Idon Naira 17
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
17
Yamma nayi zuciyarta takasa nutsuwa saidai Kuma ahakan tanajin sassaucin zama anan idan har tana tareda 'yarta akan zama a Abuja 'yarta na Cameroon batasan irin rayuwarda zatayiba acan tunda tanada tabbacin babu Wanda zai tsaya akanta ya Bata tarbiya,
Idan har Lulu zai karba Mata haqqinta na gidan babanta zataso hakan sbd Nan kawai takeda sauran hope na inda zata zauna tayi rayuwa da MARYAMAH dint hakama idan Aqeel yadawo zaiyi saukin samunsu a gidan baban nata.
Dakinsa 'daya ya bata itada 'yarta abinda bayayi baikuma taba ba
Wato barin wani ko bawa wani dakinsa 'dayaba sai akan zainab itama Dan ganinta ayau tareda gane wacece yakejin kamar 'yar uwarsa ce tadawo garesa tunda dukkaninsu har zainab din uwa daya ce ta renesu abinda baida tabbaci shine idan nono daya sukasha, wato idan iyarsa ta shayarda zainab din.
Itama zainab dayake Bata manta iyah dinba sbd kafin atafi da ita gidan Maryamah tun wancan lokacin iyah dince kawai take kaunarta take siya Mata wasu Yan abubuwan wasu lokacin har Saida aka tafi da ita gidan zainab sukai rabuwa Ashe tahar abada ce.
'Dakin baida girma sosai Amma nata na gidan Haj Maryamah baifi wannan din girma ba,
Qatuwar katifa da wardrobe ne Acikin dakin sai madubi da toilet.
Wanka tayiwa maryamah itama tayi tayi sallar ishai Dama ansake kawo musu abinci daga shagonsa sunci sun koshi.
Babu Bata lokaci bacci ya daukesu daga ita har MARYAMAH tunda a matuqar wahala suke.
Washe gari zaunar da ita Lulu yayi yai Mata bayanin gidansu dai agurin Mai anguwa Mande ds ya siya Kuma yasama tabbacin Shi Mai anguwa gidan a hannunsa su Maryamah suka barsa.
Shiru tayi Dan batasan me zatace ba,
Ita kwata kwata Bata gane komai Kuma,
Abinda takeson Jin gidan na ubansu ne kokuwa na haya ne?
Gidan na babanki ne halak malak ba haya ba
Dan haka dai yanzu haqqinki Dole zaa Baki idan DS yaci idan Mai anguwa babu Wanda zaici ya zauna lafiya.
Girgiza Kai tayi ahankali tana Dan rintse idanuwanta dasuka Dan sauya cikin mutuwar jiki tace abar maganar gidan ta hakura Dan ita din ba kowa bace,
Gadon nata ba batajin tanadashi tunda dai su umma basuma San tazo neman gidan ubanta dinba.
Fada Lulu ya rufeta dashi Yana takura da fadan sosai har Saida ta zayyane Masa komai na rayuwarta da dalilinta na baro gidan Yar uwar tata..
Sake Baki yayi jikinsa da bakinsa na mutuwa Dan bai dauka haryanxu akwai wainda zuciyarsu Bata aikiba
Dan kuwa zainab alamu sun nuna tata zuciyar a kwance take cikin ruwa ba jini ba..
Barinta yayi Yakuma ficewa Dan baisan mezai ceba Wanda zata gane Amma dai koma menene sai anbata gadonta wlh.
Daga ita zai MARYAMAH yabari wuni guda a dakin sai siddi daketa dawainiyar kawo musu abinci da abubuwan buqata.
Tunda tashigo ko kofar fita daga palonsa batayiba sbd gida koina karuwai ne da maza
Musamman yanzu da sukasan Lulu bayanan kowane namijin shogowa yakeyi ya shige dakin budurwarsa
Dan babbar qa'idar Lulu bayason maza na zuwa gidan gurin karuwansu,
Saidai kowace idan dare yayi kokum idan tana buqata tace gidan saurayin nata ko alhajin nata koma hotel ne.
Siddi sosai ta nuna musu kauna itada MARYAMAH dinta sbd siddin itace Yar hannun damar Lulu
Itama zaman kanta takeyi Amma tanada kamun Kai ba kamar yanda sauran karuwan keyiba.
Lulu idan akwai babban abinda ya tsana a rayuwarsa shine zalinci,
Bayason zalinci,
Ya tsani zalinci,
Musamman ga mace shiyasa duka Yan barikin dake gidansa aduk lokacinda aka cutatar dasu shine yake tsaya musu sai inda karfinsa ya qare Dan haka kowace Yar barikin dake gidan Kamar babbar Yaya suka dauki Lulu akwai Respect da bin umarni sosai a tsakaninsu dashi.
Yayi tir tareda Allah wadai da jinin umma da Haj Maryamah harma da 'dansu Aqeel Dan kuwa shima baiji ya Burgesa ba tunda jininsu umman ne.
Kai tsaye hukuma ya daukowa Mai anguwa aka kamasa suka kwasa zuwa police akan ya siyarda gidan marainiyar Dan Shi kwata kwata ya cire Haj Maryamah a lissafin gidan tunda tafi karfinsa ga wadda ke buqata Nan Dan inganta rayuwarta data marainiyar 'yarta Dan haka duk ubanda yakeda saka hannu a cinye gidan saiya fito.
Rigimace ta balle a gurin hukuma lokacinda aka kawa zainab ta Fadi ita wacece Mai anguwa yayi tsalle yace wlh qaryane ita ba 'yar marigayin bace Dan baisantaba...hasalima ita Yar marigayi malam adamu din itace da mahaifiyarta suka bada gidan aqara ayi masallacin da aketa kokarin ginawa a anguwar tin shekarun dasuka gabata..
Zainab najin haka jikinta yayi mummunan nauyi ta kasa cewa komai Dan kuwa Kai tsaye aka aibata sunanta daba Yar mahaifinta ba..
Riqe hawayenta tayi tana kallon Lulu Dan ya janye rigimar Amma yace wlh bazai janyeba tunda bacin suna yashigo ciki Kuma.
Case tun Yana qarami sai gashi ya girma yazama babba Dan kuwa hukuma babba tashigo ciki sbd sunan Mande ds daya fito a matsayin shine Wanda ya siya gidan.
Fitar zancen yasa rikicin yaqara girmama Dan kuwa tuni mutuncin DS yafara rawa Dan kota Ina yada zancen ake qarya da gaskia...
Ran DS yayi mummunan baci gashi tunda yaji Lulu a zancen yasan lulun bazai tsayaba saiya Gama lalata Masa suna da mutunci Dan haka take ya saki kudi aka fara neman rufe case din Amma tini Lulu ya juyar da case din zuwa gurin manyan hukuma ba Bata lokaci saiga zancen yashiga kotu.
Tun lamarin na wasa saiga komai ya girmama
Hankalin Zainba ya tashi sosai Dan kuwa Bata taba tunanin zata shiga rigima irin wannanba.
Ta bangare daya Sharia akeyi akan gidan mahaifinsu
Bangare daya Kuma duk masu shedan sun tabbatarda zainab din ba 'yarsa bace yarsa dasuka sani Haj Maryamah Kuma da kansu suka bada.
Ds yayi amfani da karfinsa da dukiya akan shariar sai gashi an wankesa tareda Kama Lulu da zainab akan kokarin Bata Masa suna..
'daga qara Lulu yayi sbd a wanke zainab da aketa aibatawa da fadin ba 'yarsa bace..
Daqa qarar tasu yasa komai ya qara lalacewa sbd tambarin sunan karuwa daya qara hawan zainab sbd alaqarta da Lulu da siddi daketa dawainiya da MARYAMAH cikin so da kauna da kulawa Dan a hannunta Dole suka barta suna wannan yawon.
Kamasu akai aka yanke musu zaman gidan yari na wata biyu Dan tashin hankali da barnar sunan dasukaiwa DS hakama su Mai anguwa sun tsaya sun murzawa idonsu toka sukace basusan wata Yar malam adamu ba bayan haj Maryamah.
Alfarma daya aka Samar musu bayan baqar wuyar da zainab Tasha a kulle sbd Shi Lulu ya Saba
Shine zaa Kira Haj Maryamah ta bada tabbacin idan Zainab din Yar uwartace da mahaifinsu ya Haifa.
Sakon gayyata kotu Haj Maryamah tasamu Wanda ya kusan kasheta da mamaki da tashin hankali tareda wani irin firgici,
Meya hadata da zuwa kotu Kuma?
Lauyanta takira shine yayi Mata bayani Kai tsaye cewar wani Dan daudu da karuwarsa aka Kama shine akan rikicin gida tace ke Yar uwartace mahaifinku daya.
Kusan yanke jiki Haj Maryamah tayi zata Fadi Saida tayi saurin zaunawa tana Jan numfashinta dake sarkewa.
Bata taba tunanin kowa sai zainab,
Haka Bata taba tunanin zainab zata zaba wannan rayuwar ta sabon Allah ba akan ta bawa umma yarta..
Umma takira muryarta ko fita batayi sosai sbd azabar da zuciyarta keyi Mata,.
Cikin ciwo da baqin ciki Mai tsanani tayiwa umma bayanin komai.
Umma ma kasa cewa komai tayi sai data Gama zaunar da zancen cikin zuciyarta tace"
Rayuwar da zainab din ta zaba kenan akan ta bamu yarta ko????
Tunda ta zaba bariki Allah ya kyauta,
'yar tata ma saita tashi da rayuwar datafi wadda take tunanin zamu Bari tayi anan ta lalacewa...
Idan ta lalata mutuncinta da sunanta to meyasa zatayi kokarin lalata Miki mutunci da suna ta hanyar cewa ta sanki?
Taje tayi rayuwarta Ina ruwanki aciki da zaa nema zubarda mutuncinki Dana familyn Mahaifin Aqeel harma Dana mijinki ayanxu Dan dukkaninsu sai mutuncinsu ya tabu idan sunanki ya bayyana a kotu.
Babban bacin Rai da tashin hankali suka shiga daga Haj Maryamah din har umma Dan kuwa yanda dangin mahaifin Aqeel suke neman hanyar cin mutuncinta suna Jin abinda zai faru zasu tarar Mata gabaki dayansu.
Umma kuwa ta tsinewa zainab yafi so ashirin tana aibatata da 'yarta akan wannan abin,
Ita Haj Maryamah baqin ciki da damuwa ya hanata tunanin komai qarshe a gadon asibiti taqare.
Kwanciyarta asibitin yasa aka daga zaman kotun Amma dai daga baya haka aka juya lamarin lauyanta yakai takarda kotu cewar Haj Maryamah batada alaqar komai da zainab rashin lafiya bazai barta tazo kotun ba.
Dayake kotun kusan dai qaramace sai aka karanto bayanin sako daga Haj Maryamah tace batada alaqa da zainab da Lulu.
Tunda zainab take Bata taba mutuwar tsaye da mamakin Haj Maryamah ba da umma sai wannan karon,
Kasa motsi tayi sbd lamarin ya Gama shallake tunaninta,
Hawaye takeson Yi Amma takasa zuciyarta nauyi da bushewa takeyi.
Suna umma ta bada wato mahaifiyar Haj Maryamah din a gabanta aka Kira umma itama ta fada abinda haj Maryamah din tafada tareda qarin cewar 'yar malam din ce Amma su basuda alaqa da ita,
A taqaice batai bayanin gamsashsheba
Dama jira kawai akeyi a tozartasu akan zalinci sai kawai aka yanke hukuncin komawa dasu gidan yari su Gama zaman hukuncinsu na batawa ds da Haj Maryamah suna idan sun fito zaa bawa zainab nata kason haqqin gadon Wanda Haj Maryamah ce zata Bata kudin gidan gabaki daya tunda sun bada ne ayi masallaci basuma tsaya sun bincika ko anyi dinba gashinan Mai anguwa ya Saida ya cinye kudin.
Lulu yayi baqin ciki da Dana sani matuqa na daga zancen sbd halin dayaga zainab din tashiga na wani irin quntataccen baqin ciki da nauyin zuciya,
Gabaki daya ta Dena gane komai bayan daskarewa da zuciyarta tayi Bata iya tunanin komai...
***Wata daya sukai cif suka fito gidan yarin,
Rungume 'yarta tayi cikeda kauna da kunci da baqin ciki da damuwa,
Tabbas a yanzu taga wani bangare na rayuwa Mai matuqar wuyar koya....
Siddi tayiwa godiya da ido sbd magana ma ayanxu wuya take Mata sbd shock daya Gama sakar da rayuwarta.
Sidda ta kula da MARYAMAH sosai tamkar 'yarta hakama Koda yaushe itace take ziyartarsu gidan yarin har suka fito.
Tunda suka dawo Shi Kansa Lulu sai rayuwarsa tayi sanyi Dan Jin kamar shine ya lalatawa zainab Yar sauran rayuwar tata da nufinln nema mata 'yanci..
Kokarin nemawa zainab din wani gurin zama can wata anguwar daban yayi sbd taje tayi rayuwarta mai kyau itada 'yarta.
Ranarda suka samu wani qaramin gida Mai daki daya da Palo qarami sai bandaki da kicin..
Kudinsa bai cikaba Dan haka Dole suka hakura suka dawo gida,
Kulawa da kaunarda Bata taba samu daga jinintaba Lulu yake Basu itada MARYAMAH,
Dukkanin kokarinsa yanzu akansu yakeyi sbd yakasa daukewa Kansa shine sanadin quncinta a yanzu Wanda yafi na baya,
Ta bangare daya har cikin Ransa kaunarta yakeyi a matsayin Yar uwa jininsa sbd mahaifiyarsa.
Ita kanta tasan bayan Mijinta da Aqeel to Lulu ne mutum na uku dayake kaunarta fiyeda komai Kuma yake shirye dayayi komai da inganta rayuwarta data 'yarta.
Fafutikan nema kudi Lulu yafara sbd hadawa a kamawa zainab din can tabar Nan sbd gabaki daya Takoma Kamar dutse batada walwala da komai,
Tunda suka fito gidan yarin rayuwarta ta canja Takoma kamar me ciwo,
Ita kanta MARYAMAH yanzu agurin siddi tafi zama sbd zainab din bayan tunanin babu abinda take a rayuwa yanzu.
Lulu na cikin wannan Fadi tashin neman kudin Samar Mata gurin zama barayi suka shiga gidan DS suka kashe Mai gadinsa tareda yiwa 'yarsa daya fyade suka ko sata basuyuba suka gudu.
Babu tunanin komai akaiwa Lulu mummunan sharri akan da saka hannunsa a lamarin,
Ds da Kansa ya bada tabbacin Lulu ne kawai zai iya yimasa hakan
Sbd fyaden kanwarsa yasa anyiwa shima tasa yar
Kuma a ranar da abin zai faru kowa ya shaida fadan maigadin gidan DS da Lulu akan taron da Lulu yayi da jamaarsa har kofar gidan ds din mutanensa ne.
##MAMUH#
#IDON NERA
#AQEEL ASAD
#LOVE/MARRIAGE
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
Leave a Comment