Gidan Aro 6
*06
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Idanunsa a rufe suke cikin bak’in glasses hakan yasa bata iya ganin k’wayar idanunsa ba, gaban Sadiya yayi wani irin yankewa ya fad’i, Ta kasa katab’us Ta kuma kasa janye hannunta daga saman k’irjinsa saima zuba masa idanu da tayi.. Mutumin yafi mata yanayi da taurarin cikin film.
Shid’inma kallonta yake ba tareda ya janye idanunsa ba saidai sam Sadiya bata iya ganin k’wayar idanunsa amma shid’in yana ganin nata Ta cikin shades d’insa..
Assad ma zuba masu idanu kawai yai yana nazarin yarinyar data bangaje abokin nasa, gata dai kaman ba mai tab’in hankali ba amma yanayin da take ciki zai tabbatar maka cewa cikin tsananin tashin hankali take dan Ko takalmi babu k’afarta..
Tamkar wacce aka zabura haka Sadiya Ta soma janye hannunta tana mai matsawa da baya da baya ba tareda ta furta komai ba, Assad da Mu’azzam da mamaki suke dubanta har lokacin musamman k’afafunta da yayi fusufusu babu ko takalmi.. Ita kaw Sady kallo d’aya kurum tai masu sukai mata yanayi da Jami’an tsaro, Allah ya gani tana mugun tsoron jami’an tsaro bata fatan wani abinda zai had’ata dasu..
Lokaci guda Ta shiga k’yafta manyan idanunta masu tsananin haske da yalwan suma, takai idanunta k’asa tana kallon k’afafunta da sukai fusu fusu dan idon mutanen naga k’afafun nata ne, tai saurin d’ingile k’afafun tana mai sosa sumarta da ya barbaje, kaman mai shirin sakin kuka tace “Sorryyyy...” Lokaci guda ta saki murmushinda yafi kama da yak’e kumatunta suka lotsa, Ta soma jada baya a hankali.. Kan kace mai ta aune a guje ta juya ta bar wajen, har juyowa take tana kuma dubansu...Mu’azzam yabi bayanta da kallo har Ta b’ace masa yana mamakin yarinyar, wata zuciya tace k’ila mahaukaciya ce sabuwar kamu..
Assad ya bud’e murya yace “Ita kuma wannan ko meke damunta sai Allah..” Ya d’anyi fasali kafin ya k’arada “But she’s Pretty, very Beautiful..”
Wani kallo Mu’azzam ya watsa masa had’ida d’an tab’e baki kad’an.. Ba tareda yace komai ba yasa kai yai shigewarsa. Assad ya biyosa da sauri yana fad’in “Amma kasan yanda kuka bige juna tamkar had’uwar taurarin cikin film.. You two zaku dace da juna sosai..”
Da tsananin mamaki kurum Mu’azzam ke duban Assad..
“Wait, what rubbish are you talking about Assad..? What exactly has gotten into you.. Ta ya zamuga Mahaukaciya a hanya ka hau had’ani da ita... Baka santa ba ban santa ba, wannan wani shirme kenan Assad..” Ya d’an girgiza kansa kafin yace “Masu hankali ma basa gabana ballantana mahaukata..”
Darawa Assad ya somayi kad’an dan dama so yake ya tab’o mutumin nasa “Kai waye yace maka mahaukaciya ce.. K’ila dai wani damuwarta ya fito da Ita haka.. Amma sam bata min kamanni da masu tab’in hankali ba.. Opps na mance ashe fah Kai ango ne, kafin Hajiya Safeenah tajini Ta sakani a blacklist tace na fara yima angonta tayin wasu matan tun kafin Ta tare a gidanta...”Ya k’arashe yana kame bakinsa da hannayensa biyu..
“Will you please stop being annoying and concentrate on your assignment..” Mu’azzam ya fad’i yana mai aikawa Assad d’in wani irin kallo..
Sara masa Assad yai yana mai fad’in “Sir, My apology.” Murmushi saman fuskarsa.
D’an girgiza kai kurum Mu’azzam yai kafin suka nufi layin gidan Alhaji Isyaku D’an canji..
Wasu samari guda biyu suka tadda zasu shige k’ofar gidan, suka taresu suka tambayesu ko nan ne gida Alhaji Isyaku.. Sukai sa’a kuwa wannan gidan shine gidan Alhaji Isyaku, take suka soma knocking a k’ofar gate d’in... Maidagi Baba Dattijo dake bayima flowers cikin sauri ya k’araso ya bud’e yana tambayansu da mai zai taimaka masu..
Assad ya gaishesa cike da girmamawa kasancewar mutumin Dattijo kafin ya bud’e wallet d’insa ID d’insa ya bayyana, lokaci guda yake furta “Mu jami’an tsaro ne daga ofishin gudanar da bincike na manyan laifuka.. Muna son ganin mai gidanka idan yana gida..”
Baba Dattijo ya d’an dubesu a tsorace yace “Amma saurayi inji lafiya koh..”
Assad ya murmusa kad’an yace “Lafiya k’alau Baba aiki mukazo ba tashin hankali ba.. Kawai ka mana iso da mai gidan idan yana ciki..”
Baba ya jinjina kai yace “Toh shikenan d’an nan.. Kuyi hak’uri, yau shekarata kusan ashirin kenan ina aiki gidan tin gina gidan ban tab’a ganin Jami’an tsaro sunzo ba shiyasa na tambayeku.. Ai Alhaji mutumin k’warai ne.. Duk anguwar nan an masa shaida..”
Abinka da tsoho Sai ya shiga basu labarin abinda bai shafesu ba...
Mu’azzam da ya riga ya gama k’osawa, k’ok’arin saita kansa yai kad’an kafin ya matso kusan Dattijon yana mai zare shades d’in dake mak’ale fuskarsa had’ida d’an rage girman idanunsa, ya d’an sosa sumarsa kad’an yace “Baba kodai mu tafi dakai ofishin ‘yansanda ne ka mana bayanin a can..” Tamkar mai rad’a haka Yai maganar
Baba maigadi ya zabura ya zaro ido waje yace “Ofishin ‘yansanda D’an nan ka rufa mini asiri.. Ni Buba tinda nazo duniya ko hanyar ofishin ‘yansanda ban sani... Barin maku iso da Alhaji kunzo a daidai domin kuwa yau d’in bai fice ba..”
Ya k’arshe yana mai nufan cikin gidan..
Mu’azzam da Assad suka dubi juna suna d’an murmusawa, lokaci guda Mu’azzam d’in ya tsume yana mai maida shades d’insa fuskarsa..
Jim kad’an Mai gidan ya fito mamaki fal saman fuskarsa, suka gaisa da juna had’ida gabatar da kansu..
Mu’azzam yaci gaba da fad’in “A k’ofar gidanka, satin da ya gabata akwai taron d’aurin aure da aka gudanar a k’ofar gidanka.. Anyi haka..?”
Da tsananin mamaki Alhaji Isyaku Ke dubansu kafin yace “Taron d’aurin aure kuma a k’ofar gidan nan..? Gaskiya ba’ayi haka ba..”
Wannan karon Assad ne yayi maganar “Ko ba kai bane Alhaji Kabir Isyaku D’ancanji..?”
Alhaji Isyaku ya jinjina kai yace “Of course k’warai ma kuwa ni ne Alhaji Kabir Isyaku.. Amma gaskiya babu wani taron aure da akayi a k’ofar gidana.. Babu ma auren da akayi kwata kwata..”
Mu’azzam ya warware takardan dake hannunsa, sketch na fuskar mutumin da aka tsinta da gawan Ikram ya bayyana, ya nuna ma Alhaji Isyaku hoton yace “Wannan shine angon da za’a d’aura aurensa a k’ofar gidanka.. Ko zaka iya ganeshi..?”
Alhaji Isyaku yai K’uri yana duban hoton lokaci guda yake girgiza kai alamun baisan mutumin ba..
“Yallab’ai a gaskiya bansan wannan mutumin ba, hasalima ban tab’a ganinsa ba..”
Duk tattaunawar da suke Baba Maigadi dake tsaye gefe sai ware idanu yake yana so ya hango hoton da ake nunawa Alhaji Isyaku, dukda cewa shekarunsa sund’an ja amma tabbas yaso ya gane fuskar wannan mutumin...
Mu’azzam ya jinjina kai ya mik’awa Alhaji Isyaku hannu sukai handshake kafin yace “Mun gode K’warai da lokacinka daka bamu.. Sannan ina fata idan muka sake zuwa zaka k’ara ara mana lokacinka.. Idan kuma Ta kama mu gayyaceka zuwa ofishin mu zaka amsa gayyatarmu..”
Alhaji Isyaku ya jinjina kai yace “Wannan babu matsala Inspector, ko yaushe kuna iya zuwa da tambayoyinku..” Sukai sallama Alhaji Isyaku ya koma cikin gidansa..
Assad ya d’an fuzar da huci yace “Gaye nan ya rantse Sai ya bamu wahala..”
Mu’azzam ya murmusa da gefen bakinsa yace “Muma kuma zamu bashi wahala.. Bazan barshi ba har sai yayi magana.. I’m positive yasan mutumin nan sosai ba abokin shan sigarinsa bane kawai kaman yanda yace.. Lets go..”
Assad ya jinjina kai kafin suka juya da zummar Barin wajen.. Baba Mai gadi yai saurin biyo bayansu yana fad’in “Rankaidad’e.. Yallab’ai...”
A tare suka tsaya suka juyo suna duban Baba Maigadi..
“Yallab’ai hoton mutumin nan da kuka nuna ma Alhaji..”
Mu’azzam yai saurin zaro takardan cikin suit pocket d’insa, ya shiga warwareta yana nuna ma Baba Maigadi...
Baba Maigadi yai K’uri yana duban hoton lokaci guda yake jinjina kai yana nuni da hoton yake furta “K’warai shine.. Shine wannan mutumin da Sabeera take kawosa suyi zance a gidan nan shida wata k’awarta.. K’warai shine wannan mutumin.. Shekaruna sunja amma idanuna garas yake.. Tabbas wannan mutumin ne..”
Mu’azzam da Assad sukai saurin duban juna, Mu’azzam yace “Baba wacece Sabeera..?”
“Sabeera ai d’iyar Alhaji ce, itace d’iyarsa ta biyu...”
Assad yaji murmushi na zuwa fuskarsa, at last sun samu wani abu..
Cikin sauri ya shiga furta “Baba muna buk’atan muga Sabeera yanzun nan..”
Shikam Mu’azzam tuni ma ya koma k’ofar gidan yana kuma bugawa..
Baba Maigadi da Assad suka dawo a tare, Baba na fad’in “Barin maka iso Yallab’ai ai inaga bata fita ba dan makarantarsu suna yajin aiki...
Koda Baba ya shiga ya sanar da Alhaji Isyaku ga mutumin da suke nema sosai ran Alhaji Isyaku ya b’aci, ya tasa Maman Sabeera da fad’a Ta yanda yake shiga bata nan yake fita ba “Na fad’a miki bana son alak’ar yarinyar nan da k’awayen banza.. Har yaushe Sabeera take kawo samari zance cikin gidan nan banida labari.. Kullum ina ja miki kunne bakiji.. Ga irinta nan kinga abinda taurin kunnenki ya janyo mana.. Toh wllhi Nidai kinji na rantse idan aka rufeta bazanyi belinta ba, Keda kike d’aure mata gindi take tarayya da ko wasu irin mutane sai kije kiyi belinta.. Aikin banza Ina Sabeeran take yanzu..?”
Maman data rapka tagumi cikeda tashin hankali take fad’in “Taje sayan Katin waya a bakin layi.. Amma yanzu zata dawo.. Oh ni Rahina na shiga uku.. Alhaji kar ka bari su tafi da Sabeera wllhi d’iyarmu yarinyar kirki ce..”
Tsaki ya buga yana fad’in “Ai Kinga irin abunda kullum nake fad’a miki, idan kukayi wasa daga rana mai kaman ta yau makaranta ma Ta daina zuwa.. Rahina sanin kanki ne Gudun kar d’iyata ta lalace yasa nak’i kaita wani wajen tayi karatu nace saidai tayi a nan, ko hostel ban amince ta zauna ba na ajiye mota da driver nace kullum a dinga kaita, toh tinda a nan d’inma ban tsira ba cireta zanyi Ta gama karatun..”
Cikin damuwa Maman Sabeera Ke fad’in “Alhaji kar kace haka, lalacewa ba daga nan take ba, Ko a d’aki kake rufe d’iyarka idan taso lalacewa sai ta lalace, tsananin tak’ura bashike tsare mana yaranmu ba, a’a ayi addu’a kuma a saka idon.. Nawa aka tak’ura masu kuma suka lalace d’in kaidai kawai addu’a shi zamuke masu.. Balle ma nasan Sabeera batayi komai ba..”
“Ke ni ki rufe mun baki, ki shige muje ki bama ‘yansanda bayanin yanda d’iyarki taje..” Ya k’arashe yana mai sab’a babbar rigarsa kafin yai ficewarsa..
Maman Sabeera ta biyo bayansa tana kiranta inaa ko sauraronta baiba..
A b’angaren Sadiya kuwa tana isowa gida ta tadda k’aninta kwance jikin Ummansu, da k’yar Umman ta shawo kan Tabawa da fad’in satin da za’a shiga tayi alk’awari dik yanda kud’ad’enta suka shiga suka fita zata nemomata Su, da wannan yarjejeniya Tabawa ta saki Habeebu bata tafi dashi ba..
Sabeera dake tsaye gefe rik’eda k’aramar bak’ar leda a hannunta, recharge ne na waya saiko sai sanitary pad da ta sayowa Sadiyar, ta cire recharge card d’in ta mik’awa Sadiya ledar sanitary pad d’in tana fad’in “K’awata barin k’arasa gida kafin a soma nemata, Baba na gida bai fice ba.. Nasan Sai ya tambayi Ina nake kafin ya fita..”
Sadiya dai tinda ta k’araso sai lek’e lek’e take a lungun, kaman mai jiran zuwan wani..
Sabeera ta d’an juya tana waige waige da mamaki tana duban mai ya d’auke hankalin Sadiyar..
“Wai lek’e lek’en me kike ne tintinin, Hajiya Tabawa dai ta tafi ba dawowa zatayi ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki..”
Itadai Sadiya bata ce mata komai ba, dan tinda taci karo da wannan mutumin k’irjinta bai daina bugawa ba, sannan gabanta bai daina yankewa ba..
D’an murmusawa kad’an Sabeera tai tana fad’in “K’awata badai tsoro ba.. Kinga bara na k’arasa gida, sai munyi magana..”
Juyawan da zatai ta hango ta hango Babanta da mamanta harma da wasu mutane guda biyu Sun karyo kwanan gidan Babanta sai masifa yake..
Ba Sabeera data kusan sakin fitsari a jikinta ba, harta Sadiya saida taji ‘yanhanjinta sun juya musamman data hango wannan mutumin da suka bangaji juna shida Ita...
Sabeera tai saurin rik’o hannun Sadiya tana fad’in “Na shiga uku Sady wllhi Baba ne... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Shikenan yau kasheni kawai zaiyi wllhi..”
Sadiya kam Ta kasa katab’us sai duban mutumin nan da suka bangaji juna take d’azu, zuciyarta taci gaba da bugawa idanunta akansa.. Har wannan lokacin idanunsa na rufe cikin bak’in glasses.
Baban Sabeera dake gaba yana sab’a babbar riga yana nunasu da yatsa yake fad’in “Yauwa Inspector, ka gansu can, gasu can.. Dama na fad’a maku a nan za’a sami Sabeera.. Tana tareda wannan annobar.. Yarinyar ta riga ta zame mana masifa a unguwar nan, banda tara maza bata komai.. Duk ta lalata tarbiyan yaran layin nan..” Ya kuma sab’ babbar rigar yana jefo dak’uwa ma Sabeera tin daga nesan yana fad’in “Zakici gidanku ne yau..!”
Sabeera Ta kuma rikicewa tana kuma b’oyewa bayan Sadiya daidai sanda suka k’araso k’ofar gidan.. Har lokacin Baban Sabeera bai daina bala’i ba mamar Sabeera na kwab’arsa hankalinta duk a tashe itama amma kaman cewa yake Ta k’ara...
Sadiya tsoro Sabeera tsoro, Sabeera na tsoron Babanta Sadiya kuma gani take Baban Sabeera ‘yansanda ya d’auko mata zai sa a rufeta a police station tinda ya mata iyaka da d’iyarsa tak’iji.. Aiko suna k’arasowa ta finciki hannunta daga rik’on da Sabeera tai mata, tuni tai jifa da ledar sanitary pad dake rik’e hannunta wanda Sabeera ta sayo mata a shago... Aiko ledar nan bai sauk’a ko Ina sai Fuskar Mu’azzam, tim kakeji ya samesa a fuska sai da glasses d’insa ya gauce.. Ya saka hannu a hankali ya zare shades d’in yana mai sauk’e idanunsa k’asa dan ganin abinda ta jefesa dashi.. A hankali ya duk’a ya d’auka yana juyawa, bai ce ma kowa k’ala ba Sai d’age suit pocket d’insa da yai ya saka ciki.. Ya gyara zaman suit d’insa had’ida maida glasses d’insa kafin ya k’arasa k’ofar gidan ba tareda yabi takan su Sabeera da Babanta dake k’ok’arin janyota tana b’oyewa bayan mahaifiyarta Assad na k’ok’arin janye Baban Sabeeran.
Hayaniyar da Umma ta jiyo daga waje ya sanyata fitowa bayan taga shigewar Sadiya d’aki a guje Ta maida k’ofa ta rufe..
Kana ganin yanda Umman Sadiya ta fito a birkice zaka fahimci suna cikin tsananin tashin hankali ne, dan ba’a jimaba Tabawa ta tafi da yarjejeniyar sati mai zuwa za’a mata kashin kud’ad’en mutane ‘yan group d’inta na online business d’inta..
Umma tana fitowa Baban Sabeera ya soma nunata yana fad’in “Yallab’ai gata nan, wannan itace mahaifiyarta.. Duk wani barikanci da tara maza Ita take koya mata, wannan mata mak’otaka da irinsu masifa ne.. Ka ganta nan..”
Mu’azzam ne ya katsesa da fad’in “Kana iya Barin mu muyi aikinmu Alhaji..”
Baban Sabeera ya jinjina kai yace “Amma nima Yallab’ai zan iya shigar dasu k’ara sabida Auren d’iyarsu da suka saka a k’ofar gidana ba tareda sanina ba.. Ina zaman zamana ‘Yansanda suka kawo min sammaci..”
Assad ya d’anyi gyaran murya ya dubi Sabeera dake mak’ale jikin Mamanta tana hawaye yace “Ki daina tsoro kinji, tambayarki kawai zamuyi..”
Sabeera tai saurin jinjina kai still tana hawaye..
Sketch d’in ya warware ya nuna mata yace “Kinsan wannan mutumin..?”
Tai K’uri tana kallo, ta kuma d’ago kai ta dubi Assad kafin Ta dubi Umma dake tsaye gefe tayi zuru zuru..
Duban yanda Sabeera take kallo Assad yayi kafin yace “Saurayin k’awarki ce da take zuwa gidanku dashi zance. Am I right..?”
Ta jinjina masa kai a hankali kafin tace “K’warai Sagir ne..”
Jin Ta ambaci Sagir yasa Umma matsowa tana duban sketch d’in..
Umma ta shiga tafe hannaye tana salallami tana fad’in “Wannan Bawan Allah shi ya jefa mu a ukun da muke ciki.. Rankaidade dan Allah ina zamu samu Sagir yazo ya sanar damu abinda d’iyarmu tai masa ya mata wannan wulak’anci da cin kashi..”
Assad ya jinjina kai yace “Bisa ga dukkan alamu kece mahaifiyar yarinyar da Sagir zai aura..?”
Tai saurin jinjina masa kai tana jin hawaye na zuwa mata..
Jinjina kai Assad ma yai kafin ya dubi Alhaji Isyaku da iyalansa yace “Alhaji mun gode K’warai kuna iya tafiya daga nan..”
Alhaji Iskayaku yace “Alhamdulillahi.! Muna iya tafiya koh..?”
Wannan karon Mu’azzam ne yai magana “Kuna iya tafiya, amma kaman yanda muka fad’a maka idan Ta kuma kamawa mu nemeku zamu nemeku, muna kuma fatan ku sake bamu goyon baya da had’in kai..”
Alhaji Iskayu ya jinjina kai yace “In sha Allahu Inspector.. Mun barku lafiya..” Ya k’arashe yana mai duban Sabeera
“Ke kuma shige mu tafi..” Tana matsan hawaye ta shige Assad ya d’anyi kaman zaibi bayansu ganin yanda mahaifin nata ke k’ok’arin janyota, d’an girgiza kai kurum yai ya dawo da baya yanda Mu’azzam ya tsare Umma da tambayoyi..
Mu’azzam yaci gaba da fad’in “Ina mahaifin ‘yarki yake..?”
Umma Ta girgiza kai tace “Ya fita tin safe..”
Ya jinjina kai a hankali kafin yace “Toh zamu gayyaci d’iyarki zuwa ofishinmu domin gudanar da bincike had’ida amsa mana wasu tambayoyi..”
Umma ta shiga salati tana fad’in “Na shiga uku ni Uwani.. Sadiya wane irin mutumi kika kwaso mana..Tinda nake ni ban tab’a zuwa police station ba.. Rankaidad’e wllhi bamu San mutumin nan ba, kuma kaman yanda na fad’a maka ba’ayi auren ba ya gudu.. Muma nan nemansa muke..”
“Zaki iya shiga ki fito mana da d’iyarki domin ta amsa mana wasu tambayoyi..” Ya fad’i babu walwala tamkar ba hawaye yake hangowa fuskar Uwani ba...
Jiki a sanyaye Umma ta shiga kiran Sadiya..
Har lokacin Sadiya tana kulle a d’aki, tana jin shigowar Umma tace “Umma Sun tafi ne..?”
Umma tace “Ki fito magana sukazo dashi akan Sagir..”
Ai Babu shiri Sadiya ta bud’e k’ofa ta fito tana fad’in “Umma mai ya sami Sagir.. An gansa ne.? Ina yake.. Ya dawo daga US d’in koh.. Ai dama ni na sani Sagir yana sona bazai tab’a watsa mana k’asa a ido ba.. Saidai ‘yan bak’in ciki su mutu.. Tabawa kuma harda abinda yafi kud’inta za’a biyata.. Event kuma Eagle square ma ya mana kad’an..”
Fizgota da Uwani tai ne ya sanyata had’iye sauran zancen nata.. Ta shiga janyota tana fad’in “Shige muje kafin Babanki ya dawo ya tadda ‘yansanda k’ofar gidansa..”
A haka Umma Ke janyota har suka fito k’afar gidan, shid’in Ta soma hangowa mutumin da suka bangaji juna shida ita d’azu, fitowarta yai daidai da lokacinda yake zare glasses d’in daga idanunsa... Sai wannan lokacin ta sami damar ganin fuskarsa complete, saidai fad’uwar gaban data tsinci kanta ciki har ya d’ara wanda tayi a baya domin kuwa a halin yanzu ya cire glasses da suka rufe masa idanu a lokacin da suka bangaji juna, fuskarsa ya kuma bayyana had’ida k’wayan idanunsa..
Tsoron jami’an tsaron da take ya ninku.. Har Mu’azzam ya soma takowa gabanta bata Sani ba.. Dan shima sarai ya genate yarinyar nan ce data bangajesa ta kuma gudu, sannan itace ta jefesa da ledar ultra pad yanzu a nan..
“Ke.!” Ya fad’i yana mai kuma tsimewa idanunsa tarau akanta..
Ta d’ago a zabure tana dubansa..
“Kinsan wannan..?” Ya tambaya yana nuna mata hoton Sagir..
A daburce ta shiga jinjina kai tana fad’in “Umma Sagir ne.. Umma wllhi Sagir ne.. Taho ki gani.. Na fad’a miki zai dawo gareni..”
“Ke.!!” Ya daka mata tsawa sosai wann karon wanda ba Sadiya kawai ba harta Assad da Umma saida suka razana, Mu’azzam yaci gaba da takowa gaban Sadiya yana furta “Gawan kike jira..?!”
Daga Sadiya har Umma mutuwar tsaye sukai suna duban Mu’azzam dake ci gaba da takowa gaban Sadiya cikin tsananin k’unan rai ya d’ago hoton yana nuna mata yake furta “Well wanann D’anta’addan ya mutu..! He’s found dead.. He’s gone..! Ya mutu, shid’in gawa ne.! Bazai kuma dawowa cikin rayuwarki ba.. Now you’re going to tell me everything you know about him..!”
Sadiya dake dafe da k’irjinta tana jin maganganun D’ansandan sama sama, kalman ya mutu an tsinci gawarsa kawai take nanatawa cikin dodon kunnuwanta..
“Umma.! Umma.. Sa...Sagirrr..!” Luuu sai fad’owa tai jikin mahaifiyarta..
Leave a Comment