Doctor Mansoor 25

 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

 


*DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 25*



                 ~Taji daɗin hakan a ranta domin Man ya fita a ranta tun lokacin da taji yana zibda ciki, zama me kama da faɗuwa yayi a ƙasa kan gwiwoyinshi, tashin hankali goma-goma yake ciki, gefenshi ta raɓa ta wuce, bata tsaya ko ina ba sai dakin da aka shiga da Kabir, anyi mishi injection kuma ya samu bacci, Ahmar ne zaune dashi a gefe yayi tagumi, fita sukayi suka bashi waje dan basa son takura mishi, ko kallon man Ammi batayi ba domin jin wai yana zibda ciki? Abin ba karamin ɗaga mata hankali yayi ba, bata taɓa zaton Man zaiyi haka ba, Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, kalmar da take maimaitawa cikin kuka kenan, Hamida wacce jikinta yayi sanyi ta taɓa ta "kiyi hakuri zai samu lafiya komai zai daidai ta"


"babu abinda zai daidaita domin komai yana cigaba da lalacewa ne, Man ya cucemu, shine sanadin faruwar hakan, bazan taɓa ya..."

toshe bakinta Hamida tayi da yatsunta cikin zaro ido tace "kada kice haka, zai iya lalacewa fiye da haka, kiyi hakuri ki mishi addu'a"


man yana tsaye a gefe yana jinsu, har jiri yaji yana ɗibanshi, hawaye ya fara bin fuskarshi yana cije leɓe cikin jin zafin abinda ya aikata, Innalillahi, shima kalman da yake ambata kenan, Hamida ce ta faɗo mishi a rai, yarinyar da bataci ba bata sha ba, akayi mata sharri, har ya bita prison ya shaƙeta yana neman kasheta ashe bata da laifi, tunawa yayi da lokacin da abin ya faru Jahad ce tayi saurin kiran police ashe itace tayi hakan, ya tuna ranan aurensu yadda ta nuna ta tsorata da ganin gawan Minal ashe itace ta kashe ta, ya kuma tuna lokacin da ta ture laila daga stair ta rinƙa nuna mishi bada saninta tayi hakan ba, hannunshi ya dunƙule ya buga da jikin bango, yana tuna yadda ya yarda da ita, ya amince ta rinƙa kaiwa Jalal abinci ashe kaɗaicewa take dashi, runtse ido yayi da karfi, wannan shine yaudara mafi muni daya taɓa gani a rayuwarshi, Jahad ta yaudareshi duniya da lahira.


Jawad da yazo wucewa ya tsaya yana kallon yayanshi cikin tausayi, bai taɓa ganinshi cikin tashin hankali irin na yau ba, gaba ɗaya ya firgice, dama shi ba yadda yayi da Jahad ba tun farkon zuwanta gidannan, a hankali ya tako zuwa wurin Man cikin sanyin murya da son kwantar mishi da hankali yace "yah Man ka daina kuka.."

rungume Jawad yayi cikin kuka yace "ta yaya zan iya daina kuka? Hamida ta mutu sanadin Jahad? mun cuci rayuwar yarinya karama, Jawad laifi na ne, ina zan ganta? ina zanga Hamida na roki gafara? Jahad ta cuceni ina sonta sosai Jawad, gashi ta tafi ta barni, ba Hamida ba Jahad"


tureshi yayi cikin jin haushi yace "yaya Jahad kake kara ambata bayan duk abinda tayi maka?"


"Manta Jahad ba abune me sauki ba a wajena Jawad, bazan iya mantawa da ita ba"


cikin jin haushi Jawad ya bar wajen, baison ko jin sunan Jahad ya tsaneta, ya tsani sunanta, shima sunanshi da yayi kama da nata ji yake kamar ya canja, Man kuwa sulalewa yayi a wajen yana kuka me tsuma zuciyan me sauraro.



*3days later*


Ahmar ya fita hanyan Man, baya mishi magana baya kulashi kula da Kabir yake sosai, Alhamdulillah kuma ya fara samun saukid dan ba karamin ciwo sukaji kishi ba, ga cizon sauro daya haifo mishi maleria.


Man yana cikin blanket sai rawan sanyi yake, zazzaɓi yana damunshi sosai, ga damuwa na rashin kula da Ammi take mishi, ga Ahmar ya ɗauke mishi wuta, babu me shiga harkanshi a gidan, wayarshi ce tayi kara a hankali ya ɗaga dan ganin ko Jahad ce ta turo mishi sako, gabanshi ne ya faɗi ganin mutumin daya siyi gidansu ne, ya tura mishi sako cewar su tashi nan da kwana uku suna buƙatar gidan, komawa yayi cikin blanket yaci gaba da rawan sanyinshi, ya rasa abinyi, ya zaiyi? ga kuma Abba a kwance ina zasu kaishi su fita dashi daga wannan gidan? idan Abba ya tashi me zai faɗa mishi? ya siyar da gidan matarshi ta gudu da kuɗin?"


Hamida ce zaune a gefen Abba ta rike hannayenshi duka biyu tana kuka

"nasan kana jina Abba amma ba zaka iya magana ba, Man yayi abinda ba kayi zato ba, ya zama dole na sanar maka ya saida gidannan matarshi Jahad ta gudu da kuɗaɗen"

share hawaye tayi "bazan bari komai ya faru ba insha Allah"

tashi tayi daga wajen har yanzu kayan tsofi ke a jikinta.


Noor tana ɗaki bata da aiki sai kuka, rayuwa ta juya musu baya, babban tashin hankalinta shine rashin lafiyan Abba, ganin Abba a kwance ba karamin tashin hankali take shiga ba, ga kuma tunanin Hamida wacce aka yiwa sharri, tana tuna lokacin da take cewa batada laifi batasan komai ba, ashe gaskiya take faɗa, wannan muguwar Jahad ɗin ta kira police a waya suka tafi da ita, gashi Hamida ta mutu, aina zasu ganta, aina zan ganki Unty Hamida na faɗa miki abinda yake faruwa damu? abinci yana neman ya gagaremu a gidannan, ga Yah man Yana cikin tashin hankali da karyewan zuciya, kuka take sosai babu me lallashinta.




*****************


jifa ake da kayansu zuwa waje, Man yana tsaye daga gefe yana kallonsu, Ammi sai kuka take tana basu hakuri su bari sai time ɗin da Abba yayi lafiya yanzu basu san inda zasu kaishi ba, 

Basu jita ba saima ture ta da akayi daga wajen, suka cigaba da jifan kayan saura suna fashewa, Noor taje wajen Ammi ta ɗaga ta tana share mata jikinta wanda ya ɓaci da datti, tace "ki daina kuka Allah zai kawo mafita"


Jawad yaje wajen Man wanda ya tsaya ya zuba hannu a aljihu yana kallonsu, ya rasa abinyi, ya rame sosai yayi baki, abinci ma ba ci yake ba "Yah Man ba zakayi musu magana  ba?"


"me zance? ka barsu su zubar, Jawad kaina ya toshe banda tacewa ka kyalesu kawai"


Saida aka fitar musu da komai kafin suka shiga suka ɗago Abba daga kan gadon da yake, maza ne biyu katti suka fito dashi waje, zaro ido Ammi tayi ganin yadda suka fito mata da miji suna shirin yadda shi kasa, Man ne yaje da gudu ya rike Abba wanda idanunshi suke a kafe suna kallon sama, cikin masifa ya kwantar da Abba ya shako wuyan mutumin da yake shirin yadda shi, dambe suka fara Ammi ganin sun taru suna dukan man ta fara ihu tana turesu, Jawad Noor suma suna wajen suna raba su, Ahmar yana tsaye a gefe yana kallonsu baice uffan ba, Kabir kuma yaje siyo magani wanda Ahmar ne yace yaje ya siyo.


da kyar Ammi ta raba faɗan cikin kuka tace "baku da hankali ne? ya zaku ɗauki mara lafiya haka kuna shirin kaishi kasa?"


"Hajiya ki fita a wannan maganan"


"bazan fita ba..."

hannu ya ɗaga zai mareta da karfi aka riko hannun cikin zafin nama yaji an wankeshi da maruka masu zafi har guda uku a jere, da mamaki gaba ɗaya mutanen wajen suka juyo suna kallon wanda yayi marin.


tana tsaye cikin riga da wando, rigan pink ne me yankakken hannu, sai wando baƙi wanda ta jashi sama kan rigan ta ɗaure da belt, takalmin kafarta dogo ne me tsinin gaske shima pink me, gashin kanta tayi Parking da ribbon pink tasa wani headband shima pink, farin skin nata ya daɗa murjewa tayi kiɓa kaɗan sai glowing take, jikinta kamar ka wanke hannu ka taɓa, ɗan karamin bakinta me shape ta shafa mishi lipstick Pink, gashin idonta me kama da eyelashes ta shafa bakin mascara wanda ya karawa gashin tsawo da baki, a hankali ta tako zuwa gabanshi ta saki hannunshi cikin wani irin salo, glass baki babba wanda ya kusan rufe mata ido ta ciro daga saman giranta tasa a idonta, nan farin fatarta ya kara fitowa sosai, ta kalleshi sama da kasa "who are you to slapped my mother?"



Cikin mamaki Ammi tace "Hamida!!!?"


"Unty Hamida?"

Noor ta faɗa tana zaro ido haɗe da murmushi tareda mamaki, Jawad cikin murna yace "Unty Hamida?"


Man yana zaune akan kafarshi ya kalleta cikin mamaki, baki buɗe idanu a waje, Ahmar ma ya zaro ido yana murmushi yace "madam tsoro?"


Kabir daya shigo yanzu ya saki ledan maganin yaje da gudu zai rungumeta da sauri tayi baya tana ɗaga hannunta "who are you?"




Jiddah Ce ✍🏻

No comments

Powered by Blogger.