Gidan Aro 19



*19*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*





Cikin tsananin b’acin rai Safeenah da har lokacin ta kasa koda motsa ‘yar yatsar k’afarta take duban Meema da har lokacin dariya take tana mata video sa waya “Meema you know I’m a very sensitive person, and I don’t take things lightly...Don’t make me take it out on you..!” Tai maganar tana bud’e hannayenta cikin tsananin b’acin rai da huci.


Daidai lokacin Ajidde ta k’araso hannu biyu aka tana dariya. Cikin tsananin mamaki Safeenah Ta karkato tana duban mahaukaciyar yarinyar wacce tai mata wannan aika aikan sannan bama tasan ta aikata ba balle Tai tinanin bada hak’uri waima dariyarta take tana duban fuskar tata..


Wani irin wawan birki Musaddiq yai ganin wacce Ajidde ta wanke da ruwan maganin nan ba kowa bace face Safeenah, dikda bai ganeta daga fari ba har saida yaji tana fad’in Meema ta damk’o mata shegiyar mai aikin nan taci uwarta ta koya mata manners. 


Baki sake Musaddiq yake duban Safeenah da sam baisan da zuwansu ba yana duban yanda Ajidde ke dariya kaman sabuwar Kamu.


Meema ta yatsina fuska tace “Ni ce zan tab’a jikin wnn mahaukaciyar Adda Feenah.. Chabd’i God forbid.! You know I’ve a very sensitive skin. I might easily catch infection.. Kawai ki rungumi k’addara kizo muje ki wanke.


Ana haka Hindu ta k’araso jin hayaniya daga parlorn.



Musaddiq ya dafe goshinsa kad’an yana jinjina rashin hankalin Ajidde wacce taima Meema gwalo tana rataye jakarta tana fad’in “Ni kuma sai na tsaya ki kamani. Tab lallai kina ruwa.. Ko banza naci dariya wllhi.. Allah bamu Alheri dodanniya.” Tana ida fad’in haka Ta kuma arcowa a guje tana ma Meema gwalo.


Daga Meema har Safeenah da tsananin mamaki suka bita da kallo yanzu kam sun gama yarda Tanada tab’in hankali.



Saida tazo daidai yanda Musaddiq ke lab’e ya janyo jakanta da k’arfi ta dawo da baya.


Ihu ta saki tana fad’in “Dan Allah Dodanniya kiyi hak’uri.” Dik a zatonta Safeenah ce ta biyota.


“Ke Crazy Dove.!” Musaddiq ya fad’i cikin daka tsawa.


Jin Musaddiq ne ya sanyata sauk’e ajiyan zuciya ta bud’e idanu tana fad’in “Wllhi kallo ya shige ka.. Kaga..”


Katseta yai da fad’in “Waike lafiyarki kuwa.. Kinsan abinda kika aikata kuwa.. Yanzu idan ‘yanmatan nan suka biyoki suka lakad’a miki duka waye zai ceceki..?”


Ta sakar masa murmushi tana kashe masa idanu guda, abindake mugun basa dariya idan tai. Lokaci guda tace “Toh ba gaka nan ba.. Na San zaka tsare min kaman yanda ka tsare min sanda mugun abokin nan Naka mai bindiga ya biyoni wanda baya dariyar nan.. Mutum kullum kaman shed’an kasan d’azu ma na gansa ya fito wancan k’ofar fuskar nan babu annuri..”


Ya tsareta da idanu kafin yana mamakin halin Ajidde, lokaci guda ya girgiza kai yace “Watau sabida ina nan shine kike taro masifa ki gudu kice zan tsare miki koh.. Toh randa banzo aiki ba fah..”


“Zan jiraka har kazo ai..” Ta bashi amsa kai tsaye kayanta.


D’an girgiza kai yai yace “Kina jina idan baki daina shiga abinda babu ruwanki ba wataran zaki taro abinda yafi k’arfinmu daga ni har ke..” Yai maganar cikin yanayin b’acin rai.


Ta d’an dubesa da kulawa wannan karon “Kayi fushi ne..?”


“Banyi ba.. Inaso kimin alk’awari gobe zaki bama matar nan da kika b’ata mata  fuska hak’uri.” 


Tsuke fuska tai ba tareda tace komai ba.


Musaddiq ya tsareta da idanu babu walwala wann karon. 


“Tau naji ince Dodanniya.. Anji anji.. Anji d’in.. Za’a  bata hak’urin.. Hankalinka ya kwanta.”


Tsareta da idanu yai yana duban yanda take maganar tana duban wani b’angare. Harga Allah mugun nishad’i take saka sa, shirmenta da shiriritar ta mugun nishad’i yake saka Sa.


Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro kud’ad’en ya mik’a mata ”Oya take this..”


Bata karb’a ba sai dubansa da take a kaikaice alamun tana fushi dashi yace sai ta bawa Dodanniyar cen hak’uri wanda bama tasan ‘yanuwansa bane.


“Karb’a mana ya kuma fad’i yana dubanta.. Ko sai na baki hak’uri nima..?”


Wannan karon murmushi tai tana wani kad’a kai dan sosai take jin dad’in yanda yake damuwa da damuwarta abu ne da ba’a tab’a nuna mata ba a rayuwarta sai akansa tasan hakan. 


Ta girgiza masa kai tace “Ai yau Inna Kyallu batace na sato mata wani abu ba, wanda ka bani jiya kace na bata kuma na bata..”


Tsayuwarsa ya gyara yace “Ke baki gane ba, Idan kika kai mata a jere  kwana biyu a matsayin sato mata kike zata rage duk wasu abubuwan da take miki tinda imaninta kenan..”


Ajidde ta tsaresa da idanu tana dubansa “Toh randa bakadashi fah..?”


“Kar ki damu badai ina aiki ba.. Zan tara mana na baki ki kai mata..”


Ta murmusa kad’an tana mai rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shima kafeta da idanu yai yana mai sakin murmushin. Harga Allah Ajidde na d’aya daga cikin dalilin da yasa garin ke masa dad’i baya fatan abinda zaisa ya daina ganinta a gidan gonar.. Zaiyi dik yanda zai ya taimaka mata Ta daina mummunan d’abi’a na sata da Innarta ke koya mata koda hakan na nufin yayi aikin k’arfi ne ya samu Kud’i ya bata Ta fanshi kanta wajen Kyallu.


“Maza Jeki kar dare yayi.” Ya fad’i yana dubanta.


Ta jinjina masa kai a hankali kafin tai masa sallama. Yana nan tsaye yana dubanta tana tafiya tana cilla Jakarta. Murmushi saman fuskarsa. Lokaci guda itama take juyowa tana sakar masa murmushi, har saida Musaddiq yaga shigewarta kafin ya nufi masallacin dake nan cikin Gidan Gonar da zummar gabatar da nasa sallar dan already sun sallame.


**


A can cikin gida kaw Inne ce ta tsaresu tanai masu d’add’aya dan babu wanda yasan da zuwansu sai ganinsu akai kaman sauk’an aradu dikda cewa Meema tace da sanin  Mommy da Daddy suka zo.


Inne tai k’wafa tana mai kuma furta “Idan da sanin iyayenku kuka taho ke Safeenah mijinki yasan kina tafe ne.. Ko kuma saran da kuka d’auko kenan, shi yazo ke kin biyosa.. Zai shigo ne ya sameni, dukkanku Ina dai dai daku nikam..”


Meema ta mik’e tana fad’in “Nidai na gaji d’aki nake son zuwa na huta.. And I’m starving already.. Hindu..! Hindu.. An gyara mana d’akin..”


Inne da Ta saki baki tana duban Meema dak’uwa tai mata tana fad’in “Kinci gidanku.. Baza’a gyara maku d’akin ba, idan baku da hannaye kuna iya kwanciya a haka.” Ta dubi Hindu da k’arasowarta kenan tana fad’in “Ummilo tana can tana gyarawa..”

Lokaci guda Inne tace kije kice mata ta bar d’akin mata ne, zasu gyara da kansu..”


Baki sake Meema ke dubanta kaman zata kurma ihu “Haba Inne Haba Inne.. Dan Allah fah we just arrived here, and I’m pretty tired wllhi Ko hanuna ban iya d’agawa.. Please mana Inne, I can’t do any house chores wllhi..”


“Ni kike ce ma kin gaji baki iya ba idan ban tashi na jefaki cikin turmi na dakaki ba, sangartacciyar banza a rasa da wa za’a mun takwara sai ke.. Matsa min a nan kafin na tashi na daddakeki.. Kuna mata kuce komai sai an maku saikace ba gidan wani zaku ba.. Ba dai kunzo nan ba, toh har girki sai kunyi ni bazan lamunci goyon sangarci da iyayenku sukai maku ba.. Kun sanni sarai ba a nan zakuyi iya shegenku ba..”


Meema ta shige tana bud’e murya kaman mai kuka  “Wayyo Wayyo na shiga uku.. Wllhi this is all your fault Adda Feenah.. I shouldn’t have followed you here.. Wayyo Allah na..” Haka Meema ta dingayi kaman wacce ake bugunta, ta shige tana tafiya tana jefa k’afafu tana fad’in dik Safeena ce ta jawo mata.


Ana haka Musaddiq yai sallama ya shigo.


Kallo d’aya yaima  Inne ya  fahimci a d’ane take yau ko ba’ace ba su Safeenah suka kunnata.. Ya nufo  parlorn yanda Inne ke zaune tana girgiza k’afafu.


Musaddiq da ya hango Safeenah zaune da bak’in fuska tana yatsina fuska dariya ya soma yana fad’in “OMG! Who do we have here.. Hey yaushe kikazo..? And  what’s that on face..?” Ya k’arashe yana kuma k’unshe dariyarsa.


Harara Feenah ta watsa masa “Kaga babu ruwanka dani.. Mind your own business..”


Musaddiq ya kame bakinsa yana fad’in “Allah baki hak’uri Dodanniya..”


“What..? Mai kace.. What did you just call me..?”


“Abinda kunnenki yaji..” Ya bata amsa kai tsaye.


“Inne Kinga kice ya fita hark’ata..” Safeenah tace tana kuma turo baki.


“Ke rufewa mutane baki ank’i ace d’in..” Sakaryar banza.


Musaddiq ya k’unshe dariyarsa yana k’ok’arin k’arasowa kusan Inne dan yanzu har wani shiri ne na musamman ya shiga tsakanin Musaddiq da Innen tinda ya fara watsar da rayuwarsa ta baya.



“Gidado na Zo ka shige abinka kaji fita sha’aninta..” Inne tace tana duban Musaddiq d’in.


“Toh Inne na..” Ya fad’i yana gwalo ma Safeenah  had’ida kashe mata idanu.


K’wafa Safeenah tai ba tareda tace komai ba dan harga Allah alla alla take Masoyinta Mu’azzam ya shigo Ta gansa.

Aiko bata ida tinanin ba ta hangosa yana tafe ya nufo k’ofar parlorn, yana sanye cikin k’anan kaya dark blue polo shirt da faded pants. Idanunsa na kan wayar salularsa dake hannunsa, hasken k’wan wutan manya manyan wutan lank’arki da suka k’awata gaban gidan sun haske masa fuska tarau, gani tai kaman ma zuwansa nan ya k’ara haske da kyau ne babu damuwar CID akansa babu komai.. Ta saki murmushi a hankali dan tama mance da abinda ke fuskarta. Idanunta akansa tana sakin murmushi har yai sallama ya shigo parlorn.

, idanunta naga masoyinta wanda shima ita yake duba cikeda mamakin bak’in dake fuskarta dan sam bai fahimci wacece ke zaune wajen ba har saida ta bud’e murya tace “My Halal.!”


“Safeenah.!” Ya furta a hankali yana mai kuma shigowa parlorn mamaki fal fuskarsa, har lokacin idanunsa na kanta. Bama mamakin bak’in fuskar nata yake ba, mamaki yake yaushe Safeenah tazo.


Inne ce takatsesu da fad’in “Yauwa k’araso dama kai nake jira.. Kazo ka sanar dani idan kai ka bata lasisin Ta dinga gantali saman kwalta da sararin samaniya Ita ba tsuntsuwa ba, tana a matsayin Amarya wacce ko tarewa batai ba.. Ai Iyayen naku ma basuda hankali da suka zuba maku idanu haka.. Toh ni bazan lamunci wannan asaranci ba.. Kafin Dangi su fara k’anan magana tinda shi Marwan ya zuba maku idanu kuyi yanda kuke so da rayuwarku ni zan masu abinda suka kasa.. Zaku tare a nan. Idan yaso a miki sabon jere a nan..Tinda abin naku ya zama haka sai a gyara maku d’aya b’angaren ki tare a nan.” Ta k’arashe tana duban Safeenah  da ta saki baki tana jin Innen Wai zasu tare a nan.


Safeenah zatai magana Inne tace “Rufe mun baki.. Ba shawarinki nake nema ba.. Bazaku bar mun abun fad’i a dangi ba.. Na riga na gama magana.” Ta k’arashe tana mai mik’ewa da zummar barin parlorn.

Sai kuma ta juyo ta dubi Safeenah tace “Ke kuma Ki tashi kije ki wanke wann bak’ar fuskar taki kafin Ki razani mijin naki da ita..”


Sai sannan Safeenah ta tina da bak’in dake fuskarta, tai saurin Kai hannu zata tab’a sai kuma ta kasa ta shiga muryar kuka tana fad’in “Oh my gosh.. Eww.. I can’t touch it, It stinks.. My Halal please help me get rid of it.. Wllhi I can’t touch it..” Yanda take da fuska da hannu Kai kace kashi aka watsa mata.


“Meye a fuskarki..?” Ya tambaya yana dubanta.


“I don’t know.. Wllhi wata mahaukaciya ce ta watsa min.. Inne tace wai magani take bawa Mamy.. My Halal wllhi Mahaukaciya ce ka koreta.. I don’t trust her around Mamy..” Ta k’arashe tana kuma yatsina fuska da hannu.


“Biyoni..” Ya fad’i yana mik’ewa tsaye. Babu musu Safeenah ta biyo bayansa..


D’akinsa suka shige ya maida k’ofan ya rufe. Ya nuna mata hanyar bathroom “Shige muje..”


Ta d’ago tana dubansa da mamaki sai kuma ta shige sim sim.. Mu’azzam ya take mata baya.


Washbowl suka nufa yace ta saka fuskarta, tanaji ya d’auko sabulu yana wanke mata.


Yana ida wanke mata ta d’ago fuskarta tana duban mirror saidai to her surprise Mu’azzam ta hanga ta cikin mirror d’in yana rage tufafin jikinsa.. K’akk’arfan suffarsa da yasha training irin na Force ya bayyana. Ta zaro ido a tsorace had’ida juyowa tana dubansa, tana ganin ya soma nufota Ta soma k’ok’arin komawa da baya..

Fincikota yai ta fad’o jikinsa hakan yai daidai da tab’a makunnin shower dake kansu ai kuwa ruwa ya soma zubowa kansu. Tana jin hannunsa saman zip d’in rigarta yana k’ok’arin zugewa.. Har lokacin ta kasa janye idanunta daga duban fuskarsa da ruwa ya wanke tas Wanda sam babu walwala..


Zuciyar Safeenah yaci gaba da tsinkewa.. Cikin sauri kaman wacce aka zabura, tamkar wacce ta tina wani abu tai saurin rik’e hannun nasa ta hanasa tana mai girgiza masa kai ga idanunta da sukai rau rau.


Wani irin duba yake mata, lokaci guda ya kamo hab’arta had’ida d’ago kanta kad’an ruwan na zubo mata a fuska. Tsoro da tsananin firgici ya hango saman fuskar tata wanda dik a nasa tinanin tsoran kasancewa dashi take a matsayinta na budurwa sabuwar aure da bata tab’a sanin wani d’a namiji ba..


“Why.? Ba abinda kike so bane..? Ba abinda kike bibiyata sabida shi ba kenan.. Well na shirya baki yanzu a nan idan har zaki k’yaleni na gama binciken mutuwar ‘yaruwata da nake in peace ba tareda Kinyi causing mun distraction ba.. Fine zan baki sai ki daina bibiyata har na natsu na ida binciken da nake..”


Lokaci guda hawaye ya soma zarya saman fuskar Feenah.. Ta shiga girgiza kai hawaye na gangaro mata “No ni dai ba haka bane.. Dama dama kawai I was missing you ne.. That’s why I followed you here..” Tai maganar hawaye gauraye da ruwa saman fuskrta.


Ya tsareta da idanu yanda take shivering.. Janyota jikinsa ya kuma dikda tsananin rawa da jikin nata keyi, saitin kunnenta yake rad’a mata “Really..? Did you miss me that much..” Ya fad’i yana mata wasu salo irin nasa wanda tuni sun kashe mata jiki.. Lokaci guda yaci gaba da furta “Dama baki shirya ba kiketa bibiyata..?” Tai saurin girgiza masa kai tana hawaye.. Zatai magana ya rufe bakinta da nasa. K’arar wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ya dawo da hankulansu.. Yai saurin zaro wayar yana duba mai kira, ba kowa bane face abokinsa kuma colleague d’insa Assad. Yai saurin kashe ruwan kafin ya shiga janyo Feenah yana fad’in “Zo ki fice..”


Ta dubesa da mamaki yanda yake fuzgota saikace ba shine ya nuna San kasancewa da Ita yanzu yanzu ba “Mu’azzam a haka zan fice.. Duba fah ka gani from head to toe a jik’e nake fah..”


Har saida suka k’araso k’ofa kafin ya turata ya janyo k’ofar ya rufe ba tareda yace mata komai ba.. Baki sake Feenah ke dubansa da tsananin mamaki.


Yana rufe k’ofar ya d’aga wayar Assad “Hey Officer, hope all is well with you..” Mu’azzam yace yana mai tsane jikinsa da towel.

Saida suka gaisa kafin Mu’azzam d’in ke tambayarsa “How are things at the CID.. Mai da mai kukai discovering so far..?”


Assad ya d’anyi gajeren tsaki yace “Things are getting tougher here, tinda ka tafi.. And Chief Jaja ya bud’e mana wuta mu kawo Danger within 2 days... Jiya ya mik’a team report d’inmu office d’in Chief Superintendent a General meeting d’in da akai, and babu wani progress har yanzu and  he was even insisting bamuda case against Danger.. Saifa da nai presenting final report d’inmu ne ya tabbata Danger’s involved toh shine ya hura mana wuta mu kawo masa Danger yanda ya shiga ya fita..Ga dukkan alamu so yake case d’in ta lalace a haka ba tareda an sami wani improvement ba.. And Danger is no where to be found.. Dik wani hideout da muke tinanin zamu samesa bamu samesa ba, duk wasu masu criminal records da muke tunanin zasuyi linking d’inmu to Danger still babu wani haske har yanzu..”


Fuzar da huci Mu’azzam yai yana tura yatsunsa a sumarsa da suke wet.. “That scumbag I’m pretty sure he’s up to no good again.. Babu wanda ya isa ya rufe case d’in matuk’a ina numfashi.. Sai mun Kai har k’arshe yana so ko baya so.. Assad yarinyar nan itace kad’ai key d’inmu.. Inada tabbacin Babanta kashesa akai ba ordinary accident bane da ya saba aukuwa.. They’re after her family, I’m pretty sure bazasu k’yalesu haka nan ba.. Ya kamata muyi monitoring duk wani abinda ahalinta ke ciki.. Sannan Kai zaka fara tinda ni bana nan.. Go there, find out everything about them.. Dik information d’in da ka samu nasan zai ma investigation d’inmu amfani.”


Assad ya jinjina kai kaman yana ganinsa “Copy Sir..”

Lokaci guda ya k’arada “Baka tambayeni mutuniyar ka Maleeka ba.. Ita kaw kullum cikin  missing d’inka take.. Tana counting days har zuwa randa zakai Reporting back to work.”


Gajeren tsaki Mu’azzam yai yace “Banida lokacinku daga kai har ita..”


Assad ya tintsire da dariya dan dama tsokanan abokin nasa yai niyya.


Sallama sukai kafin Mu’azzam ya zauna saman gado rik’e da wayar yana fuzar da fuci.. Zama bai gansa ba, yasan da biyu Chief yasa aka dakatar dashi dan ya samu sauk’in cimma burinsa cikin sati biyun idan baya nan, yasan muddin yana nan sai yanda k’arfinsa ya k’are bazai tab’a iya stopping d’insa ba.. Fuzar da fuci ya kuma yana jin zuciyarsa na masa zafi.


A b’angaren Safeenah kaw kafin ta isa d’aki wayarta ce dake cikin jakarta tai ruri, Meema da fitowarta kenan daga shower taji sautin waya na tashi daga cikin jakan Feenah. Kaman bazata d’aga ba dan tasan bazai wuce Mommy ba k’ila sunyi waya da Inne. Bata shirya ma fad’an Mommy ba. Amma jin wayar ta k’ara ruri ya sanyata k’arasawa jikin jakan ta d’ago wayar tana dubawa. Lamba ce Babu suna..


Meema dai samun kanta tai tana mai sliding kiran da ake.. Lokaci guda ta k’ara a kunnenta ba tareda tace komai ba.


Daga d’aya b’angaren Barr Ameer ya murmusa yace “Kin zaci zaki gudu mun ne Safeenah.. Dik yanda kikaje sai na biki.. Bazan tab’a barinki ma D’ansandan nan ba Safeenah.. You are mine.. Ked’in tawa ce ni Barr Ameer.!”


D’if Meema ta katse kiran tana kuma duban wayar k’irjinta na wani irin bugawa. “Barr Ameer..?!” Ta nanata a hankali.


Daidai lokacin Safeenah ta turo k’ofa ta shigo da jik’akk’un kayanta sai rawar d’ari take.

Da mamaki take duban Meema da tai tsaye rik’eda wayarta. Ta soma saurin nufo Meemar tana fad’in “Meye kikai wani tsaye a wajen sororo haka.. And why are you holding my phone.. bani kayata..” 


Saidai kafin ta mik’awa Feenah wayar saida ta tabbata ta goge kiran.. Feenah ta fuzge wayarta tana aikawa Meemar mugun kallo “Waye ya kira..?”


“Babu mana.. Naji kaman wayar tayi ringing ne nazo zan d’auka, nayi tinanin Mommy ke kira Kinsan tawa babu charge.. Nasan dole zata nemu..”

Meema tace tana mai bud’e suitcase d’inta.


Tsaki Feenah tai tana mai neman towel take fad’in “Sabida kin mata sallama sanda zamu taho Ko..”


Meema ta d’an tab’e baki tana duban ‘yaruwar tata. Sai sannan ta kula da jik’an dake jikin Feenar..


“Addah Feenah.. Ya haka..? Ya na ganki a jik’e..?”


Tsaki Safeenah tai tana mai nufa hanyar bathroom..


Dariya Meema Ta soma tana fad’in “Kardai horon watsa ruwa yai miki a sanyin daminar nan.. Amma wannan miji naki anyi bak’in mugu wllhi duk wani salon mugunta ya Sani.. Koda yake ba laifinsa bane dama D’ansanda ne ya karanci sharri Da mugunta.. Allah ya cecen wann karon ba’a had’a dani ba..”


Ko amsata Safeenah batai ba ta shige toilet kayanta.

**


Washe gari sassafe Safeenah ta nufi d’akin Mu’azzam, dan tasan ya fice sallar asuba. Tana shiga ta fad’a kan gadonsa ta lume cikin bargo ta lumshe idanunta kaman mai bacci. Tasan babu yanda za’ai idan ya dawo sallar asuba ya samu tana bacci d’akinsa ya koreta dole ya k’yaleta su k’arasa kwanan tare. 


Aiko koda ya dawo yasha mamakin ganin Feenah na bacci saman gadonsa, bai tasheta d’in ba ya kwanta daga can gefenta dan jiya bai wani samu bacci ba kusan kwana yai yana tinani tin bayan wayar da Assad yai masa yanda zai b’ullowa al’amarin Danger da Chief Jaja wanda idan yayi wasa zai iya rasa case d’in mutuwar k’anwarsa da ya d’aukarwa mahaifiyarsa alk’awarin kafin ta farka daga wannan jinya nata da izinin Allah sai ya gano waye ya kashe mata d’iyarta. Hakan yasa tuni bacci yai awon gaba dashi.


Safeenah tanajin alamun bacci yayi gaba dashi ta mirgino ta dawo jikinsa, zuciyarta fari k’al ta mak’ale cikin jikin mijinta tana shak’ar k’amshinsa dake rikitata.. Baccin ne itama yai gaba da ita.. Ba ita ta farka ba sai wajajen k’arfe bak’wai da rabi na safe sabida iska da aka soma sosai alamun za’ai ruwa hadari ya rufe sama gaba d’aya.. Ta saki murmushi tana duban yanda Mu’azzam ya rik’eta sosai cikin jikinsa alamun shi kansa yana enjoying baccin nasa. Ta k’ura ma kyakkyawan fuskarsa idanu tin daga sumarsa da suke kwance luf har zuwa idanunsa da suma suke a rufe, ta gangaro da idanunta tana duban hancinsa zuwa lips d’insa. 


Iskan da akeyi shi ya bud’e k’ofar d’akin.. Ajidde da Ta biyo corridor d’in dan zuwanta kenan, nan tazo zata shige k’ofar d’akin Mu’azzam dan kafin ka isa d’akin mahaifiyarsa sai ka wuce wasu k’ofofi ciki harda d’akin Mu’azzam.. Da mamaki take hangan k’ofar a bud’e ta tina sanda ta shiga zata masa sata ya kusa kamata.. Ta soma sauri tana fad’i cikin zuciyarta bari tai sauri ta shige k’ofar d’akin kafin ta hango wannan jakar tasa.. Tana tafe bata fasa lek’en d’akin ba aiko nan ta hango matar nan ta jiya data watsa mata ruwan magani zaune gefensa saman gado tana shafa sumarsa zuwa fuskarsa.. Ajidde ta saki baki da hanci tana duban ikon Allah.. Ji tai bakinta na furta “Kaga ‘yaniska.. Toh asirinku ya tonu tinda kuka mance k’ofa a bud’e..” Bata ida shan mamaki ba saida taga matar nan ta kifa fuskarta kaman dai sumbatar juna suke.. Jikin Ajidde ya d’auki rawa babu shiri ta kwasa a guje ta nufo parlor.. 


Tana k’arasowa tsakiyar parlorn ta saki wani irin azabebben k’ara wanda idan akwai masu bacci da basu tashi ba ma tabbas sai Sun tashi.. Ihu Ajidde take tana tsalle tsakiyar parlorn tana fad’in ta shiga uku.. Inne dasu Hindu dake kitchen suna karin kummalo Inne na monitoring nasu kaman ko Yaushe, babu shiri suka nufo parlorn.. 


Mu’azzam cikin bacci shima yaji ihun har tsakar kansa.. Ya mik’e yaga Feenah tareda shi itama da alama ta firgita da ihun da ake.. Cikin sauri ya mik’e yana janyo jallabiyar sa yana fad’in “Mamy.. Mamy na.. Something happened to Mamy..” Abinda yake fad’i kenan yana k’ok’arin zira rigar dan itace maras lafiya a gidan dole kowa yai tunanin jikinta ne ya tashi koma aka rasata gaba d’aya. Ko tsaya bi takan Feenah dake tambayarsa Ina zaije bai ba ya matsarta gefe kad’an ya nufo yanda yake jiyo ihun  cikin sauri.. Tuni Feenah ma ta take masa baya tana mai rufa siririn rigar baccin nata da na saman. 


Musaddiq ma dake bacci a nasa d’akin babu shiri shima ya fito a birkice..


Aunty Shemau da tayo rakiya wa Uncle Salman zai wuce Factory dan wataran da wuri yake zuwa, nan Suma suka soma jiyo ihu daga sashen Inne. Babu shiri suka nufo sashen suma duk a birkice dan a tinanin Shemau Nuratu ce Allah ya mata cikawa.


Harta Meema dake ta faman susa ta kasa bacci dan dama tanada allergy irin na daminan nan balle tazo gidan Gona ga dabbobi ga shuke shuke tuni allergy d’inta ya tashi.. Ta d’an samu baccin kenan itama ta soma jiyo ihun.. Ta fito rai b’ace tana soshe soshe..


Gaba d’aya aka hallara parlor ana duban Ajidde dake ihu tana tsalle idanunta a rintse.


Musaddiq kam daga nesa yaja ya tsaya  yana jiran yaji ruwan da Ajidde ta b’allo wannan karon.


No comments

Powered by Blogger.