Gurbin Ido 12
12
Ajiyar zuciya ta sauke sanda ta tabbatar ta maida sarqar wa anni,ta godewa Allah da ya hani inna furera sanya son zuciyarta a gaba ta hana a maidawa anni sarqar,ta tabbata da ta aikata haka ba zata taba samun nutsuwar zuciya ba,haka zuciyarta take,bata qaunar
haqqi koda qanqani a kanta,dalilin da yasa ta guji kiwon dabbobinta da bugu kenan,ta zabi horar dasu da magana.Sosai hankalinta yayi nisa cikin zuzzurfan tunani,abinda ya sanya kwata kwata bata ankara da tahowarsa ba,sai da taji ta bugi wani abu sannan ta tsaya cak,ta kuma ja da baya da sauri tana kai dubanta gabanta.
Himu ne,sanye da kayan fulani,ya fito a bafullataninsa sak,kayan sun matuqar karbarsa sun kuma haskashi matuqa,saidai babu fara'a ko walwala kwata kwata saman fuskarsa.
Gabanta ne yayi mummunar bugawa sanda ta tuna da gargadi da kuma izayar da tasha hannun inna furera duka akan himu,abinda ya sanyata yin gaba da sauri ta rabeshi zata wuce,saidai cikin hanzarin shima ya matsa ya tare mata hanyar,da azama ta koma daya hannun nan ma ya bita ya tare,ya kare ko ina,bata da zabi illa ta roqeshi
"Don girman Allah ka bani hanya na wuce"
"Saboda me maimunatu?,me yasa kike guduna?" Tsoro ne ya sake kamata,sam bazai fahimci halin da take ciki ba,wannan tsaiwar da yayi a gabanta sai takejin kamar ana tsigar ranta
"Magana nakeso muyi dake maimunatu" wace magana?,a yanzun akwai.maganar kuwa da ita din zata fahimta?
"Kayi haquri,bazai yiwuba,ka barni na wuce"
"Dole ki tsaya ki saurareni maimunatu,don me yasa zaki saurin bada kai akan soyyayarmu?,kodai dama bakya sona?ni daya nake kidina da rawata?" Tuni hawaye ya balle mata,himu so yake kawai ya janyo mata bala'i,baisan yanayin da take ciki ba,da bai tsaya haka a gabanta ya tilasta mata sai sunyi magana ba,bayan ita bafahimta take ba,ta juya baya a matuqar razane sanda taji takun tafiya,take qafafunta suka fara rawa,sai shima ya waiwaya yana duban hanyar.
Kaf jinin jikinta sai daya daskare sanda taga inuwar mutum kuma macace a wajen,abinda ta baiwa ranta shine daada ce ko zubaida ko safiya,ta saddaqar ta gama yawo,kashinta kuma ya bushe,tun daga fuskarta zuwa tafin qafarta sukayi sanyi qalau
"Kuyi haquri,na katse muku jin dadin ku ko?,zan dan wuce ne?" Laila ta fada tana dan sakin fuskarta,ta fuskanci akwai wani abu me kama da soyayya a tsakaninsu,to amma anni tasan da haka kuwa?.
Jin baquwar murya da sautin da ba na fulani ba ya taimaka wajen dawowarta hayyacinta,matsawa laila himu yayi ta fara wucewa,abinda ya baiwa maimunatu damar yin wuf tabi bayan lailan
"Maimunatu" ya kirayi sunanta,saita qara hanzari da kyau ta fara shawarar bi ta duhuwa don kada ma ya biyota ya jawo mata jarfa
"Ina sonki.maimunatu,kuma wallahi bazan fasa sonki ba koda ke baki sona,zanci gaba da sonki har sai na sameki a matsayin matata" kalamai na qarshe kenan dataji daga bakin himu,ta qara hanzari,tana jin cewa inama itadin tana cikin nau'in mata masu hanzari wajen tafiya,lallai da tayi amfani da wannan don ganin ta sake yin nesa da ibrahim.
"Haba 'yammata,saurin me kike haka?" Muryar laila dake biye da ita ta ratsa kunnuwanta,yadda ta juyo kawai zai gaya maka har yanzu a tsorace take
"ya kike gudun wanda yake sonki?" Laila ta fada a tausashe bayan ta iso gaban maimunatu ta tsaya,ta kuma dora hannunta saman kafadar maimunatun zuciyarta na narkewa a tausayinta.
Daddadan qamshin dake tashi jikin laila maimunatu ta zuqa zuwa hancinta,laushin turaren ya sanya zuciyarta karyewa,yadda lailan ta tambayeta cikin taushi da nuna kulawa yasa rauninta ya ninku,take hawaye ya cika idanunta,a wannan lokacin gaza tareshi tayi,sai kuka ya qwace mata.
Kasa hanata laila tayi,duba na tausayi takewa maimunatu,tana kwatanta kanta a matsayinta,tana kwatanta inda itace ta yaya zata rayu babu abbi babu momma?,ya rayuwarta zata kasance?,maimunatun jaruma ce qwarai kuma abar tausayi ce ga dukka wani me tausayi.
Dole ce zata sanyata ta guji himu ba din ya cancanci a gujeshi ba,bata da yadda zatayi matuqar tana son tsira da lafiyarta da kuma rayuwarta,goge hawayen fuskarta ta fara da tafin hannunta bayan taji zuciyarta ta fara mata sanyi daga radadi da suyar da take mata.
"Kiyi haqurk,komai mai wucewa ne,watarana sai labari" daga kai tayi ta bi laila da kallo jin abinda ta fada,tasan wace ita ne?,tana tantama,inda tasan wace ita tatabbatar ba zata tsaya tana magana da ita ba,amma duk da haka a sanyaye sai tace
"Miyatti" murmushi laila ta sake
"Me kenan?" Murmushin da bata shirya masa bane ya qwacewa maimunatu,ta manta ba da daya daga cikinsu take magana ba
"Nace na gode" murmushi lailan ta sakeyi
"Babu komai" daga haka maimunatu ta juya tayi gaba,sai kuma a sannan fargabar kada inna taga dadewarta ta qara cikata,don haka saita qara sauri.
Bin maimunatu da kallo laila tayi har sai data bace mata,ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,a yanzun tana jin zuciyarta ta gamsu dari bisa dari da daukar maimunatu da anni zatayi,saboda hakan tamkar wani babban jihadi ne a wajensu gaba daya,to amma kuma dai dai da qwayar zarra zuciyarta bata gamsu ko kuma kwanciya da qudurin annin na biyu ba,yaa ja'afar fa?,ya ja'afar take magana,ba khalid ba,ba kamal ba,bare jabir,ja'afar take cewa,saita girgiza kai kawai tana komawa hanyar gida,don dama neman network ta fito yi,cikin gidan gaba daya network ya dauke.
A ranar maimunatu tayi kuka tayi kuka qwarai da gaske,tana jin cewa farin cikin rayuwa yana sake yin nesa da ita,tana jin cewa tana sake rasa komai nata,sai ta samu kanta da addu'a a karon farko
"Ya ubangijina,ka kulaa dani,ka kula da lamarina" saita juya gefe daya tana sake curewa waje guda,hawaye masu zafi na tsiyaya har zuw cikin kunnenta.
**********Da fari sanda inna furera taga yuuma a gidanta tadan hade rai,amma kuma data tuna cewa dukka arziqin da tayi kwanaki biyu da suka wuce ta silar 'yaruwarta ce sai ta sakar mata fuska,harda sanya laulo ya dauko mata tabarma,ta kuma qwalawa maimunatu dake baya tana ta faman wankau na kayansu,wanda har yau ma jauro ya hana zuwanta kiwo
"Wadi diyam(kawo ruwa)" a nutse ta qaraso ta tsugunna gaban yuuma tana ajjiye ruwan sannan ta gaidata,yuuma ta bita da kallo zuciyarta na tsinkewa tana amsa mata,kullum kwanan duniya maimunatun sake fita daga hayyacinta da kuma kamanninta take,amma a yanzun tayi imanin inda maimunatu zata,zaya kasance mata tamkar tana hannu mahaifiyarta,koma sama da haka.
Bayan gaisuwa data biyo baya tsakaninta da inna furaira,wanda ta manta yaushe rabon irin haka ya shiga tsakaninsu,sai yuuman ta gyara zama tana lanqwashe qafafunta
"Wajenki nazo furaira"
"Allah yasa alkhairi?" Ta fada tana tattara hankalinta ga yuuma
"Alkhairin ne,don kullum mu shike tare damu"
"To ina jinki"
"Ina tunanin baki manta dattijuwar da kukayi cinikayyar nagge da ita ba kwana uku da suka wuce ko?" Fadin haka kawai ya yalwata fara'a a fuskar furaira
"Har nabar duniya ai bazan manta da wannan baquwar alkhairin ba"
"Ashe kinsan wataran zaki bar duniya furaira" yuuma ta fada cikin ranta,amma a fili saita gyada kai
"Ita din tamkar mahaifiya take a wajena...."
"Allahu akhbar....." Inna furaira tayi hanzarin fada tana duban yuuma
"Amma kike zaune cikin wannan rugar tare damu?" Murmushin da yafi kama dana yaqe yuuma tayi,saboda ita sam ba qaunar wata doguwar magana take ba tsakaninta da furaira
"Aure ya gaji haka,yakai diya mace duk inda yaso"
"Shakka babu" ta amsa tana qarewa yuuman kallo,ba banza ba ta zama macen da duk fadin rugarsu babu me sutura irin tata,hakanan yanayin hutu da jin dadi daya bayyana qarara tare da ita,hakanan cimar gidan bappa labaran ba inda labarinta bai karade ba,dama daadan ta taba bata labari kan wadda take kawowar
"Itace ta aikoni,wato kinsan jikin girma,tana fama da ciwon qafa lokaci lokaci,kuma tana da buqatar mataimaki dai a kusa wanda zai dinga mata wasu ayyukan,to taga maimunatu ta kuma yaba da amanarta,shine tace nazo na tambayar mata ko zaki bata ita,zata dauketa a matsayin ma'aikaciya da zata dinga biya da albashi me tsoka,hasalima tace ki yanka dukka albashin da kikeso a dinga biyanki duk wata,sannan kuma dabbobinki da take kiwo,ki dauki.masu kiwo suma su fadi abinda za'a dinga biyansu,ita zata dinga biya shima" shuru furera tayi,fuskarta na rage kaifin fara'ar dake kanta a dazu,ga qoshi ga kwanan yunwa,haqiqa ko shakka babu wannan albishir albishir ne me dadi a gareta,arziqi kuma har cikin gidanta,saidai kuma ta yaya za'a zabi maimunatu bayan ga gaje?,saboda.matar kana kallonta kasan tana cikin sukunin rayuwa da jin dadi,ita kuwa duk duniya babu wanda takeso ya rayu cikin walwala irin gajenta,gaskiya bata jin zata iya bada maimunatu,wadda take sanya ran tana aurar da gaje ba jimawa ta aurar da ita,ta kuma dora da kiwon da take mata koda tana gidan buderi,sunyi yarjejeniya ya kuma amince,dalilin da yasa.ma ta alqawarta masa auren maimunatu kenan.
"Me kika ce?" Yuuma ta fadi ganin furera ta shiga zuzzurfan tunani
"nakega me zai hana na baku gaaje?,babu abinda maimunatu zatayi wanda ba zata iya yinshi ba" murmushin takaici ne ga qwacewa yuuma,tana da wannan masaniyar amma ta tattarawa maimunatu dukkan wata wahalar aiki
"To ni kinga 'yar aike ce,kuma taga gaaje ta kuma ga maimunatu amma ta zabi maimunatun,ina ganin idan maimunatun ba zata samu ba,zanje na shaida mata kawai,saimu laluba cikin yaran dake rugar" yuuma ta fada tana miqewa,abinda yadan kadan hankalin furaira
"Aah,ba za'ayi haka ba,amma inason a bani lokaci kadan zanyi shawara,zan gayawa kuma jauro ma" kada kai yuuma tayi,tasan ba wani jauro da zata gayawa,amma sai ta bita a hakan,sukayi sallama ta tafi.
Yuuman na fita ta aiki laulo a sirrance yayi mata kiran daada,bata bata lokaci ba kuwa tazo,ta kuma rattaba mata dukan bayani,kishi ne sosai ya kama daadan,me yasa bata nema safiya ko zubaida ba?,indai ko haka ne bata ga dalilin da zata aika gaje ba su da sukafi kusa da daadan suna zaune,gwara maimunatun taje,ko da zata samu kudi daga gareta ai dai ba zata samu jin dadi da daular dake gidan anni ba
"Ya zakiyi ragon azanci irin haka furera?"
"Kaman yaya innar himu?"
"Ta yaya zaki tura gaaje?,tafiyar maimunatu ai shine dai dai,zata je fa samowa gaje kudin aurenta da wanda zaki mata kayan daki da sauransu,don na tabbatar miki himu gini yake na kere sa'a,kinga kina buqatar kudin da zaki mata duk wata hidima,na tabbar jauro zaiyi iya abinda yaga zai iya ne,abu na biyu idan maimunatu ta tafi dole ne himu ya sake haqura da ita,ya kuma tattara hankalinsa ga gaje,saboda maimunatu tayi masa nisan da yasan bazai ganta ko ya sameta ba,kinga komai zai tafi mana dai dai babu wata matsala,sannan ke kanki yarinyar nan alaqaqai ce a wuyanki,har mamaki nake yadda kika ci gaba da riqon diyar mai miki kiwo,kinga yanzun kuwa salamun salamun" sosai inna furera ta gamsu da shawarar daada,tabbas ita din masoyiya ce,kuma maganganunta na bisa hanya,maimunatu zata zame mata tamkar wani jari,hankalinta kwance zata zama wata me arziqi tana daga kwance,da wannan gamsuwar ta taka da kanta har gidan bappa labaran,ta kuma tabbatarwa da anni cewa ta amince.
"Nawa ne kudin da za'a dinga biyanki na aikinta?" Anni ta tambayi furaira da kanta tana kallonta,tsanarta na shiga ran annin,murmusawa tayi sannan tace
"Ina ganin a duk wata ki bada dubu biyar" inna furera ta fada tana fatan anni ta amince da kudin data yanka din.
"Na ninka miki sau hudu,zan dinga aiko miki da dubu ashirin da kuma ladan kiwo" mamaki ne ya cika furera qwarai,har ma ta rasa abinda zata fada,bata taba tsammatar samun haka daga anni ba,ashe maimunatu alkhairi ce tare da ita,ashe ita shatu ta haifawa.
Cikin tsananin murna da farinciki ta koma gida,ta samu maimunatu ta gama da wanki ta kuma dora sanwar abinci,bayanta kamar zai karye saboda duqen da tasha,sanda fureran ta kirata ta shiga fargaba da tsoro
"Zauna nan,ki kuma saurara da kyau kiji abinda zan gaya miki" qas tayi da kanta,zuciyarta na tsananta bugu,tana ayyano masifu kala kala a ranta,ko waccece ta sameta a yau din?.
"Dattijuwar da tazo gidan nan kwana uku da suka wuce,ta ganki kuma tayi sha'awar tafiya dake domin ki taimaketa da aikace aikace,na kuma amsa mata,don haka ki zama cikin shiri,daga gobe zuwa kowanne lokaci zata daukeki ta tafi dake can garinsu" da fari maganar ta razanata,ta kuma rude sosai,ta lumshe idanunta tana kiran
"Ya Allahu,ya Allahu" a hankali sai taji zuciyarta ta fara dai daita data tuna daga inda matar ta fito,daga bangaren yuuma,yummar da zata iya cewa kaf fadin rugar ita kadai ce masoyiyarta,ta tabbatar yuuma ba zata bari abunda zai cuceta ya rabeta.
Ta sake maida tunaninta ga matar,akwai cikakkiyar suffar kamala dattijantaka tattare da ita,ta tuna yadda take dubanta fuskarta dauke da fara'a da kuma tarin kulawa,tabbas akwai kyakkyawan zato a kanta.
"Bakiji bane!" Kakkausar muryar inna furera ta saukar mata cikin kunnuwa,sai ta bude idanunta tana gyada kanta
"Kina jina ko?,wallahi wallahi kikaje kika aikata wani mugun hali,ko kikaje kika gwada musu halin maitarki kikayi sanadin da kika dawo gidan nan,na rantse da sarkin da raina yake hannunsa saikin gwammace mutuwa da rayuwa,duk da bansan matar ba a zahiri,amma na tabbatar gida ne na wadata,basu damu da abun duniya ba,duk wani abu me amfani da kikaga sunyi wasarere dashi ki dauka ki adana min,ni ina da buqatarsa,kome zakici maimunatu idan zai ajjiyu baki ajjiyemin ba Allah ya isa" maganganun data dinga yi sun yiwa maimunatun nauyi qwarai,sai tayi qas da kanta tana saurarenta har sai data gama ta sallameta.
Yini tayi cikin taraddadi da kuma fargaba,duk da tana samun relief duk sanda zuciyarta ta gaya mata cewa yuuma ce,masoyiya guda daya da take da,ta bangarenta ne wannan lamarin,sai tayi qoqarin saisaita qwaqwalwarta tare da addu'ar kome meye ya zame mata sauqine na rayuwarta.
Leave a Comment