Gurbin Ido 25


  Kamar jabir din ya shareshi,sai kuma ya kasa,ko babu komai yana buqatar kwantar da hankalinsa kada kuma ya birkice musu a koma 'yar gidan jiya,bayan abubuwan suna danyi kyau ba kamar can baya ba,don haka sai ya kwasa shima ya bishi.


           Cikin rashin sa'a ya sameshi ya kulle kansa a dakinsa,yayi ta bugu ya bude masa amma yayi kunnen uwar shegu dashi,ya sani ya qulu sosai,kuma cikin bacin rai yake,haka dole ya haqura,saidai yana fatan kada ya jima a kulle a dakin temper tayi masa yawa.


        Komawa yayi ya zauna saman kujerun falon,kam kujerar dake fuskantar dakin,lokaci lokaci yana danna wayarsa yana kuma duban qofar dakin tare da fatan ya bude,saidai har kusan awa guda da rabi ba motsinsa ko alamar budewa,abun da yadan saka jabir yaji shakka a ransa,sai ya sauka daga game din da yakeyi don dama ta fara isarsa,ya kirayi layin anni.


           Gaisawa suka fara yi sannan ya gaya mata abinda yake faruwa,duk da taji fargaba itama cikin ranta amma saita dake


"Rabu dashi,zaiyi ne ma ya gama,kayi sabgarka,idan ya gaji ya fito" ta fada cikin dakiya,murmushi jabir yayi,don shi kansa yasan dakiya kawai annin tayi.


         Suna gama wayar ya isa ga makunnin kayan kallonsu ya kunna tv din,sannan ya maida channel din dake kai zuwa saudi qur'an da madaidaicin sauti,ya ajjiye remote ya wuce dakinsa ya sauya kayan jikinsa daga shi sai farar singlet da boxer,ya fidda siyayyar da yayo,yakai daki sa,saura kuma ya wuce kitchen dasu.


            Abinci ya fara shirya musu,yana aikin amma hankalinsa yana falo,yana yi yana leqawa ki ja'afar din ya fito,saidai har ya gaji da leqan baiga ya fito ba,tilas ya haqura har ya gama abincin.


           Yana fitowa daga kitchen din yana qoqarin fidda afron din jikinsa jaafar din na fitowa a dakin,sosai jabir din yaji dadin hakan,ganin fushin baiyi tsaho ba,a yanzun ma ya sake wanka ne don kayan jikinsa na dazun ba sune yanzu ba.


           "Ina zuwa?" Jabir ya tambayeshi yana fidda ruwa daga fridge


"Zamu fita da mr mickey,akwai meeting da zamuyi,so if i stay long kada ka jirani"


"Abincin fa?"


"Ka cinye kayanka" dariya  ce ta qwacewa jabir,ya sani fushi yake dashi,yaji haushin that's right da ya fada,da kuma goyon bayan anni da yayi,fushinsa ne ya shafi abincinsa


"Cikinka ba nawa ba" ya bashi amsa sanda yake takawa zai fita daga falon,saidai bai waiwayo ba ya fice abinsa,kamar ma baiji abinda jabir din ya fada ba.


        Diban iya wanda zai isheshi yayi ya sanya masa sauran a fridge,yasan idan ya dawo zai nema abincin da kansa,don duk abin nan nasa baya wasa da cikinsa ko kadan.


       Shirye shirye ake gadan gadan daga gidan dr marwan akko na aurar da ja'afar din,wanda tun ranar da sukayi waya da anni bai sake neman kowa ba,kamar yadda itama annin ta watsar dashi,hakanan daga ita har dr babu wanda ya sake nemansa,shima hakan yayi masa,don kuwa ya riga ya gama shiryama ransa komai,baiga ta yadda yana namiji me cikakken hankali,ba auren fari ba za'ayi masa irin wannan karan tsayen,ya tuhumi kansa da kansa kan ceqa ya bawa anni dama ne da yawa cikin rayuwarsa shi yasa tayi wannan tunanin,bama su da suke nigeria ba,hatta da jabir baibi ta kansa,ya shiryama ransa zai koma nigeria ne a duk sanda ya gama uzurorinsa a nutse.


           Ta bangaren jabir kuwa duk da ya damu,yana kuma ankare da abinda ke faruwa amma bai nuna ba,shima shirin tafiya gida yake,saboda a yanzun aurensu su biyu za'ayi,sbi da ja'afar din,anni taso a hada harda su salma amma sai aka samu tsaiko,hisham bai fidda gwanarsa ba,hakanan salma tana kan qadamin kammala nata karatun ita da hafsat da kuma laila,don haka annin tace a barshi zuwa sanda zasu gama din watanni shida nan gaba masu zuwa.


********Dai dai lokacin da suke shigowa farfajiyar gidan sanye da hijabansu na makaranta suna taba hira,motar dake fake a parking lot na gidan ta tsaya,mamallakiyar motar ta budeta ta fito.


         Zabgegeyar farar bafulatana,fara tas,wadda kamanninta da haj aishatu ta nuna qwarai,sanye take da wani danyan lace daya kwanta a fatarta,komai na jikinta matching ne,jikinta ba abinda yake sai fidda wani tatausan qamshi,tana rungume da baby boy wanda duka duka bazai wuce shekara daya da watanni biyar ba.


           "Auty maama" 'yammatan suka kusa hada baki wajen kiran sunanta,tana rufe motan da key ta waiwayo tana dubansu,fuskarta ta wadatu da fara'a sosai,macace m'abociyar fara'a da kuma kirki,bata debo a qasa ba,ta debo kyawawan halayen mahaifiyarta haj aishatu umar sanda da kuma dr marwan akko


"Yammatan gidan baaba dr" ta fada sanda suka qaraso gaba dayansu,murmushinsuka sako,don dukkansu sunji dadin zuwan nata,saboda akwai shirye shiryen da suke akan bikin gidan,wanda sun tabbatar bazaiyi armashi yadda suka tsara ba saita ce wani abu,a matsayinta na babbar yayarsu,wasu na shirin amsar yaron hannunta,yayin da khadija ta amshi hand bag dinta,suka soma rankayawa ciki bayan sun gaisheta hira ta balle.


         "Ina kuka baro maimunatun kuma yau?" Anty maama ta tambaya sanda suke gab da shiga ainihin ginin gidan,inda zao sadaka da qofar kowanne sashe dake cikin gidan,sai a sannan suka laluba suka ga ba maimunatun,da alama guduwa tayi saboda anty maaman


"Tare muke guduwa tayi halan,kinsan halinta,halim fulani ne har yanzu a jikinta,bada kowa yanzu take iya haduwa cikin gidan nan ba,hatta amma wasan buya sukeyi" murmushi ya kufcema anty maama,kunyar yarinyar da kamun kanta yana matuqar burgeta,duk da a cikinsu take amma bata yada dabi'ar kunya ba,har yanzu yarinyar batasan hanyar gidanta ba,da hirar maimunatun suka rakata ta gaida ammi sannan ta isa sassan mahaifiyarta amma,bayan ta aikawa anni da saqon gaisuwa gami da sanarwar ta iso zata shigo.


       "Ina duka yaran?" Amma ta tambayi anty maama


"Suna islamiyya,amma for now nasan ma sun taso,nace ma iliyasu driver ya wuce dasu wajen haj,idan na dawo zan biya na debosu"


"Yayi kyau,Allah ya taimaka" amma ta fada,don ba wani dogon hira suke da ita can can ba,kasancewarta diyar fari a wajenta


"Wai maimunatu nita gani ta gudu amma?" Anty maama ta fada tana dariya,sai amman tayi murmushi


"Kyagaji da gani indai maimunatu ce,yanzu ko sassan nan bata zuwa" kai anty maama ta gyada,kamar ba zata ce wani abu ba sai kuma ta magantu


"Allah dai ya tabbatar da alkhairinsa,ubangiji yasa ta zame ma rayuwar ja'afar haske,nafi sanya hope a kanta amma akan samiha gsky,duk da ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,Allah yasa dai manya ya riqesu da kyau" ajiyar zuciya amma ta sake,don abinda taketa tsoro da fargaba kenan,musamman da yadda kwanaki suketa matsowa,amma bataji.batun dawowarsa ba,koda kuma sunyi waya baya ce mata komai kan dawowar tasa ita kuma bata taba tambaya ba saboda.kara da kuma alkunya,amma dai duk sanda tayi sujjada tana gayawa Allah,wannnan shike bata nutsuwa.


        Bata jima sosai ba tace bari taje wajen anni ta fita a sashen.


            Bayan gama gaisuwa da 'yar tsokana da wani lokacin take kwasan annin da ita,sai anni ta kirayi sunanta


"Inaso kiyimin total na kayan jere dana kitchen,babanku ya buqata,zai siyawa maimunatu" 


"A ina anni"

"Oho,wani kamfani ne yace anan da suke kawo kaya daga turkey,da so yayi aje can direct,to kuma lokacin ya qurace,danginta daga can gembu sun nema ya barsu suyi kayan,yace ai diyarsa ce,duk da haka saida suka aiko da kudin kayan,to nace gwara a siya wani abun me daraja da kudin a bata,tunda shi yayi niyyar yin kayan"


"Ma sha Allah,abbi ya kyauta,kuma hakan yayi,ko gold ne sai a siya mata,ba matsala anni" ta amsa mata tana fiddo wayarta daga jaka


"Yauwa,sannan kuma,bashi nakeso ki bani" kai ta daga tana duban anni tana 'yar qaramar dariya


"Me zakiyi da bashi kuma tsohuwa,bayan duka lalitar familyn farouq kumo na hannunki"


"Ke banson iya shege,kiyi ta kanki,magana nake miki ta gaske,aron kudi zaki bayar,amma ni ba kawomin zakiyi ba,lefe nakeso ki hada na maimunatu dana samiha,banason sanya kudina nazo na kasa tambayar jafar,idan nakine sai nafi maida kai ya maida miki kudinki akan kari,so nake komai yayi da kudinsa saboda sai yafi jin auren a jikinsa" dariya anni ta bawa anty maama,ta wani fannin kuma jikin anty maaman yayi sanyi


"Wai har yanzu baice komai ba?,baya cewa komai?" Kai anni ta jin jina


"Eh,amma ki barni dashi,idan yasan wata ai baisan wata ba,kallonsa kawai nakeyi,zai shigo hannuna ne,baisan wace maryam kumo ba har yanzu" ajiyar zuciya anty maama ta saki


"To Allah ya kyauta,ya kuma shiga lamarin"


"Ameen ya hayyu ya qayyumu,jabiru ya turo nasa kudin ta hannun hisham,duk da naji yace akwai wasu kayayyakin daya siya musu shida jafar din,daso yayi ya biya harda na jaafar din na hanashi"


"Eh gwara da bai biya din ba,gaskiyarki anni,gatan sai yayi masa yawa ya gaza riqe abun da muhimmanci"


"Shina gani ai" anni ta fada da qwarin gwiwa,shi yasa takeson anty maama din,saboda tana da matuqar hankali da nutsuwa


"Ba damuwa,naga wasu akwatuna sabbin design masu goma goma,zan siyawa jabir a matsayin gudu mawata,shi kuma zan siya masa set daya,set daya kuma zan saka cikin lissafinsa"


"Yayi dai dai,Allah ha saka miki da alkhairinsa kema,ya qara muku zumunci,Allah ya qara hadamin kanku" anni ta fada cikin jin dadi


"Ameen summa ameen" daga nan suka shiga tsara yadda komai zai kasance daga kan kayan lefen zuwa sauran hidimomi na bikin,harda yadda za'a gyara maimunatu duka anni ta dora saman wuyan anty maama.


       Bayan ta gama da anni kuma ta koma bangaren qannenta,a sannan su salma sun shigo,nan suka zauna suka tsara komai bisa tsari da kuma burgewa,saidai har suka ci suka cinye hirarsu babu giccin maimunatu.


         Can cikin garden na gidan ta boye kanta,batajin komai a kan auren tunda batasan meye gundarin abinda ya qunsa ba,bata gama wayewa da sanin meye shi ba,bata saba da zabin abubuwa a rayuwarta ba bare tace wannan zabin bai mata ba,kota damu,kawai dai tana jin kunya da kuma nauyin mutan gidan,tunda tasan meye surukuta,ta gefe guda kuma wani lokacin zuciyarta nayin rawa da kuma d'ar d'ar,tunda ta sani cewa kowacce mace tana auren namijin daya ganta yace yana sonta,itama ta maida masa martanin tana sonshi,amma ita nata angon batasan wanne kala bane,daga wacce duniya zaizo?,yaya kuma zai karbeta?,wadan nan sune kawai abubuwan sa takan nanatawa kanta lokaci zuwa lokaci,saidai yadda taga kowa ya daukaki abun a gidan yana bata mamaki,sannan yadda su laila ke sanyata a gaba,suyita gaya mata abubuwa game da angon nata sai ta yita mamaki,don ita bataga alfanun hakan ba,kiyi kaza kiyi kaza,kullum maganarsu kenan,sun canza mata abubuwa masu yawa,kama daga manta turarenta sa sauransu,itakam duka bataga wannan takurar da tsare tsaren na meye ba,badai a daura aure bane kawai a kaita can gidan ba shikenan dai?,amma magana daya biyu sai suce kina da kishiya,saikinyi kaza kinyi kaza,itakam bataga wani abun damuwa da damun kai ba.


********Cikin tsari ilimi da kuma gogewa anty maama ta hada lefe na alfarma,kowacce amarya ta rabauta da akwati goma goma,rana daya aka kai na samiha dana amaryar jabir Aaliya,said kuma kumbo da ammi abokiyar zaman amma ta qarawa kowacce amarya guda hurhudu,shima kowanne shaqe yake da kayan al'adun aure dana zamani,abun dai ya qayatar ya kuma bada sha'awa sosai.


         Tarbar girma suka samu daga kowanne bangare na gidajen amaren,suka dawo gida suna yabon tarbar da suka samu,suna kuma tattauna yadda suka fuskanci dangin hajiya Aayah dama ita kanta haj aayah din keji da samiha,kasancewarta diyar fari a wajenta da zata fara aurarwa,su uku kuma kacal Allah ya bata.


         Gembu aka yanke za'a kai lefan maimunatu,za'a kuma tafi ne har da ita,daa sunce abar kayan basai an kawo ba saboda gudun wahala da kuma zirga zirga,amma anni tace sam,aure za'ayi mata na gata da kuma 'yanci cikin danginta kamar kowacce diya,za'a kai mata kayan kamar yadda aka kaiwa kowa,kuma za'a daukota daga gaban danginta a kawo musu ita.


       Wannan abun da anni tayi yayi matuqar qara mata kima da daraja a idanun dangin maimunatu,ya kuma qara musu qaimin fidda maimunatu kunya,tare da nuna ita din jininsu ce,duba da abunda bare tayi mata?,ina ga su da suke jininta?.


         Kamar yadda annin ta tsara kuwa haka akayi,bikin saura sati biyu suka daga gembu da maimunatu da kayan aurenta.


         Gidan kawu sule suka sauka,qani ne ga mahaifin shatu mahaifiyar maimunatu,mutum ne mai zumunci ba laifi,qaddarar abubuwan da suka farun zasu faru yasa ya barwa fulera riqon shatu dama maimunatu,uwa uba kuma da yadda ta nuna tsananin tausayawar tata ga 'yar uwarta,abinda yaja kawu sule kenan,ya dinga tunanin ko wannan abun ya kawo jituwa da gyaruwar alaqa tsakanin su shatun da yaran inno,yayi tunanin ya barta ko Allah zai sake dai daita al'amarin,kuma har yanzun nan baisan rayuwar da shatu da diyarta maimunatu suka fuskanta ba,yayita yabawa fuleran ma,ya tsammaci aiki tayi da hankali tace a kawo auren nan wajensu sabida girmamawa,baisan ko labari bata dashi ba,sai bayan da yuuma ta tabbatar sun sauka a gembu sannan ta aikaqa fulera da saqon ankai kayan,abinda ya dugunzumata,ya kuma bata mata rai,kamar yadda suke da maimunatu amma ace sai daga wajen baare zata samu labarin aurenta?,ta kuwa ci alwashin tafiya gembu cikin satin ko satin gaba,lallai sai ran kowa ya baci,idan sunsan wata ai basusan wata ba

No comments

Powered by Blogger.