Gurbin Ido 22

 


Bata da wani sauran zabi,sai ta samu kanta da gyadawa tabawa kai.


        Unexpected wata guda ta ratsa kunnuwa zuwa kwanyar maimunatu,ta rintse idanunta tana jin wani abu na mata yawo,wanda yake cakude da zallar fargaba da kuma kokwanto.


          "Alhmdlh alhmdlh alhmdlh" shine abinda anni ta dinga maimatawa fuskarta kamar wata dam daren sha hudu,bakinta yagaza rufuwa,hakanan Allah ya sanya mata qaunar maimunatu da kuma tausayinta a ranta.


            A haka maimunatu taci gaba da rayuwa,cikin kunya nauyi da kuma fargabar al'amarin dake tunkararta,saidai kuma ta sake maida hankalinta ga karatunta,wanda a yanzu ta sake maida hankalinta dari bisa dari a kai,ranta da zuciyarta na gaya mata idan tayi aure shikenan,ta rabu da karatunta,tunda abinda ta taso kenan ta gani,matan aure kowacce tana gidanta a zaune,zuwa makaranta na 'yammata ne.


          Saidai a kullum tana tambayar kanta ta yaya lamarin yazo kamar mafarki?,yaya kuma zaici gaba da kasancewa?.


**********Duk yadda yaso ya taushi zuciyarsa ya taho nigeria abun ya faskara,haka kawai yakejin baison zuwa din ko kadan,akwao memories masu tarin yawa da ya binne wanda baison tunosu,ko sau daya zuciyarsa bata sassauta daga tunani da kuma kewar shaheeda ba,wanda cikin jikinsa yakejin da wannan ciwon zai qarasa rayuwarsa ya kuma mutu shima,mutuwar da inda zabi take bayarwa shi zaice ta dauka ba shaheeda ba,koda kuwa ta dauketa zai zabi ya bita shima.


           Duk wata hanya da jabiru yake jin zaibi ya shawo kan ja'afar abun ya faskara,hakanan itama annin tabi duk hanyar da ya kamata ta lallashi amma abinda take son bai samu ba,ranta ya fara baci,don haka a wani dare ta nema ganin dr marwan


*_08:pm Dr marwan khalid akko residence_*



         Dr marwan ne zaune gaban anni,sanye da wata jallabiyya ta matsa ruwan hanta saqar qasar oman mai budadden hannu,an qawata gabanta da adon zare ruwan madara mai turuwa kadan,fuskarsa na dauke da wani annuri na zallar nutsuwa ilimi gami da samun cikakken hutu da kwanciyar hankali,yana da cikar haiba kwarjini da kuma kamala sosai a fuskar tasa da wani bangare nata ya fara samar da furfura.


          Ya miqa hankalinsa matuqa zuwa ga mahaifiyarsa


"Kaji duka irin abubuwan dake faruwa,banyi tsammanin abun na ja'afar yakai har can ba,ina ganin ya kusa fin qarfinmu dai" da hanzari dr marwan ya girgixa kai


"Kiyi haquri ki daina fadin haka,bai isa ba wallahi,koda bana raye koda aishatu bata raye,bare gaba dayanmu da ranmu.....bai isa ba don ubansa,banda wancan matsalar ma harda iya shege na fuskanta ciki lamarin nasa,ai mu muka haifeshi bashi ne ya haifemu ba,ya zubda komai da kowa nasa saboda mutuwar matarsa da diyarsa kawai?,zan nuna masa mu muka haifeshi kam tabbas,karki sake bi ta kansa anni don Allah,abinda za'ayi shine.....ki shirya ki kuma saka lokaci zuwa adamawa gurin magabatan maimunatu cikin satin nan,ni kuma zanyi magana da honorable commissioner ya tsaida randa za'a kai kudin auren tasa diyar" hakan ya yiwa anni dadi qwarai da gaske,ta dinga sanyawa dr marwan albarka,yana da tsananin biyayya,abinda yasa a kullum yake sake shiga ranta.


         Shiri ta fara yi gadan gadan na tafiyarsu adamawa,sanda ta shaidawa maimunatu wani dadi taji ya tsarga mata,amma kuma wani sashe na zuciyarta sai taji tana tsoro da fargabar wacce tarba zata samu daga wajen innar laulo dama gaaje?,dama kuma bata da wata fargaba akan jauro,duk inda mutumin kirki yakai yakai nan.


          Saura kwanaki biyu su wuce da wani yammaci anni ta kirata,tace taje aishatu tace a turota ta kama mata aiki,haqiqa tana matuqar jin kunya da nauyin matar,tunda tasan itace mahaifiyar ja'afar,duk da cewa wata magana data shafeshi bata taba hadasu ba.


            Atamfa ce a jikinta doguwar riga,sai ta zura hijab din da bata jima da cireshi daga jikinta ba saboda sallar data idar,ta zura wasu slippers dinta ta nufi sashen amma,tana tafiya a hankali tana shaqar iskar yammacin,duk bata jin dadin gidan saboda dauke amna da dangin mamanta sukayi,sun roqi alfarmar a basu ita akwai bikin da ya taso zasuyi can dangin mahaifiyar shahidan,dr yace a basu.


           Gab da zata shiga sassan ta gamu da ammi,kishiyar amma tana fitowa ita da khadim,bisa dukkan alamu unguwa zata je


       Cikin girmamawa ta gaidata,tadan tsokani khadim kadan sannan tayi musu a dawo lafiya ta wuce ciki.


          Masu aikinta biyu ta samu a falon suna kai kawo,kowa da abinda yakeyi,ta gaidasu kamad yadda ta saba,daya daga cikinsu tace


"Tana kitchen" saita miqe zuwa hanyar da zata sadata da kitchen din.


          Kamar kowanne lokaci,a duk sanda maimunatun tayi magana ko tayi sallama sai taji kamar tasan muryar,yau ma da sauri ta juyo,sai taga maimunatun ce,ta sakar mata murmushi tana fadin


"Shigo ciki" kanta a qasa take takowa,tana mamakin yadda amma ga daukaki gayu,da wahala ka sameta ba cikin kwalliya ba,wannan ya zame mata jiki,kamar yanzun da take sanye da atamfa dark blue da yarfin baqi da kuma fari a jiki,jikinta yana fidda ni'imataccen qamshi,gashinta yananan da tsahonsa da kyansa,duk da girma daya fara nunawa.


          "Matso ki tayani hada wannan dambun,babanku keso,sai daya taho hanya kuma yayi magana" amma ta fada tana murmushi,saita amsa da to,ta janye hannayen hijabin nata zuwa baya sosai sannan ta ja zogalen dake cike da kwando ta fara gyarawa.


          Da fari shuru kitchen din yayi,sai qarar kayan amfani,amman ce ta katse shirun da cewa


"Inafata baki takura ba ko da maganar auren ja'afar?" Amma ta fada a tausashe,tana son ta bincika ta dabara ta tabbatar babu wata matsala,kunya ce ta bijirowa maimunatu,ta duqar da kanta hannunta ya fara dan rawa saboda hakan,amma ta fuskanci haka,ranta ya sake fari,don dama halaye da dabi'un maimunatu ba baqinta bane,tanason yin maganar daga ita sai maimunatun tun a wancan lokacin da dr ya shaida mata komai,to sai yau ta samu wannan damar,ta umarci masu aikinta duka su fice,don tana kunyar su jita tana maganar da maimunatun,kamar yadda tayi imanin itama yarinyar ba zata sake ba


"Sai kinyi haquri da ja'afar,zuciyarsa nada tsananin so,tun yana qaraminsa,idan yaso abu yana masa wahala sanda zai barshi,saboda ba qaramin so yake masa ba,hakanan idan yaqi jinin abu,akwai mata da yawa da muka saka rai a kansu kan zasu kawo canji ga rayuwarsa,saidai babu wanda mukaci nasara,ko a yanzunma zuciyata da jikina duka sunfi bani hope a kanki maimunatu,don Allah kiyi haqurin zama da ja'afar,don Allah,kada rayuwarsa ta tabarbare a rasa kuma sauran me zama dashi" sosai wani tausayin amma ya kamata,ashe itama abun yana damunta har haka,amma kunya da kawaici suka sanya bata nunawa?,a sanyaye a kuma kunyace ta gyadawa amman kai.


         Tare suka dinga aikin,amma.tana qoqarin sanyata sakewa da ita,cikin hikima ta dinga nuna mata itama kamar mahaifiya take a wajenta,ta dauketa kamar hakan.


           Sanda suka gama aikin gift amma ta bawa maimunatu na set din kayan wanka,cream,shower gel, perfume,body spray,hair mist da sponge a ciki,kallo daya tayi musu ta tabbatar masu shegen tsada ne,don qamshin da suke fitarwa ma na daban ne,don haka ta ajjiyesu,batason fara amfani dasu bare zuciyarta ta zarme.


          Sanda ta isa qofar sassan anni taji hayaniyar mutane,taji muryoyin wasu daga cikin yaranta maza,tabbas sune,don dazu da safe taji suna magana da umar kan zuwansu gidan commissioner,don haka taja da baya ta koma can bayan gidan tayi zamanta,don yau gidan duka basanan,sun tafi gidan babbar 'yar amma,wadda taci sunan anni,saboda yau din suke dawowa daga tafiyar da sukayi ita da mijin nata har na tsahon shekara uku,sai yau suka dawo,yau dinma babu yadda basuyi ta bisu ba tace aah,zataje watarana,haka suka tafi suka barta.



**********K'arfe uku da wasu mintuna akai suka sauka a adamawa,motarsu kuma ta kutsa kai cikin rugar ummaru a hankali tana keta burtali da kuma hanyoyin da mazauna rugar ke amfani dasu.


         Watannin da suke shude sun zamarwa maimunatu wasu sababbin shafukan rayuwa ne a gareta,cuke da tarin sauyi wanda yayi wancakali da qalubale wahala bauta da kuma azabtarwa data fuskanta a baya na tsahon wasu shekaru,ware idanu maimunatu tayi,tana kallon duk wani bigire daya zame wajen kiwo ko wucewa a wajenta,kewa sosai ta cikata,ta dinga tuno mummuna rayuwar mai cike da jahilci da kuma wahala,a yanzun da take ganin muhallan da hakan ya faru da ita,sai take ganin kamar mafarki.


           Duk inda motarsu ta keta sai ta kwashi idanu,saboda abu ne da ba kasafai suke ganinsa cikin rugar tasu ba,basu tsaya ko ina ba sai qofar gidan yuuma ramatu.


            Fa'iza da khadim wannan karon sune 'yan rakiyar,kusan sunfi kowa son tafiya muhallin daba nasu ba ba kuma su sanshi ba,sune a gaba janye da akwatin kayansu,maimunatu na biye dasu anni a bayansu.


          Cikin wani hanzari yuuma ramatu ta fito daga dakinta bayan bankade labule data yi,wani irin farinciki mara misaltuwa ne ya saukar mata,a wannan karon maimunatu ta fara rungumewa cikin matuqar farinciki tana cewa


"Miyatti Allah,miyatti annabi,maimunatu?,kece haka?" Murmushi maimunatun ta sake cike da kunya,yuuma kuwa baki ta saka cike da mamaki tana kallonta


"Kinga ta canza miki kenan ramatu" anni ta fada tana 'yar dariya


"Ba kadan ba kuwa yafendo" yuuma ta amsawa anni tana maida dubanta kanta,sai a sannan ta marabcesu gami da yi musu jangora zuwa dakinta,bakinta har kunne,ta rasa inda zata sakasu.


          Bata zauna ba tahau dora musu abinci na musamman kamar yadda ta saba,duk yadda yuuma taso maimunatu tayi zamanta amma ta qiya,tare suka dinga shirya komai,suna aikin suna hira,yuuma tana tambayarta labarin rayuwa a can,bata boyewa yuuma komai ba,ta yabi anni ainun kan irin tarin karamcinta da yadda ta sauya mata rayuwa


"Indai yafendo ce,bakiga komai ba,a jininta yake,dabi'arta ce" jinjina kai maimunatu tayi,tana sake gasgata zancan yuuma.


         Tunda suka fara aikin take satar kallon qofar dakin daada dake a rufe,bata ji motsinta ba bata kuma ganta ba daga ita har yaran,cikin ranta take tunanin inda suke,daga bisani taji yuuma na gayawa anni suna ta tafi maqotan rugarsu,qanwarta Ayaana ce ta haihu,sun tafi duka ita da yaran,cikin ranta take tambayar shi kuma ibrahim fa?,ba zata iya tambayar yuuma ba,abun ma baiyi tsari ba,tunda tasan ainihin dalilin ma daya kawosu garin,wanda tabbatuwarsa zai sake nisantan tsakaninta da ibrahim din har abada.


         Gefin magriba suka gama komai,maimunatu na saman abun sallah,ta idar kenan saiga sallamar daadan ita da iyalinta,cikin murna da zumudi ta zarto dakin yuuma,don ta sani tabbas zuwan anni alheri ne,bata zuwa haka hannu babu komai.


          A girmame ta gaidata,fa'iza da khadim da sukayi zaman cin tuwo suma suka gaidata,sai maimunatu ta waiwaya kadan itama ta soma gaidata.


         Dan jim tayi na sakanni saboda ji da tayi kamar tasan muryar,amma canzawa maimunatu da kuma rashin wadatar haske a dakin ya sanya bata gane wacece ba,har sai da zubaida ta ankarar da ita


"Daada fa kamar maimunatu na gani a tare dasu" harara ta balla mata


"Maimunatun da aka kai aikatau ce zata koma haka,ke arcan"


"Wallahi tallahi daada" shuruu tayi tana nazari,ita kanta kuma taji muryar kamar tatan


"Toooo,anzo wajen,Allah yasa ba wata tsiyar ta shuka suka dawo da ita ba,in kuwa hakane nita cuta,saboda kayan dana buqata na aurensu da himu ko rabinsa ba'a gama siya ba.....maza tashi safiya kije ki shaidawa fulera zuwansu,don na tabbatar batasan tazo ba,tunda dazu da zamu gitta ta shiyyarsu mun hangi juna mun gaisa amma bata yimin maganar ba" rai safiya ta bata tana duban daada


"Haba daada,daga zuwan ta,kawai saiki fassara zuwan da mugun tunani,don Allah ki daina haka,irin wannan abubuwan su suka saka ya himu fa kullum bashi da cikakkiyar lafiya" da murfin tukunya ta jefeta,ta kuma balbaleta da masifa,a dole safiya ta miqe tana qunaqunai ta wuce gidan inna furera.


           Sanda labarin ya isketa saita kasa zaune ta kuma kasa tsaye,fargaba ta cikata,ita ba abun ta tafi gidan yanzu taji meye ba'asi ba,haka dai ta daure,ta cewa safiya tace musu tana musu sannu da zuwa.


       Bayan sun gama cin abincin daren anni ta sanya khadim da fa'iza suje su raka maimunatu ta gaisa da inna furera,a sannan ta samu sararin yin magana da yuuma,ta shaida mata abinda ya kawosu.


        "Alhamdulillahi,alhamdulillahi,lallai wani hanin ga Allah baiwa ne,Allah ya tabbatar da duka alkhairi,Allah ya baki ladan wannan jihadi da zakiyi yafendo,ubangiji yasa alkhairi ya kuma hade mana kansu fiye da yadda muke zato da tsammani"


"Ameen ramatu,ameen"


"Kinci sa'a kuwa kawunsu yana nan,nan da bayan isha'i zai shigo gidan"


"To alhmdlh" anni ta fada tana jin zuciyarta wasai.


             Zau biyu maimunatu tana yin sallama inna furera bata amsa ba,sai idanu data bita dashi bayan fa dgaa fitila ta hasketa da kyau,sai datazo gab da ita sannan ta zabga salati,zuciyarta cike fal da qunci da rudanin ganin maimunatun tamkar an sauya mata halitta,maimunatun kamar wadda aka yiwa wankan inji,duk da cewa tana nan itama lalitarta suna cika duk qarshen wata da kudin aikin maimunatun 


"Ke yarinya,ina fatan ba wata muguwar aika aikar kika tamfatsa ba aka maidoki ba,don wallahi ban gama hada kudin auren gaje ba,kika sake kuwa haka ta faru dake na rantse miki da Allah na lahira sai ya fiki jin dadi" takaici da mamaki suka cakude suka hadewa maimunatu,wai ita din yayar mahaifiyarta ce,sannan ita din a yau baquwa take ga inna furera,amma irin tarbar da zata samu kenan daga wajenta


"Babu abinda ya faru inna,kawai zuwa mukayi gaisheku" ta amsa mata tana nemawa kanta wajen zama bayan ta nunawa su khadim inda zasu tsuguna suma.


           A gaba ta sanya maimunatu da tambaye tambaye,tambaya maras ma'ana tabin qwaqwafi,har maimunatun ta fara jin kunyar idanunsu fa'iza,saboda tambayar tayi yawa.


         Zuwa jimawa kadan saiga laulo ya ashigo shi da gaje,yaja ya tsaya turus a gabanta ya zuba mata idanu,sai kuma ya washe baki yana kiran sunanta,abinda yasa gaban gaje faduwa,ta kuma waiwayo tana duban tsaleliyar matar da ake kira da maimunatu.


           "Turqashi" ta fada qasan ranta,qarara baqinciki da kuma hassadarta ta bayyana,don takawa tayi gabanta ta kuma duka taba kiran sunanta don tabbatarwa ita dince,maimunatun kuwa ta amsa da kyakkyawar zuciya,ta kuma bi gaje da murmushi,murmushin da gaje ta dinga jin cewa da biyu tayi mata shi,kawai saita miqe tayi daki fuuu.


           Ganin zaman da suke bana wani abu bane sai na banza ya sanya maimunatun tace da.inna furera


"Inna zamu wuce,sai da safe"


"A'ah,ki wuce ina?,ai kuma kinzo kenan,ke da tafiya sai zaku koma,wala'alla ma gajee ta ta fansheki,taje itama ta dandana ta dawo" maimunatu naji na gani inna fureta tace mata nan kwana fa,ko raka su khadim zuwa hanya don ba zasu gane ba ta hanata,sai laulo ta sanya ya rakasu,ita kuma taci gaba da zama a nan tana amsa tambayoyin innar,don yanzu ta samu guri sosai ganin yaran sun tafi.


           Shuru innar tayi,wani abu yazo ya tsaya mata a wuya,tana tsoron kada fa maimunatu a nan gaba ta zama wata,ta kuma fisu a komai,anya ba fitittike musu zata yi ba?,tayi kwance kwance ta zayyano musu aibubbukan data dade da laqabawa maimunatu ta bata ta a wajensu ta basugaje itama taje ta dandali wannan arziqin?.


No comments

Powered by Blogger.