Gidan Aro 15



*15*





*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





K’arfe shida na safe sukaji ana bugun k’ofan gidan kaman za’a b’alla.. Bugu ake da k’arfin gaske ana jijjiga k’ofar, bai tsaya a bugun k’ofa ba tuni aka soma jefo duwastu cikin gidan.


 Umma dake bisa sallayarta wanda tinda tayi sallan asubahi bata tashi kan sallayar ba tana zaune tana Lazimi da kai kukanta ma Sarki da babu kamansa, majib’icin lamiransu, Mai mulkin sammai da k’assai wanda babu abinda yafi k’arfin ikonsa da buwayarsa.. Babu shiri Umma ta mik’e tana mai linke abin sallarta, Ta aza cazbahan dake hannunta saman abin sallar kafin ta nufo waje.. Kusan cin karo sukai da Sadiya wacce Ta fito daga kitchen tana kalata masu abinda zasuyi karin kumallo dashi.


“Umma bugun k’ofa ake..” Batakai aya ba aka kuma jefo wani Dutsen sai a goshin Ashiru da fitowarsa kenan yana mutsuka ido. Aiko nan ya saki k’ara yana rik’e goshinsa.


A tare Sadiya da Umma suka nufosa dan tuni ya kwanta wajen yana dafe da goshinsa yake fad’in “Kaina kaina Umma.. Wayyo Allah kaina.!”


A fujajan Sadiya taje Ta nemo tsumma ta d’aure masa goshin nasa dan k’ok’arin tsaida jinin.. Umma kaw babu shiri ta nufi k’ofa ganin basu fasa abinda suke aikatawa ba.


Tana bud’e k’ofar ta hangi Tabawa na tsaye wasu k’artan maza guda uku sun sakata a tsakiya ga duwastu a hannunsu. Sai faman sakin huci Tabawa take.


“Yauwa kunaji ku shiga ku fito da dik abinda yake mai amfani ne a cikin gidan.” Tabawa tace tana duban k’artan mazan.


Da tsananin mamaki Umma ke dubanta “Amma Tabawa bakida mutunci.. Shin wace doka ce ta baki daman ki shigo har cikin gidanmu kici mana mutunci dan kina binmu bashi.? Jifan da kika tashemu dashi har kikaji ma d’ah na ciwo bai isheki ba shine zakice ma wad’annan K’artan banzan su shiga gidan mata mai takaba su kwaso miki kayanta.. Anya Tabawa akwai zuciya cikin k’irjinki.. Anya zaki wanye da duniya lafiya..?”


“Toh sai ki hani wanyewa da duniyar lafiya idan kece mai Ita... Ke har zakiyi ma wani wa’azi. Yaushe ma kika tuban.. Yaushe kika daina zuwa wajena kina rok’ona Allah Annabi na samo ma d’iyarki manyan Alhazawa shine yanzu dan duniya ta juye daku zaki bud’e tsartsaman bakinki kice zaki min wa’azi.. Toh wama zai saurari wa’azi daga bakinki.. Koda shike ba laifinki bane ke d’in dama ai tsintacciyar mage ce baki da dangi sai na bariki.. Kai Over Wai mai kuke jira ne.. Ku shige kuyi aikin da na sakaku.” 


Suka amsa da Toh Hajiya Tabai.


Umma bata iya furta komai ba Sai hawaye dake ambaliya a fuskarta.


Sadiya ce Tai k’ebebe bakin k’ofar ta hanasu shiga “Babu Wanda ya isa ya keta mana haddi ya shige mana gida ba tareda izinin mahaifiyata ba.. Hajiya Tabawa kar ki bari na maka k’ararki a ofishin ‘yansanda.. Tin muna saida juna ki tattari body guards d’inki ku b’ace mana a k’ofar gida bamu neman tashin hankali..”


Shewa Tabawa tai harda rangad’a guda “Tashin hankali ai cikinta kuke dumu dumu..” Ta k’anne ido tana nuna Sadiya da yatsa “Ke k’aramar maras kunya ni kike ma barazanan zaki kai k’arata wajen ‘yansanda.. Cikin ni da ku wanene yake da abin kaiwa k’ara wajen ‘yansanda.. Ga fili ga doki maza.. Zo ki shige kije kikai k’arata wajen ‘yansanda.. Nasan dikda asarar da na maku bazai kwatan kud’ad’en da nake binku ba... Jeki Sadiya jeki ki kai k’arata ni kuma nayi alk’awarin jaza maku wulak’ancin da ban maku ba a baya.. Over ku shige nace ku tattaro..  Idan bata matsa maku a hanya ba ku had’a da Ita dan nasan zata maku amfani ko rage dare kwayi da Ita dama sauran titi ce..”


Wannan karon Umma ce ta dakatar da Tabawan, cikin tsananin huci take nuna Tabawan da yatsa, lokaci guda take fad’in “Koda wasa kar ki sake aibata d’iyata a gabana.. Idan kuma ba haka ba..”


“Idan kuma ba haka ba Sai k’ak’a..?” Tabawa tace tana ci gaba da jijjiga “K’arya aka mata Ko ba abinda ta saba yi bane..?” 


Hawaye ne kawai suke gangarowa daga idanun Sadiya da Ta tare k’ofar gidansu cikin tsananin huci.. Jin kalaman Tabawa take kaman ana dab’a mata wuk’a tsakiyan k’irjinta.. Yayinda su Over ke binta da mayen kallo suna wani shafa hab’a suna fad’in “Kuma fah wllhi dama ta jima a ranmu.. Muna ganin yanda masu manyan motoci suke safara a unguwar nan suna kwasanta... Kawai dan bamuda kud’i ne da muma mun jima da d’anata ai..” Suka k’arashe suna masu sakin shewa irin na cikakkun ‘yan daba..


Daidai lokacin Alhaji Isyaku ya doso lungun yana aza babbar riga yake fad’in “Yaya yaya kai yaya dai meke faruwa ne Wai..?” Kafin Alhaji Isyaku ya k’araso ‘yan daban Tabawa suka aune a guje dan sunsan wanene Alhaji Isyaku yanzu Sai ya kwaso masu ‘yansanda yasa a tafi dasu.


Tabawa sai huci take tana kuma balabala wutan masifa.


Alhaji Isyaku ya k’araso yana tambayan Tabawa ba’asi tamkar baisan komai ba..

Tabawa kaw nan taci gaba da masifa tana fad’in “Toh Wai biya masu zakayi ne Alhaji da zaka wani Zo ka dakatar dani.. Rashin mutunci yanzu na fara ehe idan har baza’a biyani kud’ad’ena ba..” Ta maidoda dubantaga Umma dake tsaye Jiki a matuk’ar sanyaye tana hawaye, lokaci guda Ta kad’a ‘yar yatsarta tace “Kunci sa’a wannan karon.. Had’uwar mu na gaba sai yafi wanann muni idan har baku biyani kud’ad’ena ba..” Ta k’arashe tana mai janye mayafinta fuuu ta wuce..


‘Yan lungun kaw kaman ba safiya ba Sai lek’e ake anyi cincirindo ana bama ido abinci..


Alhaji Isyaku ya risina yana bama Umma hak’uri kan abinda ya faru, idanunsa rabi naga Sadiya wacce maganganun ‘Yan daban Tabawa ya sanyata zama sukuku da ita, gaba d’aya bama ta fahimci su waye a wajen ba, maganganun ne kurum suke Yawo a kwanyarta da dodon kunnuwanta.. Irin kallon da illahirin mutanen unguwarsu ke mata kenan, Fanko, sauran kwalta. Bata tab’a yin danasanin rayuwar da tai a baya na rashin kamun kai irin yau ba.. Ashe mutunci yafi komai.. Mutunci yafi kud’i.. Yau da ace ta rik’e talaucinta ta tsaya a matsayin da Ubangiji ya ajeta da babu wanda zai dubeta ya mata irin wannan mummunan k’azafi maras dad’in sauraro.. A nasu tinanin samaruka da suke d’aukanta a manya motoci mutuncinta take saida masu, yanda take shigan gayu ta rik’e babban waya ita ba d’iyar kowa ba dole suyi tinanin mutuncinta take  saidawa ta samu. Abinda bata tab’a kuskuran koda aikatawa ba.. Ta lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata. 


Kaman Umma tasan tinanin da take tai saurin k’arasowa Ta rik’e hannunta tana girgiza mata kai take furta “Komi kikayi sai an zageki a duniyar nan.. Kar ki bari maganganun su ya dameki kinji koh..”


Alhaji Isyaku na tsaye gefe ya kannare idanu yana dubansu.


Sadiya bata iya furta komai ba har lokacin saima duban Umman da take cikin wane irin yanayi.


Ana haka Ashiru ya fito rik’e da kansa dake jini har lokacin kuka yake.. Kukansa ne ya dawo da hankalin Sadiya, tai saurin ta nufesa tana tambayarsa ko kan nasa ke masa ciwo.


Ga mamakinta Alhaji Isyaku ne ya k’araso yana fad’in “Subhanallahi.. Garin yaya haka Ta faru.. Wannan Ai sai an kaisa asibiti..”


Da tsananin mamaki take duban Baban  Aminiyar nata yayinda mak’ota ‘yan lek’e suka ci gaba da bama ido abinci wasu na k’usk’us ganin yanda Alhaji Isyakun duk ya wani susuce kan abinda ya samu su Sadiya saikace ba shi bane kwanaki yazo masu da ‘yansanda.. Tabbas akwai wata a k’asa..


Ba tareda Sadiya tace komai ba ta shiga janyo hannun k’aninta tana fad’in “Umma zan kaisa  chemist d’in Ema..”


Alhaji Sabi’u yai karaf yace “A’a ai bazai iya tafiya kan k’afafunsa ba jini ya zuba jikinsa.. Motata na bakin layi barin d’aukesa in kaisa..”


Umma tai saurin girgiza kai tace “A’a Alhaji.. Kawai kaje mun gode Sadiya zata iya kaisa.”


Alhaji Isyaku bai tsaya sauraron Umma ba ya sunkumi Ashiru yana fad’in “Haba dai Umma ai ciwo irin haka da zuban jini ba’a wasa..” Tuni ya shige da Ashiru rungume cikin hannunsa yana masa sannu..


Daga Umma har Sadiya da tananin mamaki suka bi bayan Alhaji Isyaku da kallo babu kaman Sadiya wacce ta kuma komawa tamkar mutum mutumi.. Wai Abban Sabeera da baya k’aunan ganinta da Sabeera shine ke wannan rawar k’afar duk dan sabida Ta yarda da aurensa.. Ikon Allah Wai dama haka mutane suke ne.. Lallai mutumin nan yakai mak’ura a rashin kunya.. Babu kunya har na kiran mahaifiyarta da Umma.. Tabd’i.! Wannan abu da matuk’ar mamaki yake.. 


Duban juna sukai itada Umma cikinsu babu mai iya cewa komai sai tsananin mamaki da ya lullub’esu.. Umma ta kamo Sadiya Ta maida k’ofar gidan Ta tura dan har lokacin ‘yan lek’e basu daina ba..


Su duka biyun sukuku suka nufo tsakar gidan babu mai iya cewa komai dan har lokacin mamaki bai sakesu ba.. 

Sadiya ta taimaka ma Umma ta zauna nan tsakar gidan saman tabarma..


Sauk’e nannuyan ajiyan zuciya Umma tai tace “Hmmmm Ikon Allah..! Lallai a gaisheda namiji..” Umma tace tana kuma canza position d’in taguminta a karo na biyu.. Sadiya kam tsaban mamaki tama rasa bakin magana. Kitchen kawai ta nufa yanda take jiwo k’aurin girkin data d’aura alamun ya soma k’onewa.. 


Bayan kaman shud’ewan awa guda saiga Ashiru ya shigo rik’eda robar Ice cream yana sha ga goshinsa an rufe da bandage. Baban Sabeera na biye dashi hannunsa nik’i nik’i da manya manyan ledodi shak’e da kaya.


Bakinsa har kunne ga malum malum d’insa dik sun sauk’e sun rufe ledar.. Tsaban takaici Sadiya mik’ewa tai Ta shige d’aki dan bazama ta iya duban fuskarsa.


Umma na nan zaune tsakar gidan saman tabarma Ashiru ya k’araso ya zauna gefenta sai lasar Ice cream d’in yake.


Shafa kansa Umma tai tace ya kan  naka. Ya daina ciwo.?”

Ya jinjina mata kai yana bud’e ledar biscuit d’in dake d’aya hannunsa.


Umma ta Shafa kansa tace “Tashi ka shiga ciki koh ka bamu waje.”


Ya mik’e yana jinjina kai.. Yana shigewa Sadiya ta fuzge tarkacen da ya shigo dashi tai watsi dasu.


Kuka ya shigayi yana bori yana fad’in Maiyasa ta yar masa abinsa.. Ko takan kukan Ashir batabi ba ta shige d’aki zuciyarta na mata d’aci.


Umma da Alhaji Isyaku dik sunji abinda ya faru a kunnuwarsu..


Dikda jikin Alhaji Isyakun ya d’anyi sanyi bai fasa sanar da Umma buk’atarsa na son auren Sadiya ba.. 


Umma Ta murmusa cikeda takaici “Alhaji da ka daina wannan wahalan dan hukunci dai mun riga mun gama yankewa daga ni har Sadiya.. Kaje mun gode da niyyan taimako.”


Alhaji Isyaku yace “Baki fahimta ba Umma..”


“A’a ni dan Allah ka kirani da Uwani menene wani Umma.. Kaga Alhaji Takaba nake ba don tashin hankalin da muke ciki ba Ko barinka ka shigo gidan nan bazanyi ba.. Mun gode da kai Ashiru asibiti da kai dan Allah ina rok’onka ka tashi ka tattari kayyakinka ka tafi bamu buk’ata kuma kar ka sake dawo mana.”


Alhaji Isyaku ya murmusa kad’an yace “Umma kenan.. Barin fad’a miki kuna buk’ata na..”


Da mamaki Umma ke dubansa.


Alhaji Isyaku ya murmusa yana mai jinjina kai “ K’warai kuna buk’atana Umma.. Ya kamata ki sake tunani akan wannan al’amari.. Ki tuna makomar rayuwarku musamman yanzu da babu mahaifin yaranki.. Ki tuna halin rayuwa da zaku fuskanta.. Shin kina tunanin Sadiya zata samu miji ne bayan duk abubuwan da suka faru..? Kindai ji da kunnuwanki irin maganganun da mutanen unguwa keyi akan d’iyarki.. Kina tunanin akwai wanda zaizo ya aureta a haka..?” Ya kuma kannare idanu yana kuma duk’ar da kansa yace “Amma ni zan biya maku bashinku sannan zan auri d’iyarki na d’auketa daga garin nan, zan kaita can da nisa  yanda babu wanda ya santa, gaba d’aynku ma zaku bar nan zaku koma sabon waje ku soma sabuwar rayuwa a can yanda babu tashin hankali babu komai..”


Umma da hawaye ke gangaro mata kafin takai ga furta wani kalma suka jiyo sallama daga waje.. Babu shiri Ta mik’e dan ba muryar kowa bane face Aminu dillalin da ya basu hayan gidan da suke ciki..


Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai Umma ke nanatawa cikin zuciyarta.. Ta d’aga idanu tana duban glasses na window da Tabawa da ‘yandabanta suka fasa..


Umma murya na rawa take fad’i da Aminu “Malam Aminu Barka da Safiya..”


“Uwani ba wannan ya kawoni ba.. Zuwa nai dan na tabbata Kun fice daga gidan nan. Bazan d’auki asara irin haka ba.. Zamanku a gidan nan babu alkhairi dama baku biya kud’in hayan bara ba ga na bana.. Sabida mutuwar mijinki yasa na d’an d’aga maku k’afa. Nayi niyyan maku mutunci na barku ku zauna har ki ida takabanki kafin na sallameku amma Tunda abun ya zama haka gaskiya zaku tattara ku fice a gidan nan dan amana Alhaji ya bani.. Tinda nake masa dillancin gidajen hayansa a unguwar nan bamu tab’a samun matsala ba.. Bazan fara akanku ba, na kula masifa da tashin hankali bibiyarku suke Dan haka kawai ku biya kud’in hayanku ku k’ara gaba tin kafin Alhaji Sadi yaji wannan batu..”


Cikin rawar murya Umma ke fad’in “Malam Aminu dan Allah kai hak’uri ka taimakemu.. Ka rufa mana asiri yanda Allah ya rufa maka.. Idan muka tashi a nan bansan Ina zamuje ba.. Dan Allah kaji tausayinmu.. Ka bari Ko Takaban ne na gama.. Inada yara Malam Aminu bansan ina zan kaisu ba idan muka tashi a nan..”


Girgiza kai Malam Aminu yai yana duban wani gefen dan karma Ta basa tausayi “A’a Uwani.. Gaskiya bazan iya ba.. Gidan nan nima amana ce a hannuna, kawai ki daina rok’ona dan bazai yuwu kuci gaba da zama a nan ba.. Maganar gaskiya kenan..!” Ya k’arashe yana mai jaddada maganar tasa..


Alhaji Isyaku dake gefe gyaran murya yai yace “Aminu kayi hak’uri kar ka tashesu.. Ni zan baka kud’ed’en da ake binsu zan kuma biya damages d’in da Tabawa tayi ma gidan.. Mu k’arasa gidana ka amshi kud’ad’en..”


Umma baki sake take duban Alhaji Isyaku, Ta rasa wanne zatayi dan batada bakin maganar a halin yanzu.. Tana ganin Alhaji Isyaku da Aminu suka wuce Aminu yana fad’in “Wllhi ba don kai ba Alhaji saidai su bar gidan nan a yau dan na lura tsautsayi ke bin ahalin..”


Juyowan da Umma zatai taga Sadiya na tsaye bayanta hawaye na bin fuskarta.. Su duka biyun babu wanda ya iya cewa komai sai rungume juna da sukai had’i da sakin kuka mai ban tausayi..


**


Hindu ce taima Ajidde iso zuwa parlorn Aunty Nuratu. A nan suka tadda Inne harmada Aunty Shamau. 

Ajidde ta risina ta gaishesu sai kalle kallen kayan alatu take wanda aka k’awata d’akin dasu. Tab lallai da ace zata iya kwashe wannan kaya takaima Kyallu da ta gama saye zuciyar Kyallu da imaninta..


Yanda take kalle kalle tana d’aga kai yasa Shemau zuba mata idanu fuska a yatsine “Ke.!! kiyi abinda ya kawoki ki tafi kin tsaya sai faman kalle kalle kike..”


Tsawan da Shemau ta daka mata saida ya sanyata zabura Ta k’ame waje guda.


Inna kaw a hasale Ta katse Shemau da fad’in “Haba Shemau ki bita a hankali mana.. Meye abun fad’a a nan inyi. Baki ganin yarinya ce..”


Shemau Ta d’an sassauta murya tace “Inne babu wani yarinta muguwar k’auyanci ne kawai..”


“K’auyanci.? Ked’in yaushe ne kika waye..! Koda wasa ni Kinsan bana d’aukan wulak’anta d’an Adam.. Ki k’yale yarinya tayi aikinta a natse, Zo ki fice ma bansan zaman mai kike a nan ba..” 


Shemau ta d’an b’ata fuska ta fice ranta baiso ba Inne naci gaba da sababi..


Ajidde taima Shemau gwalo cikeda jin dad’in bayanta da Inne tabi...


Mamaki ya cika Shemau dan taga sanda Ajidde ta mata gwalo harda kashe mata ido guda.. A ranta tace lallai wannan yarinya sai ta gyara mata zama. 


Tana ficewa Ajidde ta saci kallon Inne saidai itama Inne ita take duba murmushi saman fuskarta. 


“Taho muje.” Inne tace sanda ta mik’e ta nufi k’ofar d’akin da Aunty Nuratu ke kwance.


Ajidde tabi bayanta rungume da jakar maganinta still sai kalle kalle take tana k’are ma gidan kallo.



No comments

Powered by Blogger.