Furar Danko 5
๐๐ฒ๐ฉ๐ข๐ง๐ ๐ฒ
๐ซ ๐๐๐๐ผ๐ ๐ฟ๐ผ๐๐'๐.....!!๐ซ
๐ฉ๐๐๐๐ ๐จ๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ค๐ป
๐ช๐๐๐๐๐๐ 5️⃣
_Free pages end_
.......Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti. BQ ษin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki
iyayensu mata, baya can ฦarshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buฦatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ษakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ฦanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ษakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ฦanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ฦดar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faษan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ฦwallar ษacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ฦwaฦwฦwarar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ษaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taษe rayuwarsa haka. Duk inda ษa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.ฦakine ษan babba mai ษauke da kafet maroon color mai laushi, sai ฦatuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ษan yi teburin karatu da kujerarsa. ฦakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ฦamshi kamar ba ษakin namiji ba. Uniform ษin da aka sharษanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ษakin ฦwara ษaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ษaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaฦi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ฦona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ษinkin fidda surar jikinta baฦin ciki yake ji balle wannan da gaba ษaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ฦarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaฦi barinsa yin barcin da yake buฦatar yin ko zai samu sassaucin baฦin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ฦyar ya samu barcin ya ษaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da ฦyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miฦe ya shiga toilet ษin ษakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ฦofar gidansu yake, dan baifi gida huษu ba ne tsakaninsu....
Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ษakinsa yanzu ciki ya shiga ษangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huษu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ฦalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ษan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ษauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ษaya ya amsa musu ya nufi ษakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..
Daga ษangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ฦasan carpet ษin da aka saka a gaba ษaya falon kalar blue. Basu da kuษi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haฦuri sosai, sai dai bata son raini ko kaษan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ษin jinin zazzagawa ce.
“Ammah barka da yamma”.
Ya faษa cikin muryarsa mai sauฦin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ษakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.
“Baka da lafiya ne?”.
Gajeren murmushi yayi da ษan girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na ษan yi barci ne”.
“Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”
Ta ฦarashe faษa a hankali cikin damuwa. Gaba ษaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarฦe ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.
Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ฦarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ฦarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ษazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi. Fitowar ฦannensa biyu ฦดammata Maryam da Asma'u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. ฦณammata ne ฦyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ษan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. ฦauke kanta tai, dan gaba ษaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu.
“Yayamu ina yini”
Suka haษa baki wajen faษa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ฦaunar ฦanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al'amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ษakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ฦดaฦดan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..
“Babu wata damuwa ko?”.
Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buฦatu, sai dai sun san koma sun faษa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ษakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ฦarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma'u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha...........✍️
*_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faษa muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiษar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANฦO...!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al'ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar ฦดaฦดanmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taษo fiye da inda kuke zato._*
*_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu ฦamshi, yarinyar ฦดar ฦwalisa mai tsananin wayewar rayuwa. ฦณar gata kuma ฦดar hamshaฦan masu kuษi. Uncle Smart matashin saurayi ษan talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri'a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waษan nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_*
_Minene abinda Lulu ฦamshi ke ษoyewa na rayuwarta?_
*Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taษe rayuwarsa da ga cigabansa?*
_Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR ษin nan naku abin alfaharinku. ฦณan amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._
*_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak ษinki, karki bari ki ษorama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin ษaukar watarana saboda ruษi da ษaukar komai a ba komai ba ฦดar uwata._*
_ALLAH ya ฦarama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions ษin nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri'arsa baki ษaya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al'ummar musulmi baki ษaya๐ญ๐๐๐❤️❤️❤️❤️๐_.
Garzaya ki biya naki kar a baki labari gasu nan da ษumi-ษuminsu suke๐๐๐.
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan๐
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
ฦณan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ษin๐
+22799643131
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
*_ALLAH ya gafartama iyayenku๐ญ๐_*
Leave a Comment