Gurbin Ido 34

 


Wani kallon qurilla me dauke da mamaki da kuma fargaba unaisa ke bin maimunatu dashi,zuciyarta na qiyasta mata wannan ce maimunatun?,wannan itace kishiyar tata?,yarinyar da duka duka bata wuce qanwarta ta uku biyu ba?,a qalla zata iya bata good five years,wannan zata kalla a matsayin kishiya?,no saidai ta dauketa tamkar 'yar aiki,amma kuma...... she's very beautiful,tana da wani irin kyau daya daki zuciyar unaisan,kyan da idan tace maimunatun ma 'yar aikinta ce ba shakka babu wanda zai yarda,don yarinta kam yarinya ce,amma batun tace 'yar aikinta ce ma bata taso ba,kyan yarinyar ya daketa,ya kuma tsole mata idanu tun daga kallon farko,abinda ya hanata sukuni,ko bayan data qarasa kitchen din tayi abinda zatayi ta fito,wanda gaba daya ruwan zafi ta iya dafawa ta juye a cup ta hada tea ta dauki five slices of bread ta hada dashi ta fita.


         Ji tayi sam bata jin taste na tea din,sai ta aje ta dauki waya ta kira anty talatu,ta kuma rattaba mata komai


"Keba macace bace?,meye na daga hankalinki?" Ajiyar zuciya unaisa ta saki


"Ba zaki gane bane anty,ni da nake mace ma kyanta ya tabani,ina ga da namiji?" Murmushi me sauti ta sake


"Bakisan namiji ba kenan,shi kam idan zuciyarsa ta qyasa da abu babu ruwansa da kyansa ko muninsa,abu daya ne da zakiyi shine ki kama zuciyarsa da kyau ta duka hanyoyin da suka dace,ba da bakinki kike gayan tafi marigayiyar matarsa kyau ba?" Kai ta gyada kafin tace


"Haka ne anty"


"To amma me yasa wannan kyan bai sanya ya sota ba har yanzun zuciyarsa naga marigayiyar?" Tambayar da tun kafin ta amsawa kanta ita taji gamsuwa


"Exactly"


"Da kyau,abu daya ne yanzun zakiyi,ki tabbatar kawai yarinyar bata sake cikin gidan ba,duk yadda zakiyi ki nuna mata a qasanki take,matsayinku kuma ba daya bane,wanna zaisa ta kasa kallon kanta a matsayin cikakkiyar mace da har zata maida hankali wajen ganin tayi tarayya dake akan mijinku,sannan kinfinkowa sanin daga inda ta fito,bata da cikakkiyar wayewar da zaki kasa juyata yadda kikeso,cikin ruwan sanyi zata zame miki kamar qasqantacciyar 'yar aikin ba tare da ta ankara ba" dukka wadan nan maganganun na anty talatu dama wadanda suka biyo baya sunwa unaisa dadi,sai ta saki jikinta suka sha hirarsu,tana sake bata haske game da wasu abubuwan.


          Cikin zuwan da yakanyi gida wasu lokutan idan ya tashi a aiki da wuri anni tace ya kawo unaisa da maimunatu su gaida surukansu,hikimar hakan kuwa,tayi ne don taga kamun ludayinsa da kuma yadda su din suke zaune,don tun daga washegarin randa aka kaisu ba wani dan gidan daya sake komawa gidan nasa.


         Baya buqatar magana da kowacce a cikinsu,baisan ta yadda zai sanar musu su shirya ba,don haka sai kawai ya sanya driver ya dauki laila yace ya kaita gidan su taho tare,shi kuma ya wuce aikinsa abinsa.


          Kamar a mafarki maimunatu taga lailan,ta saki ihun murna ta rungume lailan duk da baqunta da rashin sakin jiki irin na maimunatun,sanda ko ta gaya mata inda zasun ji tayi kamar anyi mata bushara,sati na uku nason cikewa ko farfajiyar gidan bata qara leqawa ba tun randa sukazo tayi musu rakiya,nan da nan ta hau shiri,kafin ma unaisa ta gama laqai laqai dinta ita ta gama shiryawa,cikin wata jar atamfa data haskata sosai.


        Duk inda maimunatun ta motsa laila na binta ne da ido,tayi wani fresh sosai,fatarta kamar babu abinda yake hawa,saidai kuma babu wata qiba ko murmurewa da tayi,kuma tana da tabbacin inda maimunatun ta qara qiba lallai zama zatayi abar kallo,don komai na jikinta ya soma cika da alamun girma da budurci tare da kwarjini na aure.


           Sanda suka fito zasu wuce laila ta leqa yiwa unaisa magana,sai ta sameta bata ma shirya ba


"Kaina kemin ciwo,kice ina gaishesu,zan sanya lokaci sai mu shigo ji dashi" amsar data bawa laila haushi matuqa,ta kuma fito tana mita,wannan ai tsabar rainin wayo ne,ita dai mainunatu batace komai ba,daga bisani ma sai ta janyo mata hirar islamiyya,wadda takejin kewarta qwarai da gaske,tana jin inama za'a barta taci gaba da zuwa,tana jin rashin dadi kan yadda haddarta ta tsaya cak,duk da tana tilawa a gida.


          Tsaki unaisa taja bayan jin tashin motarsu,me suka maidata ne?,ko sun manta matsayin ubanta a qasar nan,banda soyayyar da takewa J da ta yaya ma zata zauna a inda take yanzu?,ta yaya zata yarda ta hada kishi da wata bafulatanar ruga?,idan gaisuwar surukai ne ai basai ta hada kafada da 'yar qauyen yarinyar ba,cikin motocinta zata ja daya takai kanta gidan idan fa shirya gaishesun basai an mata jagora ko an tusata a gaba ba.


             Sai data shiga ta gaida amma da ammi sannan ta yada zango wajen anni,annin na karance da maimunatun sarai duk da ita bata fahimta ba,ta kuma samu gamsuwar gabatarwa da ja'afar qudurinta,don haka sanda yazo washegari gidan,akaci sa'a safiya ce,saboda yau din da yunwa ya tashi,don jiya bai samu tsaiwa yaci abinci a inda ya saba tsaiwa cin abincin ba


"Makaranta nakeso ka dauki maimunatu da kanka ka sanyata" ta bashi umarni nakai tsaye idanunta a kansa sanda yake zaune gabanta amna na saman cinyarsa yana bare mata chocolate.


           A hankali ya daga kansa zai kalleta,sai ya samu itama shi take kallo,ba tun yau ba,yasan anni sarai,yasan kuma tunda ta tada zancan nan akwai abinda ta taaka,kamar zaice wani abu sai kuma yace


"Ba damuwa" a taqaice,yadda yayi saurin amsawar ya bawa anni mamaki,ya kuma tabbatar mata akwai wata a qasa,kuma ruwa baya tsami banza,amma kuma zata zanya idanu taga me zai aikata


"Idan ka tashi ka hada mata da waya,don ya kamata ace tana waya da 'yan uwanta,bawai don ta taho ta taho kenan ba"


"To" ya sake cewa da ita


"Kiyi picking ledojin chocolates din ki biyoni mota zaki rakani unguwa" yace da amna bayan ya sauketa daga kan cinyarsa ya kuma miqe,ta sauka kuwa da sauri tana murna,ta hau tsincewar tana ta yiwa anni da ta bishi da kallo surutu,hankalinta bai kwanta ba,tasan halin ja'afar itama,wannan saurin amsawar da yayi ba'a banza ba,amma koma meye ya shirya yi,indai cutuwa ne ga maimunatun ba zata bari ba.


        Shegen miskilanci gami da zurfin cikinsa yana nan har yanzu,yana da wannan nuna shakulaton bangaron kan abubuwan da yana sane dasu sarai,suna kuma cikin ruhi da zuciyarsa,amma sai yayi kamar bai damu ba,kamar baya ankare da abun,kuma kamar baya gani,saidai duk randa ya magantu ko ya dauki wani action akai kowa zaiyi mamakin hakan,wannan ya sanya anni ta sake sanyama ranta zata kula da komai da irin abinda zai biyo baya,ta sauke ajiyar zuciya tana hade hannayenta waje daya,fuskantar ja'afar ko yin gaba da gaba wajen saukeshi daga ra'ayinsa ya zuwa wani babban aiki ne da ba kowa zai iya shi ba,fatanta ubangiji ya dubesu,rayuwarsa ta sai saita,ya kuma riqe amanar yaran mutane kada suji kunya.


*********Kwanaki anni tayita qirgawa tana jiran taji yace wani abu,ko kuma ya tanka game da maganar da sukayi da ita,saida har ta gama irga kwanaki bakwai baice komai akan maganar ba.


         A daren ranar ya koma gida da wuri kai tsaye daga wani gidan saukar baqi,inda suka tattauna da wani babban mutum da ya bawa company dinsa kwangilar ginin wata university da zai bude.


             A gajiye ya shigo gidan,ya wuce sassansa kai tsaye ya fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa,duk da gajiyar da yayi amma yanason yaje gida wajen anni,don haka  sai ya shirya cikin wani irin straight leg jeans da shirt masu azaban kyau,ya kuma sakaya qafarsa cikin wani rufaffen sneakers daya dace da kayan jikinsa,ya sake gyara sumarsa tsaf,kai bakace dare bane,ya dauki maqullansa da wayarsa guda daya a gurguje ya sauko,yana so yaje yayi ya gama ya dawo ya kwanta,don gobe yake sanya ran zai wuce lagos.


        A nutse yake tuqinsa,yana kuma amsa wayar da suke da jabir ta speaker din motar har ya isa gidan,sai daya tura hancin motar zuwa farfajiyar gidan sannan sukayi sallama dashi,ya dai daita tsaiwar motar a parking lot na gidan yana duban inda masu gidan ke ajiye motocinsu,akwai kotar hisham data abbi duka a wajen,da alama suna gida,sai ya balle murfin motar ya fito zuwa cikin gidan,cikin takun nan nasa dake nuni da qasaitarsa da kuma aji da yake dashi cikin jininsa,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar qamshinsa a wajen,wani qamshi na musamman da zaiyi wahala ka jishi jikin wani,turare na musamman yake amfani dashi,na jiki kuma ya banbamta dana kaya,hakanan na gashin kansa daban da wanda yake shafawa qirjinsa,dama can haka yake,dan gayu ne daya zarta kowa cikin gidan dama familyn khalid akko.


       Jifa jifa ma'aikatan gidan ke kawo masa gaisuwa har ya dangana da sassan ammansa,wanda kusan ko da yaushe yazo gidan wajenta yake fara zuwa,ya sameta zaune a falon gidan,sanye da hijab,yatsarta kuma sarqafe da da tasbah counter,idanuwanta na kan tv.


        Fuskarta fadade da fara'a ta gyara zamanta tana masa maraba


"Kaine a daren nan?" Ta fada tana ajjiye masa ruwan data dauko masa da kanta,sai yasa hannu ya karba,duk da baya jin qishi amma kuma bazai iya wucewa tayinta ba,saboda kima da martabar da take dashi a wajensa,ya gaidata cikin girmamawa


"Lafiya qalau,yasu maimunatu?" Sunan yajishi tamkar baqo a wajensa,don bai gama tantance wacece maimunatun ba,wadda ya lura duk zuwa shine suna na farko da take fara tambayarsa


"Lafiya qalau" ya amsa mata,yana zarcewa da shan ruwan daya tsiyaya din,sai daya ajjiye cup din sannan ya dubi amma


"Amna fa?"


"Ina zaton tana wajen ammi,suna can sassan babanku da ita,yau rigima takeji tun yamma,wai sai an kaita gurin adda maimunatu" bai fahimci gundarin abinda maganar ta amma ke nufi ba,yadai dauka key dinsa ya maqala a yatsan hannunsa yana shirin tashi,dai dai lokacin da salma ta fito daga dakinsu,ta kuma ratso cikin falon cikin kwalliya,tana baza qamshin turare.


            Kafin ta qaraso ta ankara dashi,sai duka karsashinta ya zagwanye,ta sake saita kanta da kyau don kada tayi wani laifin,ta qaraso ta rusuna tana cewa


"Barka da dare yaaya"


"Yauwa barkanki dai" sum sum tafara takawa zuwa gaba,sai a sannan ya waiwaya zuwa inda take


"Ke!" Ya kirata da nannauyan muryan nan tasa da take sanyasu cikin rudani da tsoro


"Na'am yaaya"


"Zo nan" ya fada yana mata sign da hannu ba tare daya sake dubanta ba,gabanta nata dukan uku uku ta dawo,ta sulale saman carpet din ta zauna tana dubansa yana danna wayarsa,sannan ya karata a kunne,second uku kacal yace


"Ka bude ka shigarmin dasu sassan anni" iya abinda ya fada kenan ya katse wayar,sannan ya maida dubansa ga salma,sai tayi qas da kanta,yana da wani irin kwarjini wanda ba kowa ke iya sanya idanunsa cikin nasa ba


"Ina zakije?" Dan muskutawa kadan tayi,duk sanda ya sanyata gaba da wata tambayar komai qwace mata yakeyi,kamar ba ita salman ba,'ya gayu me aji,wadda take kadawa maza ganye,'yar jami'ar dake gab da kammala degree dinta


"Yaa..... Ahmad ne yaxo" wani kallo ya watsa mata,wanda yasa tayi dana sanin bashi wannan amsar


"Koma ciki ki saka hijab dinki" iya abinda yace da ita a taqaice kenan,ya maida dubansa ga wayarsa,bata da iko ko qwarin gwiwar musu dashi,don dole ta miqe ranta a bace kan yadda zai bata maka kwalliya ta koma dakinsu,ahmad din nan ba baqo bane,koshi kansa yasan da zamansa,tunda sai da iyayensa sukazo nema masa izinin fara zuwa wajenta,amma shi da yake wani irin mutum ne mai shegen tsari da qa'ida,ji yadda yayi kamar bai ganeshi ba.


          Da sallama ya shiga sassan annin,tana zaune a qasa,ta dora qafafunta saman tuntum,daya daga cikin masu aikinta na mata yankan farce,fa'iza khadija da laila na zaune daga gefe suna kallo duka harda annin.


         Sallamarsa tasa dukkansu suka gyara zamansu,hadi da hada baki wajen amsa sallamar tasa,anni ta waiwaya ta zuba musu harara


"Ya'yan nema marasa kunyar Allah,ni da yake marainiyar wayonku ce magana nayi muku har babu adadi amma ba wadda na samu ta tankani,amma da yake dodon naku ke magana har hada baki kuke wajen amsa sallama kamar na Allah....." Laila daketa motsi tana yiwa anni sign na tayi shuru don Allah amma tayi kamar bata gani ba takasa shuru


"Amma anni don Allah ba cewa nayi bari mu qarasa ganin wannan ba?" Da yatsa annin ta nunata


"Ke arcan,kiyi ta kanki yarinya,ni zaki yiwa sanabe?" 


"Barka da dare" mai rahila me aikin ta gaidashi kanta a sunkuye


"Kina lafiya" ya maida mata yana daga tsaye


"Alhmdlh yallabai"


"Ajjiye ki tafi" ya fada mata kansa tsaye,da hanzarinta ta miqe bayan ta ajjiyr nail cutter din,sai data bace a falon sannan ya waiwaya ya dubesu duka su ukun,ya sauke kallonsa ga fa'iza babbar cikinsu


"Xoki dauka ki qarasa mata" cikin sauri ta taso ta zauna inda rahila ta tashi


"Nidai ki bini a hankali,kada garin rawar jiki ki yankemin jiki ina lallaba rayuwata".


        "Tashi kije ka karbomin abinci wajen amma,idan kinso ki xauna ko kiyi mistake" ya fada cikin gatse,yana zama a qasan carpet daura da anni tare da duba agogon hannunsa,saura minti daya a fara haska wasan tseren dokuna, favourite thing nasa kenan,ya yiwa khadija umarni da ta bashi remote,tana miqa masa ta samu ta sulale daga falon,ya canza tashar yana jin anni na mitar me zasu kalla a nan?,shi dai baice da ita komai ba ya maida kansa ga kallonsa,har zuwa sanda laila ta dawo da wani qaramin kwando kamar na kaba,saidai an saqa wannan ne da wata irin roba me kyau,ta ajjiye masa a gabansa,sannan ta duqa ta fara shirin serving dinsa.


"Stop" ya fada da sauri,a dan tsorace ta daga kanta,sai ya sauke dubansa ga yatsunta ba tare da yace komai ba.


         A tsorace ya dunqulesu cikin tafin hannunta,sai a sannan ta tuna,babu abinda yafi tsana irin tara farce


"Na baki minti biyar ki tabbatar sun koma kamar na hannun kowa" abinda yace da ita kenan,ta gyada kanta tana miqewa,bataso ya gani ba,saboda bikin rumaisa za'ayi,cousin dinsu,diyar uncle umar,mai bin dr marwan.


*Ku bibiyi shafina na arewabooks don samun sabbin shafuka*


No comments

Powered by Blogger.