Gurbin Ido 6
*06*
"Alhmdlh" anni ta furta sanda motocin suka faka a qofar ginin gidan bappa labaran,mahaifi ga ibrahim,qafafunta ta zuro qasa tana fadin
"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim" kana tayi bismilla ta yunqura,gaba daya qafafuwanta sun riqe,jikin tsufa ga kuma zaman mota
"Salmanu ku jirani,idan mun gama gaisawa inajin tare daku zamu fita can cikin gari na duba masauki" cewar matashiyar,dakatawa da tafiyar da anni keyi ta waiwayo tana yamutsa fuska
"Laila....me naji kina fada?,au dama ba rakiyar Allah da ma'aiki kika yimin ba?" Shaf ta manta da annin tana jinta,fuska tadan kwabe
"Kuma me nayi anni?,duk wannan dawainiyar?,ina cewa flight zamu bi kikace kefa sai mota,amma ban fasa rakoki ba"
"Yo rakiyar banza da wofi?,tunda ba zaki iya kwana a gidan ramatu ba" hannayenta laila ta hade waje daya
"Shikenan,zan kwana abar maganar" don sarai ta sani mitar annin ba abu bane me kyau ko dadi ba,duk da hakan taci gaba da takawa zuwa cikin gidan tana ci gaba da mitar,ta dauke kanta tana sake ajiyar zuciya,idanunta na sauka ga yaran da suka fara baibayesu suna kallonsu,sannan ta dubi su salmanu
"Kuyi tafiyarku kawai,amma ina buqatar ruwan sha"
"Akwai ai za'a samu" yahaya ya amsa mata,sai ta juya tana bin bayan anni zuwa cikin gidan.
Dai dai lokacin da yuuma ke qoqarin daura alwalar sallar magariba,wadd ta saba duk lokacin da tayi girki ta kammala,tana hadawa da alwalarta sanna ta wuce daki.
Cikin mamaki ta ajjiye butar data gama zubawa ruwa ta waiwayo da hanzari jin muryar annin
"Yafendo?,yafendo yau kuma ni kika tuna?" Yuuma ta fada cikin madaukakin farincikin da ya kasa boyuwa a fuskarta,kana ta kasa jiran qarasowa anni,ta taka da kanta ta cimmata a tsakiyar gidan
"Nice rahama,yau dai Allah ya qaddara ganawarmu,kimin aikin gafara" anni ta fada tana kama hannun yuuma,murmushi ya kuncewa yuuman,ta shiga marabtarsu,dai dai sanda aka fara shigowa da kayan amfani na abinci,wanda ya zamewa anni kamar ibada duk sanda zata ziyarcesu,takan sauke musu kayan abincin da sai su kusa shekara basu qare ba,mota biyu takeyi,daya ta kayan abinci,daya kuma wadda zata taho a cikinta.
Hajiya maryama wadda ake kira da anni,tamkar uwa take a wajen yuuma,saboda da ita da mahaifiyar yuuman 'yan mata zarr suke,'ya'yan yaya ne(namiji) da 'ya'yan qanwa,kakanninsu daya,a turance ake cewa(cousins),tun zamanin yammatanci akwai shaquwa sosai tsakanin anni da mahaifiyar yuuma,uwa uba sunansu daya,maryam da maryam,kakan yuuma asali dama bafullacene,mazaunun ruga,koda ya tashi aurar da diyarsa maryam saita auri jinsinsu,mahaifiyar yuuma a ruga tayi aurenta kamar yadda ta taso a nan,yayin da daya maryam din anni tayi aure cikin gari itama kamar yadda ta rayu a nan,saidai duk da hakan zumuncinsu bai yanke ba,duk sanda dama ta samu suna ziyartar juna su da 'ya'yansu,har zuwa sanda suka fara tara zuri'a,rayuwar mahaifiyar yuuma batayi tsaho ba Allah ya karbi abarsa,a sannan duka duka yuuma din bata wuce shekara sha biyar ba a duniya,sosai anni taso ta riqe yuuma ta kuma aurawa danta na fari,saidai kuma mahaifin yuuma yaqi bada ita,saboda ita daya ce 'ya mace a wajensa,dole ta haqura,taci gaba da kulawa da ramatu(yuuma) da kai mata ziyara har zuwa sanda aka aurar da ita ga bappa labaran,ita ta yiwa yuuma komai kamar diyar cikinta,saboda ita dinma Allah bai bata diya mace ba,sai maza da take dasu guda hudu.
Tun daga sannan takan ziyarci yuuma akai akai,ramatu yuuma ta zama 'yar gata,batayi kukan rashin mahaifiya ba ko kadan,saboda anni ta tsare mata komai,bata da matsala ta kowanne fanni na rayuwa,tun daga sutura zuwa cima,ko yaushe anni naka hanya wajen yo mata aike koda bata zo ba.
Sanda shekaru suka fara tafiya yuuma bata haihu ba hankalin anni ya tashi,ta kashe kudi sosai akayita duba yuuma,saidai ba wata damuwa data nuna wadda zata hanata haihuwa bare a maganceta,daga qarshe anni taso fita da ita waje,don tana cikin sukunin rayuwa sosai annin,dukka yaranta ba wanda bai zama wani ba cikin garinsu na gombe amma yuuma tace ta barwa Allah,kome za'ayi idan haka Allah yaso ganinta ba wanda ya isa ya canza mata qaddararta,hakanan dole anni ta haqura,da kanta yuuma ta baiwa bappa labaran shawaran qaro aure,da farko yaqi amma ta matsa ganin cewa shi ba abinda ya nuna bazai iya haihuwa ba,bai kamata ta rageshi ba,daga bisani ya haqura,ya laluba ya zabo karimatu mahaifiyar himu,sanda tazo gidan itama sai data shekara biyu sannan ta samu cikin Ibrahim,bayan ta haifeshin ma sai daya kusa shekara bakwai ta haifa safiya sannan xubaida,sai auta sadam.
Ramatu macace mai tsananin haquri da hangen nesa,ita kanta fureran tasan da haka,shi yasa itama take qoqarin kiyaye wasu abubuwan kada ta shiga haqqinta da yawa,saidai kuma Allah ya jarabceta da son 'ya'ya,sam bata iya yiwa kowa kara a kansu,tun daga sanda bappa yace zai dauki ibrahim ko safiya ya baiwa yuuma daadar himu ta runtse ido ta dunga diga rashin mutunci sai yuuma ta sake kiyayewa,kyautatawa da nuna kulawa da duk uwa zata yiwa danta idan ya ratso tsakaninta dasu tana musu,ta daukesu kamar yaranta,amma ta kiyaye duk wani abu da tasan zai bata ranta ko yaja musu cece kuce da furera,abunda yasa xaman nasu ya sake dadi kenan,zaman lafiya kuma ya wanzu tsakaninsu,duk da wani lokacin daadan himu kan dan taba,amma hausawa sukace idan kace wargi waje yake samu,kuma sai bango ya tsage qadangare ke samun qofar shiga,dole itama wasu abubuwan fureran ke kiyayewa.
Fadin irin murnar da yuuman a yau ta tsinci kanta ma bata bakine,saboda anni tadan kwan biyu batazo mata ba,ba kasafai yuuma ke zuwa wajen anni ba,saboda bappan mutum ne mai kulle sosai,itama anni bata zafafawa saboda tasan ya tsarewa diyarta komai,yayi mata riqo na amana bai barta ta wulaqanta ba,sannan ita annin a yanzu babu nauyin kowa a kanta,sakamakon mijinta ya kwan biyu da rasuwa,don haka kafin ma yuuma taje ita taje mata.
Yuuma bata dubi dare daya fara yi ba,haka ta tashi takanas ta yiwa anni sabon girki,cikin cimarsu ta fulani da tasan annin tafi so,a ranar kusan raba dare sukayi suna hira,sai gab da zasu kwanta anni tace da ita
"Wajen fa labaran nazo....."
"Lafiya yapendo?"
"Lafiya qalau ramatu,shanu nake da buqata zan qara cikin gidan gona ta,wancan yaron hamdan naso aikowa,naga zai batan lokaci nace gwara nayi tattaki nazo da kaina" murmushi yuuma tayi,tasan dramer din anni da jikokinta sarai,takan gani idan taje musu,annin irin matan nan ne da basa daukan raini,bata da haquri akan abinda tasan kan gaskiyarta take,amma tana da matuqar kirki da kuma tausayi
"Aiko dai bappansu gaba daya dabbobinsa na garin yayi kudu dasu,kwana goma yace zaiyi ya dawo kinga muna ta zuba idanu shuru,amma naji suna waya da himu yace nan da jibi ko gata zai dawo,saidai ko ki tsimayeshi,cikin rugar nan nasan zai duba miki irin wadanda kikeso din"
"Kash.....kuma sai da nayi wannan tunanin,amma bari mu gani,Allah yasa ya dawo kafin na wuce,don kwana uku zanyi,ranar litinin zan koma ga likitan qafata abuja"
"Har abuja anni?" Yuuma ta fada tana kama baki,baki anni ta tabe
"Ina zaman zamana rigimammen yaron nan ya hadani da zirga zirga,duk kusan qarshen wata sai yasa an sakani a jirgi ba gaira ba dalili na tafi ganinsa,nace ya canzamin ya kafe,wai duk nigeri shine lamba daya.....kijimin qarya ramatu" anni ta qarashe fada tana yatsina fuska da tabe baki.
Murmushi yuuma ta sake tana kada kai,tana matuqar sha'awar yadda suke kula da anni,tana jin cewa dama ace itama tana da arziqin da zata ramawa anni koda dan kadanne cikin irin alkhairanta gareta
"Tunda ya fada ai hakanne anni" kashingida tayi kan lallausan katifa da bargo da yuuma tayi mata shimfida da ita
"Ke rabu da shi ramatu,bokon tasu ma ta wannan qarnin tafi qarfin hankalinka,ke bakya ce sunyi muhammadiyya ba" anni ta fada tana fadawa wani tunani can,wanda har sai da yuuma ta ankara
"Yanzu anni har yau baki bar sana'a ba?" Idanunta ta bude sosai tana kallon yuuma
"Ramatu,kome arziqin mijinki jikoki da 'ya'ya kada ki kuskura kice zaki rabu da sana'a,duk tsiya naka naka ne,koda ba'a rageka da komai ba,amma naka yana da dadi" kai yuuma ta jinjina tana gamsuwa da zancan anni,tun tale tale anni bata saba da zaman banza ba,har kawo yau da babu abinda ta nema ta rasa,ko rai tace tana so idan ana siyar dashi za'a siya mata,amma bata daina nema ba,tana da makeken gidan gona,wanda tafi ji dashi fiye da komai nata.
Tun suna hira sama sama har bacci yayi awon gaba da anni,sai a sannan yuuma ta gyara nata wajen ta kwanta itama.
*_WASHEGARI_*
K'arfe takwas na safe yuuma ke dosar dakin daada dauke da turamen atamfa gudu hudu a hannunta da shadda ta maza yadi goma,sai takalmi na maza me kyau wanda ta tabbatar zaiwa ibrahim.
Da sallama ta daga labulen dakin daadar,safiya dake zaune tana shan kunu ta amsa mata tana gaidata,dai dai lokacin daada ta fito daga uwar dakinta tana daura zani,kafadarta saqale da hijabi.
Gaisawa suka fara yi da yuuma sannan ta'ajjiye mata kayan
"Gashi inji anni"
"Too.....anni bata gajiya,to Allah ya amfana ya qara arziqi" daadan ta fada cikin farinciki,mutum ce dake matuqar son ka yiwa 'ya'yanta alkhairi,safiya dake shan kunu tataso itama tana daga atamfofin tare da fadin
"Bara na zaba tawa kafin zubaidata iso ta dauke wadda tafi kyau......gaskiya anni nada kirki,bata gajiya" murmushi yuuma tayi ta miqe,har takusa da qofa ta juyo
"Af.....niko daada nace ba,ko ibrahim ya gaya miki inda yaje ne?,tun jiya anni keta tambayarsa,kuma kamar banga shigowarsa gidan nan ba tun shekaran jiya,abincinsa ma sai da safen nan na hada a dumame" tana shirin saka hijabinta ta amsa mata
"Eh.....na turashi gidan sukaina"
"Sukaina?" Yuuma ta maimaita a ranta cike da mamaki,saidai ba kasafai take magana akan wasu abubuwan da daada ke yankewa kan yaranta ba
"Ayyah...to Allah yasa zasu hadu,don jibi annin zata koma"
"Ba lallai gaskiya,inajin sati zaiyi acan kafin ya dawo"
"To ba laifi" yuuma ta fada tana ficewa,kanta ya daure tamau,sukainan yayar furera ce,bata da kirki ko kadan,masifaffiya ce ta bugawa a jarida,tana aure ne a wani qauye dake maqotaka da rugarsu,ta yaya za'a tura saurayi kamar himu gidan yayi kusan sati?,duk da itama tana da samarin yara kamarshi,amma kuma tafiyar ai ba ta radin kansa bane,kamar wani qaramin yaro?,da wannan tunanin yuuma ta koma dakinta,inda tabar anni da kuma laila wadda ke jira a kawo mata qosai da yuuma ta bayar a siyo mata,tace shi take sha'awa,tunda suka tashi da safen take jiyo qamshinsa.
Suna tsaka da hira daada ta shigo a shiryenta tsaf,suka gaisa da anni sannan tayi mata godiya daga bisani tace
"Zanje na dawo yuuma,ba dadewa zanyi ba" kallonta yuuma tayi cike da mamaki,ina zata da safen nan,uwa uba kuma ma kusan dokar bappa ce,basa fita unguwa a gidan matuqar ya tafi kudu irin haka sai ya dawo,kamar anni tasan tunanin da yuuman take sai tace
"Labaran ya sassauta tsaurin nasa kenan?" Tayi maganar tana dariya.
Kai daada ta kada fuskarta na nuna zallar damuwa
"Ko daya anni,dole ta kama na fita ne,zanje na yiwa wata yarinya data nacewa himu gargadi,waye zaiso hada iri da irin tsiya irin jaraba",laila dake dan sauraron voice note na watsapp ta earpiece din dake kunnenta sai ta zareshi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon daada,saboda yadda taji maganar banbarakwai,ita kanta anni dake rayuwa cikin tsakiyar birni,cikin ahali da muhallin da wayewa da kuma boko suka yiwa katutu sai data ji maganar bawai
"Tooo....ikon Allah,to....abi a sannu dai,Allah ya maganta mana"
"Ameen ameen,sai na dawo"
"Allah ya kiyaye" yuuma ta amsa mata.
Shuru yuuma tayi tana juya batun cikin ranta,me yasa daada take haka?,akan yaranta gaba daya idanunta suje rufewa?,yanzu Allah ne kadai yasan idan taje me zasu aiwatarwa da yarinyar,tunda ta riga data sani,innar laulo qawace kuma aminiya a wajenta,ita kanta banda ubangiji ya riga da ya qaddara tafi qarfinsu,da ba qaramar wuya zata bata ba ta hannun daadan.
"Wai....nace ba" laila ta fada tana duban yuuma,sai ta maida hankalinta ga laila
"Wai daada kuwa cikakkiyar bafulatana ce yuuma?" Murmushi yuuma tayi,tasan me lailan ke rayawa cikin ranta
"Gaba da baya,har gwara ni innata itama ruwa biyu ce,amma ita babu sirki"
Tun gabanin lokacin tafiyarta kiwo yayi yau din ta shirya,da wurwuri tayi wanka don kada innar laulo ta farga ta hanata yi,ta gyara jikinta sosai,ta kama jelar gashinta ta nannadesu tayi musu wata lanqwasa me qawanya me kyau,hatta da duwatsun kwalliya na kanta da hannunta sai data qara wasu,ta sake fita bufalatana zam.
Can qasan ranta takejin cewa tana yin wannan kwalliyar ne duka saboda ibrahimu,tana ji a jikinta zaiyi wuya ace yau din baizo inda take ba,saboda yaune kwanaki uku suka cika bata ganshi ba,bata saurari wani abincin safe ba,tunda ba ita zatayi ba yau,ta cika gorarta da nono wanda ta tatsa ta barwa innar laulo xatayi aikinsa za'a fiddashi kasuwar qauyen dake maqotansu wadda take ci yau.
Tun kafin innar ta tashi ta kada dabbobin kiwo,yau fes takejin zuciyarta,da wani nishadi na daban,ba kuma lallai ka fahimci haka ba,amma idan ka kalli fuskarta da kyau xakaga akwai banbancin yanayi a tattare da ita.
Wajen daya zame musu gurin zama ita da ibrahim din ta koma ta zauna bayan ta gama duk abinda ya kamata tayin,lokaci bayan lokaci tana daga kanta zuwa sama,ta wurga kallonta hagu da dama,tana ji kamar ibrahim din yana hanya,kamar yana tahowa inda take.
"Kin fara son ibrahim ne?,me yasa zuciyarki ke canzawa?" Ta yiwa kanta wannan tambayar karo kusan na uku kenan,sai ta girgiza kanta a hankali,har yanzu batace ga dalili ba,amma rashin zuwan ibrahim din a kwana uku rak sai takejin kamar tans komawa izuwa wata duhuwa ne data fita ta bari.
Duk da yadda lokaci ke qara jaa amma bata saare ba,bata rasa qwarin gwiwarta ba,taci gaba da dube dube,har daga bisani ta miqe daga wajen,ta fara kewaye cikin dabbobin,wai ko hakan zai sanya lokaci yayi gudu,ya kusantata da zuwansa wajen.
"Maimunatu na!" Kakkaurar muryar mai cike da kaushi ta doki kunnenta,ta kuma zama musaya ko ince madadi ga muryar ibrahim da take ta dako da fatan ji.
Buɗeri ne,ba shakka shine,saboda shi daya yake mata wannan kiran mafarautan,kiran dake sanya zuciyarta luguden bugu,ta sauke sandarta a hankali tana nufin juyawa zuwa gareshi,saidai kafin ta waiwaya din har ya iskota ya sha gabanta,taja baya da sauri saboda yadda kusancin dake tsakaninsu yayi qanqanta da yawa.
Fuska ya hade yana kallonta
"Meye na ja da bayan?,kin manta ke din tawa ce?" Ya fada yana nunata da yatsa,kau da kanta tayi,idanunta suka sauka ga qafarsa dake cikin huffaje,saidai shi kansa huffajen yayi daqal daqal dashi,kamar yadda sutturar jikinsa take cidin cidin,sau tari tana mamakin uban tulin qazanta irin naa buderi,abune me matuqar wuya ka sameshi fes cikin tsafta
"Amma kinyi kyau maimunatuna......ina fata babu wanda ya kallemin ke" yayi maganar yana washe baki,kanta ta daga a hankali tana duban gefe da gefanta,tana fatan kada Allah ya kawo Ibrahim a yanzu har sai buderi ya wuce,tasha jin alwashi daga bakin buderin na cewa,duk randa yaga wani ya rabi maimunatunsa,wala shakka sai ya sha jininss,tana kyautata zaton wannan na daya daga cikin dalilan daya sanya babu wanda yake mu'amala da ita
"Me kike nema kuma?" Ya fada yana hade rai,kai ta girgixa
"Babu komai" amsarta tasa ya saki fuska
"Na sani,kinfi kowa hankali cikin 'yammatan rugar nan,nasan babu wanda zaki kula,ungo wannan" yayi maganar yana miqa mata wata leda.
Babu batun ma tace ba zata karba ba,don kuwa bata baki ne,don haka ta saka hannu ta karba tana cewa
"Na gode"
"Yauwa,medillu,dan men waratam?(zan tafi,yaushe zanzo?" Mummunan faduwa gabanta yayi,kada dai xancan da innar laulo ke gaya mata ya tabbata,buderi..... Buderi ne zai fara zuwa tadi wajenta?
"Ban sani ba" sandarsa ya wulwula sama ya caketa a qasa
"Shikenan,ni xan saka rana da kaina" sai ya juya abinsa ya fara tafiya,dama can shi din ba mutum ne da ya iya yin sallama ba,da ya gama abinda ya kawoshi xai saka kai ya wuce abinsa,har ya dan bata rata sai taga ya dawo da tsaya a gabanta
"Baki taba cewa kina so ba maimunatu,ate ayyam?,ayid'iyam?(zaki aureni?,kina sona?)" Banbarakwai taji maganar tasa,ta kuma rasa amsar da zata bashi,tana matuqar tsiron buderi,batajin xai kasa maketa a wajen idan tace bata sonshi,amma kuma idan tace tana sonsa din tayi masa qarya,sannan yaudara ta shigo ciki.
Dariya ya bangare da ita
"Ja'ira,kunyar gayamin kikeji kenan.....shikenan,idan nazo saiki gayamin tunda zuwan dare ne,bana ganinki sosai" daga haka ya juya abinsa yana waqar tauri.irin ta matasan fulani yana cilla sandarsa.
Baya taja a hankali ta jingina bayanta da bishiyar dake wajen,ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana lumshe idanunt,sannan ta saki ledar hannunta a hankali ta sulale zuwa qasa.
A matakin rayuwarta gaba daya ba zata iya dorar da komai ba,ba zata iya fadin meye ainihin rayuwa ba,kamar yadda ba zata iya fadin me rayuwa ta qunsa ba,meye manufar tata rayuwar?,me ta cimma?,me takeso ta cimma?,tabbas a karan kanta tasan cewa akwai abubuwa da dama da takeso ta cimma,tana da mafarkai da burika masu yawa irin na kowanne dan adam,saidai ita kanta batasan wadanne ne burikanta ba,me takeso ta cimma din,dukka bata sani ba,rayuwata qwaqwalwarta dama komai nata na tattare ne a waje daya,a yanzun kumma innar laulo ta dauko hanyar da zara qara ruguzata zuwa pieces gaba dayanta,aure da buderi?,me hakan yake nufi?,wanne buri ne a ran innar da takeso ta cimma?.
Ta jima a haka kafin ta iya bude idanuwanta,dukka wani fata da take dashi na ganin ibrahim ya fara zagwanyewa daga zuciyarta gaba daya,ganin yadda lokacin da ya dace tabar wajen zuwa gida ya gabato,jiki a mace ta miqe daga jikin bishiyar,saidai tana taku biyu takalminta ya katse
"Innalillahi" ta fada gabanta yana faduwa,ta duqa a hankali da zummar daukoshi,sai tayi arba da ledar da buderi ya kawo mata wadda ta jima da faduwa a wajen,ta sanya hannunta a nutse ta budeta,sai tayi arba da gasashen naman daji,cikin tashin zuciya ta dauki ledar gaba daya tayi wurgi da ita can cikin daji,sannan ta dauki takalminta ta duba da kyau,ya gama moruwa,bataga laifinsa ba,saboda yayi mata iyakar qoqari,bata da wata sauran dabara data rage mata,abu dayane a yanzu yayi mata saura shine ta cire dayan ta dauresu a qugunta,sannan taci gaba da tafiya da zallar tafin qafarta tana fara hade kan dabbobin,tanayi tana takatsantsan kada ta taka qaya.
Leave a Comment