Gurbin Ido 36
"barka da warhaka" anty maama ta fada,yadan saki muryarsa kadan,duk da haka akwai heaviness din nan a cikinta dake qara masa kwarjini ya amsa mata
"Barka kadai,yasu hamood"
"Kowa yana nan lafiya qalau"
"Ma sha Allah" ya amsata a taqaice,sai ta danyi shuru kuma,ita kanta wani lokaci kwarjini yake mata,duk kuwa da cewa duk irin miskilanci da zafin kai irin nasa bai taba qin bata girmanta ba,saidai babu wani dogon magana me yawa tun dacan a tsakaninsu,shi yasa lokuta da yawa hisham dinne abokin maganarta,amma tuna wannan attitude din nasa na respect ya bata nutsuwar cewa
"Muna tare ne da hisham,yanzun yake gayamin wai kaine kace akai maimunatu boarding school?"
"Maimunatu?"ya dan maimaita sunan,sai kuma yace
"Oh.....eh,hakane,abinda anni ta buqata kenan,komawarta makaranta"
"Amma sai nakega anni bawai tana nufin a kaita makarantar kwana ba ko?" Ta fada cikin kwantar da murya
"Ban sani ba gsky,na duba kawai makarantar dake da kyau ne,kuma sai naga kamar abun arziqi nayi" shuru tayi ta jinjina kai
"Shikenan,Allah ya rufa asiri"
"Qarata ya kawo kenan?" Ya jefa mata tambayar,saita gyada kanta da sauri
"A'ah sun dai biyo ne shi da ita mu gaisa"
"Ok,yayi" ya fada kana ya sauke wayar yana kashewa ba tare da yabi ba:asin me yasa suka biyo din ba,tunda basu gaya masan xasu biyo ba.
Gefe ya aje wayar yana duban titin lagos da suke ratsawa cikin sa'a yau babu cinkoso da yawa,sai yake jinsa sakayau,ya rufe case din wannan,saura dayar,ita dinma da bata wuce lavel don boarding din ba hadasu zaiyi ko xai samuu peace of mind,haka kawai ya samu yana lallaba rayuwarshi annin ta hadashi da aiki.
**********Bakwai da rabi na safiyar litinin a pen resources academy tayi musu ita da hisham wanda shine ya kawota da kanshi,sanye take da uniform dinta da duk wani abu da sabon dalibin boarding na private school zai buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,saboda makarantar suna da tsari ba kamar government boarding school ba,makaranta ce ta wadanda sukaci suka tada kai,saboda haka duk wanda ka gani a cikinta ba dan kuci ku bamu bane.
Tunda suka shiga makarantar ta tabbatar da haka,duba da irin motocin da suke sauke daliban da a yau suka dawo daga hutun zangon qarshe na shekara.
Sai da aka kammala komai hatta daki aka bata hisham yana zaune,bayan ya tabbatar komai yayi settling ya dubeta,murmushi yadan qwace masa ganin yadda idanunta suka tara qwalla
"Zan koma matar babban yaaya,Allah ya bada sa'a,yasa a fara a sa'a" hakanan sai taji zuciyarta ta karye,kamar wadda aka kai nisan duniya,tana qoqarin maida qwallarta ta amsa da amin,tana nan a tsaye har ya isa motarsa ya budeta ya shiga,har ya tadata sai kuma ya kashe ya sake fitowa,hannunsa dauke da madaidaicin kwali ya miqa mata
"Na manta,ga waya koda zaki buqaci communicating da mutanen gida" wayar ta kalla sannan ta maida dubanta gareshi,wannan shine karo na farko da aka soma malllaka mata waya a rayuwarta,sai tasa hannu bibbiyu ta karba tana masa godiya
"Babu komai fa" ya sake amsa mata yana murmushi,har zuciyarsa yana jin tausayinta,tun dava randa laila ta bashi labarin wacece ita,sai data ga fitarsa a makarantar,sannan ta juya jiki a sanyaye,saita duba agogon dake daure tintsiyar hannunta,lokacin shiga aji yayi,don haka ta ciro school bag dinta dake saqale a bayanta ta cusa wayar a ciki sannan ta kama hanyar da classes dinsu yake.
Da sallama ta shiga ajin,sai ta dan tsaya tana dawurwura,don ajin adan hargitse yake da hayaniyar dalibai,wanda basu ma lura da wanda ya shigo din
Ta gefanta taji alamun shigowa,saita waiwaya kadan,daliba ce kamarta take shigowa ajin,hannunta dauke da water marker da kuma wasu litattafai,suka hada idanu saita dauke kanta,ta isa gaban allo ta zube marker din,sannan tazo zata giftata,har tadan gota ta waiwayo ta dubeta
"Sabuwar daliba?" A hankali maimunatun ta gyada mata kai,sai ta waiwaya tana duban cikin class din sannan ta sake maido dubanta gareta
"Ga seat din muje ciki" hakan ya bata damar bin bayanta,har suka isa gaban wani seat,sai taga ta zauna daga gefe,kamar yadda ta karanci duk set daya yana daukan mutum biyu ne
"Zauna a nan,akwai abokiyar zamana,amma dawowarmu wannan hutun ashe ba zata dawo ba,an canza mata makaranta,saiki maye gurbin wajenta" tace da maimunatu tana dauko jakarta gami da zugeea tana fiddo da sabin exercise tana dorsawa saman desk din
"Na gode" ta amsa mata a taqaice,cike da tsarguwan kallon qurillar da daliban ke binta da shi.
Tun zamansu a wajen ta fuskanci lokaci bayan lokaci sukan hada idanu da class captain din,wadda taji suna kira da afrah Ateeq Muhammad,tana taqaitawa da afrah A muhammad,duk sanda suka hada idanun sai ta dan sake mata murmushi kawai taci gaba da abinda takeyi,itama maida mata martani take,sai taji kallon bai dameta ba.
Lokacin break har tayi gaba sai ta dawo ganin maimunatu a zaune
"Zamuje dakin cin abinci,ko kinsan hanya?" Kai ta girgiza
"Okay,kina iya tasowa mu tafi"
"Na gode" ta fada tana miqewa,ta ajjiye jakarta tabi baya afran.
Abinda ta lura afra nada kirki,tana kuma da kyakkyawar mu'amala da jama'a,hakanan tana da mutane sosai,a nutse take,bata da tarin hayaniya ko rawar kai,tare suka gama cin abincin sannan suka dawo aji.
Karfe biyu aka tashi daga makaranta,masallacin cikin makaranta taga yawancin daliban suna tafiya,bataga afran ba,don gab da zaa tashi ta fita a class din,tana buqatar koyon wasu abubuwan da kanta,don haka sai kawai tabi sahun daliban itama ta wuce zuwa masallacin.
Batayi gaggawar barin masallacin ba sai data fuskanci lokacine na komawa daki kowa ya huta,ta dauki jakarta ta nufi inda dakunan kwanan dalibai mata yake,tana tafiya ne a hankali don kada ta bace a dakin,jifa jifa tana cin karo da dalibai a verender,duk wadda tazo giftatan kuma sai ta bita da kallo,a haka ta isa dakinsu,ta murza handle din sai taji qofar a bude take,ta tura da sallama tana shiga.
Madaidaicin daki ne,mai dauke da gadon kwanan dalibai guda hudu,shimfidadden tiles qaramin toilet da kuma locker ajiyar kaya da aka bawa kowanne dalibai,wutar na'urar solar da fankar sama dake juyawa a hankali,fes dakin yake sai qamshin freshener da yake fiddawa.
Gadon da yake qasan nata gadon tunda a sama take taga mutum a kwance,ta motsa sannan ta dago tana amsa sallamar tata,suka hada idanu,sai taga afra dince,murmushi tayi mata tana miqewa daga kwanciyar da tayi
"Ah,baquwa,ashe dakinmu daya?" Murmushin itama maimunatu ta maida mata
"Ban sani ba nima sai yanzu,dazun da nazo ajjiye kayana babu kowa a dakin"
"Yanzun ma saini kadai,su feena basu shigo ba,sun tsaya karbomin magani a pharmacy" afra ta fada tana dan yatsina fuska
"Ayyah,baki da lafiya ashe?"
"Wlh,yau duka daurewa kawai nakeyi,da ciwon mara na tashi" ta fada tana cije labbanta,da alama ciwon ya motsa mata ne
"Sannu,Allah ya sawwaqe"
"Ameen na gode" ta fada tana kwantar da kanta saman qafarta,maimunatu kuma ta matsa gaba kadan,ta taka gajerun steps din da suka sadata da gadonta,ta ajjiye jakarta ta kuma canza uniform din jikinta zuwa kayan gida a dan wajen da suka kebe saboda sauya kaya.
Leqawa ta sakeyi tana yiwa afra sannu,dai dai lokacin da wasu 'yammatan guda biyu suka shigo dakin bakunansu dauke da hira cai cai,da alama wata gulmar suka qunso daga waje suka shigo da ita.
Bin maimunatu sukayi da kallo,duk da a dazun sun ganta a aji,da alama suma suna mamakin ganinta a dakinsu,duk da dama sunsan akwai sauran space na abokiyar karatunsu data canza makaranta.
Itama dan bin nasu tayi da kallo,dukkansu kana dubansu zakasan cewa kowacce daga gidan gata ta fito basai an gaya maka ba,ta amsa sallamarsu tana debe idanunta daga kallonsu,suka qaraso kusa da afra,kusan a tare suka ce da maimunatu
"Sannu New roommate" murmushi tayi musu
"Sannunku"
"Sunana fatima baqo" sai dayar ma ta kama
"Ni kuma ummu ayman buhari" ta qarashe maganar tana miqa mata hannu
"Maimunatu Abubakar muhammad" ta amsa musu tana miqa musu nata hannun itama
"Nice meeting you" suka amsa fuska sake kaman sun saba da ita dama can.
To hausawa sukace juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,dukkan alamu sun nunawa maimunatu zataji dadin zama da abokan karatun nata ainun tun a waninsu na farko,wasu irin mutane ne masu sauqin kai da kuma dadin zama ainun,yadda suke nan nan da ita da kuma haba haba sai ka zaci an jima da haduwa tare.
Takeaway mai yawan gaske suka zube musu sukaci,sunayi suna duba jikin afrah,duk da cewa da sauqi saboda maganin data sha,har sukayi sallar la'asar,sannan suka fara shirin tafiya islamiyyar cikin makarantar,wadda suke shiga hudu na yammaci
"Inaga tunda ku kun saba zuwa,kuje kada ku rasa karatunku na yau,ni zan zauna da sister afra(ta fadi kamar yadda taji suna kiran juna),idan yaso ko zuwa gobe sai na fara zuwa"abunda ya yiwa afran dadi qwarai,ta kuma sake jin maimunatun cikin ranta fiye da daxun farkon zuwanta,bayan fitarsun kuwa hira suka dinga yi sosai da afran,a nan ta fahimci dukkansu 'ya'yan manya ne,sai maimunatun taji a ranta ya kamata ta kama kanta,tunda ita din ba 'yar kowan kowa bace,amma duk da hakan sai ta saki jikinta,ta dinga dan tambayar afran game da wasu abubuwa na makarantar,ta samu haske kuwa sosai,don su tun daga js one suka fara,ba kamar ita ba data datsi ss one.
Ta fahimci team ne na masu son karatu aka hada daki guda,afra ayman da fatima,wannan yasa itama ta sake jaddada niyyarta na zage damtse tare da yin karatu tuquru haiqan,son karatunsu ne ya sanya a aji suka raba set,don kada suje kasa maida hankali,kowacce a cikinsu akwai babban alqawarin da aka yi mata daga gida na idan ta gama ta fita da sakamako me kyau a dukka record nata,to zata zabi duk abinda takeso kuma shi za'a bata,wannan yasa a tsakaninsu duk term ake samun first second and third position,saidai sukanyi exchange a tsakaninsu wata ta karbe position din wata.
Fadan me uwa inji hausawa sukace,idan ana masa mara uwa labewa yakeyi ya saurara ya kuma yi aiki dashi,dama da niyyar karatun ta shigo,haduwarta dasu afra yasa ta sake ninka qudurinta.
Kusan abinda ya tashi hirar qarar wayar afran dake daman katifarta,ayman ce ta miqo mata,tana duba number ta miqe ta haye gadonta basu sake jin motsinta ba,maimunatu dai na jinsu suna mata tsiya amma bata fahimta akan meye ba,don tayi nisa a tunanin yadda zata tafi da tata rayuwar,qarar wayar ya sanyata tunowa da tata wayar da yaa hisham ya bata,ta miqe ta haura,ta dauko tata jakar ta bude ta ciro wayar ta bude kwalin.
Ido da baki ta saka tana kallon kyan wayar,sai takega wayar tafi qarfinta,ko ba's gaya mata ba tasan mai tsada ce ainun,don haka ta bude cikin locker dinta ta turata ciki ta mayar ta rufe.
********Cikin kwanaki qalilan sabo mai qarfi ya shiga tsakaninsu,musamman tsakaninta da afra,irin sabon da ita kanta maimunatu tayi mamaki,saboda sabo ne da tun zuwanta duniya batayishi da kowacce halitta ba idan ba mahaifiyarta ba,tunda kusan a tsangwame ta tashi,batasan dangin mahaifinta ba,dangin mahaifiya kuwa babu wannan fuskar,wajen inna furera ma kam ba'a wannan maganar,bata jima sosai tare dasu anni ba bare ta gama tantance wannan,duk da dai alhmdlh,ta samu sakewa sosai dasu,don ma ta gaza sakin jiki dasu,wala'alla don tana musu kallon iyaye,su laila kuwa sun dan girme mata kadan,fa'iza da khadija ne kusan sa'anninta.
Yadda suke rayuwa basa boyewa junansu komai,infact tama lura kusan kowa yasan family din kowa,don ko waya daya tayi da gida zatace wance tana gaidaku,kusan tasan labarin kowa a cikinsu,har da na mahaifin afra da bashi da lafiya,wannan yasa itama bata boye musu ko wacece ita ba,ta shaida musu,saidai bata gaya musu tana da aure ba.
Zamansu tare ta fara koyon abubuwa daga garesu,kowacce nada tarbiyya gwagwadon iko,hakanan itama sun fara koyon nata dabi'un,ada basu wani damu da islamiyya ba,bata dadasu da qasa ba,suna zuwa,amma suna mata asha ruwan tuntsaye,zuwan maimunatu da yadda sukaga ta maida hankalinta ga zuwan,shine yaja hankalinsu,ita da kanta data fuskanci yadda malamin yake da sauqin kai fahimta da kuma iya koyarwa ya sanya ta roqeshi da kanta ya sanya musu wasu litattafan,hakan yayi masa dadi shima,saboda kusan itace daliba ta farko data fara mai da hankali kan karatun,harta nema a sanya musu wasu litattafan bayan qur'ani da ake musu,ba bata lokaci kuwa ya laluba litattafan da suka shafi fiqhu hadis da sira ya saka musu,tun dalibai da dama basu wani damu da karatun ba,sai gashi sannu sannu abun yana jan hankalinsu,ba'a wani bata lokaci ba islamiyya ta cika da dalibai,abun da ya fara tambara sunan maimunatu a makarantar,haziqa ce sosai musamman ta fannin islamiyya,bangaren boko ne yake dan bata kashi,saboda kusan jumping tayi,a sannan taga amfanin lesson din da anni tasa aka dinga yi mata lokacin da tana gida,ya taimaka mata matuqa da gaske,da batasan yadda zatayi da karatun makarantar ba.
Leave a Comment