Idon Naira 5

 


*_IDON NAIRA_*

_Mamuhgee_

_Arewabooks@Mamuhgee_

_ZAFAFA BIYAR 2023_


5

LAST FREE PAGE




*_MAAB LUXURY HOME_*

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._


_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._


_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_


*_MAAB LUXURY HOME_*

*_MAAB LUXURY HOME_*

*_MAAB LUXURY HOME_*


_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _


_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_


_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._


_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _


_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._


_FACEBOOK: @maabluxuryhome._


_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_


_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_


_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_

______





*********""

Ahankali sukaci gaba da renon babyn itada Anty Maryamah din Dan kuwa saidai ace su biyu ke renon.


Wata uku Da haihuwar Maryamah tafara fita Aiki a babban guri Mai kyau da matsayi a kamfanin mijinta Dan haka kusan renon Aqeel da dawainiyarsa yadawo hannun Zainab Dan tsakanin Maryamah da jaririn nata sai dai ta bashi Nono da Yan sauran kauna da kulawar da baa rasaba Amma ko Aiki Bata zuwa dashi sbd Bata wani dadewa take dawowa sbd shayarwan datakeyi.


Zainab ce ta zama uwar renonsa da Dole da qarfi da yaji ta koya komai na kulawa da babys da hidimarsu,


Tun Tana tsoro da fargaba tareda taka tsan tsan akan kada tayiwa 'dansu ba daidaiba harta fara sakewa tana iya Masa wasu abubuwan,


Wanka ne kawai Bata iya Masa sbd shima Tana tsoron abinda zai iya faruwa Tunda har lokacin yarone sosai Amma Bayan wanka itace goyansa,

Basa Madara,

Sauya Pampers da sakasa bacci.


Ayyukanta kokuma ace nauyin dayake kanta saiya Ninku sbd lalurar renon yaro wani sabon aikine Mai wuya da taka tsantsan Amma haka take daurewa tayi dukkanin aikinta Yana bayanta Yana bacci wani lokacin Kuma Yana daki ta kwantar.


Sam batajin damuwa ko gajiyar kulaw da renon Aqeel sbd tsananin kaunar datake Masa har cikin ranta,


Jinsa takeyi kaman itace ta haifesa Kuma wahala ko Wace irice zata iya Masa Dan haka Sam batajin komai akan dawainiyarsa.


Da farko ganin yanda Zainab take shaquwa da kaunar Aqeel yasa Maryamah daukar me Reno Tana zuwa dashi gurin Aiki ta rabasa da Zainab ganin yafara wayo Yana gane Zainab din fiyeda kowa gashi shi Dadynsa ko ajikinsa Dan haka ta rabasu dan kada yayi mugun sabo da Zainab fiyeda ita.


Tashin farko Aqeel din kullum rigima yake musu harsu je Aiki su wuni su dawo baya zama 

Bayan rigima Babu abinda yakeyi ko cereals dinsa da nono daqyar yake karba

saidai idan yayi barci ne kawai suke samun sukuni Amma ahakan ta dage taqi maidawa Zainab renonsa duk da ta fahimci rashin Zainab ne ke sakasa wannan rigimar ta tashin hankali.


Ita kanta zainab kusan har qaramin zazzabi tayi da aka rabata da renon nasa Dan kuwa ta shaqu dashi fiyeda komai da kowa data sani rayuwarta Bayan mahaifinta Aqeel shine Dan Adam na biyu datake tsananin ji har cikin ranta.


Mai renonsa Rabi'a tsabar rigimarsa yasa idan Maryamah Bata kusa ubansa takeci  tayita yi Masa tsawa harda marin kumatunsa ko bakinsa duk tanayi tareda zare Masa idanuwa Tana zaginsa duk tabi ta firgitasa Sam ko ganinta yayi sai kuka.


Taurin zuciya Maryamah tayi taqi maidawa Zainab renon nasa duk kuwa da yawan kukan tashin hankalin dayake Mata a gida da office qarshe haka ya shide sai gasu a gadon asibiti.


Hankalin Dadynsa ya tashi sosai sbd baisan abinda yake faruwaba kwata kwata akan hakan Tunda bawani zama yakeyiba koyaushe Aiki 

Idan Kuma Yana gida suna harabar gida gurin karatun addini Dan shi din maabocin karatun addini ne Yana kaunar zurfafa iliminsa akan addininsa.


Alh Asad dinne dabai San meyake faruwaba Amma dai yasan akwai shaquwa sosai tsakanin Zainab da Aqeel din Dan kuwa harshi wasu lokutan idan Yana hannun Zainab qyuya yake Masa baya yarda da kowa indai Yana hannun Zainab.


Baisan Maryamah ta rabasu ba da haka yasa driver yakawo Zainab asibiti sai gashi itama Zainab din Tana Jin kaman zatai kuka lokacinda ta ga Aqeel din kwance a gadon na asibiti Yana bacci da Alama har yunwa akwai ataredashi.


Tana zaune gefensa ya farka Yana bude ido da ita yafaracin Karo sai kawai ya fashe da kuka Yana Kiran sunanta cikin rashin iya fadan sunan sosai Dan bai wani dadeba da fara koyan magana.


Dole uwar naqi tasaka Maryamah barwa Zainab din jinyarsa qarshema daga wannan jinyar sai kawai aka yayesa daga nono Daman yayi shekara daya harda watanni goma.


Tun kuma daga ranar bata ƙara ƙorafi akan kulawar da Zainab ke bai wa AQEEL basai ma tafi jin nutsuwar zuciya akan gwarama Zainab ɗin ta dinga rainonsa don ta fahimci ta fi Rabi'a iya bashi kulawa cikin nutsuwa hakama Rabi'a komai nasa aka Ba cinyewa takeyi tace shine yaci Bayan tasan qarya take Masa Dan rigimarsama Bata Bari Yana cin komai.


Zainab kuwa daman ita hakan takeso renon nasa yadawo hannunta Dan haka taci gaba da kulawa dashi da gidan harma da masu gidan Dan yanzu Anty Maryamah din Bata zama sosai itama kullum Tana office sai yamma take dawowa idan ta fita tun safe,


Rayuwar gidan da kula da gidan duk ya dawo ya rataya akanta yanzu har cefane itace mai zuwa tayo sai a hadata da driver abasu kudin cefanan zuje har wani qaramin kauyen dakeda manyan lambuna acan suke ciko Bayan motar dasuke zuwa cefanan.,


Itace tsaftar gidan,

Itace girkin gidan,

Itace Reno dakuma wankinta Dana Aqeel harma da wasu daga cikin kayan Anty Maryamah din.


Masu Aiki kuwa saidai can can a dauki daya idan aka kwana biyu sukaga bazasu iyaba su tafiyarsu ko suyi sata su gudu Dan babu Wanda zai iya aikin gidan me shegiyar wahala idan ba itaba Dan haka Tama Dena tsayawa adduar aringa samo masu aikin sbd ganin zuwan nasu baida amfani Dan haka saita share ta maida hankali gurin bautar data saba.


Yanda take tsananin so da kaunar Aqeel ahaka yake tsananin kaunarta Dan kuwa Sam yanda yake jinta Tunda baigama wayoba yasan son mahaifiya dabam yake shi Kai tsaye yafi jin Zainab din cikin ransa.


Sbd gurinta dayake barci yasa Dole aka siyawa Zainab din lafiyayyan gado aka sanya Mata a dakinta dan kada sanyi ya kamasa da kwanciyar qasa datakeyi ko kwanciyar katifa.


Albarkacinsa ta samu taci suke kwanciya abinsu akan lafiyayyan gado da beddings masu taushi da tsada.,


Ahankali ahankali sai gashi dakin nata an sauya komai an saka Mata AC harma dasu bedside fridge qarami da center carpet masu taushi da tsada duk akan sbd Aqeel dayake wuni gurinta tasamu albarkacinsa tanaci.


Kasancewar kusan daga Kansa Bata Kuma samun cikiba yasa kowa dangin dasu iyayen Aqeel din sonsa yake

Komai na wasa siya Masa ake shiyasa dakinta Dama daki na musamman din da aka cika da jeran tsadaddun furnitures da kayan yara koina kayan wasansa ne da abubuwan koyan karatunsa sbd yafara iya magana sai aketa siya Masa abubuwan koyan karatu Dan bakin nasa yafara qwarewa akan karatu maimakon surutun banza duk da shi din Sam ba yaro bane Mai surutu da rawar Kai Sam ko surutun ma bayayi idan kaji surutunsa to Yana tareda Zainab dinne a daki Tana Masa wasa haka.



Rayuwarta da Aqeel yashigo yasa takejin sassaucin kadaicin rayuwa da damuwar batada kowa da zata Kira nata,


Yaron qaunarta yakeyi sosai kaman itace ta haifesa,

Shaquwarsu tasa Sam baya neman mahaifiyarsa sbd kusan itama Bata zama ta zama maaikaciya sosai Dan haka gabaki daya komai na dawainiyarsa da rayuwarsa Takoma kacokan akan Zainab.


Alokacinda maganarsa ta fita ras Yana iya fadan komai daidai sunan Mami shine abinda yafi qwarewa a ambata Kuma shine Karan Kansa yake Kiran Zainab da hakan sbd Dadynsa da lokuta da Dama yake kiranta da Mamin Aqeel cikin 'yar raha haka sai Kuma idan yacewa Aqeel din


 "jeka gurn mamynka"


 Hakan yasa Aqeel din yakama sunan tun bai Gama tantance waye mahaifiyarsa a tsakanin Zainab din da Asalin mahaifiyarsaba sbd duk wata shaquwarsa da Zainab da tsananin kulawa da kaunar datake Masa ya wuce Wanda uwarsa ke Masa Dan haka Zainab ta shiga zuciyarsa sosai ta zauna.



A bangaren Zainab dinma Yana sake girma dawainiyarsa Tana sake Mata yawa sbd hatta nonuwanta dasuke  tsaye qyam a girke  duk sun fara Dan ranqwafawa sbd goyonsa

Gashi yayi nauyi da girma yanzu Amma haka yake hayewa bayanta sai anan yake bacci,


Haka take goyasa ta ringa ayyukanta dashi 

Kafin tagama duk ta Gama fita hayyacinta Amma haka take daurewa.,


Haka Kuma Aqeel din yarone Mai matuqar qyanqyamin zabar abinda yake ci Dan kuwa ba komai yake ciba 

Wani abin yanaci zai fara ciwon ciki da amai Dan haka ko anan bangaren saida Tasha wuya kafin ta fahimci da kyau abubuwan da cikinsa bayaso Dan haka kusan koyaushe abincin datasan yafi basa lafiya take Masa dabam Dana gidan.


Haka zalika Sam jikinsa bayaso sanyi sosai shiyasa kamar mace kullum qafafuwansa cikin safa masu taushi suke 

haka dai ya zamar Mata kaman wani qwai Koda yaushe komai nasa lallabasa akeyi.



Wani sabon Al'amari daya sauya a rayuwarta sanadin renon Aqeel zatace ko riqonsa shine komai na rayuwarta ya sauya yanzu Dan kuwa Alh Asad sosai yake kokarin daidaita matsayinta data Aqeel a gidan sbd ya lura irin kaunar da Aqeel kewa Zainab din matuqar Basu inganta rayuwarta ba ya girma zai iya qullatarsu akan hakan sbd lokuta da Dama ko Aiki takeyi wani time din yakan Bata fuska akan bayaso tanayi din,

Gashi qarfi da yaji baya iya zama taredasu a bangarensu suyi Wasa da dariya irin ta iyaye da 'da 

Har gwara shi akwai shaquwa da kauna tsakaninsa da Dan nasa Amma Maryamah Sam Babu irin wannan shaquwar kaman yanda yake da Zainab.


Tunda Alh Asad ya dauki damarar inganta rayuwarta abin yaso kawo matsala tsakaninsa da Maryamah Amma bai Wani samuba sbd idan sun inganta rayuwar Zainab to rayuwar Dan su suka inganta Dan kamar itace malamar tarbiyarsa.



Malam Sanda shine makusancin malaminsa dayake koyar dashi karatun addini sosai duk da bawasu shekaru ne dashiba Dan bazai wuce shekarunsaba Amma suna tsananin girmamasa kasancewar yanada ilimin  addini sosai kusan duk masu kudin anguwar manyan mutane dake shaawar karatun addini Bayan magriba zuwa ishai shine yake zaunawa dasu anan harabar gidan alh Asad suna karantar manyan litattafan addini.


Aqeel yayi girma da wayan dazai fara zuwa makaranta Dan haka dana addini suka fara sai Tunda yaqara wayo dashi Dadynsa yake fitowa karatun Daren kafin daga baya Malam Sanda din da Kansa yake koyarda Zainab da Aqeel din.

##MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo




Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070



MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.