Gidan Aro 18



*18*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*










Da kuka Sabeera ta k’araso gabansu tana fad’in “A’a badai Babana ba.. Badai k’awata Sadiya ba.. Mama kar ki yarda da maganar wannan matar I’m sure k’arya take.. Ki tashi.. Tashi ki fice mana daga gida..!” Tai maganar tana k’ok’arin finciko Asabe dake duk’e wajen ta zuba masu ta mujiya. 


Maman Sabeera kam tama kasa tantance abinda ke faruwa. Kaman daga wani duniyar take sinkayo kukan Sabeera da maganganunta.


Asabe ta mik’e tana fad’in “Idan k’arya nake maku ku tare mutanen lungunsu ku tambayesu ko kuma kuje da kanku dan ance zuwa dakai yafi sak’o. Nidai na gama nawa tinda sanar daku.. Ya rage naku ku yarda ko kar ku yarda. Allah bamu alheri.” Tana ida fad’in haka ta mik’e ta aza bahon kayan Kolinta aka Ta nufo waje, tuni Ta cika ma rigarta iska aka bar Sabeera da Mamanta babu mai iya ba ma wani hak’uri. Cikin muryar kuka Sabeera ke duban mahaifiyarta tana fad’in “Mama k’arya take kar ki yarda da ita.. Wllhi nayi imani Sadiya bazata tab’a aikata haka ba.. Nasan Sadiya nasan halinta wllhi sharri ne kawai irinta mutanen unguwar nan.. Mama dan Allah Kema kice min baki yarda ba..!”


Maman Sabeera bata iya furta koda kalma ba sai hawaye dake zarya saman k’uncinta. Cikin sauri ta mik’e ta nufi d’aki tana jin kukan da gaske na zuwa mata. Sabeera tabi bayanta da sauri tana kiranta amma inaa bata ko tsaya ba balle ta saurari Sabeera ta shige d’aki kayanta.

Silalewa Sabeera tai a wajen kukanta na k’aruwa itama. Hiran wasu course mates d’insu take tinawa data sinkaya wataran a makaranta cewa akasari ba duka ba iyaye  da suka faye tak’ura da tsanani ka bincika ta yuyu shima watsewarsa yake da yaran wasu baiso ayi da nasa shiyasa yake masu mugun tsanani. Tai saurin toshe kunnuwanta tana girgiza kai dan bata so ta amince da hakan.. Wani tinanin ne ya kuma d’arsuwa mata a zuciya.. Ita kad’ai ta aminta da Sadiya, itace bata mata kallon da sauran mutane suke mata a unguwar.. Ta yarda da ita d’ari bisa d’ari sannan ta saka ma ranta cewa Sadiya ba mutuniyar banza bace but Maiyasa yanzu take jin shakku akan hakan.. Kardai da gaske Sadiya cin amanarta take.. Take taji zuciyarta na wani irin bugawa, gwara taji labarin mahaifinta na neman wata daban badai Sadiya k’awarta data d’auki yarda ta d’aura mata ba.. Waima tsaya mahaifinta ya mata iyaka da Sadiya ta ya za’a ce su biyu d’in suna tare.. Cikin sauri ta shiga girgiza kai tana furta “No.. no .. no I can’t take this anymore.. I need to find out myself..” Tana ida fad’in haka Ta mik’e Ta nufi nata d’akin dan shiryawa.


Cikin kuka Maman Sabeera ta kirawo k’awarta Ramatu a waya tana sanar da ita tashin hankalin da suka wayi gari dashi, a fujajan Ramatu tace gata tafe maganar yafi k’arfin ayita a waya dan dama basuda nisa unguwar tasu.


Sabeera kaw tuni ta fice dikda mahaifinta ya mata iyaka da waje balle gidansu Sadiya tin bayan abinda ya faru. Ta’aziyan mahaifinsu ne kawai Mamanta Ta mata cover suka tafi tare. Tafiya Sabeera take a layin  tana jin zuciyarta na mata wani irin d’aci, babu addu’an da take cikin zuciyarta face Allah yasa duk abubuwan nan da taji k’arya ne babu gaskiya ko guda a ciki.. Bata jin zuciyarta zata iya d’aukan cin amana daga babban aminiyarta irin Sadiya wacce ta d’auki yarda da komai ta d’aura mata. Tana tafe tana tinanin tazo wuce shagon Maman Emeka ai kuwa saiga wasu ‘yanmata ‘yan unguwar a k’ofar Kantin sun Sai bredi da dangin abin kari kumallo.. D’ayar ta tab’a d’ayar tana nuna mata Sabeera dake had’a hanya zata nufi lungun gidansu Sadiya.


Cikin azama suka nufo Sabeera suna kiran sunanta, taja Ta tsaya tana dubansu da idanunta da tuni sun kod’e sunyi ja dan kuka..


“Laa Sabeera ina kika nufa..? Kardai gidansu Sady Pretty..” Ta d’an tab’e baki kad’an yace “Ai kuwa ko Jiya naga Babanki k’ofar gidan yana zance  kuma kaman Sady Pretty na gani..”


D’ayan ta cab’i zancen da fad’in “Ni da naga motar Babanta bakin lungun ma nayi zaton Sabeerar ce ashe ashe dai Baba ne..”


Cikin tsananin huci Sabeera ke dubansu, ta kasa magana sai dubansu da idanu da take.. ‘Yanmatan suka dubi juna kafin d’ayar ta tab’e baki ta janyo hannun ‘yaruwar tata tana fad’in “Kinga k’awata Zo muje.. Allah dai ya kyauta k’awancen cin amana..”


Tamkar wacce aka dasa dutse haka Sabeera ta tsaya a wajen.. Shikenan dai Wato ta tabbata da gaske Mahaifinta saurayin Sadiya ne.. Kuma ko da wasa bata tab’a hasasho hakan ba, bata tab’a tunanin hakan ka iya kasancewa ba.. Da k’yar take d’aga k’afafunta tana ganin hanya na rabe mata bibbiyu.. A haka Ta k’araso gidansu Sadiya.


Sadiya da Umma na zaune tsakar gidan tana duba k’afar Umma da har yanzu yake d’an mata ciwo, tamkar wacce aka jefota haka sukaga Sabeera akansu..


Zuciyar Sadiya yai wani irin tsinkewa yayinda Sabeeran ta zuba mata idanu.


Umma ce tai k’arfin halin cewa “A’a Sabeera kece tafe.. Sannu da zuwa.. K’araso ki zauna.”


Ko gizau Sabeera batai ba saima duban Sadiya da take. Umma ta dubi Sadiya ta kuma dubi Sabeeran da irin kallon da take ma Sadiya. Kafin Umma tai wani aune Sabeera ta k’araso ta duk’a yanda Sadiya ke duk’e suna fuskantar juna saidai kan Sadiyar a k’asa yake.


“Ki fad’a mun gaskiya da bakinki.. Shin da gaske ne..? Sadiya da gaske ne abinda nake ji tsakaninki da mahaifina..?!”


Izuwa lokacin hawaye sun soma ambaliya saman fuskar Sadiya, ta kasa d’agowa ta dubi Sabeera sai hawaye dake zarya saman fuskarta.


Cikin zuban hawaye da tsananin d’aga murya Sabeeran ke ci gaba da fad’in “Talk to me Sadiya.. Tell me the truth.! Ki fad’a mun gaskiya.. Wacece ke a wajen mahaifina..! Ki fad’a mun Sadiya..!!” Ta k’arashe tana damk’o kafad’un Sadiya tana mai jijjigata da iya k’arfinta hawaye na ambaliya saman fuskarta a yayinda kukan Sadiyar ma ya k’aru.


Umma dake gefe ta kasa tab’uka komai sai hawayen da itama taji suna zubo mata.


Cikin muryar kuka ba tareda ta d’ago ta dubi Sabeeran ba take furta “I’m sorry.. I’m sorry Sabeera.. Please forgive me.. Dan Allah ki yafe mun..!”


Take jikin Sabeera ya sake gaba d’aya.. Maiyasa Sadiya take bata hak’uri.. Kenan da gaske ne.. Kenan maganganun da mutane suke fad’i gaskiya ne.. Sadiya da mahaifinta... Ji tai Ta kasa k’arasa tunanin sabida wani irin jiwa dataji na neman kaita k’asa. Take taji wani irin k’arfi yazo mata.. Ta hankad’a Sadiyar da k’arfin gaske Wanda saida ya kaita k’asa.. Sadiya ta buga kanta had’ida gwiwan hannunta da tuni ya karje ya soma jini.. Babu shiri Umma ta mik’e da k’yar dikda k’afarta dake mata ciwo Ta nufi kan d’iyarta.


Sabeera ta kuma yowa kan Sadiyar tana kuka sosai take fad’in “Sai na kasheki kafin ki zama matar Babana..!” Tayo kanta tana k’ok’arin fuzgota saidai tuni Umma ta raba tsakaninsu ta tallafi Sadiyar dake kuka sosai tana duban Sabeera dake k’ok’arin funcikota..


Cikin kuka Sabeera ke furta “I trusted you.. I believed in you.. I never doubted you.. I never judged you.. Duk abinda mutane zasu fad’i akanki Sadiya dai dai da rana guda ban tab’a yarda ba.. Ashe duk ba haka bane.. Ashe ked’in da gaske macijiyace mai bak’in guba.. Ta yaya zaki min haka.. Ta yaya zaki aminiyar data aminta dake irin haka Sadiya..!” Ta kuma yowa kanta tana kuma janyota tana fad’in sai tayi ajalinta.


Daidai lokacin Baban Sabeera ya shigo da shopping bags hannunsa, nan ya tadda wannan hargitsi dake tashi cikin gidansu Sadiyar.


Da tsananin mamaki yake duban Sabeera dake k’ok’arin kaima Sadiya duka Umma na tarewa.


“Ke Sabeeraa.!!” Ya fad’i cikin daka tsawa yana mai fuzgo Sabeeran had’ida d’aura mata mari maiji da lafiya..


Sabeera ta tsaya Cak tana duban mahaifin nata cikeda tsananin mamaki hannunta guda dafe da k’uncinta.


Sadiya kaw tuni ta rungume mahaifiyarta tana kuka sosai..


“Dan gidanku ashe  bakida hankali.. Ashe ke shashasha ce ban Sani ba.. Uban wa ma ya baki izinin fitowa daga gida.. Matar nawa zaki daka dan bakida kunya bakida hankali Ko..!”


Baki sake kurum Sabeera ke duban mahaifinta da kalaman da yake, tana ganin kaman mafarki take ba gaskiya bane.. Tanada tabbacin ba don zafin sauk’ar marin dataji  a k’uncinta ba zata iya cewa mafarki take ba gaskiya bane..


A guje Sadiya dake tsananin kuka ta shige parlor yayinda Baban Sabeera yai yunk’urin bin bayanta yana fad’in “Baby.. Baby kiyi hak’uri dan Allah I’ll deal with her myself..”


Cikin hawaye Umma Ta katsesa da fad’in “Ya isa dan Allah..!” Tai saurin bin bayan Sadiya tana ambato sunata ga k’annenta da tuni sun fito suna kallon abinda ke faruwa.


Baban Sabeera kaw hannunta ya damk’o yana fad’in “Shige muje ki sanar dani ubanda ya koya miki rashin kunya..”


Haka ‘yan lungun sukaita lek’e wasu na k’us k’us d’in an fara dan kaf lungun gidansu Sadiya ne bai rabuwa da hatsaniya da tashin hankali.. Daga wannan sai wancan..


Sadiya kam kulle kanta tai a d’aki tana kuka sosai kaman ranta zai fice.



A b’angaren Maman Sabeera kaw Ramatu tazo sun k’ule a d’aki suna tattauna lamarin tareda neman mafita. 


Ramatu Ta nusa tace “Ai wllhi Rahina Kema da naki, idan b’era da sata daddawa da wari.. Ni tin yaushe nace ki raba ‘yarki da wannan yarinya Sadiya mai shegen kyau kaman aljana.. Wannan yarinyar tana shigo miki gida Ta shnatak’e kaman gidan Ubanta, santaleliyar yarinya irin wannan kice min mijinki bazai d’aura idanu kanta ba..”


Maman Sabeera tace “Wllhi Ramatu ban tab’a kawo haka ba tinda naga bama ya son alak’arsu.. Kuma ni ban tab’a yarda yarinyar lalatacciya bace kaman yanda ake cewa _Never judge a Book by its cover_ toh ban tab’a munana ma yarinyar nan zato ba dan wataran wanda kake zaton mutumin kirki ne bashi ne mutumin kirkin ba, wanda kayi zaton na banza ne sai kaga shine mutumin kirkin.. Ni da har ina sha’awanta ma Abdallah (yayan Sabeera dake karatu k’asar waje..) Amma ni koda wasa ban zaci Wai Alhaji zai d’aura idanu kanta ba...Yayi aurensa ni bazan hanasa ba ya auri ko wacece amma kam banda Sadiya k’awar Sabeera... Ina zan Kai wannan d’imbin bak’in ciki da tashin hankali ga uwa uba Sabeera taji komai..”


Ramatu ta tab’e baki tace “Rahina zama fah bai ganki ba, tashi zakiyi muje har gidansu yarinyar nan muci uban uwarta da kyau dan itace tsararmu ba d’iyarta ba.. Ki daina wannan simi simi d’in  nan naki ki tashi ki karb’a ma kanki da yaranki ‘yanci idan kuma ba haka ba ki zuba ido ki zama ‘yar kallo cikin gidanki.. Kinaji kina gani yarinya ‘yar cikinki Ta k’unsa miki bak’in ciki. Keda gidanki yafi k’arfinki.”


“Ramatu sanin kanki ne ban isa na hana namiji son mata ba dan a halittarsu ne amma damuwar shine kar ya nemi na banza, yayi auren dan shine mafi a’ala tinda Allah ya huwace masa daman auren mace sama da guda. Sannan ni idan zai auren ya auro ko wacece amma tsakani ga Allah banda Sadiya.. Idan ni zan iya jura Sabeera fah.. Sabeera bazata iya jura ba.. Ni wllhi tashin hankalin da ‘yata zata shiga nake tunani.. Yaran nan fah bacci ne ke rabasu sanda suke makaranta kafin su tafi yajin aiki har karatu tare suke..”


Ramatu Ta katse Ta da fad’in “Ni dan Allah kin isheni, kin cika ni da surutun da babu gaira babu dalili.. Dik kin San da wannan shine kika d’add’agoni ko karin kummalo banyi ma mijina ba.. Dama Kinsan wa’azi zaki kirani kimin shine baki sanar dani tin a waya ba.. Ni wllhi indai hakane kar Ki sake neman shawari daga wajena.. Kije can ki k’arata da sanyin zuciyarki aita cutanki bak’in ciki ya turaki rami.. Idan kin canza shawri kya nemeni.. Ni Kinga tafiyata..”


Bata ida rufe baki ba sukaji kukan Sabeera na tashi Babanta rik’e da Ita yana fad’in ta gama rashin kunya daga yau..


A tare Maman Sabeera da Ramatu suka nufo parlorn.


Sabeera ta fad’a bayan mahaifiyarta a guje tana kuka.. Yayinda Babanta yaci gaba da aza babbar riga yana k’ok’arin ciro igiyar decoder yake fad’in “Har ni zakije ki wulak’anta.. Kije kici wa matar da zan aura mutunci sabida bakida hankali.. Yau zakiji a jikinki..”


Ramatu kaw yab’e baki saitin kunnen Maman Sabeera Ta rad’a mata“K’awata ni na wuce kafin mijinki ya had’a dani yace ni ce uwar zigi..” 


Maman Sabeera da tuni Hawaye ya wanke mata fuska Ta tare d’iyarta tai tana fad’in “Wllhi bazan Barka ka daketa ba..” Lokaci guda ta tura Sabeerar d’akinta ta maida k’ofa ta rufe.. Tare k’ofar d’akin tai tana hawaye alamun bazata barsa ya shige ya daki Sabeera ba.. 


Sai sakin huci yake yana duban Maman Sabeera yana fad’in “Rahina ki bani hanya na koya ma yarinyar nan tarbiya.. Tarbiyar da kika kasa bata..”


Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke dubansa, lokaci guda take furta “Wane tarbiya kake magana..? Wane tarbiya ne zaka bata wanda na gaza bata..? Tarbiyar rufeta a gida ka hanata fita Ko k’ofa dan kana tsoron kar a lalata maka Ita Ko mai..?”


Da tsananin mamaki yake dubanta “Rahina kike fad’awa magana irin haka.. Kina cikin hankalinki Rahina..? Dan kawai nazo da batun zan k’ara aure sai ki nemi ki jefeni da sharri..!”


Cikin zuban hawaye Maman Sabeera ke fad’in “Ni ban jefeka da sharri ba, sannan ban tab’a zarginka da aikata abu maras kyau waje ba, na sani idan kana gida Kai nawa ne amma idan ka fice zaka iya zama na kowa idan ka zab’a hakan.. Saidai ka Sani yaran nan kanadasu.. Idan ka lalata na wani ko cikin Tandu kake saka Naka ka b’oye wllhi sai an rama irin abinda kayi ma na wasu akansu..”


Katseta yai da fad’in “Anya Rahina kina cikin hankalinki.? Ni kike yab’awa magana dan nace zanyi aure.. Toh bari kiji na fad’a miki Asabar d’in mai zuwa d’aurin aurena tareda Sadiya, Idan an kawota idan Kinga dama kar ki zauna..”


Da tsananin mamaki Maman Sabeera ke dubansa hawaye basu daina zarya saman fuskarta ba “Aure kace.. Aure wannan asabar d’in.. Yarinyar da kak’i jinin alak’arsu da Sabeera shine zaka zago kace ita zaka aura nan da kwanaki biyu rak..” Tai maganar tana mai d’ago yatsun ta guda biyu hawaye na gangaro mata.. 

Cikin sanyin jiki Ta nufi d’akinta ta maido k’ofa ta rufe ba tareda ta kuma cewa komai ba, amma kam kaida gani kasan da zata samu ta fidda bak’in cikin dake k’unshe cikin k’irjinta ko ta hanyar kuka ne da Ta d’an ji sanyi cikin zuciyarta.


Tsaki Alhaji Isyaku ya buga yana fad’in “Aikin banza aikin wofi.. Ni ma na tsaya Ina miki bayani.. Idan na aurota idan kinga dama kar ki zauna a gidan.. Aure kuma babu fashi.” Ya juyo ya dubi k’ofan d’akin Sabeera yace “Ke kuma k’ofa na kumaji kin lek’a balle har kije kici mutuncin matata sai na aurar dake sadaka a masallaci..” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan fuu kaman zai tashi sama yana aza babbar rigarsa.


**


Sadiya na kwance saman gado ta kasa cin komai har yamma, banda aikin kuka bata komai, harta k’annenta su Ashiru da basu wani fahimci wainar da ake toyawa ba saida suka taru suna bata hak’uri Ta tashi ta saka wani abu a cikinta.. A ‘yan kwanakin tun bayan fasa aurenta da Sagir idan kaga Sady Pretty sai ta baka tausayi musamman idan ka santa a lokutan baya lokacin da tashen kyaunta. Gaba d’aya Ta rame tayi duhu kaman ba Sady ba..


A haka Umma ta shigo ta taddata da k’annen nata sai aikin lallashinta suke. Umma ta shafa kansu tace su fita su basu waje. Babu musu Asiru ya ja hannun k’anins Habeeb suka fice. Suma yaran duk sun koma abun tausayi..


A hankali Umma ta zauna gefen kan Sadiya tana shafa kwantattun sumarta wanda suke a kwance luf ga sulb’i ga tsawo. 


“Sadiya ki tashi kici wani abu kinji, zama haka bazai taimaka ba.. Ki tashi dan Allah idan nima ba so kike nak’I ci ba..” Umma tace tana kuma gyara mata sumar nata wanda ke zube saman pillown da take kwance bisa.


Bud’e baki tai da niyyar magana amma sai taji kuka na zuwa mata, da k’yar Ta iya furta “Sabeera  gaskiya Ta fad’i Umma.. Nid’in tamkar macijiya ce.. An yarda dani nayi yaudara... An aminta dani naci amana.. Umma I’m nothing but a betrayal.. Tell me please Umma, am I really a bad person.?!” Tai maganar tana mai mik’ewa zaune had’ida fuskantar mahaifiyar tata.


Hannayenta Umma Ta rik’e tana mai share mata hawayenta “You are not a bad person Sadiya.. You are only human.. Dukkanmu muna kuskure, mafiya kyawun masu kuskure a cikinmu Sune wad’anda idan sun gane kuskurensu sai su tuba su gyara.. Ki kwantar da hankalinki kinji.. Inada tabbacin Sabeera will come to understand cewa baki ci amanan ta ba.. Da sannu lamura zasu daidaita kinji koh..” Ta k’arashe tana mai janyo Sadiyar cikin jikinta.

Sadiya bata iya furta komai ba Sai lamo da tai cikin jikin mahaifiyarta tana mai lumshe gajiyayyun idanunta.

**


Yamma lis ana kiraye kirayen sallar magrib suka shigo gidan gonar, ko waya basuyi ba balle suce aje airport a d’aukesu dan dama tafiyar ‘yar solo ce. Motar haya suka yo shata suka taho garin. Meema sai mita take tana fad’in yau sai tayi ciwon jiki dan ita Allah ya gani bata tab’a shiga motar haya ba sai yau.. Safeenah tai gajeren tsaki tace “Toh wai da kika damen da mita nid’in na saba shiga ne.. Ni bama wannan ba Allah yasa muna shiga Inne tace  duk mu tattara koma gobe gobe.. I’m sure zata goyi bayana wann karon.”


Meema ta danna mata harara cikeda takaici tace “Malama returning flight zuwa Abuja sai an shiga next week.. Zamuyi weekend mu kwashe kwanaki  kawai kiyi shirin zaman garin nan..” Tai tsuka tana kuma jan suitcase d’inta “Ni wllhi Adda Feenah kin gama dani dan banyi niyyan zuwa ba ga jaraban wannan masifaffiyar tsohuwar na jiranmu..”


Feenah tabi bayanta cikin sauri tana kiran sunanta tana jan nata jakan da k’yar gashi babu kowa da alama ma’aikatan dik sun tafi sallah da alama. Safeenah Ta kuma sakin tsuka tana jan jakan.


A daidai mashigar da zai sadaka da k’ofar babban parlorn Ajidde dake rik’eda bak’in ruwa mai kaman black ink cikin kwano sukai karo itada Safeenah wacce shigowarta kenan tana kokawa da Jakarta, ai kuwa bak’in ruwan nan bai shek’e ko Ina ba Sai fuskar Safeenah da yake fari tas Wanda lokaci guda bak’in ruwan nan ya maidasa bak’ik’irin kaman tayi wanka da ruwan da aka wanke bayan tukunya..


Meema dake gefe baki sake take duban fuskar Safeenah da yai bak’ik’irin yayinda Ajidde ma ta saki baki da hanci rik’e da kwanon tana duban matar data wanke mata fuska da maganin Kyallu.



“Wow.! What a nice welcome gift you’ve received Addah Feenah.” Meema tace tana mai tintsirewa da dariya.


Ajidde kaw tuni Ta arce a guje tana fad’in “Kai wllhi Allah bazanyi dariya ni kad’ai ba.. Kuran tashe dole yaga wannan.”


Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsawa da tsananin mamaki take duban yarinyar kafin ta maidoda dubanta ga Meema da ke ta faman k’yalk’yala dariya harda ciro waya tana fad’in Ta tsaya tai mata video..



A daidai exit d’in da sukai zasu had’u ta taddasa, da alaman isowar Ta yake jira..

Musaddiq na hangota ya kuma duba agogon dake d’aure hannunsa yana girgiza kai “Ya na ganki haka.. Ina maganin..?”


Ajidde bata amsa sa ba sai dariya da take har tana zama a k’asa.


Takaici ya cika Musaddiq jin har an kusa sallamewa a masallaci “Ke Crazy Dove ki tashi kimin magana kafin su fito daga masallaci su samemu a nan.. Ina maganin yake..?” 


Ta kuma tintsirewa da dariya tana fad’in “Ka tab’a ganin dodanniya..?”


Mu Sadiq ya girgiza kai yace “Dodanniya kuma..”


Ajidde ta mik’e tana fad’in “Kai sauri ka biyoni kar ta b’ace..”


Da tsananin mamaki Musaddiq ke dubanta, sai kuma ya girgiza kai yana furta “Crazy Dove, you truly are crazy..” Lokaci guda ya take mata baya.


No comments

Powered by Blogger.