Idon Naira 18
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
18
Tunda Lulu yake baa taba Masa zargi ko sharri Mai girma da munin wannan ba,
Kisa da fyade fa ake magana....
Innalillahi wainna ilayhi rajiun""" shine abinda zainab da siddi suke nanatawa cikin mafi girman tashin hankali lokacinda akayiwa Lulu mummunan kamu.
Gabaki daya jamaar anguwa kowa da abinda yake tofawa lamarin wasu alkhairi wasu sharri da mugun kalami.
Zainab ce da siddi suka fara yawon neman mafita Amma babu sai wahala da qara gurbacewa da lamarin keyi.
Tun lamarin na wasa harya girmama Dole suka nema lawyer da taimakon wani saurayin siddi..anan suka fara kashe kudi sbd case din babba ne sosai tunda kisa ake magana.
Zainab Bata ankaraba ta samu kanta dumu dumi a wani bangare na ruyuwa irin wannan ta kaida kawon cikin maza nagari da Bata gari,
Lulu shine Dan uwanta daya da bazata iya gani cikin wannan halin ba Dan haka itada siddi suka Dage dan ganin sun taimakesa alokacinda yakeda buqatan hakan.
Tun Ana iya ganin lulun har andena barinsu ganinsa,
Sannu ahankali komai da siddi ta mallaka yaqare Daman ita zainab batada komai sai nauyin restaurant din lulun daya dawo kanta sbd kallon uwa daya uba daya da ake musu ita dashi,
Tun suna iyawa harsunkai basa iyawa haka aka Saida restaurant dinsa da komai suka bada kudin Dan a fiddo lulun Amma babu sauki.
Komai na Lulu Saida aka Saida suka bada kudin Amma babu wani sauki sai agurin ubangiji.
Ds suka koma gurinsa roko da neman alfarmar akan case din.
Da farko kin kulasu yayi sbd tsanar dayayi a gansa da karuwai sbd tsoron abinda zai taba mutuncinsa da siyasarsa.
Daga baya Kuma dasuka ci gaba da roko da magiya akoda yaushe saiya nuna raayinsa akan zainab..
Kai tsaye ta sanar dashi ita din ba karuwa bace sbd kadama su batawa juna lokaci,
Siddi ce ta miqa Masa kanta a maimakon zainab din yayi abinda zaiyi da ita qarshe yaqi Yi musu abinda yace din saima kamasu daya saka Yan hisbah sukai akan suna bibiyarsa da mummunan dabiarsu akan ya asaki Dan uwansu...
Yayi musu hakan ne da a kamasu su ta yanda babu Mai sake kokarin tada maganar Lulu.
Hisbah ta kamasu tareda kaisu gidan gyara Hali na tsawon sati uku kafin aka sakosu,..zuwa wannan lokacin Lulu anriga an yanke Masa hukuncin zama gidan yari har ankaisa da hakan aka rufe case din.
Bayan fitowarsu wata muguwar qaddarar ta samesu ta bayyanar ciki a jikin siddi Wanda yake tabbas na DS ne,
Sun shiga tashin hankali da damuwa sbd siddi tai duk yanda zatayi cikin yaqi fita sai zainab tace ta hakura tabarshi tunda hakan Allah ya qaddaro.
Rayuwar zainab da sunanta sun Jima da lalacewa daga ranarda ta saka kafarta a anguwar,
Kowa da sunan karuwa yake kiranta Wanda ita masifar datake ciki Bata barinta Jin zafi ko takaicin sunan,
Babu ta yanda zata iya wanke kanta sbd ba yarda zaayiba,
Wayema ya damu da mutuncinta da zata tsaya wanke kanta..
Rayuwarta data MARYAMAH ta sauya
Babban burinta shine fitowar Lulu da saukar siddi data koma yau lafiya gobe ciwo,
A ayanxu da siddi Takoma cikin duk ya Gama lalatar da rayuwarta sbd tsananin ciwo da laulayi kala kala
Zainab itace take dawainiyarsu,
Itace take karban kudin hayar kowane daki na gidan da karuwan ciki ke biya,
Itace take sanaar Saida kayan planning da siddi keyi a gidan harma da wasu abubuwa da karuwan gidan ke siya komai ya dawo kanta
Duk tabi ta qara hargitsewa,
Siddi ta rayuwarta ta koma abin tausayi gabaki daya sbd cikin yazo da matsala sosai...
Zagi da zunde tareda bacin suna babu wanda baa musu akan ita ta Haifa shegiyar da baasan ubataba,
Lulu ankamasa sbd yayi fyade da kisa,
Siddi Kuma tayi shege lafiya ta gagareta.
Zainab dakejin irin wannan zagin da cin fuskar Bata damuwa sbd abinda yake gabansu yafi qarfin tsayawa biyewa zagin mutane.
Cikin siddi Yana fita wata takwas tafara zubar jini
Tun Yana zuwa kadan kadan daga Baya yafara zuwa da yawa
Hankalinsu ya tashi suka nufi asibiti.
Zuwansu asibiti yasa yanayin tsanananta nan hankalin Zainab ya tashi ta rasa was zata nema,
Wa zata tinkara.
Jikin siddi tsanani yayi kuwa qarshe dai ta haifi 'ya mace itama saidai take ta rasu bayan haihuwar tata.
Rungume da 'ya cikin tashin hankali da firgici Mai tsanani zainab ta fito asibitin MARYAMAH na biyeda ita
Cikin tsanani rikicewa take jefa qafafunta Bata ko gani sosai....
Innalillahi wainna ilayhi rajiun"" take furtawa a fili tana tafiya da jinjirar a hannu batamasan Ina ta nufaba tsabar tashin hankali.
Da magriba siddi din ta haihu kafin ishai ta rasu...
Ga 'ya a hannunta yanzu inane makomarta da yara har biyu...
Bata ganin gabanta haka tabi hanya tana tafiya kamar mahaukaciya.
A daidai wani layi ta tsaya bayan tayi tafiya Mai tsayi ta durkusa a gurin tana neman kukan dake cikin zuciyarta ya fito Amma yakasa fitowa sai gurnani takeyi tana gunji...
Motar dazata shiga bakin gidan datake durqushene ta hasketa tareda danna Mata horn....
Shafi'u driver ne ya zubawa gurin idon cikin Dan mamaki yace,
"Haj Kamar Zainab ce a gabanmu.
Umma da Haj Maryamah dake bayan motar zaune suka dago lokaci daya suna kallonsa
Umma ce ta iya cewa,
"Kace waye???
"Zainab dai ta Nan gida,
matar marigayi malam sanda.
Tsit sukayi wuta ta dauke musu lokaci daya sbd zallan mamaki da firgicin abinda ya kawota gaban gidan kakannin mijin Haj Maryamah din,
Isowarsu garin kenan yau daga ita har umma sbd gaisuwar mahaifiyar Mijin Haj Maryamah din data rasu jiya.
Cikin sauri umma tace"
Shafi'u ka tabbatarda zainab ce kuwa?
Haj Maryamah datake tsananin kaunar mutuncinta da sunanta fiyeda komai Bata tsaya komaiba ta bude motar tafito dan bazata tsaya tambaya ba har wani ya fito yaga zainab din agurin asan sunada alaqa sunanta yabaci.
Turus ta tsaya batareda ta qarasaba tana kallon zainab din cikin shahararren mamaki da tsoro harma da wata irin qyama dake bayyane ganinta da sabon 'da a hannu dunkule Acikin zani.
Umma data fito motar tana tafiya ahankali sbd manyanci sosai daya kamata tsayawa tayi kallon abinda ke hannun Zainab din kafin a rude tace"
Ke,Meye haka?
Daga Ina?
Me kikeyi anan?
Bibiyarta kikeyi ne?
Meye wannan a hannunki?
Wata haihuwar Kika sake Yi kenan??
Shi Dan daudun naki bai fada Miki baa haihuwa a bariki ba???
Me kikeso da kikazo Nan da wannan abin naki?
Me Maryamah tai Miki da kikeson Bata sunanta agun dangin Mijinta da mutanen dake ganin girmanta matuqa......
Haj Maryamah da baqin ciki Mai tsanani da tashin hankali sukai Mata yawa kasa magana tai ta dauke kallonta daga kallon Zainab din da yaranta biyu dake tareda ita,
Wace qaddarar ce wannan ace ubanta daya da karuwa Mai 'da
Tabbacin ita Yar barikin ce kenan....
Muryarta kunshe da damuwa da zallan baqin ciki da damuwa tace"
Bayan kudin gadonki dake hannuna banajin akwai dalili ko alaqar dazata saka ki zo inda nake,
Me kikeso?
Kudin gadonki???
Mota ta juya ta dauko Jakarta tabude ta fiddo rafar 100k guda uku ta jefa Mata cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin dake neman rufe zuciyarta tace"
Rayuwar da Kika zabarwa kanki da zuriarki kenan ko Zainab??
To kije kiyi rayuwar yanda kikeso saidai kada ki sake zuwa inda nake sbd har abada bazan taba iya kallon karuw.....
Kasa qarasa sunan tayi sbd baqin cikin fadarsa ma datakeyi...
Kije Zainab...
Kije...
Tashi kije....
Zainab data kasa dagowa ta kallesu sbd batasan ta ina suka diroba itama...
Sai alokacinda Haj Maryamah ta jefo Mata kudin ta dago ta kalleta idanuwanta na radadi da zafin kalaman 'yar uwarta.....
Magana zatayi umma ta katseta da cewa"
Idan kincika Yar halak dakiketa fada kotu to karki Kuma ambatar ko sunan Maryamah da 'danta bare zuwa inda suke sbd kin Riga kin lalata sunanki Dana zuriarki to karki lalata Mata nata....
Har abada babu abinda zai hada tsaftatacciyar rayuwarta da zuriarta da wainda suka qazanta rayuwarsu.......
Zainab kin zama tamkar rubabbiyar rayuwa wadda zata lalata suna da mutuncin duk Wanda ya rabeta...
Allah yasa kada ki lalata rayuwar wainnan yayan naki Kamar yanda Kika lalata taki.......
Hawayen dataketa nema tsawon lokacin ne yau Allah yabasu ikon saukowa daga idanuwanta dasukai jajir...
Haj Maryamah take kallo da dukkanin Idanuwanta dake tsayayar hawaye sbd ayanxu tana ganin ita kadaice takeda alaqa da ita Dan itace jinin,
Itace suka bada uba daya
Amma umma batada alaqar komai da ita tunda Bata haifetaba Kamar yanda ta fada....
Hawaye sosai takeyi masu radadi daga zuciya,
Kuka Mai qarfi ta fashe dashi agaban Haj Maryamah din wadda itama zuciyarta wani radadi da nauyin take Mata...
Share hawayenta tayi dukda sunkasa tsayawa ta dago takalli Yar uwarta Kuma yayarta Acikin wani irin sauti Mai bayyanarda tabbacin abinda zata fada tace,
"A yanda umma takira rayuwata da rubabbiyar rayuwar da zata lalata rayuwar Wanda ta raba
Ayau Ina Miki alkawarin har abada bazaki sake ganin Zainab ba,..
Alaqar da kuka yanke Dani ayau Nima na yafe na yanke alaqa ta jini data zahiri dake,
Kece jinina kece nakeda alaqa dake ba umma ba kema to ayau din na yanke kamar yanda Kika fada ba Ni bake har abada,
Bani ba jininki,
Bani ba zuriarki,
Ayau har sunan mahaifinmu na yafe Miki daga yau ko sunan mahaifi daya bazaa sake kiranmu dashiba...
Sunanki ma a bakina nayi alkawarin bazan sake fadarsaba har ranarda zan bar Miki duniyar na...
Wani mahaukacin Mari umma ta sakarwa Zainab din cikin tsananin fushi da takaici tareda bacin rai Mai tsanani tace,
"Basai kin nuna Mana cikarki Yar barikiba mun tabbatar tunda gashinan munga shaidar a hannunki,
Itace tafi kowa baqin ciki da takaicima idan kinkira sunanta ita da aka sakawa 'yarki sunanta........
Daga sakannin da nayi alqawarin yanke alaqar Nan a wannan lokacin na rufewa 'yata sunan.....
Baniba ko Wanda bai sanniba bazai sake Kiran sunan 'yata wannan sunanba.......
Kudinsu dake qasa ta kalla kafin ta Kama hannun MARYAMAH tace,
"Kudin gado na Kuma na barwa Allah tintini.
Jan hannun yarta tayi suka bar gurin zuciyarta na wata irin zafi da tafarfasa.
Asibiti Takoma ta tadda gawar siddi na jiran Azo a dauka Dan Haka ta Kuma fitowa ta nufi gidansu tarasa was zata sanarwa haka tadawo asibitin ta sanar musu basuda kowa ayi janaizarta anan.
Gida tadawo tayi kwanan zaune,
Zuciyarta zafi,qunci,radadi da hayaqi takeyi Mata..
Komai yasake juyawa Mata akaro na babu adadi..
Yaya zata fuskanci rayuwa da yara biyu bayan ita kanta haryanxu bata tsayarwa kantaba...
Washe gari acan asibitin akaiwa siddi komai aka Kai maqabarta saima data biya kudin mota dasu likafani.
Anan gidan take koina ya dauki labarin mutuwar siddi.
Madara ta siyo tana shayar da babyn wadda ta sakawa sunan mahaifiyarta wato siddiqa itama tana kiranta da siddi....
Sabuwar rayuwar jaruma Kuma tsayayyar mace ta budewa kanta sbd 'yayanta Wato MARYAMAH wadda ta sauyawa suna AMAL da Siddi..
Sanaoi da gwagwarmaya tafada gadan gadan Kuma Allah ya tallafa Mata sai gashi tanata tsayuwa da kanta.
Hausawa sukace zama da madaukin kwanwa.....
Rayuwarta ta sauya sosai Dan kuwa ta tashi daga Zainab mai sanyin jiki Dana zuciya zuwa Zainab mai zafi da rashin daukan Reni.
Zama cikin karuwai da Yan bariki kala kala yasa idanuwanta budewa fiyeda su dinma Amma duk da hakan Bata taba aikata Zina ba.
Babban matakin nasarar data fara samu na taka Wanda ya takasu shine sonta da Ds ya fito ya nuna yanayi har lokacin baya Yana sane da mutuwar siddi sanadin haihuwar cikinda yasan shine yayi.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
Leave a Comment