Gidan Aro 25
25*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali take k’ok’arin bud’e idanunta da suka mata nauyi, tas ta Ware idanun nata tana duban yanda take. Wani had’add’en d’aki ne da ya tsaru iyaka tsaruwa. Tsoro ya kuma bayyana saman fuskarta, itadai tasan a wani d’aki mai kaman store ya barta wanda Tim wani haushin kare dataji bata kuma sanin meke wakana ba. Zumbur Sadiya ta mik’e tana duban d’akin.. Kallo guda zakai ma d’akin ka fahimci cewa d’akin Amarya ce. Ta saka hannayenta biyu tana kuma mutsuke idanunta ganinta da tai kwance saman gado har an rufeta da duvet. Kalle kalle ta soma tana kuma Shafa gadon dan dai ta tabbatar da gaske ne.. Toh ya akai tabar wancan d’akin yaushe aka kawota nan..? Tambayoyi ne da batada amsoshin su.. Gefen bedside ta hango hoton wata mata kyakkyawa an aje cikin k’aramar frame. Ta matso tana duban Matar.. Gani tai kaman ta tab’a ganin fuskar matar amma saidai sabida heavy makeup dake fuskar matar bata iya ganeta ba.. Bata kuma gane ina tasanta ba. Hasken rana data hango ya tabbatar mata gari ya waye. Tsalle tai ta diro daga saman gadon tana kuma juye juye zuciyarta naci gaba da yankewa “A ina nake..?!” Ta tambayi kanta cikeda firgici.
Sallar asuba da batayi bane ta soma tinawa.. Babu shiri ta nufi wata k’ofa dake nan cikin d’akin wanda takeda tabbacin bathroom ne. Aiko tana tab’a k’ofar ya bud’e, kaman yanda take zato bathroom d’in ne komai na buk’ata akwai a ciki sannan komai Sabo ke sealed ba’a bud’e ba.. Harta toothpaste da toothbrush dik sabbi ne jere a wajen. Ta tab’e baki kad’an ba tareda tace komai ba.. Ita a halin yanzu babu abinda take so face ta ganta a gida.. A gurguje tai alwala ta fito tana tinani ina zata kalla ya zamto mata alk’ibla.. Bata ida tinanin ba ta hangi k’aton darduman turkey an shimfid’a ready to pray.. A ranta tace k’ila mata mai d’akin ne ta shimfid’a.. Sauri sauri ta isa saman darduman ta tada sallah.. Koda ta idar mik’ewa Tai tana kuma bin d’akin da kallo wanda ya tsaru iyaka tsaruwa, harta wardrobe d’in da yake transparent tana iya hango kaya jere cikinsa. Ta d’an tab’e baki a hankali kafin ta nufi k’ofa tana tinanin toh ina ne nan..
A hankali ta tab’a k’ofar d’akin ta bud’e.. Nan taga corridor ne madaidaici da k’ofofin da bazasu gaza guda uku ba. Tana tafe ta hango stirs wanda zai sauk’arta k’asa kenan. Nan take ta nufo staircase d’in zuciyarta bai daina yankewa ba. D’aga idonta da zatai ta hango wani k’aton hoto da akayisa in full kaman ka kira mutanen ciki suzo.. Mu’azzam ne da wannan Matar da taga hotonta a d’aki.
Take ta tina walak’acin da ya mata a daren jiya. Ganin fuskar tasa take kaman wani bak’in kumurci. “Rascal..!” Ta fad’i a hankali tana aika masa mugun kallo dukda kuwa cewa Sunyi kyau sosai kaman ka sure ka gudu, ko ba’a ce ba hoton ran aurensu ne dan sunyi shiga ne irinta Amarya da ango. Dikda manyan kayane a jikinsa tsaf ta ganesa, sky blue shadda da akai mata d’inkin babbar riga mai gajeren hannu daga ciki sai hular dake kansa navy blue zanna bukar mai k’anan zane tasha tangaran sai k’yalli take. k’afarsa rufe cikin bak’ak’en covers.. Yayi kyau sosai dan ba k’aramin karb’ansa manyan kayan sukai ba. Ita kaw matar bridal gown ne jikinta all white tayi kyau sosai itama fuskarta cikeda annuri wanda da gani zaka fahimci tana tsananin k’aunar mijin nata..
A fili Sadiya tace “Bakiyi dacen miji ba.”
Sadiya ta k’ura masu idanu tana tinani Wato gidansa ne kenan nan.. Toh ina matar tasa..? Rashin samo amsar da batai ba ya sanyata tab’e baki a hankali tana mai kuma dubansa cikin hoton, dan a hotonma fuskar nan tass babu wani annuri.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta furta a fili “Mugun banza azzalumi.!” Tai maganar tana dungurinsa cikin hoton.
Mu’azzam dake zaune dining area dik yana kallonta ta cikin k’atoton mirror d’in da aka k’awata dining area d’in dashi.
Yi yai kaman bai ganta ba kuma baiji mai take cewa ba, yaci gaba da abinda yake yana kallon yanda take sakin huci tana dungurin hotonsa tana fad’in mugun banza
Yai murmushi yana dubanta ta mirror, saida yai sipping tea d’in sau biyu kafin ya bud’e murya yace “Welcome to GIDAN ARO.. Where everything here doesn’t belong to you..!”
Sadiya ta juyo a razane dan sam batasan da mutum a wajen ba.. Mu’azzam ya taso yana takowa a hankali har dai ya k’araso kusanta.. Hannayensa sakale cikin aljihun jeans d’insa yake furta “Take your eyes off my photo, I’m not the rich husband you’re looking for..!” Yai maganar yana mai mata nuni da hotonsu shida Safeenah da idanunsa.
Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Correction Mr Inspector, bani na kawo kaina nan ba, as a matter of fact kidnapping d’ina akai.. Zan fi kowa Farin ciki idan ka maidani yanda ka d’aukoni.!”
Ta k’arashe cikin tsimewa itama.
Ya murmusa kad’an da gefen bakinsa yana mai kuma takowa gabanta.. Lokaci guda ya tsime kaman dai bashine mai murmushin ba. Nan yaci gaba da furta “If you cooperate with me and do exactly as I say zaki koma yanda kika fito, because I don’t intend to keep you here for good.. Like I told you gidan nan tamkar GIDAN ARO yake a wajenki.. Kinsan ance ba’a baje Koli a a GIDAN ARO.. Toh kar kiyi gangancin baje naki kolin domin dik gidan da akace na aro ne any moment any time za’a iya sallamanka without notice..”
Ya k’araso jikin hoton yana mata nuni da Safeenah “Kin ganta nan, she’s the lady of this house.. Aro aka baki na wutin gadi..”
“Ban nema ba balle a bani Aro.. So don’t delude yourself.!”
Da mamaki yake dubanta, dik ajiyeta a wannan store d’in da yayi jiya a matsayin warning ashe bai shiga kanta ba. Ya kula bakinta sam bai mutuwa. Ya tina yanda daren jiya baiyi bacci ba har saida ya dawo ya d’auketa cikin hannunsa ya kaita d’aki ya kwantarta ya tabbata ta samu sound sleep. Da yasan wannan bakin tsiwar nata bazai mutu ba da barinta yai a wannan d’akin ta Kwana ko zatafi shiga hankalinta.
Takowa kusanta yake tana jada baya, bai tsaya ba har saida ya k’araso kusanta sosai ya tabbata bata da sauran wajen gudu kafin yai mata rumfa da kansa ya bud’e duka hannayensa ya tareta dasu yanda ko k’wakk’waran motsi bazata iya ba “Mai Kikace.. Maimaita abinda kika fad’a.!”
Kasa magana tai Sai k’walla dake k’ok’arin ciko idanunta.
Dubanta yake tin daga fuskarta mai cikeda rauni gauraye da tsoro kafin ya murmusa kad’an yace
“Be careful how you speak to me.!” Yai maganar yana duban d’an bakinta wanda kaman ba daga nan maganganun ke fitowa ba.
Saida ya tabbata tsoro ya shiga jikinta kafin yaci gaba da fad’in “Kar ki damu everything here is free of charge.. You can sleep in my wife’s bedroom, free of charge.. You can use her kitchen, free of charge.. You can watch her television, free of charge.. You can have all the luxury here free of charge.. You don’t need to pay with your body.. Kaman dai yanda kika saba..!” Ya k’arashe yana mai dubanta daga sama zuwa k’asa.
K’walla masu zafi suka ciko idanunta.. Ta lumshe su a hankali hawaye suka gangaro mata.
“I can’t take this insults anymore.. Tell me.. Ka sanar dani mai kake nema wajena.!”
Ya murmusa kad’an kafin yace “Worse abinda zai faru dani a rayuwata shine a ganni tareda ke... Amma idan har sai nayi hakan na gano makashin ‘yaruwata, zanyi.. Zanyi dan na gano gaskiyar komai yanda akai aka samu gawan ‘yaruwata tareda watsettsen saurayinki who was about to marry you.!”
Sadiya ta murmusa hawaye na gangaro mata lokaci guda tace “Ashe K’anwarka ma tanada connection da Sagir tinda har aka gano gawansu tare.. Ashe bani kad’ai bace dai watsettsiya...!
Katseta yai da fad’in “Don’t you dare mention my sister..! I forbid you..!” Yai maganar yana mai nunata da yatsa hannunsa har rawa yake.
Taji tsoron yanayin da taga ya shiga, lokaci guda kuma sai taji kaman bata kyauta ba ganin cewa k’anwar tasa ta rasu bai kamata tai magana irin haka akanta ba koda Mu’azzam ya gaya mata maganganu marassa dad’i.. bata iya k’ara furta komai har ya fice daga gidan cikin sassarfa..
Haka Mu’azzam ya fice da tinanin maganganun Sadiya cikin zuciyarsa. Cewa k’anwarsa tana da connection da Sagir.. Bazai tab’a yarda Ikram tana da connection da wannan d’anta’addan ba... No no no baima so ya amince da hakan.. Wasu irin hawaye ne yaji suna k’ok’arin ciko idanunsa.. Maiyasa all of the sudden yaji ya fara tunanin binciken k’wak’waf da yake yi.. Ji yake cikin tone tonensa zai digging abinda zuciyarsa bazata iya d’auka ba.. Hawaye ne yaji from no where suna gangaro masa.. Ya shiga girgiza kai yana furta “No no.. Sace Ikram akayi.. Batada wani connection da wannan mutumin.. Babu wanda yakeda connection da wannan d’anta’addan dik cikin ahalina...” Birki yai had’ida kifa kansa saman steering yanaji zuciyarsa na barazanar tarwatsewa.
A b’angaren Sadiya kaw yana ficewa itama Ta nufo waje da zummar ficewa daga gidan.. Saidai tana sako k’afa taga k’artan karnukan nan suna nan a harabar gidan suna shawagi..
Ta koma da baya had’ida jinginuwa jikin garu Ta lumshe idanunta hawaye na gangaro mata. Umma da ‘yanuwanta kawai take tunawa tasan dole suna cikin damuwan rashinta.
Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’e ta komo cikin gidan, ga wani irin yunwa dake azalzalanta.. Nan saman dining table d’in taga mug na tea, da alama dai shima a nan yaci karin kumallon nasa.. Ta tab’e baki kad’an kafin ta nufi hanyar da take tinanin kitchen zai kaita.. Aiko kitchen d’in ne wadatacce wanda shima aka k’awatasa da kayan alatu irin na zamani kana gani kaga gidan Amarya. Tai tsaye tana k’are ma kitchen d’in kallo sai kuma taji hawaye na k’ok’arin ciko idanunta, bata son tab’a duk wani abu da ya shafi wannan gidan amma batada wani zab’i cin abinci dole ne a wajen ko wane rayayye abin halitta.. Fridge ta bud’e tagansa shak’e da abubuwan buk’ata.. Ala dole ta had’a mai zata had’a dan ta saka a cikinta.. Saida ta koma d’aki ta d’auki sabbin abubuwan da takeda tabbacin shi ya aje su kafin tai brush ta fito taci sandwich d’in data had’a Wanda take jinsa kaman magani take taunawa.
Zama tai ta rapka tagumi tana tinanin rayuwa da yanda yake zuwa mata.. Mahaifiyarta da ‘yanuwanta suna buk’atar ta bazataso taita zama a wannan kurkukun ba.. Zatayi k’ok’ari taga Ta bar wannan gida Ta koma ga ahalinsa as soon as possible.
**
A b’angaren Mu’azzam kaw saida suka had’u da Assad ya basa update cewa basu iya gano masu lambobin da ake tura masa sak’o dasu ba.. Lambobin basa kan waya sannan ta iya yuwa ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in yayi disposing d’insu. Nan yake sanar dashi tareda Maleeka sukai k’ok’arin gano mai lambobin amma basu samu ba.
Mu’azzam ya d’an dubesa yace “Maleeka kuma.?”
Assad ya jinjina kai yace “Kasan itace computer guru.”
D’an Jim yai sai kuma ya jinjina kai ba tareda yace komai ba.
Shiru ne ya gifta tsakani kafin Assad ya tambayesa Sadiya dan ko a daren jiya ya kira Mu’azzam d’in yaji hayaniya lokacin yana Passion Trust Super market yana mata sayayya a daren. Bai iya basa amsa ba sai cewa da yai zaijesa yaga Daddy yana jiransa akwai yanda zasuje.
Assad ya jinjina kai kafin sukai sallama... Ya kula da gaba d’aya jikin Mu’azzam d’in a mace yake. Dukda bazaice ga abinda ke damun abokin nasa ba b’angare na zuciyarsa na raya masa mutuwan jikin Mu’azzam nada nasaba da shigowa rayuwarsa da Sadiya tai...
A k’ofan parlor ya had’uda Daddy fitowarsa kenan, yana k’arasowa Daddy ya fad’ad’a murmushinsa sanda suke gaisawa.
“Officer ka iso..” Daddy ya fad’i yana mai sab’a babbar rigarsa.
“Eh Daddy Allah sa ban makara ba.”
Daddy yace “A’a no baka makaraba.. Kace ma Adnan kar ya fito da Mota zakai driving d’inmu.”
Mu’azzam ya jinjina kai cikeda risinawa yace “Alright Daddy..” Lokaci guda ya shige ya sanar da Adnan sak’on Daddy.
Mu’azzam ya k’araso da motar tasa zuwa yanda Daddy ke tsaye. Daddy ya shige suka d’auki hanya.
Ta saman bene Mommy ke hangosu.. Ta jinjina kai ita kad’ai tana tinanin toh Ina zasuje su biyu rak.
Cikin tsanaki Mu’azzam ke driving Daddy ma basa direction har suka iso wani makeken gida mai babban gate.
Aka bud’e masu gate masu tsaron k’ofa suna ma Daddy sannu da zuwa.
Shidai Mu’azzam sai kallon gidan yake wanda yake kashi kashi flats da dama. Sai kuma ya soma ganin mutane nakasassu masu deficiency suna fitowa daga wasu ginin nan cikin building d’in, wasu da wheelchair wasu da crutches wasu ma kaman rarrafe suke.. Tunanin mahaifiyarsa ce ya fad’o masa sanda yaga wata mata saman wheelchair kanta a karkace kaman dai yanda mahaifiyarsa take saidai ita wannan matar tana iya motsa hannayenta.
Mu’azzam yaji rauni ya cika zuciyarsa. Yana gani ma’aikatan wajen suna k’arasowa suna gaida Daddy wasu ma cikin nakasassun Sai tururwar zuwa gaida Daddy suke.. Take yaji wani irin nastuwa had’ida sanyi na ziyartar zuciyarsa.. Wani yaro mai karkataccen k’afafu ya k’araso yana janye Mu’azzam d’in.. A hankali ya duk’a yana shafa kan yaron murmushi saman fuskarsa. Da yawan yaran ko magana basu iya ba wasu kuma gwalamniya suke.. Duk yanda ka kai ga taurin zuciya idan kaga wad’ann bayin Allah dole kaji rauni ya ziyarci zuciyarka, ka kuma tina cewa kai d’an Adam ba komai bane, yanzu labarin rayuwarka zai iya canzawa.. Wad’ann mutane basuyi laifin komai ba ba wai kuma dan Allah yak’isu ba ya jarabcesu da irin wannan jarabawa. Sannan kaima ba wai dan yafi sonka bane ya baka cikakken lafiya.. Saidai dan ya jarabceka da lafiyar nan da ya baka yaga zaka gode masa ne ko zaka bijire ma rahamarsa.
Muryar Daddy ya sinkayo yana fad’in “Mu’azzam my Son, this is where I invited your inheritance.. Ban Sani ba ko na maka katsalandan amma tin lokacin da na fahimci bakada interest akan tara dukiya da abin duniya sai nayi tinanin bud’e wannan cibiya na taimaka ma nakasassu, da nusar dasu cewa nakasa ba gazawa bace.. Ana koyar da yaran karatu wasu ma ana koya masu san’a sannan wanda dik ya k’ware a sana’arsa ana tallafa masa da kayan sana’a sai a sallame sa a kuma d’iban wasu.. Wannan Cibiya taimakon masu jarabawar nakasa take domin a rage yawan barace barace da nakasassun mu keyi saman kwalta wanda zaka samu wasu ma a garin wannan barace baracen sun rasa rayukansu, wasu an sace su anyi tsafi dasu wasu idan sun fita shikenan ba’a sake ganinsu..”
Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Ko wani budget na Company Naka kason nan yake zuwa..A halin yanzu kayi aure .. And very soon zaka fara tara iyali so ban Sani ba ko zaka ci gaba da tallafa ma wad’annan yaran, amma daga wannan lokaci kasonka a company zai ci gaba da tafiya asusun ajiyarka ne.. Idan kanada interst d’in ci gaba da taimaka masu falillahil hamdu idan kuma kanada wani tunanin in mind shima Alhamdulillah..”
Ya d’an nusa kafin yaci gaba da fad’in “Kai hak’uri idan nayi maka katsalandan..”
Saurin girgiza kai Mu’azzam yai hawaye na ciko idanunsa.
“Haba Daddy.. Mutumin da ya nema maka Aljannah kana gadon baccinka irin haka har zai nemi yafiya wajenka.. Daddy ni ya kamata nai maka godiya bisa wannan sadaukarwa da kai min.. Allah ya saka maka da gidan Aljannah Daddy. And wad’annan mutane masu jarabawar nakasa zasuci gaba da samun kulawa daga wajena in sha Allah da duk mai niyyan taimak masu. Allah yasa manyanmu a k’asar nan suyi koyi da irin wannan tinani da kayi Daddy.”
Daddy ya murmusa yana mai kamo kafad’un Mu’azzam d’in suka nufi cikin building d’in yana saka ma Mu’azzam d’in Albarka.
Har kusan azahar suna foundation d’in. Basu bar wajen ba har saida suka amshi list d’in kayan amfani da nakasassun bayin Allahn nan ke buk’ata musamman na sana’ar hannu da ake koyar dasu.
A wannan ranan Mu’azzam ya kuma ganin girman Daddy da jin nauyinsa. Ya kuma yarda Daddy uba ne na K’warai a wajensa.
**
Koda Sadiya tai wanka bata yarda ta tab’a kayan dake jere cikin wardrobe d’in ba dan tasan bazai wuce na matarsa bace.
Tai tsuka a hankali tana furta “Yanzu ya zanyi..? What do I do now..!” Tai maganar cikeda shagwab’a kaman wani yana ganinta.
D’aura hijab d’inta tai a k’irjinta ta nufi toilet da rigar nata tana fad’in “Zaka gani kayana zan wanke.. I’m not wearing your wife’s cloth Mr Inspector.!”
Ta tab’e baki tana kwaikwayon maganarsa “You can use everything here free of charge.. Mtsww Mannerless.!” Ta k’arashe tana mai tura k’ofar bathroom d’in.
Ta shiga ta wanke rigar ta fito ta nufi balcony tana bibbige rigar.. Sam bataji ko alamun shigowarsa ba balle rufe gate.. Tana nan tsaye wajen tana aikin bige rigarta.
Shiko Mu’azzam koda ya shigo bai ganta parlor ba, tab’e bakinsa yai kad’an kafin ya nufi upstairs yasan ba lallai dama ta zauna a parlorn ba. Kai tsaye upstairs ya haye.
Sautin buga abu da yake jiyowa daga d’akinta shi ya janyo hankalinsa. Yai tsaye yana duban k’ofan d’akin yana tinanin Toh meke faruwa da Ita. Lokaci guda ya yanke shawarin tura k’ofan d’akin.. Bai ganta cikin d’akin ba amma ga k’ofan balcony a bud’e. Lokaci guda ya nufi balcony d’in mamakin sautin k’aran buge abu da yake jiyowa bai bar saman fuskarsa ba.
Da tsananin mamaki Mu’azzam ya tsaya yana duban Sadiya dake d’aure da Hijab tana buge jik’akk’en rigarta.
“What.!” Ya furta da d’an k’arfi.
A wani irin birkice ta juyo tana mai sakin k’ara dan bataji shigowarsa ba sai muryarsa.
Ta shiga manna jik’akk’en rigar jikinta tana kare Jikinta dashi.. Cikin huci take furta “What are you doing here..?”
“This is my house, and I don’t remember asking for your permission idan Ina son shiga ko Ina a cikin gida na.. Get ready we are going out..!” Ya fad’i yana mai juyawa.
Kaman kuma wanda ya tina wani abu ya juyo yana dubanta k’asa k’asa musamman k’afafunta da take ta k’ok’arin d’ingilesu tana b’oyesu yace “And don’t think of wearing that thing you are holding.. wear something nice and decent..” Daga haka Sa kai ya fice ba tareda ya kuma cewa komai ba.
Rausayar da idanunta tai tana mai rakasa da mugun kallo.. “Tyrant.!” Ta fad’i tana jan gajeren tsaki.
SameenaAleeyou📚
Leave a Comment