Idon Naira 21
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
21
AMAL Idon Nera ayanzu datake cikin cikakken lokacinta kaf familyn IDON NERAn tafi suna sbd irin Yanda take rayuwarta a yanda takeso a yanda tayi raayi..
Kuma ayanzu da ita kadaice budurwa a gun momyn kusan duka abokan huldarta manya Neras AMAL din suke ta sakon aura shiyasa kowa ke sakarwa Haj Zainab din kudi,
Uncle Lulu ma ta nasa bangaren akwai masu son auren nata Amma duka AMAL din batada raayin auren a yanzu sukuma su Haj Zainab basa takurawa yayan nasu ko kadan shiyasa Bata takurataba,
Shima uncle Lulu din Bai takura Mata dinba,..Suma masu son auren nata Basu takura dinba sbd ba abune na gaggawa ko daga hankaliba tunda Daman karatu takeyi Dan Haka ko ajikinsu kudaden dasuke sakarwa Haj Zainab din da Lulu Idon Nera.
Siddi a Abuja take da aure Amma kusan duk baya wata biyu tana hanyar Lagos cikin jirgi idan tazo ma takanyi sati biyu,uku koma fiye a gida suna hutawarsu sbd Mijin nata nada Mata kowacce da gidanta ita tana maitama dayar matar tana gwarimpa..
Aurene babu takurawa sukeyi irin na masu kudi da yayan masu kudin,
Bata wani zama sbd batada kowa abujan sai Mijin da danginsa wainda Suma kusan hakan suke basa wani zama Dan Haka take hanyar Lagos kusan ko yaushe
Kuma momynta basa ganin laifinta tunda Mijinta Bai hanataba Dan ba komai bane agunsa.
AMAL na final year dinta a karatunta na Amma har lokacin raayinta Bai sauyaba akan mazan dake shirye da aurenta,
Duk yanda mutanen duniya ke musu kallon musu kallon ahalin Yan bariki karuwai masu lasisi Mai tsada wannan tunanin a iya gurin Yan wahala ne sbd mutanensu na arziki babu abinda ya damesu da wannan zancen basama jinsa sbd iya gurin Yan wahalar mutane ya tsaya zancen sukam duk wani matsayin mutunci Haj Zainab da ahalinta sunkai tunda suma sunada arzikinsu Kuma tanada 'yaya masu daukan hankali dasukeso hakama Koba 'yayanta ba tanada 'yan Mata masu inganci harma da manya Matan masu aji a qarqashinta da zata baka ka aura idan kanaso,
Ga iya business da sanin hanyoyin hada harqallar business tsakanin manya Wanda take qaruwa da hakan sosai Dan Haka su a gurinsu Haj Zainab IDON NERA mutuncinta yafi musu na kowa ma.
SSG Hayat Nasir shin mafi mutuwa a soyayyar Amal IDON NERA,
Ya gama mutuwa tareda wani irin nisa a sonta Wanda kusan da yawan mutane sunsan da hakan,
Matarsa da 'yayansa sun sani,
Yan uwansa da abokansa sun sani hakama media ta sani Dan duk zamansa Mai fada aji to hidima ta Haj Zainab IDON NERA data Amal IDON Nera baya hadata da komai,
Komai zai iya dakatarwa akan hidimar AMAL da haj Zainab...
Ita dukiya kuwa kamar su ya Tarawa Dan iyalansama duk yanda suke Jin Dadi da rayuwa basa wulaqanta dukiyarsa Kamar yanda ahalin IDON NERA keyi,
Uncle Lulu kuwa jinsa yake kamar uban daya haifesa tsabar biyayya da 'barin dayake Masa shima.
Duk wanna abin AMAL Bata taba sonsaba,.
Bata taba Kuma Jin zata so shi dinba,
Shi kadaine yake kidansa yake rawarsa,
Ba tsoho bane bakuma dattijo bane irin matasan da kudi yasa suka zama dattijai ne,
Abokin manya ne,
Kyakkyawane ba laifi gashi yasan sutura Yana dukanta yanda yakamata.
Matarsa da yayansa Idan akwai abinda duniya ta tsana a fada a gabanta ko a mafarkine shine sunan AMAL IDON NERA,
AMAL itace babbar masifar rayuwarta,
Amal itace quncinta,
Itace baqin cikinta,
Itace damuwarta..duk yanda zatayi ta raba Mijinta da zafaffiyar soyayyar AMAL a Ransa tayi ta kasa,
Har rabuwa tayi dashi ta kwashe yayanta tabar qasar gabaki daya akan hakan Amma takasa rabasa da AMAL
abin baqin ciki da haushi da takaici ma shine duk lokacinda zata tunkari AMAL din saita tozartata ta qunso Bata baqin ciki Mai tsanani ta Kuma fada Mata ko so daya Bata raba son Mijinta ba shine yaji zai iya yake nacinta.
*********Kwance take tana bacci cikin bargo iya kanta ne kawai a waje..
Tun baccin bayan sallar asuba ne data koma Bata tashiba gashi kusan karfe goma na safe.
Kofar bedroom din nata aka bude Kai tsaye aka shigo
Dayake baccin yafara sakinta tashi take son Yi Amma Bata tashinba tanajij shogowa dakinta Kai tsaye tasan Siddi ce sbd masu aiki basa shigo Mata daki Kai tsaye.
Ahankali ta bude manyan idanuwanta masu haske dasukai Dan duhu sbd bacci ta zubawa Siddin wadda ta nufi gaban madubinta zata dauki Abu...
Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda yaye bargon datake ciki ta tashi zaune ahankali...
Idanuwanta akan siddin ta ziro qafafuwanta qasa tareda miqewa tsaye kyakkwar surarta ta bayyana..
Cotton fararen kayan bacci ne ajikinta Riga da wando na Asceno ko hula babu akanta sai safa Qarama a qafarta....
Fresh take koina jikinta na bayyanarda hutu da kafiyar dayake da ita..
Daga inda take tsaye ta bude baki cikin muryarta Mai tafiye Kai tattare da class tace,
"Siddi,me yasa kullum idan kina gidan Nan kece kike tashi na¿??
Ke ko knocking bazakiyiba kike shigomun Kai tsaye...me zakimun gurin Kuma???
Washe Baki siddin Tai batareda ta juyoba tana cigaba da duba key din motar AMAL din tace,
"Zan fita da motanki ne sbd mommy ta fita tunda safe da nata,
Uncle ma ya fita Anty Fareedah ma ta tafi aiki na nata nakin shine a qasa sai dayar motar mommy na duba koina Banga key din ba nakira wayar a kashe may be tana wani gurin ma mahummanci...
Qarasowa AMAL tayi ta gurin tana cewa"
Inada gurin zuwa Nima kije ki shirya Zan ajeki inda Zaki na tafi idan nadawo Zan tsaya na daukeki kokuma Idan kingama ki Kira Sharif yaje ya daukoki Yana gurin gyara da dayar motan wani ya buga mun ita jiya a makaranta.
Juyowa siddi tayi tana kallonta tace,
"Asibiti fa zanje inason confirming ne kaman inada ciki...
Dakatawa Amal tayi tana kallon siddin cikin Dan mamaki da takaita farin cikinta sbd ba yau suka Saba jiran cikinba Amma yaqi samuwa...
Kin tabbata kinajin alaman ciki Siddi???
Ina tunanin hakan Amma dai sai abinda asibitin suka gano...
Ki shirya Zamuje asibitin tare muga likitan.""Amal ta fada hakan tana ajiye key din data karba hannun siddin ta nufi toilet na bedroom din nata.
Tubewa tayi tareda jefa kayan data cire a qaramin laundry basket bag din dake toilet din.
Brush tayi kafin tayo wanka ta fito tana qamshin asalin original makari bath gel.
Mai da turaruka ta shafa sai lip balm da eyeliner da Bata rabo dashi a idonta sbd hasken idonta liner din na rage Mata Shi sbd bakin mutane akanta..
Long sleeve Moroccan doguwar Riga ta saka ash sai chanel chain shoulder flap bag ta fito.
Flat ne a qafarta sbd ta fasama zuwa inda zata asibitin zasu Dan samun cikin Siddi kusan duka shine burin ahalin nasu,
Kowannensu ya saka Rai da samun cikinta Dan qara fadada zuriarsu Dan dukkaninsu suna tsananin son qari,
Sunason ganin sunata fadada a familyn Amma babu 'yayan,
Anty Fareedah tun haihuwar Fahat tasamu matsalan dayasa aka cire Mata mahaifan gabaki daya Dan Haka basa ran haihuwa daga gurinta Kuma Basu taba shaawar Uncle lulun ya qara aureba Dan suna matuqar son Anty Fareedahn kamar yanda take sonsu...
Dan haka gidan nasu sukeda yunwar samun 'yaya musamman ta wani bangaren Shi kansa Mijin siddin Barade abin fahari ne hada zuriar dashi..
Kusan duk lokacinda Siddi zatayi batan wata to mommyn ce da kanta suke zuwa asibiti a duba musu ita Amma babu wani bayani.
Sanin idan mommy da uncle suka fita tunda safe to abune Mai mahummanci Dan Haka daga AMAL din har siddi Basu nasar Mata ba zasu tafi asibitin.
Tana fitowa babban palonsu tayi hanyarda dining dinsu na cin abinci yake kamar yanda ta tsammata ko breakfast babu Wanda yayi komai a jere baa taba ba.
Zaunawa tayi tareda siddi da itama batayi breakfast dinba suka fara cin abinci.
Sama sama su duka sukaci abincin sbd tunanin abinda result na asibiti zai bada.
Atare suka Gama siddi takira Bilkisu Mai aikin gidan ta kawo musu bottle water guda daya sbd siddin Bata fita Saida ruwa tun tana budurwarta Haka take.
Amal ce take driving din Siddi na Dan chat a wayarta har suka Isa asibitin Dr Inayah majeed.
Dr Inayah din sukaso gani amma Bata Nan so sai wata likitan ta dubasu Dr farhat...
Kamar ko yaushe wannan karon ma anduba batada komai Dan haka suka fito jiki a mace..
A daidai kofarsu ta fitowa asibitin motarsu takusan karo da wata motar wadda tasa AMAL din yiwa motar kallo daya ta dauke kai tana sakin qaramin tsoki ahankali tace,
"Wannan matar Wai bibiya takeyi ne ko me??
Da sauri siddi ta dago ta kalli motar tana cewa,
Kaman motar gidan SSG right??
Yamutsa fuska AMAL tayi tana cewa,
"Matarsa ce da wahala be qare Mata ba ko 'yarsa may be.
Karkatawa Amal din tayi ta wucewarta Saida suka wucesu Siddi tace,
"Ba matarsa bace 'yarsa ce tareda qawarta da akace kwana kin baya suka dawo Nigeria daga UAE..
Amal da babu ruwanta da koma su waye a motar ko matar ko 'yar ko wata qawar Yar koma Yar uwarsu ce
Dan Haka batai magana ba suka fice abitin zuwa inda Tai niyar zuwa tun farko wato makaranta.
Tare sukaje da siddi din suna Isa Sharif na isowa Dan sun Masa waya tun a hanya Dan haka juya da siddin zuwa wani gurin itama da zata.
A makaranta ta wuni sai kusan 4 ta fito nata nufi gida Kai tsayeba Saida ta biya ta dauki Fahat daga gidan iyayen anty Fareedah dake lekki tukana suka dawo gida...
Koda ta iso gida mommynsu ta dawo suna palon sama dukkaninsu harda uncle da Anty Fareedah da siddi suna fira da Haka itama wanka da sallah tayi ta nufi saman saidai Balkisu takai Mata abincinta can saman.
Kallonta Haj Zainab tayi lokacinda take zama gefen uncle dinta sanyesa milk Riga da wandon Calvin Klein masu Fadi sosai da kauri
Cikeda kulawa tace,
"Amal lafiya kuwa?
You look pale.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Uncle dinta dake kallonta cikin kulawa kafin ta kalli haj Zainab din tace,
"Mommy karatun Nan ne Yana neman juyar mun da Kai nafara gajiya fa.
Murmushi momyn tayi tana cewa,
"Kin shirya yin auren ne to sai abawa SSG daman fitowa...
Dariya siddi tayi tana cewa,
"Wane SSG din mommy?matarsa fa haukace take neman Yi ko sunan AMAL aka fada bare taji maganan aure mutuwa zatayi Kila..
And banajin Amal dinma zata aura SSG din da alama haryanxu Bai samu shiga agunta ba.
Uncle Lulu ne ya kalli AMAL data fara Shan Mango juice din da Balkisu da takawo Mata da abinci yace,
"Koda batasonsa ai tasan takusa aure tunda karatu zata gama,
Idanma ba SSG ba akwai wainda ke jira.
Itadai Amal batace komaiba sbd irin hakan Bata saka Baki tunda dai sai lokacinda tace tanaso tasan zaayi Mata.
Fira sukayi har zuwa magriba tukuna kowa ya tashi ya tafi sallah.
Bayan sunyi sallar magriba suka zauna dining cin abincin dare Banda momy da uncle Lulu wainda suke Palo suna tattauna maganar data taso musu haiqan na yanda malaman addini suka fara shiga cikin lamarinsu sosai abin yafara kawo musu illa da maganganu.
##MAMUH#
#AQEEL MUHAMMAD ASAD
#AMAL IDON NERA
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
Leave a Comment