Idon Naira 24
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
24
Su balkees duk yanda suke tunanin lamarin SSG Hayat ya wuce Nan akan maganar aurensa a ahalin IDON NERA,
Da fari bayan yakarbi yayansa ya Dan sauko sbd yanda yaran suka damu da rashin dawowar mahaifiyarsu Dan Haka ya Dan ringa lallabata tadawo Amma ta nuna bazata dawoba idan Bai fasa auren Amal Idon Nera ba,
Ta yarda ya aura duk wadda yakeso Amma Banda Amal..
Bilkees dayasan kusancinsu yaso yiwa magana sai itama ya lura da tsanarta akan lamarin Dan Haka saiya fasa ya tattarasu ya watsar yaci gaba da harkokin gabansa idan taga anyi auren zata hakura ta yarda har ita har yan uwanta dasu bilkees harma da Amrah wadda cikin 'yayan ita kadaice takeda girman datasan wani taya uwarta kishi.
****Ta dayan bangaren kuwa Haka su balkees da 'yarta suka ara suka yafawa kansu tsanar wannan auren na SSG sbd tsakanin Nafee da balkees Aminci da kaunar Yan uwantaka ce tun yarinta sai gashi Allah yasa suka auri Aminai duk da ita Bilkees aurenta da nata Mijin kamar na Hadi ne.,
Aurenta da Mijinta DR SHAYKH AQEEL ASAD Hadi ne daga mahaifiyarsa Haj Maryamah sbd yanda yaqi auren kwata kwata duk iliminsa da addininsa harma da wayewarsa da arzikinsa sai Allah ya cire Masa shaawar aure da wuri Wanda ta rasa gane ko meyasa hakan,
Ummansa tayi tayi Amma zuciyarsa a wannan bangaren kamar ta mutu ne gashi tako Ina samun tayin aure yake daga 'yayan manya Dana malamai amma Bai taba karba ba,
Rayuwarsa wata irin baudaddiyar rayuwace yakeyi Mara hayaniya da son takura Kansa ko wani,
Ummansa itace rayuwar kadaicinsa take damunta ta nema Masa auren Bilkees wadda take ganin tanada ilimin addini sosai Kuma Dama hakan shine raayinta.
Da farko baiyi naam da zancen aurenba sbd bayason duk wani Abu dazai takurasa kokuma shi ya takura koma wacece zai aura da halayensa na rashin ko inkula da yawan rashin zamansa Amma Haka umman ta Dage sbd tanason ya dawo qasarsa dayaqi dawowa tun bayan zuwansa daya daya koma Bai Kuma dawowaba acan yake ayyukansa da rayuwarsa,
A yanda ummansa ta sansa da magana daya akan Abu yasa tasan bazai dawo dinba tunda yace bazai dawo ba
Rashin dawowarsa Kuma tasan zai iya qin yin auren har abada tunda baida lokacin Kansa ya tattara rayuwarsa akan aikinsa da Kuma karatun addinin da Bai denaba har lokacin sai qara zufafa yakeyi.
Tana tsananin buqata da kaunar 'danta a tareda ita kusada da ita Dan Haka Dole ta nemar masa auren Bilkees Wanda ya aminta daqyar akai auren saidai Kuma ko bayan auren komawa yayi da matarsa UAE saidai ita umman sbd kadaicin rayuwa da rashin kowa sbd ga arzikin sun Tara Kuma kullum sai habbaka yakeyi Yana qaruwa Amma Bata cikin dadin rayuwa sbd rashin 'danta hakan yasa dole ta tattara ta bisa acan suka koma rayuwarsu gabaki daya.
Bilkees batayi wani dogon karatun Boko ba iyakacinta secondary Saida taga zata auri Cikikken namiji Mai aji da ilimi yasa ta fara diploma Amma dai batama gamaba akai auren ta watsar tabi Mijinta Wanda tagama mutuwa akansa dan kuwa ko kallon DR AQEEL ASAD tayi Jin takeyi kaman zata shide sbd tsananin son datakeyi Masa sbd saa ce ta aure ta samu ummansa ta yaba da ilimin addininta badan hakan ba tasan tako Ina AQEEL ASAD yafi qarfinta,babu Ma inda zai ganta yace yanaso sbd baya zuwa Cameroon gurin kakarsa wadda itace tasake kurarata agun umman har aka aurota.
Bilkees ba mummuna bace itama tanada nata kyan na fuska Dana jiki babu laifi,
Tanada zafi da tsananin kishi duk da iliminta na addini kuwa,
Kusan ma aka kishin Mijin nata data Gama macewa akansa mantawa takeyi da ilimin nata saidai takanyi kokarin danne halinta agaban umman sbd kada kada ta fice ran umman tunda AQEEL ASAD baya tsallake maganar umman ita Kuma umman na yinta dari bisa dari.
Bilkees din Bata taba Koda Bari ba Wanda hakan yafara Dan damun umma Amma Kuma batai yunqurin cewa komaiba sbd sanin Allah ne Mai badawa saidai Kuma harga Allah tana son haihuwar sbd idan ta biye AQEEL ASAD din bazai taba magana ba bare damuwaba tunda rayuwarsa yake ayanda tazo Masa ba cusawa Kai wahala.
Ita kanta Bilkees hankalinta fara tashi yayi da rashin haihuwar
Ko Bari tanason tayi Amma babu damar.
Daga umma har ita tun suna dannewa har hankalinsu ya kasa kwanciya Dole da roko da kukan Bilkees da dagewar umman suka tafi asibiti sukaga likita..
Kai tsaye dubawar farko aka tabbatarda Bilkees din ce da matsalar rashin haihuwar.
Kusan qaramar hauka Bilkees tayi cikin tashin hankali da mummunan yanayin datashiga na wannan mugun labarin.
Basu fadawa umman ba sbd irin kukan da Bilkees keyi cikeda damuwa.
Yanda ta sakawa ranta qunci da damuwa yasa AQEEL ASAD din kaita wata qasar suka sake ganin likita saidai acan dinma result din dayane Dan Haka Dole ta dauki qaddara.
Ko bayan dawowarsu Basu sanar da umman komaiba Dan Haka har lokacin umman kesa Rai a samun haihuwarsu..
Wani ciwo umman Cameroon tayi sosai Wanda yasa umman AQEEL ASAD din tafiya Cameroon kusa tsawon shekara biyu Bata dawoba Wanda ya bawa Bilkees damar adopting mufeeda itada AQEEL din acan qasar sbd mahaifiyarta data rasu a qasar batareda ansan danginta ba kasancewarta Yar Nigeria yasa aka bawa Aqeel din ita Kuma yasan mahaifiyar tata sosai tun kafin yayi aure lokacinda tayi auren ne Bai saniba bare Mijin data samu cikin dashi Dan Haka Bai musaba da Bilkees ta nace akan tanason babyn.
Ta karba babyn ne sbd kare matsayinta agun umma kada tasan Bata haihuwa shikuma ya amintarwa Bilkees karba babyn ne sbd tallafa rayuwar yarinyar kodan Allah yasa sakamakon hakan shima Allah ya basa wadda zai tallafi tasa 'yar uwar da Maminsa aduk inda suke duk da yasan tini Maryamah tayi girma yanzu.
Babban kuskuren dasukayi shine rashin sanar da umma ba Bilkees ce ta haifi mufeeda ba,
Shi yayi hakan ne sbd idan umman tasa daukota sukayi bazata taba barin su riqetaba sbd hakan kawai yayi shiru akan sune suka Haifa mufeeda Dan Haka a duniya bayan shi da Bilkees babu Wanda yasan basune asalin iyayen mufeeda ba har ita mufeedan wadda ta taso cikin gata da kulawa tareda daular arziki tana yanda takeso duk da kasancewar daddyn nata Mai zurfi a addininsa.
Ita kanta umma sosai take kaunar mufeeda kusan fiyeda komai Wanda hakan kesa Bilkees sake Jin Dadi tana sake sakewa a rayuwar aurenta data samu yanda takeso tako Ina wadatacciya rayuwar hutu da kwanciyar hankali sukeyi.
DR SHAYKH AQEEL ASAD lafiyayyen kyakkyawan matashi abokin manya ne dayakeda wayewarsa da ilimin Boko Dana addini masu zurfi dasuka kamasa,
Iliminsa na addini Sam Bai Hana wayayyar rayuwarsa ta matashin Alhajin Nera bayyanuwa a duk inda yake,
Rayuwarsa yakeyi cikin aji da nutsuwa da kwanciyar hankalin Wanda kudi da hutu suka Gama shiga tako Ina,
Shekaru da yawa shaawar dawowa kasarsa suka fita Ransa gabaki daya sai yanzu da mahaifiyarsa ta takura tanason dawowa gida yasa dole suka tattara suka dawo bayan shekaru masu tsayi da yayi acan tareda iyalin nasa,
Dawowarsu a Lagos zasu zauna sbd Manyan kamfaninsu da kusa duka huldodinsu da dukiyarsa suna Lagos din tun na mahaifinsa harma da nasa daya mallaka ya hade Dan Haka ya zabi zaman Nan din,
Babban qatoton gidansa da aka Gina Masa tun Bai dawo ba suka tare dake Victoria island,
Tareda ummansa suke zaune a gidan da nata bangaren na musamman.,
DR SHAYKH AQEEL ASAD yanada raayi da aqidar Boko sirke Acikin aqidunsa ta rashin raayi ko shaawar qarin Aure ko kula wata macen,
Dayar ta ishesa baya bugatan qari sbd rashin son damuwa ko tashin hankali Acikin rayuwarsa.
Dawowarsu duk duka baifi watanni ba aka saka mufeeda a university 100 level cikinma karatunta yayi sauri Dan batafi shekaru 17 ba,
Tarbiyar mufeeda gabaki daya ta ummenta ce Bilkees,
Komai kusan tare sukeyi kamar wasu Aminai shiyasa duk abinda Bilkees tayi raayinsu daya yake zuwa da mufeeda...
SSG Hayat Aminin AQEEL ASAD ne tun a UK suke tare harsuka Gama karatu suka dawo Nigeria suna tare sosai sai daga baya da AQEEL ASAD din yabar kasar suka rabu Amma still suna tare sbd iyalansu da daman sun san juna sun shaqu da juna matuqa sun zama kamar family daya,
Duk fushin da Nafee keyi ta tafiyarta da yayanta subar qasar akan AMAL IDON NERA da Mijinta gidan AQEEL ASAD take tafiya gurin Aminyarta Yar uwarta Bilkees su taru suyita jajanta lamarin, shiyasa Bilkees da mufeeda Suma sukaiwa IDON NERA muguwar tsana tun Basu sansu ba sbd ayanda suke tsananin kauna da so da kishin AQEEL ASAD dinsu akace wata zata shigo ta lalata rayuwar farin ciki da kwanciyar hankalinsu basusan ya zasuyi iya daukan lamarin ba.
***Ayanzu ma da maganar auren ya tabbata na AMAL Idon Nera da SSG din Basu Dena tsinewa zuriar Idon Nera din ba Dan Haka kusan kullum babu ranar da basa adduar Allah ya kawo abinda zai Hana auren su huta.
***Yauma suna tareda Nafee din wadda tafara figewa kamar ba matar a dah take rayuwa cikin hutu da kwanciyar hankaliba.
Nafee dai zuwa lokacin ta fara hakura ta sare sbd SSG dai ya nuna zai iya rabuwa da ita akan hakan Dan Haka takejin tayi sanyi zata hakura.
Cikin zafin zuciya da takaici Bilkees tace,
"Nafee Ni inaga tunda matar Nan kowa yasan karuwai ne bayan barna babu abinda suke yadawa a duniya
Mezai Hana mu shigarda qarar barnarsu ga kotun musulinci kokuma ga shugaban Yan hisbah gabaki daya,
Kinga fa ba Dan Allah zasu auresaba shigowa kawai zasuyi su tarwatsa zamanki da Mijinki da Yayanki su qara gaba,
Wallahi karki yarda duk haukar da SSG zaiyi ki Dage ki qwacesa daga tarkon wainnan mutanen da babu Allah a ransu.
Inaga kawai mu sanarwa da hukumar hisba babba abinda suke aikatawa
Wannan barna ce da cin mutuncin auren sunna,
Su ringa auran maza suna fitowa sbd kwadayi suna Tara kudin Haram...zamu sanar kawai a kamasu ayi musu hukuncin abinda sukeyi daidai yanda shariaa ta tanada...Ni so nakema idan an Kama uwar ai Kinga komai zai lalace ba maganar aure
Mijinki ya tsira sai aqara gaba
Allah yasa su samu Wanda ya fisa kudi da komaima saisu karkata zuwa can mu huta da zancen wannan masifar Mai suna IDON NERA...
Amin Amin ya Allah yasa su samu Wanda yafi nawa Mijin su qaratacan na samu aurena ya dawo daidai.
A ranar Bilkees takira babban Dan hannun damar DR SHAYKH ta sanar Masa qarar datakeson ya shigar akan a San irin barnar dasu Idon Nera din sukeyi.
Baya komai bada sanin Dr SHAYKH din Dan Haka ta fasa Dole qarshe Dan uwan Nafee din ne yakai zancen hisbah wadda Daman Suma sun San da IDON NERA takuma zamar musu kamar qayar makoshi,.
Dukkanin laifin da suke tihumarta dashi saita fita bayan ga barna Nan da yawa da ake aikawata da sunanta....
Amma wannan karon lamarin ya ishesu sbd ko jiya ankama mota biyu ta kusan Yan Mata marasa tarbiya da qazamar rayuwa karshe da sunanta sukai qarya suka kubuta sbd akwai Wanda acikinsu yasan asalin halayyar Haj Zainab din Kuma Yana bada shedar gaske akanta sosai babba ne acikinsu.
Bayanin dasu bilkees suka bayar akanta yayi muninda wannan karon babu wani sauki ko shirun da zaayi akanta Dole suna buqatan zama da ita.
Lamarin ya ishesu Kuma wannan karon zasu dauka mataki akanta idan har dabiarta ce aure aure tana fitowa itada yayanta sbd kawai Tara arziki da Kuma koyarda barna ga alumma.
Motar hisba aka Aika har babban gidan Haj Zainab IDON NERA Wanda hakan ya kawo wani irin tashin hankali da mamaki tareda zantukan koina...
Ahakan sbd su Bilkees su tozarta ahalin sai suka sake saka Kara a gun police akan Amal tayiwa Nafee bara zana akan Mijinta..
Wannan masifar ta saka zancen yaduwa Kamar gobarar daji Wanda da yawa wasu ke fatan ayi maganin Idon Nera kokuma a tozartasu tunda sunfi karfin hukuma.
Shi case din Amal a police ko zuwa batayi ba cikin mintina kalilan aka kashesa tareda watsi da qarar tasu Bilkees Wanda hakan ya tinzira Bilkees suka fito fili suka fada waye mazajen nasu.
Hisbah sun kasa samun zama da Haj Zainab sbd duk dalilan da aka kawo na Kamata ko ganin laifinta sun watse karshe take ta saka babbar qara akan matar SSG din sbd ko tana Wasa da komai Bata Wasa da yarta...babu Wanda zai taba yarta ta qyale.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
Leave a Comment