwance kasa, da kyar Sabir yarike Abba yamike, Jawad yana gefe yayi tagumi shikam baisan me yake faruwa ba, gani yake kamar shine next target na makashin, da kyar sukayi jana'iza basu bari labari ya zaga duniya ba, domin basu son mutane su sa ido, saide Abba ya kira masu tsaro sojoji wanda zasu rinƙa kula da duk wani shiga da fice na gidan, hatta driver yanzu saida ya canja ya zama soja ne, duk inda zasu fita sai anyi musu rakiya musamman Jawad da yake zuwa school shida Sabir, gidan ya zama shiru basu sanarwa laila cewar Shaira ta mutu ba, saboda halin da take ciki, Abba yace taje kasar cairo domin kula da wasu abubuwan zata dawo bada jimawa ba, Man ya susuce sai kiran ƴan station yake yana tambayar ina Hamida, Jahad na gefe fuskarta alaman tsoron zuwa wurinshi ya bayyana, ajiye wayan yayi yana kallon Ahmar wanda ya rame sosai ya zama shiru, a halin yanzu baison ganin Ahmar a wannan yanayin, a hankali yaje gefenshi ya zauna, hannu yasa yana ɗago kanshi cikin tausayawa yace "kayi hakuri"
"to ya zanyi Bro?"
rungumeshi yayi ya fashe da wani irin kuka, a hankali yake shafa bayanshi shima yana hawayen "ka daina banson ganinka kana kuka Ahmar, inason ganinmu cikin farin ciki kamar yadda muka saba"
"farin ciki bazai taɓa dawowa cikin family ɗinmu ba, tunda aka lashe Dady da Momy sannan aka sace Kabir, bansan wani hali yake ciki ba, bansan ina yake ba, bansan yana cin abinci ko baya ci ba, bansan halinda Kabir yake ciki ba...gara naga gawanshi na tabbatar ya mutu amma kullum zuciyata tana cikin alhini, me nayiwa Hamida take min wannan hukuncin? me nayi mata?"
shiru Man yayi yanajin ciwo a cikin ranshi, so yake ya maida kukan dake shirin fito mishi ba shiri, kasa daurewa yayi shima ya fashe da kuka kamar karamin yaro, Noor dake gefe ta haɗa kai da gwiwa itama tana kuka sosai, Abba yana tsaye daga nesa yana kallonsu, ya rasa waye ya sasu, juyawa yayi shima yana share hawaye, Ammi tana daki a kwance batada lafiya, mutuwan ya jijjiga ta ba kaɗan ba, Jahad na zaune a gefe tana cikin hijabi hannunta rike da carbi tana kuka, ranta fal farin ciki, da taga kukan nasu yayi yawa tace "kuyi hakuri mana kuna maza ai ya kamata Ku daure, Allah ne ya ɗaura muku yaga zaku iya shiyasa yayi hakan, dan Allah ku daina kuka"
da kyar ta lallaɓasu tasamu sukayi shiru, a ɗakin suka zauna kowa yayi shiru yana tunanin abin duniya.
ɓangaren Hamida kuma tana kwance cikin ciwon ciki suka jiyo harbi, kafin su ankara ma'aikatan sun fara gudu, da sauri wata crazy mata ta buɗe musu kofa, ganin suna gudu itama Hamida ta bisu, a bayan prison ɗin suka ɓuya ciki hadda Hamida, saida abu yayi sauki kafin suka dawo, buɗe musu akayi suka koma ciki, Hamida bata iya mikewa, tayi rama sosai sakamakon rashin cin abinci me kyau, ko maganan kirki bata iya yi.
Jahad ce ta kira a waya tace a shirya akai hari gidan yarin amma kada a kashe kowa, a time ɗin da suka kai hari a time ɗin Shaira ta fita, saida ta tabbatar Shaira ta mutu kafin tace su bar gidan yarin, suna barin gidan aka shigo da gawan Shaira, tayi haka ne domin zargi ya hau kan Hamida, lokacin da akayi kisan bata nan bale a samu wani shaidan kareta.
*kuɗin littafina ₦300 ne biya ta nan 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849, turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*
Leave a Comment