Gidan Aro 9

 


*09*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Dafe da k’unci Maleeka ke dubansu da tsananin mamaki “Lafiya su waye ku..?”

Cikin azama Meema ta b’arke Babban roll d’in sanitary pad dake rik’e hannunta, kan kace mai sun shiga jifan fuskar Maleeka

dashi. 

Maleeka ta duk’a tana kare fuskarta da hannuwanta tana kuma tambayarsu su waye su mai ta masu..


Meema ta kuma jefa mata a fuska tana fad’in “Kinji Munafuka Adda Feenah tambaya ma take su waye mu.. Toh uwarki ne mu, ‘yar iska kawartuwa mai bin mazan mutane.”

Safeenah ta cab’i zancen da fad’in “Gashi nan kece matsiyaciya mai jiran namiji ya mata hidima, ki tattara duka.. Idan shi guda d’aya Yayi niyyan baki toh ga roll an baki.. Matsiyaciyar banza sauran kwalta..”


A hankali Meema ta soma jada baya sakamakon hango su Mu’azzam da tai sun fito daga building d’in.. Meema ta aune a guje ta nufi mota, tana bud’e marfin motar ta shige backseat.. Yanda ake aje k’afafu a wajen ta kwanta tai flat yanda babu mai iya hangota..


Safeenah kaw ta yanda take shiga bata nan take fita ba Sai jifan Maleeka take da sanitary pads tana kwashe mata albarka.. Mutane dake shigewa jefi jefi sai kallonsu suke da tsananin mamaki..


Assad ne ya soma hangosu.. Babu shiri ya tab’a Mu’azzam yace “Ai gacen Officer Maleeka.. But wait what’s going on..? Itada wacece..?”


Daidai lokacin Mu’azzam ya juyo, Assad na furta “Kaman Safeenah ce fah.. Mai take a nan..?”


Cikin sassarfa suka nufo yanda su Safeenah suke.. Da tsananin mamaki kurum Mu’azzam ke dubanta, bai zaici Safeenah zatayi abu makamancin haka ba..

“Safeenah.!!” Ya kirawo sunanta cikin tsananin b’acin rai


Cak ta tsaya ta dena abinda take.. Mu’azzam ya tsareta da idanunsa da suka kuma rikid’ewa zuwa ja, dama ransa a b’ace yake dan har ya kamo Danger Chief yasa ya sake shi gashi yanzu ya tabbata Danger nada alak’a da crime d’in da yake bincike..


Kallon wajen yake da mamaki, Wato abinda Safeenah ta gani cikin aljihunsa shine ta biyo Maleeka har Office taci mutuncinta dashi, watau a haukan Safeenah Maleeka budurwarsa ce.. Muryar Maleeka ne cikin kuka ya katse masa tinanin nasa “Sir, wllhi ni bansan mai na mata ba.. I don’t even know her, kawai gani nayi Ta soma attacking d’ina..”


Assad ne ya tari Maleeka da fad’in “Kiyi hak’uri Maleeka let’s talk somewhere else.. Kiyi hak’uri please..”


Maleeka ta d’ago tana duban Mu’azzam dake ci gaba da tururi ga Safeenah tsaye gabansa sai faman huci itama take tana ture turen baki..


Assad ya tasa Maleeka gaba yana fad’in suje.. Bataso tafiyan ba taso taga yanda Mu’azzam zasu kwashe da matarsa.. Ta kula matar Mu’azzam ce wannan wacce akayi aurensu sati biyu da suka shige, dama an fad’a mata cuna masa ita kawai akayi Mu’azzam ba sonta yake ba, Lallai yau ta tabbatar da hakan. Wani irin sanyi mai gauraye da annashuwa ne suka gauraye Zuciyarta.. Watau matar Mu’azzam tana tinanin Ita d’in budurwarsa ce, aiko bazata tab’a losing hope akan Mu’azzam ba tinda har ta zamto babban threat ga matarsa irin haka.. Da wannan rashin hankalin matar tasa tsaf zata iya samun gurbi a zuciyar Mu’azzam.. Ta saki murmushi mai sanyi tana biyeda Assad..



Wane irin duba kurum Mu’azzam ke aika mata, kallo guda zaka masa ka fahimci zuciyarsa a tsananin b’ace take, daga wannan sai wannan “Are you out of your mind..? Have you lost it..?! Kin kuwa San mai kikazo kika aikata a nan Safeenah.. Kinsan inane nan wajen kuwa.. Kinsan wa kikayi attacking da haukarki..?!”


Da tsananin mamaki Feenah ke dubansa wai tasan wa tayi attacking Wato ta wancan shegiyar yake bama ta ita ba.. Watau budurwarsa yake defending.. Ita kuma tayi laifi since she attacked his girlfriend..


Cikin muryar kuka take furta “Yes. Yes na San abinda na aikata.. kuma nasan wacce nayi attacking she’s nothing but your mistress wacce kake cin amanan aurenmu da Ita, kak’i na tare a GIDANA dik sabida Ita...”


“Feeeenahh..!” Ya daka mata wane irin tsawa had’ida d’ago hannunsa kaman zai kwad’a mata mari.. A hankali kuma ya sauk’e hannunsa nasa ba tareda ya mareta ba, yaci gaba da dubanta zuciyarsa ba masa zogi..


Cikin kuka Safeenah ke fad’in “Go ahead and hit me, nasan baka mance a k’ofar ofishinku muke ba.. Hakan zai zama hujjan cewa kaid’in maci amana ne kana cin amanata da wancan ‘yariskar so called Colleague d’in taka...!”


A hankali yake jinjina kai still yana dubanta da rinannun idanunsa “Wannan shine hujjarki na zuwa har wajen aiki na kici mutunci na.. Fine, Yayi kyau Safeenah.. Zan tabbatar kin biya duk abubuwan da kika aikata.. You’ll pay dearly Safeenah.. Daga rana mai kaman ta yau kin gama rashin kunya, Idan kuma ba haka ba sunana ba Mu’azzam Abubakar Gamji ba...!” Ya k’arashe yana sakin murmushin nasa da gefen baki wanda tasan idan yayi wani sharrin nasu na ‘yansanda zai k’ulla a cewar Safeenah..


Tai raurau da idanu tana dubansa yanda ya tsime kaman ba shine ya saki muguwar murmushin nan ba..


“Shige muje..!” Ya fad’i yana nuna mata hanya.


Jiki a matuk’ar sanyaye Safeenah tabi bayansa tana goge hawayen dake kwance idanunta..


Front seat ya bud’e yace ta shige, babu musu ta shige kafin ya zaga mazaunin mai driver ya shige.. Dik wannan drama Safeenah tama mance tareda Meema suke.. Ita kaw Meema tana jin shigowarsu Ta kuma mak’alewa k’asan Seat tana addu’an Allah ya ceceta yasa kar Ya Mu’azzam ya ganta.. Ita batasan Addah Safeenah wace irin sokuwa bace da har zata bari Ya Mu’azzam ya kamata gashi yanzu shi zai driving d’insu home, ai kuwa wllhi saidai ta kwanta k’asar motar har su isa gida a haka..


A rashin hankalin Meema Mu’azzam bai ganta kwance k’asar motar bane, saidai Ta kula kaman da gangan ya dinga tsalle saman speed bumps da motar.. Idan Meema taji zafi saidai ta toshe bakinta kar tayi ihu ya jita ya gane tana motar.. Haka ya dinga gwarata saman kwalta tana matse bakinta dan azaba..


Ga tsananin mamakin Safeena gidansa da akai mata jere ya kaisu.. Ta d’ago tana dubansa da Mamaki...


“Mai Zamuyi a nan..?”


“Isn’t it obvious. Gidanki na kawoki.. Ki zauna har lokacin da gidan zai gundureki..”Ya bata amsa kai tsaye yana mai ficewa daga cikin motar..


Meema dai taji anyi parking batasan Ina akazo ba har saida taji Muryan Mu’azzam yana Fad’iwa Safeenah gidanta ya kawota..


Safeenah kaw tab’e baki tai kad’an zuciyarta na mata sanyi, tana ganin ya bud’e motar ya fice Ta soma furta “Weldon Feenah.. Kinyi daidai..Ko banza kwalliya Ta biya kud’in Sabulu gashi da kanka baka jira wani ya kawo maka ni ba ka kawoni da kanka..” Ta saki Murmushi tana k’ok’arin bud’e motar taji wani irin haushin police dogs irin manya manyan nan masu kaman kuraye..


Wani irin k’ara Safeenah ta saki ta jawo marfin motar babu shiri..


Ihun da Safeenah ta saki ya sanya Meema mik’ewa zaune cikin motar tana kallon yanda suke...


Itakam Safeenah har Ta mance Wai tare suke da Meema saida Meemar ta taso daga mab’oyarta..


Meema ta soma salati tana fad’in “Mun shiga uku mun mutu mun lalace.. Addah Feenah Police Dogs d’insa ya kwance mana ya barmu rufe cikin Mota yayi tafiyarsa..”


Idan karnukan sukai haushi sai Safeenah da Meema sun manne waje d’aya dan tsoro suna sakin ihu.. Wane irin haushi mai diri da ban tsoro suke..Gashi babu hali Su bud’e glass d’in motar Karnukan zasuyi tsalle su shigo motar, gashi Mu’azzam ya kashe motar ya cire key balle su kunna motar ko AC ne Su kunna.. Ga zafin cikin Mota ga Karnuka waje sai haushi suke jikin motar suna zagaye motar..


K’iris ya rage Meema bata saki fitsari ba  ganin Mu’azzam ya fice daga cikin gidan ya kullesu ya barsu rufe cikin Mota police dogs na kewayesu suna shawagi a jikin motar..


Meema ta saki ihu tana fad’in “Adda Feenah wllhi ficewa zaiyi dan Allah ki kirasa ya dawo ya cecemu ya fitar damu.. Wllhi suffocating zamuyi cikin motar nan idan ya tafi ya barmu.. Dan Allah ki tsaidashi.. Na shiga uku ni Meema Wllhi ni tsautsayi ne dama ya sani biyoki.. Mun shiga uku  wllhi horo zai mana irin tasu Ta ‘yansanda mu ba criminals ba.. Adda Feenah dan Allah ki ceceni a fiddani daga gidan nan dama ke gidanki ne..”


Cikin kuka Feenah tace “Ke ni Kimin shiru duk na kece kika kawo shawarin ba.. Wayyo na shiga ukku..” Ta sake sakin k’ara a daidai lokacin da karnukan suke kuma haushi..


Shi kaw Mu’azzam Ko ajikinsa yana ficewa ya tari cab ya nufi location d’in da abokan aikinsa ke jiransa..


**


A b’angaren su Sadiya saida suka biya wani chemist aka duba k’afar Umma aka d’aure mata cikin bandage kafin suka nufi Gida.. Saidai suna dosowa layinsu gabansu yayi wani irin yankewa ya fad’i.. Cincirondon mutane suka hango, hakan ya sanyasu d’an k’ara sauri dikda cewa Umma d’ingishi take Sadiyar ce mai taimaka mata..


Gabansu bai ida yankewa ba saida suka hango mutanen tare suke k’ofar gidansu, ga mutum kwance cikin jini Habeeb da Ashiru sun kifa Kai saman k’irjin mutumin suna kuka.. Take Sadiya taji duniyar na juya mata, Ta rasa tafiya take kan k’afafunta kokuwa a iska take, zuciyarta yaci gaba da tsinkewa suna mai kuma tunk’aran dandatson mutanen..


Duniyar Sadiya bata ida juyewa ba saida ta sinkayo muryar Ashiru yana jijjiga mutumin yana fad’in “Abba..! Abba dan Allah ka tashi.. Abba ka tashi dan Allah.. Abba naaa..!!”


“Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un” Shine kalman da Umma ta iya furtawa.. Sadiya kuwa hannu biyu Ta saka aka had’ida sakin wani irin k’ara tana mai silalewa wajen..


No comments

Powered by Blogger.