Idon Naira 1



1

_Bismillahir rahmannirRaheem_


_*Uba daya ne ya haifesu, yabasu tarbiya daya,kauna daya,matsayi daya..*_

*_Qaddara ta bambamta rayuwarsa ga bangarora guda Kashi biyu Wato haske da duhu,_*

_*haske da duhu shine qaddarar data zama tazara a rayuwarsu har suke tsananin qyamatar junansu,*_

*_qaddararsu ta gangaro har kan 'yayansu Wanda suke tamkar black and white maana baqi da fari suma gurin bambamci fiyema da iyayen nasu,_*

*_kaman yanda haj Maryam ta fada har abada babu alaqa ko kusancin dazai hada zuri'arta tsarkakka mara najasa da daudar zina da zuriar Yar uwarta dasuka kasance gewaye cikeda daudar rayuwa mara kyau da amfani ta karuwanci.._*

*_Labarin IDON NERA kenan Wanda yazo cikin wani qayataccen salo da sabon tsari tareda nutsatsiyar kauna da soyayya kaman yanda muka saba wannan karon salon na musamman ne._*

_ALLAH YABAMU IKON GAMAWA LAFIYA KAMAN YANDA ZAMU FARA LFY.Amin_



**************

Daga kwancen da ta ke bisa kan gadon ɗakin baccinta, ta kai hannu ta shafa cikinta ɗan watanni bakwai zuwa takwas, tana jin tarin ƙauna da soyayyar cikin na sake huda zuciyarta.

Sai dai a duk lokacin da ta tuna irin zaman da ta ke yi da uwargidan mijinta da kuma ƴarsa, sai ta ji wani tsoro na shigarta na yadda za ta haifi ɗa ko ƴa su rayu irin  kalar rayuwar da ta ke yi a cikin gidan.


Wata iriyar rayuwa me sanya kewa da ƙunci wanda ba a taɓa ɗaga ido anyi mata duba na sassauci, bare har ta sanya rai watarana za a ƙaunaceta ko abinda za ta haifa ba. 

Basu taɓa faɗa da juna ko musayar kalamai a tsakaninta da kishiyarta ko ƴar kishiyar ba, sai dai irin zaman shariya da wofintar da ita da suke yi a cikin gidan, ta gwammace ace faɗa su ke yi kullum ko banza a ce suna musayar kalamai marasa daɗi a tsakanin junansu.

Amma zaman da ta ke yi dasu zama ne na ba ruwan wani da wani a cikinsu, idan sun haɗu sai dai su kalli juna kawai, don ko ta kwantar da kai ta gaida abokiyar zamanta, ba za ta taɓa tada kai ta dubeta ba bare ta sanya ran za ta amsa mata gaisuwarta,

Kazalika Maryamah wacce ke amsa matsayin ƴar mijinta tilo da ta zo ta tadda a gidan budurwa me kimanin shekaru sha bakwai a duniya, wacce ta fi uwarta nuna mata zafin kishi da tsana tamkar ita ce kishiyarta ba uwarta ba,

Maryamah nada kishin abinda takeso take Kuma ganin nata ne,

Kaunar datakewa mahaifinta yasa takejin kishin aurensa sbd zai Haifa wasu yayan ya hada da ita,


A duniya abinda tafi tsana shine 'yan ubanci,

Tanada wata irin fitinanniyar qyama da qyanqyami akan a hada Jininta da wasu shiyasa take Jin rashin kaunar matar mahaifinta.


Sam bata shiga duk wani sabga da zai haɗata da ita, kallo ma bata ishe ta ba bare ta sanya rai wani abu zai iya shi ga tsakaninsu,

Babu abinda hafsatu ta ke hangowa a cikin idanun Maryamah face qyanqyaminta da kishinta me zafi,


Ko mahaifiyarta takan jisu wasu lokutan tanawa maryamah din fadan rage qyamar shiga mutane Wanda ita Kuma tamkar halittace hakan Allah yayita idan tanason Abu tanaso,

Idan tana kaunarsa to tana kaunarsa

Idan batason Abu to da gaske take qin ko son kallonsa.


Hannu hafsatu takai ta shafa cikinta dake juyawa ahankali cikin cikinta  tana sake jin wani irin abu na danne zuciyarta,


''Shin za su ƙaunaci abinda za ta haifa?

ko shi ma ba zai samu arziƙin ko kallon banza daga gare su ba? Maryama za ta rungumi ɗa ko ƴar da za ta haifa a matsayin ƴan uwanta na jini ko kuwa ƙiyayyarta da ta ke bangowa a idanunta shi zatawa abinda za ta haifo?"


Waɗannan tunanikan suka sake sanyaya zuciyarta har ta ji hawaye na biyo fuskarta ta Dan gyara kwanciyarta daidai lokacin da muryar mijinsu Malam Adamu ke ratsa kunnuwarta lokacin da ya ke kiran sunanta,


"Hafsatu! Hafsatu!"


Sai ta yi saurin kai hannu ta share ragowar hawayen da suka zubo mata tana amsawa da cewa, 


"Na'am Malam gani nan fitowa


Daga haka ta nufo hanyar fitowa falon gidan wanda yake na tarayya ne kuma anan suke haɗuwa su ci abinci kowane lokaci sai dai idan randa Malam ɗin ya yi balaguro ne kawai ba a zaman cin abincin.


Ta samu wajen zama daga gefensa na dama ta zauna idanunta na satan kallon yadda Maryama ta ɗauke kai daga duban sashin da zata zauna ma baki ɗaya ta maida idanunta kan mahaifiyarta da ke hidiman zubawa Malam Adamu abinci a plate.


Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd takasa sabawa da wannan yanayin na Maryamah sbd rashin ko inkulan Maryamah yafi damunta akan na kishiyarta sbd ganin Maryamah itace Yar uwa kuma jinin abinda Zata haifa zatafi son kome Zata Haifa yasamu kauna da kulawa daga Yar uwarsu wadda Zata iya Zama kaman uwa a garesu tunda babban Yaya kaman uwa ko ubane.


Ta mayar da dubanta kan uwargidarta wacce sam ba ma asalin ƴar ƙasar bace daga can Cameron ya aurota shekaru ashirin da biyu da suka wuce, kuma Maryama kaɗai ta haifa masa bayan ita ba ta kuma haihuwa ba sai yanzu ne da ya aurota ita za ta sake haifa masa wata ƴar ko ɗan.


"Bismillah Hafsatu zuba abincin mana."


Malam Adamu ya yi maganar idanunsa akanta waccce yasan ta kasance shiru shiru mara son haniya kyakykyawa bafulatanar asali da ya aurota daga jihar Adamawa Marainiya ce da ta rasa uwa da uba tun tana tsummar goyo a yanzu bata da wani cikakken dangi ko gata da ya wuce Malam Adamu dayake mijinta Kuma zai zamo uban yayanta.


Hafsah ta zuba tuwan ɗanyar shinkafa miyar kuɓewa ɗanya da Hadeeza ta yi (Wato Uwargidarta) Ta sanya hannu cikin robar ruwan da Malam ɗin ya wanke hannunsa a ciki ita ma ta wanke nata hannun tare da sanyashi cikin plate ɗin tuwan ta fara ci.


Shiru ya ratsa falon daga ƙaran fankar da ya fara gajiya da ya cika falon ba ka jin sautin komi sun yi tsit suna cin abincin babu me kallon kowa a tsakanin junansu sai Malam Adamu kaɗai da ya kan bi matan nasa da kallo yana takaicin yadda har yau gidansa ya rasa walwala da farin ciki kaman kowane gida sbd Hadeeza ta kasa haɗa kanta da Hafsatu domin duk irin kallon rashin Inkula da suke gwada mata yana sane da shi.


Maida kallonsa yayi kan Maryamah wacce zuwa yanzu ta ke matakin kammala karatun diploma ɗinta akan harkan kasuwanci da ta ke karanta wato (Business Administration)


Ya ɗauke idanunsa daga gareta yana jinjina kai ganin yadda gaba ki ɗaya ta juya musu baya tana cin abincinta a natse ko kaɗan bata so ma ta kalli direction ɗin da Abban nata suke zaune sabida kada ta damu kanta ta Kuma damesu,


Ta kasa gane dalilin rashin son kula da matar  duk irin sanyin halinta da rashin kwaramniyarta da hakurinta duk da ko so daya gidan Basu taba ko gardamaba bare hayaniya sai dai tana yawan bai wa kanta amsa da cewa jininta ne bai haɗu da matar ba. 


Maryamah ita ce ta fara tashi ta shige ɗakinta bayan ta kammala cin abincin Abbanta ya rakata da ido yana jinjina kai ba tare da ya ce komi ba Hafsatu ta miƙe da ƙyar sabida nauyin da jikinta ya fara sosai ta dubi su Malam Adamu da matarsa ta ce


"To Allah ya bamu alkhairy zan shiga daga ciki Malam,

Anty Hadiza Saida safe.


Malam Adamu ya bi ta da kallon ƙauna yana tausayin yadda ta riski rayuwarta a cikin gidansa ba tare da ta samu walwala da sakewa cikin iyalinsa ba ya ɗaga sautin muryarsa ya ce,


" To Allah ba mu alkhairy Hafsatu, Allah Ya tashe mu lafiya."


Hadeeza kuwa da qaramin sauti itama ta amsa Tai Mata Saida safen kafin ta Dan daga murya ta kira Maryama don ta zo ta kwashe kayan zuwa kitchen., 


Abbanta ma kaman yanda ya saba Saida yakuma Yi Mata 'yar nasiha akan su yaqi shedan su tsarkake zuciyoyinsu duk da yasan tana  taimakon hafsatu da wasu ayyukan kamar yadda ta ke wa uwarta duk ranar girkinta,

Zata tayata ayyuka da dama Amma Babu wata doguwar magana shiyasa itama hafsatu Bata takurawa Maryamah din da magana sbd tasan ko ahakan yarinyar tanada tarbiya sosai tunda ko kallon wulaqanci bare rashin kunya batai taba mataba.


Tana kwashe kayan ta kai madafin ta aje ta dawo ta wuce ɗan ƙaramin ɗakinta ta kwanta ba bacci za ta yi ba wayarta ta ɗauka Android me arhar kuɗi wanda Abban nata ya siya mata ta hau chatting sai wajen 11:30pm ta kashe wayar ta kwanta don tana da lactures ɗin safe 8 za ta bar gida.


Washe gari karfe takwas daidai Maryama ta fito cikin shirin fita makaranta tana sanye da riga da zani da suka amsa jikinta ta yafa mayafi me Dan girma sbd Maryamah ba laifi tanada ilimin addini sosai hakama tanada irin yanayi na rayuwar uztazan Yan mata.,


Baƙace Maryamah amma kyakykywace sosai tanada jiki Mai kyau da kyakkyawar fuskar Mai kyau itama.


A falon nasu ta samu Abbah da su Ummanta suna kalacin safe ta tsuguna ta gaida su gaba ɗaya a jam'i tana ɗauke idanunta daga duban sashin da Amarya Hafsatu ke zaune ta zauna daga gefen Ummarta ta zuba kunun tsamiya da ƙosai ta fara ci.


"Maryamah ƙarfe nawa za ki dawo daga makarantar yau?"


Abbanta ya tambaya idanunsa a kanta, sai ta ɗaga kai ta dubesa tana amsa shi da cewa, 


"Ƙarfe biyu Abbah."


Malam Adamu ya gyaɗa kai yace"


Madallah, Ga kuɗin motarki na kwana biyu zan baki don tafiya Lokoja ya kamani sai jibi zan dawo idan Allah Ya yarda.


Ya yi maganar yana zura hannu ya zaro kuɗin ya miƙa mata

Maryamah ta amsa kuɗin ta yi godia tana cigaba da cin abincin har ta kammala Ta yi wa Abbah da Umma sai ta dawo ta fice daga falon.


Bayan tafiyar malam har kusan yamma tana dakinta Bata fitoba 

Ta muskuta tana sake rintse idanunta kewa da kaɗaicin rashin abokin hira ko wanda za ta yi walwala tare da shi na sake danne zuciyarta

ta buɗe idanun tana janyo radio ta kunna don shi ne abokin hirarta idan Malam ya fita kasuwa ko idan ya yi tafiya baya gari gaba ɗaya don sam bata iya fita zaman falo sabida gujewa ɓacin rai da kallon ƙasƙanci daga abokan zaman gidan.


Wannan shi ne kalar irin rayuwar da Hafsatu ke yi a gidan Malam Adamu tun da ya auro ta shekaru biyu da suka wuce har kawo yau da take ɗauke da cikin watanni bakwai Sam Ummar Maryamah da ita kanta Maryamah basu taɓa nuna cewa akwai lokacin da za su amsheta da daraja,

Basa zaginta basa komai hakama basa Shiga sanbarta,


Anty hadeeza kuwa Sam batayi Mata kallon mace ma take gani bare harta dauketa kishiya ko cikakkiyar mutum ma,

Ita ko Maryamah tsakaninta da ita gaisuwar safe ce idan ta gaidasu a tare da iyayenta sai sallama idan tashigo guri hafsatun na gurin.


Hafsatu abin na damunta ƙwarai gashi Malam ba mai son shige shigen gidajen maƙwafta bane bare ta yi ƙawaye waɗanda za su dinga ɗebe mata kewa Mace ɗaya ce dattijuwa da ta saba da ita me suna Iyah me ƙosai ita ma ɗin ita ke shigowa gidan ba Hafsah ke zuwa nata gidan ba kwana biyu ma tayi tafiya ta tafi can garinsu shiyasa bata da abokin hira sai dai ta shige ɗaki ta kunna radio ta yi ta saurare.


Ƙarfe biyu Maryama ta shigo gidan tana tafiya tamkar ba za ta taka ƙasa ba sabida gajiya ta wuto matsakaicin tsakar gidan nasu ta shigo zuwa falon gidan Cikin sa a tana sanyo kai cikin falon idanunta ya sauka akan Hafsatu da cikin jikinta ta yi saurin kawar da kanta ta raɓa Hafsatu za ta wuce sai Hafsatu ta yi ƙarfin halin kiran sunanta,


"Maryamah" 


  cak ta tsaya ba tare da ta waiwayo ta dubi matar uban nata ba


Hafsatu ta sake cewa,


"Don Allah ki taimaka ki amso min batir a shagon nan kusa damu don Allah!"


juyowa gaba ɗaya tayi ta zube idanunta akan Hafsatu ta kalleta  kamar ba za amsa kuɗin ba sai kuma ta karba batareda tace komaiba ta raɓata ta fice don zuwa yi mata saƙon.


Ajiyar zuciya me sanyi Hafsah ta sauke tana jinjina irin wannan halayya ta Maryamah gashi ita Kuma kaman mayya Allah ya saka Mata kaunar maryamah din cikin zuciyarta.


"Gashi!"


Shine kalmar da Maryamah ta furta da muryarta me nutsuwa lokacin da ta shigo cikin falon tana miƙawa Hafsatu manyan batira biyu da ta siyo mata.


Karba tayi tana cewa,


"Na gode Maryamah."


Daga haka dukkansu suka shige ɗaki ba tare da Maryamah ta sake furta ko da kalma guda ba.


*********

Bayan watanni biyu cikin Hafsatu ya shiga watan haihuwa wata ranar asabar da misalin ƙarfe shida na safe naƙuda ya kamata aka kaita asibiti.


Bayan ta sha matuƙar wahala ta haifo kyakykyawar yarta mace fara da ita babu in da ta baro kamannin Hafsatu tamkar an tsaga kara.


Malam Adamu da maƙwafciyarsu Iyah me ƙosai dattijiya me shekaru hamsin su ne ke tsaye daga bakin labour room ɗin suna dakon haihuwar  Likitar ta fito ta sanar da su an sauka lafiya tare da miƙa musu Babyn wacce aka naɗeta cikin showel da kayan sanyi farare ƙal

  Hannun Malam Adamu har rawa ya ke yi lokacin da ya amsa jaririyar yana ƙare mata kallo wani irin ƙaunar Yarinyar na huda zuciyarsa Ya yi mata addu'a tare da miƙawa Iyah ita yana kutsa kansa cikin ɗakin da aka fito da Hafsatu bayan an gama kintsa ta ganinta cikin ƙoshin lafiya ya sanya shi yin hamdala da jin ƙarin farin ciki mara misaltuwa.


Bayan sun dawo daga asibiti zuwa gida ne Iyah ta wanke jaririyar tas Aka sake naɗeta cikin kayan sanyi sai a lokacin Umma da Maryamah suka shigo ɗakin don ganin Baby.


Maryamah tun kallon farko dataiwa babyn taji jikinta na neman sanyi sbd haka kawai taji kaman qaddarartace aka haifo Mata.


Hadeeza ma bayan ta gama ƙarewa jaririyar kallo ne ta aje ta tana duban Hafsatu ta miƙe tana cewa,


"Allah shi raya mana ya baki lafiya."


Daga haka ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake cewa komi ba maryamah na bayanta.


Bayansu hafsatu tabi da kallo ƙwalla na taruwa a idanunta sbd tana kaunarsu Kuma tana Jin inama Suma zasu Dan kaunaceta su dukan zuciyoyinsu su huta da wannan zaman quncin dasukeyi su dukan.


"Hafsatu ki yi haƙury da halin abokiyar zamarki da ƴar mijinki ki rungumi ƴarki ta zama abokiyar hirarki da shawaranki idan Allah ya raya miki ita Ba lalle sai kowa ya soka a duniya za ka rayu ba 

bai zama lallai sai waɗanda ka ke tare da su sun nuna maka ƙauna ba 

ki godewa Allah ba cutar da ke suke yi ba kawai dai basa shiga sha'aninki ne kuma basa maraba da ke a cikin gidan Kuma Inshallah wataran hakan ma saikiga ya wuce Kun zauna cikin walwala kaman baayiba

don haka ki yi haƙury tunda ke ma gashi Allah ya baki rabo sai ta zama abokiyar ɗebe miki kewa."


Iyah ta yi maganar tana duban yadda hawaye ke gudu a idanun Hafsatu

ta cigaba da rarrashinta da kalamai masu daɗi har sai da ta tabbatar Hafsatu ta samu nutsuwar zuciya.


Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya Iyah ce ke shigowa tana hidimar kula da Hafsatu tunda bata da kowa a garin Kano bata da wani sauran gata da dangin da za su iya yo tattaki tun daga Adamawa su kula da ita ba. 


Ranar suna Jaririya ta ci suna ZAINAB sunan mahaifiyar Malam Adamu da ta jima da rasuwa ba wani taro aka yi sosai ba daya wuce maƙwafta da jama'ar arziƙi da ya ke huɗɗa da su a unguwar Sabida shi ma zuwa ya yi garin Kano don kasuwanci, amma asalinsa ɗan Lokoja ne ba shi da ƴan uwa sam a garin sai dai abokan kasuwanci da maƙwafta kawai.


Iyah ita ta dinga kulawa da Zaynab da Hafsatu har suka gama wanka

sam bata taɓa gajiyawa ba tamkar jikarta ta jini haka ta ɗauki Hafsatu shiyasa Hafsatun ke jin cewa bata da tamkar Iyah don ta maye mata gurbi da dama waɗanda danginta na jini ne kawai za su iya mata hakan.


Har kawo wannan lokacin da suka gama wanka koda wasa Maryamah bata taɓa shiga ɗakin Hafsatu ta ga ƙanwarta Zaynab ba tun ɗaukar da ta yi mata ran da aka haifeta bata sake daukantaba saidai lokuta da dama idan Hafsatu tafito da zainab din haka zata ringa kallonta tanajin rashin nutsuwar zuciya.

Daga Iyah sai Malam Adamu su kaɗai suke nuna soyayyarsu ga Hafsatu da jinjirarta Zaynab harsun Saba.


Watannin Zainab shida da haihuwa ciwo me zafi ya kama Hafsatu aka wuce da ita asibiti kwananta tana jinya Ubangiji ya amsa rayuwarta ta bar jaririyarta Zaynab.


Faɗin irin tashin hankalin da Malam Adamu da Iyah suka shiga ba zai faɗu ba, don rumgume gawar matarsa ya yi yana kuka me asalin motsa zuciyar duk wani me saurarensa.


Har aka kai Hafsatu makwancinta Malam Adamu baya cikin hayyaci da nutsuwarsa tun yana kuka da idanunsa har ya koma na zuci wanda yafi na fili illah.


Daga Hadeeza har Maryamah mutuwar Hafsatu ya doke su matuƙa sbd halayenta masu sanyi da hakuri duk da kusan su dukan sunada hakr sosai sai dai lokacin da aka watse zaman makoki sai kowa ta koma sabgar gabansa Iyah me ƙosai ita ce ta sanar da Malam Adamu cewa za ta riƙe masa Zaynab har zuwa lokacin da za ta cika shekaru biyu ko uku sai ta bashi abarsa ya baiwa matarsa riƙonta Sabisa ta san Hadeeza ba za ta raini Zaynab a yanzu ba Ranar Malam Adamu yayi sabon kukan rashin hafsatu dukkanin ƙauna da soyayyar da ya ke ma Hafsatu sai ya dawo kan Zaynab har ma da ƙari. 


A kwana a tashi Zainab tafara wayo yar kyakkyawa da ita da kamanninta na uwarta na sake bayyana matuƙa kamar yadda kullum kwanar duniya ake sake ninka ƙaunarta a zuciyar Malam Adamu Koda wasa Umma da Maryamah basu taɓa cewa za su shiga gidan Iyah su ga Zainab ba tun Iyah na mamakin ƙarfin halinsu har ta daina ta cigaba da kula da Yarinyar har ta cika shekara guda tana gudunta ko'ina Duk in da suka shiga da Zainab sai an yabi kyawunta shiyasa Iyah ke dagewa wajen yi mata addu'a sabida gudun bakin mutane.


Zainab na cika shekaru biyu da rabi Iyah ta tattaro kayanta ta dawo ma Malam Adamu da ƴarsa hannunsa domin ta so cigaba da riƙon Zaynab amma sai aka aiko cewa mahaifiyar Iyah babu lafiya dole za ta tafi jinyarta acan gida ƙauye Hakan shi ya tilasta dawo ma Malam Adamu da riƙon ƴarsa Zaynab hannunsa wannan ne kuma ya zama silar da riƙon Zainab ya dawo hannun Umman Maryamah wacce daga ita har Maryamah ba su taɓa nuna so ko qi wa zainab ba.


Kasancewar Malam Adamu tsayayye kuma jajirtacce a gidansa shiya sanya Umma ta kasa cewa ba za ta riƙe masa Zainab ba

Don haka ba don ranta ya so ba ta amshi riƙon Zainab.

##MAMUH#

#LIFE#

#LOVE#

#SISTERS

#CHILDREN#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo



Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.