Gurbin Ido 28
28
Wani kallo ja'afar ya watsa masa,da alama gayyar al'umma yayo musu,wanda shi baisan da hakan ba,bai kuma shiryama tarbar kowa ba,dakinsa ya wuce ya sauke amna saman gadonsa,tana ta faman zuba masa
surutu,labarai iri iri,a lokacin idan kaganshi kai baka ce miskilin ja'afar din nan bane,mai yawan dakiya tsare gida da kuma shan qamshi,duk yabi ya cika fuskarsa da fara'a,hakanan duk tambayar da amna tayi masa sai ya bata amsa,saidai da yake halin a jininsa yake,ba jimawa yaji kansa ya fara cakewa da surutun amnan"Amnee.....pls be quiet for a while,ki huta kada maqogoronki yayi ciwo,zanyi wanka,idan na fito then sai muci gaba" kai ta gyada masa,sai dai tun bai gama fidda kayan jikinsa ba taci gaba daga inda ta tsaya.
Yana daga toilet din ma yana saurarenta,murmushi kawai ya saki ya girgiza kai
"Surutun waye tayi haka?,shaheeda?,nooo....shaheeda nada hira,amma bata da surutu me yawa,salma?,laila?,hafsah?,maybe ya amsawa kansa da kansa yana tabe baki.
Sanda ya fito ya taddata da jabir,da yake shi din sarkin yara ne ya biye mata sosai sunata sabgarsu,sai ya juya ya buda walking wardrobe dinsa ya shiga yana duba kayan da zai saka,kafin ya futo sun fita,sai ya fasa shirin fitar da yayi niyya,ya saka boxer dinsa kawai ba tare daya nema ko singlet ba,turarukansa ya fesa,sannan ya shafe lallausan baqin gashin dake cike aqirjinsa wani irin azababben oil perfume,yabi lafiyar gadonsa ya kwanta,bayan ya ragewa dakin haske ta hanyar sauke duka labulayen dakin,ya kuma kashe duka fitilun dakin.
Bacci yayi sosai mai wani irin nauyi da dadi wanda ya jima baiyi irinsa ba,knocking da ya dinga ji sama sama cikin barcinsa ya sanyashi bude kyawawan idanunsa da suka qara girma saboda bacci,yadan mutstsukasu kadan,sannan ya ture lallausan duvet din daya rufe jikinsa dashi,ya zuro qafafunsa qasa yana miqewa,ya isa qofar ya bude.
Jabir ne dauke da amna,kwalliyar jikinsa ta bambanta data dazun
"Wanne irin bacci kake?,ko a masallaci ban ganka ba"
"What?" Ya fada calmly,ya aza idanunsa ga agogo,sai yaga har bakwai tayi,a hanzarce ya saki handle din qofar ya shige toilet don ya daura alwala.
"Na shirya zan fita mukaci karo da abbi yana dawowa,yace na gaya maka yanason ganinmu after isha prayer" kai kawai ya gyada masa,yana budewa amna hannunsa,ta taho da hanzari tana ci gaba da zuba masa surutunta,tare da bashi labarin inda sukaje dazun,sai jabir ya miqe ya fita ya basu waje.
Yana shirin fita sallar isha din hisham ya shigo,cikin girmamawa ya gaidashi,ya amsa masa yana sanya qaramar hular tashi ka fiya naci saman sumarsa
"Ina kaje duka yau?" Kansa yadan shafa
"Ina da patient ne yau a asibiti da yawa da zan gani,so bayan kuma na gama dasu na wuce wajen gidan yaa jabir,na sallami companyn da suka zuba home decor na gidan" kansa ya gyada kawai,hisham din ya daukar masa abun sallah suka fito zuwa masallacin suna taba hira kadan kadan.
Sai daya sake komawa ya duba ammansa,sannan ya wuce sassan anni,ya nema abinci wajen baba tabawa,wadda dama tun da can gurinta ko wajen ammansa yake cin abinci duk gidan,to sassan amman nasa yaga ya soma cinkoso,bazai iya tsayawa karbar komai na sassan ba,don bashi da tabbacin amman itace ta girka duk abinda za'a bashin.
Yana ankare da yadda annin keta faman cin magani,sai shima ya basar kamar bai gani ba,ya zauna sosai hankali kwance yana cin abincinsa,cokali daya bakinsa,cokali daya bakin amna hira,duk tabi ta cikashi da zancen adda maimoon,kome yayi mata sai tace 'haka adda maimoon takemin'.
Yana gamawa cikin sa'a yaji shigowa abbi,don haka ya miqe yana dauke da amna
"Kaje ka dawo,kazo muyi lissafin kudin kayan lefen da maama ta ranta maka ka zube mata abunta"
"lefe?,lefen wa?"
"Au da tattabaru kayi zaton za'a aura maka?,ko kuma babyn roba na wasan yara?,'ya'ya ne kamar kowa masu gata,ehe" anni ta maida masa amsa sannan ta fuske,sai kawai ya juya baice da ita komai ba ya fice,yana jin haushi yana sake cika masa zuciya.
Da sallama ya shiga katafaren falon dr marwan khalid akko,can ya hangesu saman dining shi da jabiru,da alama zamansu kenan,yayi masa izinin ya qaraso,yana jawo kujerar sake daura dashi hadi da nuna amna yace ta zauna,tayi daraf kuwa fa haye ta fara masa surutun nata,har sai da ja'afar yace cikin lallausan muryarsa,very calm
"Amnee,pls....keep quiet" narai narai tayi da idanunta,don bata gama bawa daddy dr kamar yadda take kiran abbi ba labarin da take bashi,to amma ita kanta duba daya uban nata yake mata take laushi,dole tayi shuru,ta fara saka yatsanta tana dangwalan romon pepper soup din kifi da aka yiwa abbi.
A sannan ya samu suka gaisa da abbi din,ya musu maraba,sannan ya tura masa warmers din yace ya diba abinci yaci
"Am full abbi,yanzu na gama ci wajen anni"
"Yayi kyau" yace yana ci gaba da cin abincinsa,sai dinning din yayi shuru,kasancewar dabi'ar abbi din,ba kasafai yake cin abinci kuma yana magana ba,har sai ya kammala,shurun da ya sanya ja'afar ciro wayarsa,yanajin abbin da jabir suna magana jefi jefi,wanda kusan duka kan tsare tsaren bikinsu ne.
"Bismillahi" abbi ya fada yana zama saman kujerun falon,yayin da jabir da kuma ja'afar kowanne yayi matsugunni a qasa
"Kai jabir alhmdlh,mun gama duka maganar da zamuyi dakai.....am ja'afar,abinda yasa na kiraka" abbi ya fadi yana gyara zamansa sosai,gami da cire hularsa ya aje gefe
"Inason in tambayeka......wacece ta haifeni?" Girma maganar ta yiwa ja'afar sosai,har sai daya dago suka hada ido da abbi,kana ya maida idanunsa qasa
"Anni ce abbi"
"Ma sha Allah,to ban sani ba,ko ka manta ne,dani da umar da sagir da abbas da usman.....dukkaninmu anni ce ta haifemu,kuma qarqashin ikonta muke damu da dukka abinda muka mallaka,ba zanyi magana me tsaho ba,saboda nasan kasan matsayinta a wajenmu,hatta da mahaifiyarka zabin anni ce idan baki sani ba,shi yasa ta zamto ta musamman a wajena,na kuma yi dacen da maza dubu basuyi ba,dukka hukuncin da anni ta yanke a kanka yatabbata,kuma ba komai bane ya janyo hakan ba ina da.imanin qauna ce da kuma damuwa da halin da kake ciki,Allah yayi maka wata iriyar zuciya data banbamta data kowa,amma ka sani,jajircewa da karbar al'amura a yadda sukazo suna iya kawo sauyi,hakanan lokaci yana iya warkar da kowanne irin ciwo komai girmansa,duk wani abu da zakayi a yanzu akan aurenka shizai nuna dai dai matsayin anni a wajeka,idan ka wulaqantata ko ka watsa mata qasa a idanu to ni ubanka marwan ka yiwa haka,idan ka karba abun da kima da mutunci,ka kuma riqeshi da daraja to ni ubanka marwanu ka mutunta,saboda haka zabi ya rage naka,dan halak dai shike rama halacci,anni kuwa halacci tayi maka ba butulci ba,zanga dame zaka sakawa mahaifiyata".
Maganganu ne gajeru marasa dogon zango,saidai nauyinsu yafi qarfin wani ma'auni ya iya gwadasu,shigen shigen magana irin wannan bata taba hadashi da mahaifinsa ba sai a wannan karon,nauyin maganganun da har dr ta sallamesu basu bar dukan sassan jikinsa ba,har sun kusa fita ya sake kiransa
"Ka shirya daga yau zuwa gobe,kaje gidan minister ka gana da unaisa"
"Unisa?" Ya fada cikin ransa,yana jin he knew the owner of the name UNAISA,to amma a ina?, somewhere..... somewhere,for sure,indai gidan minister ne,bu he may not remember ainihin inda yasan ta din.
Dukka wannan shi da zuciyarsa yake wannan tadin,wanda tuni ya riga yace da abbi "To" yabi kuma bayan jabir sun fice.
"Ya?,yau din zamu wuce?,don inason naje naga fatima gaskiya,i missed her badly" yana jin iya maganarsa ta yau ta qare,so saboda haka bashi da abinda zai cewa jabir din,saidai ya masa wani kallo,yana shirin yi gaba jabir din yasha gabanshi
"Shawara guda daya J.pls and pls,kayi qoqarin bin maganar abbi,indai har kai din masoyin shaheeda ne da gaske,na tabbatar da tana raye itace mutum ta farko da zata fara tursasaka kabi abinda dukka magabatanka suke so,for the first and last time may be da sukeso kayi musu wani abu cikin rayuwarka,we will see if you can do it" jabir yakai qarshen maganar yana duba yanayin ja'afar,duk da cewa ya bashi baya,kamar yadda ya zata din,baice masa komai ba sai gaba da yayi ya barshi a wajen.
Sassansu ya yanke ya koma kawai,saboda kansa gaba daya ya gama daukan zafi,tako.ina abbi ya gama daureshi,tun jabir baice komai ba dama ya riga daya yankema ransa dole ya tsaya ya fuskanci komai,zaiyi duk yadda abbi da anni keso for the sake of them.
Ya jima a haka kafin yayi qoqarin dai daita nutsuwarsa,ya daga waya ya turama hisham tex kan ya kawo masa amna,ba jimawa sai gashi da ita,ya dire masa ita ya juya.
Jaka guda ta kayan wasan daya jima yana siya ya tura mata,duk sanda ya fita yaga wani abun wasa saiya tuna da ita,sai kuma ya siya ya ajjiye,murna ta ishi amna,ta dauki wancan ta ajjiye,ta dauko wannan ta ajjiye,komai sai data nuna masa,kamar ba shi ya siyo ba.
A gaba ya sanyata yana kallo kawai,iya wannan farincikin nasa ya sauke kaso mai yawa daga cikin nashi bacin ran,abu na qarshe da yarinyar ta fada shi ya tashi zaman nasu,ya kuma dawo da mutuwar shaheeda da twin sister dinta amra danya a ransu duka su biyun,kewa da maraicin shaheedan ya kamasu
"Daddy.....mommy taqi dawowa,taqi kawomin amra muyi wasa,daddy yaushe zasu dawo?,zanyi fushi fa daddy" cikin jikinsa ya rungumeta,yana shafan gadon bayanta
"Kada kiyi fushi,kita musu addu'a kinji?,zamu hadu dasu in sha Allah sooner or later"ya fada yana qoqarin hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya.
Ta jima a haka kwance a jikinsa,yana jin yanayin saukar numfashinta da yadda ta qara nauyi a jikinsa ya tabbatar tayi bacci,sai ya miqe sabe da ita,daya hannun nasa kuma yana riqe da jakar kayan wasanta yayi sassan ammansa da ita.
Yana shiga tana shigowa itama falon daga ainihin qofar baya na sassan nata da zata sadaka da masaukin baqi na gidan,ita da masu aikinta su biyu,lili da laraba,suna dauke da jibga jibgan duvet da ana fiddosu yawanci a lokacin taro irin wannan musamman saboda baqin.
Jikinta sanye da Egyptian hijab daya saukar mata har qasa,duk da dare ne amma akwai eye glasses tare da ita,wanda takanyi amfani dashi lokaci lokaci idan taji bata jin dadin idanuwanta.
"Karbeta lili,ki kaimin ita dakina,idan kin shiga ki rage qarfin acn nan,don naji kaman mura nason kamata" a ladabce ta amsa,ta dauki amna da ja'afar ya shimfide mata saman kujera ta wuce ciki
"Manya" ta kirayeshi da sunan da takan kirashi dashi don ba kasafai zakaji ta kirayi sunan nasa kai tsaye ba
"Zauna muyi magana" kamar yadda ta umarceshi haka yayi,ya koma ya zauna din yana bata hankalinsa
"Kayimin wata alfarma man" sosai yake duban amman tasa,abinda yasa ta fahimci tambaya yakeson yi kan alfarmar data ambata
"Don Allah na roqeka,ka daure ka karba qaddararka a duk yadda tazo maka,kada kayi wani abu da kasan cewa ba dai dai bane,ka riqe amanar da aka baka bisa gaskiya da na sanka da ita,don Allah"
"Ku daina roqata hakanan amma,kunfi qarfin haka a wajena" ya amsa mata yana bata assurance din haka ta cikin qwayar idanunsa,ta san yana da qoqarin bin umarnin na sama dashi daman,saidai sanin halinsa yasanya mata shakku kadan,amma a yanzun hankalinta ya gama kwanciya gaba daya
"Allah yayi ma rayuwarku albarka,shikenan sai da safe"
A daren gaba daya ya gama lissafa yadda zai tafi da komai,yadda zaibi umarnin mahaifansa ta gefe guda ba tare da rayukansu sun baci ba,hakanan ba tare kuma da matan da aketa qoqarin liqa masa sun dameshi ba,don haka a washegari bayan ya shirya ya fito,ya nema ma'aikata daga cikin kamfaninsa,ya tsara musu abinda yakeso.
Cikin gidaje hudu da yake dasu ya zaba daya,wanda yake dan nesa kadan da nasu gidan,yasa aka hau aikinsa baji babu gani,don dama gidan kusan an gama komai nasa,fenti da saka qwayaye da sauran kayan qawata gidanne kadai ya rage,abinda yasa yayi saurin yin hakan,don bayason abbi ko anni wani yace su zauna a ainihin gidansa dakegovernment house road,don yafi kusa da nan gidan nasu,gidane iya gida,wanda ya amsa sunansa,kuma ya ginashi ne musamman a sannan saboda shaheeda,a sanda ta haifa masa twins,ya zuba musu komai da komai,sanda zasu tashi zuwa gidan suturar jikinsu kawai suka dauka,kuma ko bayan rasuwar shaheedan babu abinda ya bari aka taba cikin gidan,hatta da suturarta,da anyi maganan kwasan wani abun sai a rasa kansa,sai aka yanke shawarar a jinkirta ko yana kan tsinin zafin mutuwar ne,saidai har kwanan gobe komai yana nan a muhallinsa,a baya cikin gidan yake rayuwarsa,saidai yadda yake dada komawa yasa anni ta yanke shawarar ya tattaro ya dawo gida cikin jama'a,a kulle wancan gidan ko za'a samu sauqin wasu al'amuran,an dan samu din,saidai babu abinda ya canza shaheeda daga zuciyarsa har kwanan gobe ita da amransa *SO BAYAN RAI*
Gidan daya zaba din gida ne sama dake da babbar haraba da zata iya daukan motoci goma,akwai balcony da zaka shiga wanda yake dauke da babban falo,hagu da dama na bangon falon qofofi ne guda biyu,kowacce qofa akwai babban falo hade da bedroom a cikinsa, kitchen daya ne wanda yake falon,saidai babba ne,babu wanda zai takura wani,hakanan side biyu gareshi,a falon akwai stairs da aka qawata da wasu irin makarai masu kyau,marbles ne zube har zuwa saman,inda zai sadaka shima da falo babba ne dakuna guda uku ne a saman kowanne manne da toilets dinsa,sai wani balcony din daga sama wanda zai baka daman ganin ainihin harabar gidan fetal,a qasan akwai spare din daki guda daya,sai dakunan baqi maza da na me gadi daga can wajen gidan.
Gidan yana da girma,don kowanne daki da falo babbane qwarai,hakanan yadda aka tsara ginin ya bada sha:awa ainun,saidai jabir da ya gani yaga gazawar ja:afar din,a matsayin da Allah ya bashi,duba da gidan da zai dauko unaisa
"Idan gidan bai mata ba saita fasa dani ta zaba wani fine,iya abinda zan iya kenan" ya gayawa jabir,kamar shine unaisan.
Duka kudin anty maama na lefe ya tura mata abinta ba tare daya sake wani musu ba,hakanan dukka wata zirga zirga ta samarwa da baqinsu masauki tare dashi aka yita,saidai sau tari har suje su dawo ba zakaji yace kanzil ba,lokutta mafi yawa wayarsa na a hannunsa ne,cikin abokansu guda biyun da suketa zirga zirgan tare babu wanda ya kawo komai ransa,saboda sunsan wayeshi,captain j din haka nan dabi'arsa take sun sani tun ba yau ba,magana ko surutu shine assignment mai wahalar cinyewa da zaka hadashi dashi.
Sai daya qara kwana biyu sannan ya samu ya sukunin saka time na zuwanshi gidansu unaisa kamar yadda abbi yayi masa umarni,ganin yadda yake shiga cikin sabgogin yasa abbi bai tanka masa,don yana ganin sauyi muraran da kuma qoqarin bin umarni daga wajen ja'afar din.
A ranar yayi zamanshi a sassansu kamar bashi da plan na zuwa ko ina,tab ce saman cinyarsa yana duba wasu abubuwa,sanaye yake da bawin boxer wanda ya fidda ainihin qirar tsayayyun qafafunsa dake cike da tarin gargasa,jabir ya turo qofar dakin ya shigo,a shirye tsaf cikin shadda,sai yaja turus ya tsaya
"Me zan gani?,J baka duba agogo ne?"
"What happened?" Ya tambayeshi a nutse abinsa,kamar ma baisan meke faruwa ba
"You are very stubborn manya,me yasa kakeso ayita maimaita magana daya?,just simple instruction amma ka kasa bi" idanu ya watsa masa bayan ya kashe tab din
"Yaushe na gaya maka fasa zuwa na?"
"Ai banga alama ba"
"Kamar?" Ya tambayeshi yana shafa dan qaramin gemun dake manne a habarshi,ya kuma hade da zagayayyen gashin dake kumatunsa zuws qasan hancinsa
"Gashi nan kuwa ina gani,you are sitting properly,dafa'an kamar babu inda zaka?" Yatsansa ya sanya yana bin tsahon karan hancinsa daga sama zuwa qasa,ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana furzar da iska,sai daya sauke qafafunsa qasa daga samam glass table din da take kai sannan yace
"Okay,so kake kazo ka sameni ina ihu guri guri ina announcing ma mutane zanje naga hurul'een ko?" Idanunsa ya lumshe yana sake girgiza kai alamun a'ah
"You should remember.....ita din ba kowa bace a wajena face GURBIN IDANUN da ba zasu taba zamowa idanu ba,koda zasu shekara miliyan anan din" daga haka ya miqe a nutse yana ajjiye kayan hannunsa ya nufi toilet
"Oho dai,no matter how dolenka kaje,na baka minti ashirin ka taddani falo,idan kuma ka wuce hakan....,basai na qarasa ba"
Kusan sai da jabir yayi dana sanin fadin wannan maganar,saboda sai da ja'afar ya ninka ashirin sau uku,don sai daya dauki awa daya cif sannan ya fito,saidai ya dauki kyau iya kyau yadda ya kamata,sanye yake da wani lallausan farin yadi na maza dake da shara shara,takalmin qafarsa baqi ne dan qasar Italy,hular dake kansa tun daga nesa take qyalli kamar farin tangaran,sosai kwalliyar tabi jikinsa,ta kuma dace da yammacin,hatta jabiru sai daya yaba da adon,amma sai ya fake da qorafin dadewa da yayi,bai kulashi ba,saima seat mai zaman banza da yayi zamansa,ya fidda wayarsa yana aikawa wani client dinsu saqonni,ya kuma turawa saubam secretary dinsa saqon ya sameshi a wani eatery goben yanason su tattauna.
Cikin wata farar Rolls-Royce ghost v12 mallakin ja'afar din suka fita,suna cillawa saman kwalta jabir ya qarawa motar gudu sosai,bayan ya cikasu da ac kamar yadda suka saba amfani da ita,basa ko ji ga jikinsu.
Leave a Comment