Furar Danko 4
๐๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง
๐ซ ๐๐๐๐ผ๐ ๐ฟ๐ผ๐๐'๐.....!
๐ฉ๐๐๐๐ ๐จ๐๐ ๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ 4️⃣
........Idanun dattijuwar cike da ฦwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ษaga ฦafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma
itafa da sauฦi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ษaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ษin ษakin ita kaษai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ฦamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki ฦดarnan” ta faษa cikin tausasawa tana ษauke ฦดar ฦwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaฦancin da Lulu ke mata tana ฦyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ฦดaฦดanta dake ฦauye da ฦดan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, dan in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ษin ne ya ษan fi cin nasararta, dan shi har faษa yakan ษan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ษin bane ba....Wannan kenan
∆•••••∆ ★ ∆•••••∆
Da ga airport babban kamfanin Jiฦamshi's ya nufa ransa a ษace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa'ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ฦara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ษin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ษan rubutu ya haษa da key ษin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ษan taษe baki...
Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ฦofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ฦasan maฦoshi har yanzu zuciyarsa na masa ฦuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika'il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ฦasฦantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ฦarfin ฦwanjinsa amma ba ฦasฦanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ฦarฦashin takalmin kowa ba. Da'ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ฦasusuwa ya zubar da ita a airport ษin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ฦดa mace.....
“ฦan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faษa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ษin maimakon amsa, ya zaro ษari biyu a cikin aljihunsa ya miฦa masa. Bai jira mai napep ษin da ke faษa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..
*_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ฦasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuฦar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. ฦa na bakwai a gurin Malam Mika'il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huษu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuฦar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ฦwallon ฦafa. Ya iyata matuฦa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ษinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ฦwallo sai ya yanke jiki ya faษi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al'amarin da asiri, sai dai shi yaฦi ษaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ฦwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ษan gwada yin ฦwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ฦasa ma, ya fara neman aiki amma yaฦi samuwa duk da takardunsa sunyi ฦyau matuฦa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ษaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaฦanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ษaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ฦwallon ฦafa ya ajiye gefe ya shiga ฦoฦarin sana'a, sai dai anan ษin ma dai komai yaฦi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ฦanฦanin lokaci al'amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ฦoฦarin kamo can idan nan taฦi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ฦดan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika'il Idris Mawashi huษu ne cif, hakama ฦดaฦดa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ฦดammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan๐
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
ฦณan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ษin๐
+22799643131
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐ญ๐_*
Leave a Comment