Fulani 2


Free Page -2*


Police din da suke gadin Masarautar ne suka bude masu gate, suna dagowa Shattima hannun duk kuwa da kasancewar ba su da

tabbacin yana ganinsu domin bakin gilashin motar ba zai basu damar ganin ya karbi gausuwarta su ba ko akasin haka


“Fada za mu biya ranka ya dade?”


“A a sai na fara duba Labib”


Kai tsaye Baba Adamu ya nitsa da motar cikin harabar Masarautar kamin ya dauki wani bangare da zai sadashi da bangaren Momy. 

Kamin su karasa wayar Shattima ta sake ringing cirota yai daga aljihunsa yana dubawa Hajiya Karama ce rubuce a gaban wayar, sai da tai ringing kamar ba zai daga ba sai kuma yai picking.


“Shattima, Labib ba lafiya”


“I know na shigo cikin Masarautar ai”


Mikewa tai tsaye daga saman kujerar da take zaune ta fito daga dakinta ta zagayo ta fito backyard ta tsaya tana hango motarsa.


“Okay”


Ta sauke wayar da already ya kashe kiran tun da ya bata amsa.

A gaban wata katuwar kofa wacce ta sha ado kamar ba za a mutu ba Baba Adamu ya faka motar sannan ya fito da sauri ya budewa Shattima. Cikin wata irin isa da kasaita Shattima ya sako da kafafuwansa waje ya fito daga cikin motar yana wata irin tafiya ta takama kamar wanda baya son taka kasa, a zahirin takamarce da isa da kuma kasaita a tare da shi kamar yadda idon kowa na cikin Masarautar ke gani, sai dai a badini sam babu hakan a tare da shi ko da rana daya be tana jin ya fi wani ba dan yana dan sarauta, be taba jin wani ba sa'ansa ba ne dan yana da dukiya da ilmi, ba zaka taba fahimtar hakan ba har sai idan ka zauna da shi ka fahimce shi sosai da sosai. 

  Fadawan da ke gadin kofar ne suka bude masa da sauri suna risinawa tare da zuba gaisuwa, dayan kuma nata aikin isar da kirari, ko kallonsu be yi ba balle ya amsa musu gaba daya hankalinsa yana gun dansa kiran da Zainab tai masa bayan na Nana yasa hankalinsa ya kara tashi. 

Cikin tafiyarsa ta kasaita ya natsa kafarsa cikin wani babban guri. 

Wani irin katon falo ne mai dauke da Turkish furnitures tun daga kan kujeru har carpet da center table, da kuma side table dake kowace kusurwa ta kujerun, ga katon Hoton mai Matarba, sai kuma hoton Ammy sai na Hajiya daga gefe na mai Martaba a tsakiya sai hotunna wasu muhimman mutane na Masarautar dake tsaye a falo, idan ka cire farin fentin da ya kawata falon komai na cikinsa ja ne gwanin sha'awa, falon ya sha ado sai dai ba ado irin na komai a zuba ba, a a adon yan zamani wanda za a kawata falon da abu kadan amman masu kyau da tsada ta yadda duk wanda ya shiga ciki sai ya manta a wace duniyar yake, idan kana a cikin falon za kayi zaton akwai hadari a waje ne ko kuma yamma ta yi ko ma kai zaton farkon budewar safiya ne sakamaon hasken da aka kawata falon da shi kadan ne, mai daukar hankali, sanyin ac ta ko'ina, ga wasu manyan kyandira irin na zamani masu aiki da wutar lantarki suna bada haske a falon gwanin burgewa, ta dayan bangaren kuma wani irin kamshi ne ke tashi a cikin falon kashin da ba zaka iya tantance wane irin kalar turarene ba.


Wata babbar kofa ya nufa mai kyau da kyalle kamar an am mata ado da zinari, ya kai farin hannunsa ya tura kofar ya shiga, sai ya tsinci kansa a wani matsakaicin corridor mai kama da karamin falo an cika ko'ina da na gurin da manyan fulawoyin na kasko da jan carpet.

Mikewa yai straight zuwa katon stairs din da ke gabansa, gabansa kawai yake kallo har ya haye sama, kofar farko ya fara turawa tun kan ta karasa budewa ya jiyo kukan dansa, hakan yasa shi hanzarin cira kafa ya shiga cikin falon mai kama da da wata karamar fadar turawa, a wannan falon kam komai na cikinsa blue ne idan ka cire farin fentin mai kawata ko'ina na gidan, ta bangare daya kuma wani gini ne akai a cikin gurin mai kamar swimming pool sai dai wannan anyi shi da dan yi tsayi, an masa kwalliya da kwaryar da kuma rudayi sai dawusu a samansu yana furzo ruwa gwanin sha'awa, a iya cikin gilashin ruwan ke tsawa ko kadan basa digowa kasa balle har su sauka. 

  Falo ne mai dauke da set din kujeru uku kujerun farko kanana ne an jerasu kamar kujerun dinning wato a zagaye, sai dan karamin tebur a tsakiya da kuma wani karamin carpet blue, na biyun su kuma manyan turkish ne masu daukar hankali, sai  wasu daga can karshen falon su ma blue kamar dai sauran an zagaye gefen da su, su ma kuma suna da karamin carpet da center table. 

A gaban falon kuma wani katon kirsten tv stand ne fari mai gloss fronts da haske blue, left and right na tv stand din matsakaicin show glass ne mai haske a ciki blue color an masa kwaliya da turaruka na alfarma masu kyau da tsada gwanin burgewa. 

Ga wani katon plasma da aka kawata tv stand da shi kamar matanen ciki za su fito waje. 

A dayan gefen kuma wani karamin madubi ne na aka manna mai dauke da gurin wanke hannu, yamma da falon kuma matattarar cin abinci ce mai zamam kanta wacce aka ware mata kofarta dabam kusa da wani katon freezer mai kofa biyu, a dinning area din ma akwai madaidaicin plasma wanda zai bawa duk wanda yake zaune a dinning din damar kallo.

Kofar da Umar ya shigo ce kawai gini a cikin falon sauran duka glass ne gwanin burgewa. 

  A dayan bangaren kusa da dinning akwai wata karamar kofar glass, shiga cikinta na sadarda mutum da wani kebantaccen guri mai dauke da set din karamin dinning har biyar an rarrabasu an jera ko wane set dabam da wani. 


Ta backyard din mutum zai iya hango wanda ke tafe da kuma abunda ke gudana a harabar Masarautar sai dai ba zai bawa mutum damar hango bangaren mai Martaba ba, dama da shi kuma wanda ke tsaye a gurin zai iya hangon garden din dake bangaren Momy, shi ma kuma ganin mai shiga ko mai fitowa ne kawai mutum ke da damar yi ba wai komai da komai na cikin ba kasancewar garden din na da manyan itatuwa da katon Swimming pool a gafe na dutse.....


Nana na ganinsa ta mike tsaye rike da Labib da tana jijjigashi ta nufi gurinsa. Cike da kulawa da tausayi da kuma kaunar dansa ya sa hannu biyu ya karbe sa. 


“What happened?”


“Ba wanda zai fada maka ga abunda ya faru fa, ina dakin kawai yai kyalowa”


“No karya kike na fada muku a daina barinsu su kadai”


Bata sake unkurin cewa komai ba ta koma ta zauna tana kallonsa. 

A kafadarsa ya dorashi yana jijjigashi tare da karanta masa ayatul kursiyu ya tofa masa sannan ya nufi hanyar dake kusa da dinning da kansa ya bude kofar ya shiga, yana shafa bayan Labib a hankali yana kallon abunda ke gudana a kasa.


Ta kofar farko Hajiya Karama ya fito ta nufo inda yake tsaye. 


“Har ka iso, ya jikin na shi?”


“Da sauki”


Ya amsa mata domin ya daina kukan da yake. 


“Me ke damunshi”


“Ban sani ba”


“Kawo shi”


Ta karbe shi tana jijjigashi cike da kulawa domin ita ma kanta tana kaunar yaran. 


“Nana tace kyallowa yai, na fada musu a daina bar min yara su kadai, if not zan dauke su daga gidan nan”


Ya fada yana juyawa ya kalli wata harabar dabam kana ya aje numfashin da sautin da ke nuna ba da wasa yake ba, biyoshi tai tana girgiza kai. 


“Nono Ammy ba zata jidadi ba, am samu mai kula da dakinsu fa, na ce a barta ta kula da su Iya tace bata yarda da ita ba”


“Wacece?”


Ya juyo yana tambaya. 


“Wata ce ba zata wuce 16-17 years ba”


“Miyasa ba ta yarda da ita ba?”


“I don't know ko maybe saboda ta yi kankanta ne”


Kare mata kallo yai ya dauke kai


“Ji dress dinki, na sha fada miki ki daina irin shigar nan”


Ya karasa yana takawa a hankali zuwa gurin karfen dake gabansa. Sai ta kalli jikinta. 


“What's wrong with my dress?”


Be amsa ta ba ya juya ya fice daga gurin ya barta rike da Labib din a kafadarta.

Murmushi tai tana kara kallon kanta, dogon wando ne da wata riga mai guntun hannu wacce ta tsaya iya kwankwasonta, ba laifi kayan sun matse ta sai dai ba irin matsuwa can can sosai ba, a gurinta hakan normal ne ko ba komai tana jindadin yadda hankalin maza yake tashi idan sun yi arba da irin halittar da Allah yai mata, hakan na mata dadi sosai wai sai dai a gani a hade yawu babu yadda za'ayi da ita. 

Bin bayansa tai ta kofar da ya shiga tana cigaba da murmushi, a kujerar da ke kusa da kofar ta zauna ta sa dayan hannunta tana gyara yar karamar jar hular da ke kanta. 


“Yayi shiru?”


Nana ta tambaya tana nufo inda Zainab din take zaune.


“Yeah i think yayi bachi”


Ta taba jikinsa sai ta ji shi da dan zafi za tai magana Zainab ta mike tsaye tana kallon Doc Deen wanda ya shigo rike da dan karamin akwatin magani, fuskarsa sanye da farin gilashi.


“Sannu da zuwa Doctor”


“Hajiya Karama”


Ya amsa mata yana murmushi tare da kallon Shattima wanda ke tsaye jikin window ya rumgume hannayensa ta baya yana kallon harabar gidan. 

Har Doc ya zauna Zainab ta mika masa Labib ya fara duba shi Shattima be juyo ba. 


“Miya same shi?”


“Ba komai haka kawai yai ihu”


Nana ta amsa shi tana zaunawa kusa da Doc kamar ita ce zata duba yaron, Doc Deen yayi murmushi yana kallonta. 


“Ko na baki ki duba shi?”


Dariya tai mai sauti ta make kafada tana girgiza masa kai. Zainab ta yi murmushi ta nufi gurin da Shattima yake tsaye ta tsaya ta jera tare da shi tana kallon dokin da yake kallo wanda ake yi wa ado irin na sarakuna. 


“Yaushe ka dawo?”


“Jiya....”


Ya amsa mata a takaice duk kuwa da kasancewar yana a cikin yanayin da baya son magana, amman ba zai iya kin amsa ta ba, babu abunda Zainab zata bukata ya kasa mata, bayan girman da tai a kusa da shi ta bude ido, kusan ta fi shakuwa da shi fiye da kowa, tana jin maganarsa kamar yadda shi ma yake saurarenta yana girmamata a ciki har da sunan mahaifiyarsa da ta ci, wanda hakan yasa ake mata lakabi da Hajiya Karama, gashi tana da sirri idan ya fada mata A babu mai ji sai idan shi ya umarce ta data fada, babu abunda za tai ba da saninsa ba, babu abunda take boye masa ita da shi abokai ne kuma shakikai. 


“Wannan shi ne karo na biyu da ka sauka wani guri ba Masarautar nan ba, and i don't think hakan zai mana dadi”


A hankali ya busar da iskar bakinsa ya zuba hannyensa aljihu yana cigaba da kallon dokin ta cikin gilashin falon ya ce. 


“Abubuwan gidan nan basa min dadi”


“Yeah amman some time muna bukatar shawararka, ko bukatar wani abu kusan kai ne Sarki a gidanan tun da Mai Martaba bashi da Lafiya, be kamata ace kana nisa da gida ba, and the way you act Ammy ba zata jidadi ba”


Murmushin gafen baki yai ya kalleta. 


“Zan gyara Hajiya Karama”


“Good”


Ta fada with smile on her face, sannan ita ma ta saka hannunta aljihu tana wasa da dayar kafarta, shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleshi 


“This time around ina son nai wani abun da zai bawa kowa mamaki as a photographer i want to do something differently like..... ”


Sai kuma ta kasa karasawa ta ware hannayenta kamar mai tunanin abunda zata fada. Kallonta yai kadan ya dauke kai. 


“Well i think ki shiga kauye, ki duba wata culture ko yare ki duba wasu addinai na wasu da suke wanda ya sha banban da wanda ake gani sai ki dauka”


Ta wara idonta tana murmushin jindadi. 


“Wow shiyasa bana son kai nisa da ni, a duk lokacin da na nemi shawara sai ka sama min mafita”


Murmushi yai mata kamin ya juyo da sauri jin muryar Muhseen. 


“Wow wow wow..... Longest time Dude”


Tsakanin shi da Muhseen aka rasa wanda ya fi wani sauri, a tsakiyar falon suka hadu suka rumgume junansu ko wanensu fuskarsa dauke da dariya da farincikin arba da dan'uwansa. 

Nana ta taso da sauri ta rumgume Muhseen. 


“Ya Muhseen oyoyo”


“Hey Little One”


Zainab ma side hug tai masa tana welcoming dinsa, sai da ya kai wa Doc Yazeed hannu suka gaisa sannan ya zauna kusa da Zainab. 


“Hajiya Karama how far?”


“Fine ya Abuja?”


“Kalau”


“Ina Aliyu and Mama Fulani?”


“Yana nan kalau Mama kuma tana kasa tare da Mai Martaba”


Shattima ya karbi Labib dake bachi a hannun Doc Deen yana fadin. 


“Doc me ke sa su yawan zaburar nan ne wai?”


“To Wallahi ba zan iya fada ba, adai rika yi ana hada musu da addu'a especially idan za su kwanta bachi ko idan sun farka, and a daina barinsu a duhu ko barinsu su kadai”


Yana fadar hakan ya mike tsaye ya rufe akwatinsa yana musu sallama, sai Nana ta mike tsaye ta bi bayansa suka fita falon tare, yana saukowa stairs din ta ce.


“Doc yaushe zaka kai ni gurin wannan sister taka wace kace tana kama da ni”


Kallonta kawai yai ya dauke kai yana murmushi be ce mata komai ba har ya sauka ita kuma bata fasa tambayarsa tana masa magiya ba har ya isa gurin motarsa. 


“You know what? Sometimes dabi'unku daya da Ya Shattima, sai ku rika yi ma mutum wulakanci idan kun ga yana son abu” 


Sai da ya bude motarsa ya saka akwatin sannan ya juyo ya kalleta daga sama har kasa, green lace ne jikinta kanta ba dankwali ta kulle gashin kanta, babu yan yankunne a kunnenta babu makeup a fuskarta amman hakan be hana kyauta fita ba, kallo daya zaka mata ka san cewar jini daya ce ita da Shattima domin kamarsu ta bace kamar an tsaga kara. 


“Ba a nan take ba”


Ya amsa mata with smile.


“A ina take?”


“Abuja”


“Abuja ai gurin zuwan mu ne zan iya binka na kaini na ganta, tun ranar da ka fada min nake son na ganta har yau”


Ya zaro ido


“Ki bini? So kike ace na sace ki?”


“A a zamu je da sanin Ammy da kuma Hajiya kuma zan fada musu ba za su hana ba”


“Ba za su bari ba”


“To mu tsere idan mun dawo sai mu fada musu”


Wannan karon dariya yai sosai. 


“Nana ba ki da wayo”


“Ina da wayo mana, amman ai ina da hankali”


Ta fada ita ma tana dariya kamar shi. 


“Fine, zan san abun yi ko dai na dauko miki ita na kawo ko kuma na baki address dinta idan kin shiga Abuja ki je ki ganta”


“Okay”


Ta fada tana daka tsalle, kamar ance ta daga kai ta gani, sai ta hango Sirleem a sama daga can bangarensu yana kallonsu. 


“Idan kai tunani ka kira Ya Shattima ka fada masa sai ya fada min ka ji?”


Tun kamin ya amsa mata tai saurin barin wajen ta koma sashensu. 

Kai Doc Deen ya daga ya kalli Sirleem wanda ke watsa masa wani irin kallo na rashin kima, murmushi Deen yai ya bude motarsa ya shiga.


Daga backyard din da yake tsaye zuciyarsa take wani irin tafarfasa ganin Nana da Yazeed da yai, ba tun yau ya lura a duk lokacin da Deen ya shigo  Masarautar sai ya tsaya yayi magana da Nana yake tafiya.

A fusace ya nufi bangaren Ammy zuciyarsa kamar zata fito tsabar kishi, cikin fusata ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Shattima da Muhseen Zainab da Nana zaune a falon, dukan su kallonsa sukai ban da Shattima da yai kamar be san da shi a duniya ba, be damu ba ya soma gabatar da abunda ya kawo shi. 


“Ke me kike yi waje da Deen?”


“Ina ruwanka?”


Ta amsa masa ita ma tana turo baki gaba kamar za tai kuka sannan ta mike tsaye rike wayarta ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta. 

Zainab ta daga kai tana masa wani shegen kallo.


“Look at you Sirleem sai ka rika yin abu kamar wani fool ya zaka shigo a gaban mutane kana tambayarta miye take a waje? Kamar wani ubanta”


Runtse ido yai ya bude cikin bacin rai ya ce


“Hajiya Karama babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan ina magana da Nana ki daina saka min baki”


“Oh really? To ko dukana zaka yi?”


Ta fada tana mikewa tsaye, daman can ita da shi ba sa shan inuwa daya. 

Sai a lokacin ne Shattima ya daga ido ya kalleshi ya kalli Zainab. 


“Please Hajiya Karama tafi dakinki”


“Amman....”


Bata karasa ba maganar ta makale sakamakon kallon umarni da Shattima yai mata sai ta duka ta dauki wayarta ta fice daga falon. Shattima ya kalli Muhseen yana murmushi kamar ba shi ba yace. 


“Muje sashena ka huta na san yanzu za a fara jera maka abinci dan gidan Mai Martaba”


A tare suka fice da Muhseen din aka bar Salim tsaye a falon kamar wani wawa. 


FADIME POV. 


Busar sarewar nan da take yawan ji a mafarki ta soma jiyowa tana tashi a hankali. 

Kwantar da kanta tai jikin kafafuwanta tana sauraren yadda busar ke ratsa kunnuwanta tana saukar da nishadi a zuciyarta busa ce mai ban tausayi mai saka shauki da dadin saurare, a iya lissafinta tana tuna mafarkinta ne shiyasa take jiyo busar, hakan yasa ta rufe idonta tana ta ganin mutumen nan mai busar sarewa na mafarkinta, a kullum idan tai mafarkinsa baya yake bata bata taba ganin fuskarsa ba, yana daure da walki jikinsa babu riga. 

Jin kamar a zahiri ake busar yasa ta bude idonta ta mike tsaye ta saki sandar korar shannun da ke hannunta, sai ta ji karar busar sarewar yana karuwa kamar ana kusantota, waige waige ta fara yi sai kuma ta juya da sauri ta nufi gurin itatuwan masara ta kusa kai ciki domin a ciki take jin kamar busar na fitowa, tana tafiya tana juyawo tana ratsa shukar masara ta ko'ina, can kuma ta juyo sautin kamar a inda ta baro ta juyo a guje ta dawo gaba daya hankalinta ya tashi domin bata taba jin busar a zahiri ba sai a yau, saman katon dutsen dake gaban shanunta ta haye tana hawaye tana waige waige ko zata hango mai busar ko kuma tabbatar da inda sautin busar ke fitowa amman sai ta ji abun ya karade ilahirin dajin gaba daya, faduwa tai a gurin ta dafe kanta tana kuka domin a yanzu ta fara tunanin ba azahiri take jin busar ba a cikin kwakwalwarta ne. 


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Ta furta tana kara runtse ido tana girgiza kai domin har lokacin bata daina jin busar sarewar ba, ta dade a gurin tsugune, sai da ta daina jin busar sannan ta mike tsaye tana kallon shanunta da ke kasa, a take saniya daya ta yanke jiki ta fadi a gurin tana shure shuren mutuwa, Fadime na ganin haka ta sauko da mugun gudu ta nufi hanyar gida tana wani irin kuka na tashin hankali, @250 ta isa gida kamar wata mahaukaciya ta fada cikin gidan tana kururuwa. 


“Inna Inna yau ma nagge guda ta fwadi, gata can tana shure shure Inna mutuwa za tai”


Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata. 


“Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa”


Ta amsa masa ta yaren da suka fi gwarewa, a take Fadime ta tashi da gudu ya fice daga gidan zuwa gonar mahaifinta, Inna Amo ce ta fito daga bandakin lullube da bakin gane ta nufo tsakar gidan tana.


“Inna Fadime lafiya kike?”


“Nagge ce ta sake faduwa da sannu naggen Malam sai karewa suke Amo”


“Allah ya kyauta”


Shine abunda ta fada ta nufi bukkatarta tana koda tsatsagar hakora. 

  Ko da Fadime ta isa ta fadawa Mahaifinta ya tafi tare da mutunensa da suke aiki tare sun isa a kuraren lokaci domin kuwa tuni saniyar ta mutu sauran kuma na tsaye suna kiwonsu. Faduwa Fadime tai ta dafe kai tana kuka, har sai da Mahaifinta ya tasheta tsaye. 


“Haba Fulani komai ai na Allah ne? Ki daina wannan kukan”


“Bappa kullum fa idan na fita kiwo sai Nagge ta mutu, ni kadai take ma haka”


“A a daman can haka Allah ya rubutu”


Ya amsa mata cike da karfin hali, sai daya daga cikin mutanen da suka zo tare da shi dayan ya ce. 


“Malam da dai ka daina barinta tana fita kiwo da su”


Malam Jauro yayi murmushi yana girgiza kai. 


“A a babu abunda za a fasa, idan mutanen gari sun canfa ta ni ai be kamata na yarda a matsayi ne na mahaifinta, idan Fulani bata ji dadi a gurin iyayenta ba a gurin wa zata ji? Ko da duka sanu na za su kare ba Fulani ba zata daina zuwa da su kiwo ba”


“To Allah Hukkumo sa'a”


Dayan ya fada cikin jin haushin be dauki shawararsa ba. Malam ya dafa kan Fulani ya ce. 


“Ki cigaba da kiwon idan yamma ta yi sai ki dawo da su gida, annani?”


“Iyyiye”


Ta amsa masa tana gyara kai har lokacin bata daina hawaye ba, kuma bata san ranar dainawar ba domin wannan matsalar ta shiga cikin jininta ta zauna ta hanata sukuni da walwala duk kuwa da irin ficen da tai a cikin kauye na amsa sunan yarinya daya tilo wacce ta iya turanci kuma ta iya rubutu da karatu a kauyen. 

Sai dai wannan abun yasa mutane na tsoronta ga rashin farin jinin da yake damun mahaifiyarta, tun tasowarta har ta girma ta kawo yanzu babu namijin da ya taba nuna yana ra'ayinta balle har ya furta yana sonta, ko irin zuwa dandalin da take sai dai taje wani lokacin dan ta kai sana'arta wani lokacin kuma dan tai kallo, domin ko da ta shiga tai rawa babu namijin da zai mata kari, sai dai tai wasa da yan 'uwanta mata duk kuwa da irin kyau da Fadime take da shi. 


Haka ta zauna a gurin tana kula da shanun har rana ta raba sannan ta nufi sandarta ta dauka ta kora shanun suka nufi hanyar gida tana tafi tana rare wakarsu ta fulani kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba. 

Ita ta kanta ta saka shanun a gurin zamansu sannan ta daure ko wanne ta dauki abun shan ruwansu ta debo musu ruwa ta kawo musu sannan ta fita daga wajen. 

Bukkarsu ta nufa ta shiga ciki tana cigaba da rera wakar da take tun da ta turo shanun har ta kawo gida, tufafin Fulanin dake jikinta ta cire ta daura zane ta fito tsakar gidan ta dauki wata karamar roba ta nufi tukuyar ruwansu ta debo ruwa a ciki ta nufi bandaki, sai da ta tube tufafinta sannan ta lura da kadangaran dake leke da windin da aka zagaye akai bandaki da shi suna a kai suna kallonta, bayan mutane abu na biyu data tsana yana kallonta kadangaru ne, dan ta lura har wani kada kai suke idan suna kallonta, abun haushi ma kallonta suke ba kakkautawa ko dauke ido basa yi. 

Haka ta debi ruwan ta rika watsa musu suka fara gudu banda daya wanda ya tsaya yana kallonta sai wani rausayarda kai yake. 

Hakan yasa ta tsorata ta fara ja da baya tana cigaba da watsa masa ruwa, aiko kamar jira yake sai ya sauko da sauri yai cikinta, tsakanin ihunta da fallawa da gudu da kuma sakin robar ruwan ba a san wanda ya riga wani ba, kamar bera haka ta shige bukkarsu har wani tsale take sama tsabar gudu da tsoro. 


“Inna Kadangare ne ya bijoni”


“Ba dai zaki daina watsa musu ruwa ba ko? Wata rana sai kin watsawa aljani”


“Inna wannan ma da gudu yake, ba zan iya wanka a ciki ba”


Duk maganar da take da Inna ba ta dago ta kalleta ba sai aikin auna giÉ—a take a kwarya, sai da ta mike tsaye sannan tai arba da yarta. 


“Innalillahi Fulani a tsirara kike fa, zindir Subhanallahi”


“To Inna kadangaren ne ya biyo ni ai ba zan iya tsayawa daura zane ba”


Ta fada tana turo baki tare da sa hannu ta kare kirjinta wanda da shi da babu duk daya kamin ta nufi inda zane yake ta dauka ta daura. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fito sannan ita ma ta fito waje tana labe bayanta kamar wacce zata sake arba da shi.


“Ni ban ga komai a bandakin ba”


“To Inna ki tsaya na gama wanka tukuna sai ki tafi”


A bakin kofar bandakin Inna ta tsaya Fadime ta dauki robar taje ta debo wani ruwan ta tsaya daga baki-baki tai wankan ta fito da sauri...


No comments

Powered by Blogger.