Gurbin Ido 43


 Sai da suka tsaya masallaci sukayi sallar azahar sannan hisham ya sake daukansu wuce asibitin,gab da zasu qarasa ya soma slow da motan,jaafar dake duba wani abu a tab dinsa ya daga kai ya dubeshi


"Uhmmm,ya dai?" 


"Naga masu fruit ne,akwai paw paw a ciki,zan siya ma maimunatu" sai ya maida kansa ga abinda yakeyi baice dashi komai ba,har ya buda motar ya fita yaje ya siyo,ya dawo ya tashi motar suka wuce.


        Dakin babu kowa,don duka sun yoye sun tafi,daga ita sai amnan sai baba talatu data shiga bandaki zata dauro alwala,tana zaune a saman gadon amna ta zame mata dankwalinta ala dole wai sai ta yi mata kitso,tana ta jagwalgwala mata sassalkan gashinta ta kasa kitsawa saboda sulbi da santsinsa,jikinta akwai sauran zazzabi,an yima likitan bayani yace zai shigo ya dubata,tana biyewa amna dinne kawai don kada yarinyar taji babu dadi.


          Batayi zato ba bare tsammani sassanyar muryarsa ta furta sautin sallama hadi da turo qofar dakin gaba daya,tashin farko kuma idanunsa suka sauka a kanta lokacin data rude ta kuma tsorata tana neman dankwalinta,wanda bata sani ba amna ta jefa mata shi qasan gadon,shi yasa ta kasa ganinsa,idanunsa ya dauke ya waiwaya baya inda hisham ke biye dashi


"Wait for a while"


"Okay" hisham ya amsa masa ya kuma ja baya ya tsaya ba tare da yasan dalilin ja'afar na fadin hakan ba.


       Koda ya shigo din gaba daya ya maida hankalinsa ga amna wadda ta diro a gadon fa kuma rugo da gudu zuwa gareshi tana kiran sunanshi,haka kawai yaji baya son ganinta haka,ya budewa yarinyar hannayensa bayan ya durqusa yana jiran qarasowarta,zuciyarsa kuma na tuna masa da lokuta irin haka a baya,lokuta mafiya farinciki a rayuwarsa,lokutan da ita da twin sister dinta amra ke rige rigen isowa gareshi,mamansi shahida na tsaye tana kallonsu tana kuma murmushi,sai gashi a yau yarinyar ita daya ta rage masa a cikin guraben farinciki guda uku da yake dasu,tana qarsowa kuwa yayi sama da itama ya cillata kan ya rungumeta cikin jikinsa.


         Kafij su gama ganin murnar ganin juna ta lalubo dankwalin da qyar ta yane kanta gaba daya zuwa saman qirjinta,duk da hankalinsa na kan amna amma yana ankare da ita,baisan me yasa take tsoronsa haka take kuma rudewa duk sanda yazo wajen ba,tun ranar daya tsorata tan randa suka baro gembu zuwa gombe,sauke amna yayi a hankali


       "Kice da uncle ya shigo yana waje" da dan gudunta ta fice,sai a sannan ya sake maida dubansa kanta,ta nutsu guri guda,wanzuwarsa a wajen tana sata jin kamar wani zazzabin zai sake qaruwar mata,kwata kwata batason ganinsa a waje idan tana nan


          "Ina wuni?" Ta fada da muryar nan tata dake da tsananin zaqi da sanyi,shi kansa ya yadda da hakan,idan tayi magana wani sauti take bayarwa na musamman


"Ya jikin?" Ya tambayeta ba tare da ya amsa gaisuwarta ba,yana bin ledar qarin ruwa da aka cire mata da kallo


"Da sauqi" ta bashi amsa dai dai da fitowar baaba tabawa daga bandaki.


        "Barka da zuwa,yaushe ka shigo?"


"Yanzu" ya amsata yana waiwaya ga hisham dake shigowa dakin da sallama,kanta ta daga tana amsa sallamar,yadan kalleta ta gefan idanu,akwai dan qaramin murmushi saman lebanta tana dubansu shi da amna,gaisawa shima sukayi da baaba tabawa,ta tayar da sallah,sannan ya matsa inda maimunatu take


"Yanzun don kada a bamu tsarabar boarding shine aka kwanta ciwo?" Shima tana jin nauyinsa sosai,amma ko kwatar na miskilin yayansa me fuskar shanu bai kai ba,akwai dan sabo haka a tsakaninsu,don haka murya can qasa ta yadda take zaton ja'afar bazaiji ba tace


"Kaidai tunda sai yau kk zuwa dubiyan ai shikenan" 


"Am sorry.....wallahi ayyuka ne suka yimin yawa kwana biyu,ga teaching hospital da nake zuwa musu sau biyu a sati suma kyauta...."


"Allah ya taimaka" ta fadi duk a darare,ita inda zai fita ya basu waje ma da sai tafijin dadin hakan,ledar gwandar ya tura mata


"Nayi dubiya me kyau,tunda.na kawo miki mutuniyarki ko?" Ya fada yana dubanta yana murmushi,maganar da ta sanya ja'afar karantar fuskarta a fakaice,wanda a zahiri zaka dauka kacokam hankalinsa na ga surutun da amna ke masa,sai yaga fuskarta ta washe sosai,karo na farko da ya taba ganin irin haka tattare da ita


"Na gode sosai,Allah ya saka da alkhairi,ya bada lada" maganar ta tsaya masa a rai,kwatankwacin addu'ar shaheeda kenan duk sanda aka yi mata alkhairi komai qanqantarsa.


           Juya gwandar kawai take,tana son sha amma dashi da hisham din duk sun cika mata waje,sanda baba tabawa ta idar da sallar likitan ya shigo,maimunatu ta daga kai a hankali gabanta yana faduwa,ta tuna maganarsa ta jiya,yace indai yazo yau ya samu da sauran zazzabin a jikinta to lallai duk qinta da allura saidai tayi haquri ayi mata ita,a duniya allura itace abu na farko data tsana ta kuma qi jini,daada tafi kowa sanin hakan,don tun kafin rasuwarta akwai sanda bata da lpy,ta takura sai anyi mata takusa shide mata,abinda yasa tun daga ranar bata qara bari anyi mata ba.


           "Dr hisham marwan?" Likitan ya fada yana diban hisham,da alama akwai sanayya sosai a tsakaninsu,don shima hisham din yana kallonsa ya kama sunansa,hira suka barke da ita,yana duba file din maimunatu,da treatment din da aka bata daga daren jiya zuwa yau,sai ya daga kai ya dubeta


"Har yanzu da zazzabin?" Kafin ta amsa baba tabawa ta rigata


"Akwai likita,ai har magana aka yo muku dazun"


"Ba damuwa,zai sauka yanzun in sha Allah,qila ma idan akayi wannan allurar basai an sake wata ba" fadin haka kawai sai idanunta ya fara tara hawaye,cikin mamaki a kuma sace ja'afar ke kallonta,bawai tana nufin kiran za'a mata allura ke shirin sanyata kuka ba?,ya hangi zallar tsoro baro baro a idanunta,ta kuma kasa sukuni sanda taga yana hada ruwan allurar waje daya.


          Kida wayarsa ta farayi,sassanyar busa me ratsa zuciya,ya cirota ya duba me kiran,sai ya soma takawa a hankali yana ficewa a dakin yana amsa wayar.


         Daya daga cikin amintattun ma'aikatansa ne,suke gaya masa motocin da ya siya sun iso,suna lagos,za'a biya kudin clearance da sauransu


"Ayi duk abinda ya dace"

"Okay sir" ya amsa masa a ladabce,ya kashe wayar yana juyowa,dai dai sanda baba tabawa ta iso riqe da hannun amna


"Manya inaji fa sai kaje maimunatu zata tsaya,taqi bari ayi mata allurar nan sam" a mamakance yake duban baba tabawa,wanne irin abune haka kamar qaramar yarinya?.


"Daddy tsoro takeji wallahi,ka cewa dr ya rabu da ita" kallon amnan yayi,yadda tayi maganar har zuciyarta,hakanan itama fuskarta kamar zata saki kuka,baice mata komai ba,yadai saka hannunsa saman kanta ya shafa,sannan ya wuce zuwa ciki.


            Ba wanda ya lura da tsaiwarsa a bakin qofar,da gaske ne tsoro takeji,don gashi nan a bayyane baro baro saman fuskarta


"Tsaya dr" ya fadi yana takowa zuwa cikin dakin,dukkansu suka waiwayo suna dubansa,sai hisham ya sulale ya fice,shigowarsa kadai ta sake sanyata jin kamar alqiyamarta ce ta tsaya,yaci gaba da takowa fuskarshin nan sam babu annuri,hannayensa zube a aljihun wandonsa.


          Dab da ita ya tsaya,har tana jin yadda numfashi ke zarya a qirjinsa,ya kafeta da idanuwansa wanda har cikin jininta take jinsu,abinda ya sake sakar mata da jiki kenan,qasa qasa cikin murya me kama da rada yace


"Kar naga kin motsa.....if not......" Bai qarasa yadan ja qwafa


"Matso kayi mata" ya fada da heavy voice dinsa dake nuni da seriousness dinsa,sannan ya waiwaya ga likitan,ya masa magana da ido kan ya taho.


        Kallon likitan take sanda taga da gaske matsowa yake inda take,bata manta yadda taji kamar zata mutu ba sanda aka sanya mata canular,sannan yanzun yace ta ciki zai mata allura?,ai batasan sanda ta kalleshi da shanyayyun idanunta da suka bude sosai ba,suka kuma cika taf da hawaye ba


"Don Allah......dan Allah" tayi maganar tana girgiza kai muryarta tana rawa,idanu ja'afar ya zuba mata,mamakinta na sake cikashi


"Tsaya" yace da likitan sanda yaga ta dunqule waje daya,hawaye na gangaro mata lokacin da yazo gab da ita ya daga allurar,wani abu me kama da tausayinta ya tsarga masa,halitta ce qin allura,ta tuna masa da marigayiya amransa,haka ake shan daga da ita idan zaa mata allurar.


         A hankali ya sanya hannunsa guda daya ya kamo tafin hannunta ya saka cikin nashi,tsigar jikinsa ta zuba gaba daya,tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafarsa,karon farko da hannunsa ya sake taba wata mace tun bayan rasuwar shaheeda,laushi da dumin da tafin hannun ke dashi ya ratsa kowacce gaba ta jikinsa,a hankali ya soma murza tafin hannun,abinda ya daukewa maimunatu wuta kenan gaba daya,ta kuma wara dukka idanunta dake jiqe da lema akan fuskarsa dKe gab da tata,idanu ya zubawa fuskarta data yi wani kyau saboda lemar data jiqe eyelashes dinta,abinda ya basu damar yin wara wara,har yanzu da cikarsu da kuma tsahonsu


"Relax....babu zafi fa,yanzu zai gama,just a few seconds" yayi maganar da wani irin sound da yasa taji zuciyarta ta sauya bugu,idanunta ta lumshe cike da kwarjinin daya ma idanun nata,tana kuma jin shigar qarfen a hannunta,saidai kuma kamar ya dauke duk wani tsoro fargaba da kuma zafi da take zaton zata ji.


              Batasan an gama ba,tadaiji ya danne mata wajen,likitan kuma na tsokanarta


"Randa zaki haihu bansan ya zata kasance ba" murmushi gefan baki ya subucewa ja'afar,shima yayi wannan hasashen tun dazun,sai ya samu kanshi da daga kai yana kallon fuskarta,wadda ta fito clearly very close to him,jajayen lips nata suna motsawa a hankali kamar wadda ke karanto addu'a,har yanzu idanunta a kulle suke,taqi ta budesu,quruciyarta na bayyane saman fuskarta,lips dinta suka ci gaba da daukar hankalinsa,ya samu kansa da ci gaba da kallon fuskartata kallo irin na qurilla,jira yake ta bude idanuwanta yaga yadda zatayi,akwai wani irin haske da kyau da idanunta ke qarawa a duk sanda ta tsorata,abinda ya kula dashi tun a ranar,bakinta yana sake tsukewa,idanunta na dada girma da haske,abinda ke sashi cikin wani dan qaramin nishadi da gajeran tunani.


         Hannunsa dukka biyun ya sanya yana yafa mata mayafinta saman kanta sanda ya jiyo muryar hisham da jabir gab da dakin,da alama shigowa za suyi,kafin yace wani abu sun turo qofar sun shigo,hisham a gaba,abir din na dauke da amna,sai fatiman jabir din,sai ya janye baya a hankali,suna hada idanu da jabir din ya sauke masa wani murmushi,tuni ja'afar din ya fahimci abinda yake nufi,tsananin shaquwarsu ya sanya suke saurin karantar juna koda basuyi magana ba,murmushin da ya sanya ja'afar sake dinke fuskarsa tsaf


"Allah ya taimaki boss" jabir din yafada cikin qan qan da kai,kamar yadda yaron gida ke magana da uban gidansa,amma saidai can qasan ran ja'afar yasan bawai yayi bane da gaske,akwai manufa na wannan gaisuwar,duka salon tsokana ne,don haka bai wani nuna masa ba ya bashi hannu sukayi musabaha.


          Jin baqin murya ya sanyata soma bude idanunta da suka sauya kala saboda rufesun da tayi gam da kuma kukan data fara a dazun,idanunta akan fatima tanason tuna inda tasan fuskar,muryar jabir data ji ya tuna mata,wannan shine haduwarsu da ita na biyu tunda sukayi aure,tayi qoqarin sakar mata murmushi duk da yadda takejin wani irin abu yana mata yawo a jikinta,uwa uba kasalar data saukar mata.


       Kujerar gaban gadon Fatima ta zauna suna gaisawa tana mata sannu,jabir shima ya matso yana mata sannu,sannan suka fice a dakin,abinda ya basu damar sakewa kenan gaba dayansu.


          Hira sosai suka sha da fatima,lokaci guda wani haduwar jini ya shiga tsakaninsu,duk da fatiman ta girme mata da kusan shekaru hudu a qalla,don zatayi shekara ashirin da biyu,kafin fatiman ta wuce har zazzabin da takeji ya sauka,alamar allurar ta fara mata aiki kenan,basu suka tafi ba sai bayan magrib ya aiko amna yace ta fito,ta sake mata sannu da jiki ta bata phone number dinta,ta nema ta maimunatun,sai taji nauyinta tace mata bata da waya,tana ganin kamar ba zata yadda da hakan ba,don haka tace da ita idan ta koma gida zata kirata,bata haddace number din ba,a zuciyarta ta yanke shawarar bude wayarta ta soma amfani da ita itama,don tun sanda hisham din ya bata ita take ajjiye bata yi komai da ita ba.


         Kwana biyu ta qara likita ya sallameta,zuwa sannan taji qwarin jikinta,amma sai anni tace


"Tabawa,ku tafi gidan tare zuwa sanda zata sake jin qwarin jikinta,ban sani ba ko qaramin ciki ne,don namiji ba kunya gareshi ba,yana bayaso baya so,amma fa tsaf zai iya lallabawa ya dirkawa yarinyar mutane ciki" tana qarasa zancan yana turo qofa cikin dakin,hada idanu sukayi da anni,sai ta fuske kawai,sometimes ita kanta yakan mata kwarjini,kamar baiji zanca ba haka ya nuna,sai ma ya fasa shigowa dakin sanda aka kirayi wayarsa,ya juya ya fice yana qoqarin daga kiran.


         Sanda suke drivern ya gama sanya kayansu a mota,sai anni taja baba tabawa gefe


"Tabawa,don Allah kisanya min idanu sosai akan zaman yaran nan,inaji a jikina kamar yana cutar musu da yarinya,maimunatu marainiya ce,sannan kuma amana ce a hannuna,nafi damuwa sa lamarinta akan na unaisa,saboda ita din akwai quruciya sosai ajikinta fiye da warcan,ita zata iya yaqi dashi ta qwatoshi,amma maimunatu nada buqatar kulawa"


"In sha Alla haj anni,kada ki damu,koda akwai kusakurai zanyi qoqarin nusashesu tare da gyara mata"


"Yauwa tabawa,na gode"


"Har yau ban biyaki ba haj anni,kawai bashinki a kaina" murmushi annin tayi,tabawa tafi qarfin me aiki a wajenta,ta zama wani bangare na familyn dr marwan akko,duka gidan da wannan idanun suke kallonta,don babu wanda baiyi wasa a cinyarta ba,babu wanda bata raina ba,babu kuka wanda bataga quruciyarsa ba.


         Sanda maimunatu ta fuskanci tare da baba tabawa zata koma gida wani irin farinciki mara misaltuwa ya cikata,har hakan ya kasa boyuwa saman fuskarta,itama baba tabawan tafuskanci hakan,abinda yasa ta sake sanya ayar tambaya kenan,ta kuma ciwa kanta alwashin gano komai da kawo gyara dai dai iyawarta.


No comments

Powered by Blogger.