Doctor Mansoor 30

 


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  *DOCTOR MANSOOR*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

    Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 30*



                 ~Man a office tunanin Hamida yake, ya gagara yin komai tun safe yana zaune duk sanda ya rufe ido sai ya ganta tana murmushi, ko ya tuna yadda yaga tana rungumar su Jawad, ya hana kowa shigowa office nashi yau, jikinshi duk a mace, ganin ya gagara yin komai ya mike ya ɗau makulli da wayarshi ya fita, motarshi ya shiga ya fara driving zai koma gidane kawai dan ya samu ya kwanta ko zaiji sauki a zuciyarshi, da haka har ya isa gida ummanta ne da Samha a palour sai Ammi suna hira, gaishesu yayi yana ɗan satan kallon gefe ko zai ganta, ganin bata nan ya mike ya wuce up, Samha tana lura dashi saida ya shiga ɗaki ta mike ta nufi ɗakin Hamida, cikin murza ido tace "untu hamida wallahi cikina yana ciwo period nawa yazo gashi umma tace na wankewa Man toilet nashi kuma banson nayi mata musu"


ɗagowa tayi ta kalli Samha, hannunta rike da littafin take me home tana karantawa, jikinta sanye da riga silk da wandonshi, coffe color ne yayi mata kyau sosai farin fatarta ya kara fitowa, murmushi tayi wanda ya lotsa gefen fuskarta tace "ba damuwa zoki kwanta zanje ba wanke"

yatsine fuska tayi "unty hamida ai zan saki gajiya"


"no kada ki damu zanyi zoki kwanta kinsha magani?"


"eh nasha"

sauka tayi daga kan bed ɗin ta kwantar da Samha, blanket ta rufata dashi kafin ta fita daga ɗakin tana gyara zaman hulan dake kanta, tasan yanzu haka yana hospital shiyasa ta shiga ba wani fargaba, Samha kuwa tana ganin ta fita ta mike ta kira wayan Kabir, cikin kasa da murya tace "done"

murmushi yayi yace "good".



tura kofan tayi tana kallon yadda ɗakin yake a kimtse komai da komai yana ma'ajiyinshi, sai ƙamshi ke fitowa ta ko ina, bata tsaya ko ina ba sai toilet da karfi ta tura kofan ta shige kai tsaye dan tasan baya gida yanzu, ido huɗu sukayi yana zaune a gaban shower ya manna bayanshi da jikin bango ya ɗaga kanshi sama yana jin sanyin ruwan yana ratsa jikinshi.


tunaninta yake so ya daina saide hakan ya gagara, jikinshi babu riga sai wani guntun wando, da sauri ta juya baya cikin ɓacin rai tace "yaushe ka dawo?"


baiyi mata magana ba, itama bata juyo ba ta fara cewa "gaskiya bakada kunya sam, kasan zan shigo meyasa ba zakace da mutum a ciki ba? a rayuwata ban taɓa haɗuwa da mara kunya...."

shiru tayi jin ya wani irin rungumeta ta baya,  jikinta ne ya fara ɓari tayi shiru tana zazzare idanu, hannunshi yasa a cikinta ya riketa gam yana shafa fuskarshi a gefen wuyanta, da karfi ta tureshi, ko gezau baiyi ba saima kara riketa da yayi sosai, cikin masifa tace "baka san inada aure bane? ko kayi hauka ne"


juyo da ita yayi zata gudu ya mannata da jikin bango yana kallon cikin idonta, ɗauke kai tayi "idan baka sakeni ba zanyi maka ihu, ka sakeni"

a hankali ya kai bakinshi kunnenta cikin kasa da murya yace "kiyi ihun mana"


kwace hannunta ta fara tana cewa "inada aure ka sakeni"


"haba? Kinada aure? waye mijin naki? meyasa bakwa video call kuma kullum saide kuyita maimaita magana ɗaya? shin recoding kikayi a wayarki ne?"


"ka sakeni ba recoding nayi ba ai kunnenka yana ji kaiba kurma bane"


"niba kurma bane amma a kanki ni kurma ne kuma makaho ne, Hamida ban yadda kinada aure ba"


sakinta yayi ya durkusa kan gwiwoyinshi yace "dan Allah ki yafemin ki gafarceni abinda nayi miki, wallahi soyayyan Jahad ne ya rufemin ido.."

wani katoton bakin ciki ne ya cika mata zuciya jin ya ambaci Jahad, juyawa tayi zata fita yace "koda na mutu sanadinki ne, ina sonki badan komai ba sai dan kyaun halinki, cikin jikin Jahad nine na cire nasa a jikinki, a lokacin bansan Jahad bace domin fuska a rufe tazo, dan Allah ki yafemin na tuna na daina, koda aikin asibiti kikace na daina wallahi zan daina, i love You Hamida, i love you so much"



batayi magana ba ta buɗe kofan ta fita, bata tsaya ko ina ba sai ɗakinta, ta rasa abinda zata fara tunawa, Man ko Ashman, Samha ta zuba mata idanu tana kallon yadda ta ɗaura hannu a goshi tana murzawa alaman tana tunani sosai.



Ahmar sun shaƙu da Samha soyayya me karfi yake nuna mata, tun farkon ganinshi da ita yaji ya kamu da sonta, itama Samha ta sakar mishi fuska suna soyayyansu ba tareda kowa ya sani ba.


Kamar kullum yauma tare suke breakfast kowa yayi shiru yana cin abinci, Hamida wacce tasha dogon rigan atamfa purple da ɗauri me kyau ta kalli Ammi "gobe zan tafi insha Allah"

Man kallonta yayi ta kasan ido zata tafi kuma?


"kinma yi kokari Hamida tunda kika yadda kika zauna damu, amma ki kara koda sati ɗaya mana"


"Ammi kuyi hakuri kirana ake wallahi banjin daɗin rashin zuwa"


Ahmar wanda yake zaune kusa da Samha ya matso da bakinshi kunnenta yace "ya dai? yayarki zata tafi ta barmin kani, ba zaki hanata ba?"


girgiza kai tayi "bazan hana ba tayi tafiyanta"


hannunta ya riko ta kasan table ta yadda babu wanda zai gani ya fara murzawa yana kallonta, cije baki tayi tana kwatan hannunta tana kallonsu umma alaman batason su gane, caraf a idon Kabir, ya zaro ido yana kallon yadda Ahmar yake rike da hannun samha, tari yayi kaɗan ya ɗibo ruwa a cup yasha, kallon Jawad yayi kafin yayi mishi alama da ya kalli kasa, shima kallonsu yayi ya kauda kai.


Abba yana jin komai kuma yana ganin komai baice komai ba.



*Washe gari*


Umman Hamida ta kirata tace ta gaya mata gaskiya shin tanada aure? jijjiga kai tayi alaman eh tana da aure, umma tace zasuje gidan nata tare saboda taga inda take, ta yadda da hakan, ganin haka yasa umma ta yadda cewar ba karya Hamida take yi ba, shirya kayanta tayi cikin akwati dasu jaka, wanka ta shiga ta fito ta gyara kanta tayi parking, riga da wando suit na mata shi tasa black, ta ɗau after dressing me adon duwatsu a jiki tasa, rolling kanta tayi kafin ta ɗau wani babban glass baki tasa, dogon takalmi da jaka tasa suma bakake, ta fesa turaren ta me ƙamshi kafin ta  kalli umma wacce ta zuba mata ido tace "ummana saina kara zuwa dubaki naji daɗin auren Abba da kikayi koba komai kin samu rayuwar ƴanci, saɓanin wannan mugun babansu Samha wanda ya cutar dani ya kuma cutar dake"


"ki cire komai a ranki Hamida ki yafe mishi ya mutu ba amfanin tuna da"


"na daɗe da yafe mishi umma"

zuwa tayi ta rungumeta tace "bye Umma na"


rakata Umma tayi zuwa kasa, Hamida hannunta rike da akwati tana jaa gefe kuma jakanta ne a rataye, Samha ce tazo itama ta rungumeta tace "mu tafi tare mana unty hamida"


lakace hancinta tayi tace "no zaki zo daga baya saimu zauna acan ba?"


Jijjiga kai tayi, su Jawad dasu noor da laila sukazo suka rungumeta, Kabir ma yazo jikinshi a mace ya rungume ta, saida suka gama sallama taje gaban Abba ta durkusa tace "zan wuce Abba"


shafa kanta yayi "Allah miki albarka"

"Ameen Abba"


kallon Ahmar tayi wanda yake rike da makullin mota shine zai kaita airport, tayi murmushi muje "ya ahmar"

kallon Samha yayi "jeki ɗauko mayafi ki rakani"

da gudu taje ta ɗau mayafinta tazo suka nufi hanyan fita.


"Hamida!!!!!"


Ammi ta faɗa da karfi, a ruɗe ta juyo tana kallon inda taji sautin kiran ya fito, ganin Ammi ta rike Man da karfi yana shirin dirowa daga upstair yasa ta ajiye jakan ta nufi wurin da gudu, rikeshi sukayi a tare yana shirin watsar dasu Ahmar yazo suka rikeshi, Abba ma yazo "kai meya sameka?'


"Abba ku barni na kashe kaina tunda babu me sona, ku kyaleni"


ganin yana shirin kwatan kanshi ya diro yasa suka jashi da kyar suka maidashi gefe, cikin kuka yace "koda kun tafi saina kashe kaina"

rungumeshi Abba yayi "meke damunka?"


"Abba Hamida zata tafi ta barni"


"ko bazata tafi ba muje ciki"


"Abba zata tafi.."


janyeshi sukayi su duka suka kaishi ɗaki, hannun Hamida ya riko yace "zaki tafi ki barni? zuciyata zata karye dan Allah ki zauna tare dani"


Ammi tace "tanada aure ba zaiyi ta zauna anan ba dole mijinta yana bukatanta"


kwace kanshi yayi yana shirin fita daga ɗakin, da kyar suka rikoshi suka maidashi kan gado, Ahmar ne ya ɗauko allura yayi mishi, a take ya fara gyangyaɗi yana kallon Hamida cikin muryan bacci yace "ba zaki tafi ba ko?"


girgiza kai tayi ta ɗaga after dressing ɗin ta zauna a gefenshi kan bed ta riƙo  hannunshi, cikin sanyin murya tace "bazan tafi ba zan zauna tare da kai"

har bacci ya fara ɗaukanshi yace "kinada aure?"


"banida aure Man"

tayi maganan cikin kuka sosai, tana shafa hannunshi har bacci ya ɗaukeshi yana murmushi jin amsan data bashi.


gaba ɗaya wurin jikinsu yayi sanyi, saida yayi nisa a bacci Abba ya riko hannun Hamida wacce take aikin kuka ya fita da ita zuwa waje, su umma dasu Ammi suka biyosu a baya, zaunar da ita yayi akan kujera ya ɗibo ruwa a cup ya bata, girgiza kai tayi alaman a,a bazata sha ba, ɗago cup ɗin yayi yasa mata a baki, karɓa tayi ta fara sha, saida ta shanye tass ya zauna yana kallonta yace "ki ɗaukeni a matsayin Mahaifinki ba mahaifin Man ba, ki gayamin gaskiya meke faruwa? da gaske baki da aure?"


kuka sosai ta fara, saida tayi me isanta kafin ta kalli Abba cikin kuka tace "banida aure Abba"


hamdala gaba ɗaya sukayi, sunji daɗin jin wannan kalman.


"to waye Ashman?"

cikin kuka tace "tsohon mijina ne"

tana cigaba da kuka tace.



"Ashman ya kasance captain ne, Mahaifinshi me kuɗi ne sosai shima Ashman yanada kuɗi har yaso yafi Dadynshi kuɗi, Unty maryam itace wacce muka haɗu a prison har ta kaini gidansu suka karɓeni hannu bibbiyu, kanwarsu Manal da kannenshi maza Faiz da Zayn, sun nunamin kauna sosai, Ashman ya fara sona tun ranan daya haɗa ido dani, baya dariya baya sakewa da kannenshi yana haɗuwa dani na canja mishi rayuwa, ya zama bashida abokai sai kannenshi, bayan anyi auren unty maryam shi yake kaini gidanta, tare dashi muke yawo, mun shaƙu sosai mun saba da juna, soyayya me karfi ya shiga tsakaninmu, Dady ya yanke shawaran ɗaura mana aure, akasa ranan biki munata murna, ashman yana nuna kamar yayi mishi nisa haka har Allah ya kawomu ranan bikin, aka daura mana aure cikin gata, kamar su suka haifeni haka sukamin komai, Unty maryam ta gyarani tayimin duk abinda akewa budurwa idan zatayi aure, ranan da aka ɗaura aure bayan na tare a ɗakin Ya Man, ya zauna kusa dani yana cewa jikinshi ba dadi, nace ko gajiya ne, yace a,a haka kawai yana jin gabanshi yana faɗuwa, nace ya rinƙa addu'a, haka dai muka kwana idonshi biyu yanata kallona yana murmushi, kuyi hakuri dole nayi muku bayani dalla dalla, babu abinda ya shiga tsakanina dashi sai kiss, bakina kawai yasha, daganan ya rinka shafa gashin kaina har yayi bacci, da asuba bayan mun idar da salla aka kirashi a waya ana bukatanshi a wajen aiki, badan yaso ba, yana kwaɓe fuska tareda shagwaɓa baison tafiya da kyar na lallaɓashi har ya yadda ya tafi, bayan ya tafi da awa biyu muna waya dashi yace bari yana zuwa minti biyu, minti biyu da ban kara jin muryanshi ba har yau, sai kiranmu akayi a waya wai sunyi accident a jirgi ko ganin gawansu ba'ayi ba ya kone ya zama toka"


na kusa haukacewa lokacin da naji labari, nan fa na fara jinya da kyar aka gano kaina, bayan komai ya lafa Dady ya kirani yace za'a raba gado amma sai an jira ko inada ciki ko babu, ni kuma nace musu babu abinda ya shiga tsakanina dashi, jin dadin gaskiya dana faɗa ban cucesu ba yasa Dady ya raba dukiyanshi kashi biyu ya bani kaso ɗaya a ciki, naki karɓa saida ya tilasta min kafin na karɓa, bayan komai ya dawo daidai inajin mutuwarshi a raina naji bazan iya zama a gidan ba, gizo yakemin na kasa mantawa dashi, nacewa Dady zanje garinmu na nemo mamana, yace ba komai idan na nemota na dawo gidanshi domin na zama ƴarshi, kiran waya da nakeyi nace Ashman ne bashi bane, Unty Maryam nake kira sai tasa a magic voice, Ashman ya mutu baya raye, yanzu haka zan tafine domin na koma gaban dady da zama, bayan nazo garinnan naga babu umma na babu Samha, mutane sunce Baba ya mutu, zan tafi kenan na tuna da abinda Man yayi min, hakan yasa na samu wata mata na dawo gidannan da zama a matsayin kaka wacce take kula da Abba, nayi hakan ne domin na samu daman ɗaukan fansar abinda akayimin, sai kuma naga Jahad tana abinda ba daidai ba, hakan yasa na ɗau mataki, na siye gidan na maidawa Abba kuɗinshi, cikin jikin yayata Amrah kuma Man ne ya zubar, tareda na Ra'eefa, saide yace ya tuba, na buɗe asibitin karɓan haihuwa da kula da masu ciki kyauta a garin abuja, asibiti me suna Amrah and Ra'eefa hospital, nayi hakan ne domin ladan ya rinka zuwa musu har makwancinsu"


Abba da sauran mutanen wurin duk saida sukayi hawayen tausayi, cikin dauriya Abba yace "zaki iya auren Man?"


girgiza kai tayi "Abba bazan iya ba gaskiya kayi hakuri bazan iya zama da man ba"


riko hannunta yayi yace "kiyi hakuri nasan ranki a ɓace ne yanzu amma babu mijin da zai soki fiye da yadda Ashman ya soki kamar Mansoor, Mansoor shine wanda na zaɓa miki matsayin mijin aure, yau alhamis gobe Jumma'a zan ɗaura muku aure"

kallon Ahmar yayi yace "harda kai da Samha gobe Jumma'a ɗaurin aurenku"


rungume Samha Ahmar yayi yana murna, da sauri ta tureshi, ya manta da akwai mutane a wajen, shiru Hamida tayi tana kallon akwatin da yake bakin kofa, jikinta yayi sanyi da jin hukuncin Abba gashi bata da daman yin musu.




_Jiddah S Mapi_

No comments

Powered by Blogger.