Idon Naira 9

 


*_Arewabooks@Mamuhgee_*


9

Duk da Maminsa ce bayajin zai tsaya boyon zancen dake ransa gameda shawarar tasa,


Qari Kuma Daman zuciyarsa Bata kwanta da barinta gidanba sai ga wannan lamarin daya faru harya sakata cikin damuwa,


Sosai ta canja a kwanakin kwata kwata ta sake kame kanta sosai ta maida kanta a matsayinta na 'yar Aiki Mara gata ko mutuncin dayafi na Hakan,


Ta yarda cewan 'dan wani Baya taba zama 'danka duk da tanajin radadin raba kanta da tayi da Aqeel Amma Hakan shine kwanciyar hankali da mutuncin kowa duk da tasan bawa mutuncin take dashiba a gidan..


Tsakaninta dashi share Masa sashensa ta gyara takai Masa abincin ta jere saita komawarta cikin masu aikin gidan Yan uwanta.


Hakan Yana tsananin cizon ransa Dan hakama yake sake Jin nutsuwar shawartarta akan auren idan har zata aminta sbd rayuwarta ta inganta dan kuwa Allah bazai barsuba dagashi har mahaifiyarsa harma da umma Idan har suka Bari rayuwarta ta qare ahakan batareda sun Bata damar aure ta samu daidai iya nata farin cikinba.


Bai tuntubi Mamin da zancenba saida safe guraren 10 zuwa 11 haka Bayan tagama gyare koina na bangarensa zata fice ya fito daga bedroom dinsa sanye cikin casual wears qafafunsa sanyeda black footwears marasa nauyi na yawo cikin Palo da daki.


"Mami"  Kai tsaye yakira sunanta Yana qarasowa tsakiyar palon inda ta tsaya tareda waiwayowa ahankali ta kellesa cikin yanayi na alamar akwai wani aikin ne?


Qarasowa yayi gabanta Yana kallon kyakkyawar fuskarta da sai yanzu yake ganin diban kamanninta da ummansa 

Ahankali ya Kai hannunwan duka biyu ya kamo nata hannuwan Yana sake kallonta cikin kulawa da kauna irin ta uwa da 'da yace"


Mami Ni meye nawa da laifin maganar umma zai shafeni?

Tafiya fa zanyi zuwa farkon nxt year

Idan kina shareni haka bazan iya tafiyar nanba gaskia.


Kallonsa tayi Jin yanda Yar shagwaba take cikin sautin muryarsa 

Duk saiya tuna Mata lokacinda yake yaronsa...


Sanyi jikinta yayi duk da tanajinsa cikin ranta fiyeda kowa Amma kuma kusancin nasu Yana neman zama damuwa ga kowa Dan haka har cikin ranta ta dangana zata danne zuciyarta akansa bawai Dan Bata son 'dan nata ba sai Dan mahaifiyarsa dake ganin kamar ta rabata da danta data Haifa abinda.


Janta yayi ahankali ya zaunar kan kujera cikin kulawa tareda zaunawa gefenta hannunta daya yasake riqewa ya Dan sauke numfashi tareda nutsuwa ya kalleta.


Take tagane maganar dazaiyi Mai mahimmanci ce Dan haka ta dauke kallonta daga Kansa Tana sauraron abinda zai fada.


Mami aure nakeson kiyi kamar umma..


A bazata taji sakar zancen cikin kunnuwanta.


Kasa kallonsa tayi sbd Bata Kama zancenba Tunda dai yafi kowa sanin Hakan kamar abinda bazai yiyu bane gareta,


Ina mijin?

Waye zai aureta tagama fita layin budurwai?

Waye zai Bata gatan yin auren? Sbd tasan Haj maryamah ba lallai ta Bari ba,

Ina ita Ina wannan gata da rufin asirin..


Ganin zancen bai shigetaba yasashi sake fuskantarta yakuma Kiran sunanta'


"Mami da gaske nakeyi Aure nakeson kiyi,.


Juyowa tayi wannan karon Tana kallonsa da alama kosawa da zancen Dan tasan ana maganar aure ne a inda akeda miji Kuma Idan har zaka auru kenan.


Kai tsaye yace'


" Mami Zaki yarda babana Malam Sanda ya aureki?


Nine waliyinki Kuma na aminta da Hakan idan kin yarda.


Kasa magana tayi sbd maganar tasa tafara girmama da Bata tsoro,


Aure Kuma?

Ita din ce zatayi aure?

Dama akwai ranarda sunanta Dana aure zai Hadu Koda da raha ne?


Duk da tasan Hakan ba lallai Abu Mai yiyuwa bane saidai kuma yanda Aqeel din ya tattara nutsuwarsa akan maganar yasata kasa cewa komai.


Tabbas da tanada ikon kanta a gidan dakuma gurin tafiya da tafiyarta zatayi sbd tasan fitinar da zaayi idan wannan zancen na Aqeel ya bayyana,..


Haj maryamah ba qaramin bacin rai zata shigaba Amma Kuma a yanzu da Aqeel din yake maganar tareda magiya sosai yasa takasa cewa komai bare ta musa masa,


Wannan Wace irin sabuwar qaddarar ce Kuma?


Zamewa tayi ta tafi tabar Aqeel din Yana sake binta da magiya qarshe dai dakinta Takoma ta zauna tareda rafka taguma Tana tunanin abubuwa da Dama.


Shi Kansa malam Sanda din dayakeson aura Mata kamar yafi qarfinta sbd yanada rufin asirinsa,

Tsaftataccen malami kyakkyawan bafulatani Mai haiba shine zai bige da aurenta ita data Gama rasa kanta a mace,


Wahala da aikin wuta duk yagama dafar da fatarta ta rasa kyanta na mace,

Duk wani adon da mace ke buqata Babu daya data samu Bayan kitso wadda shima matar Maigadin gidan Dan majalisar dake kusa dasu itace take Mata wanda shima sbd tsaftar abincinsu yasa Haj maryamah ta lamunce Mata zuwa.



Da gaggawa ta kori tunanin zancen Auren dayake neman shigarta sbd kaucewa fada da gorin da zatasha dagasu umma da Haj maryamah sbd zaa ce itace ta kitsawa Aqeel din zancen.


Tattara zuciyarta tayi guri daya ta dangana ta dauki qaddarar da Allah yariga ya qaddaro Mata Dan haka kwana biyu tayita kaucewa Aqeel kadaicewarsu sbd kada yasake tayar Mata da zancen Amma kamar a banza sbd Hakanan yanzu daya riga ya furta tareda qudurta zancen sai yakejin idan ba auren sukaiba hankalinsa bazai kwantaba....


Ganin Mamin tasa batada niyar amincewa hankalinsa ya tashi sosai ya dage tareda hanata sukuni da magiyarsa Wanda yasata shiga mamaki da tsoron ganin yanda ya qwallafawa ransa maganar auren Dan harkomawa yayi kamar zai zauna yayi Mata kuka Dan kuwa har cikin tsakiyar ransa yakejin so da buqatan auren nata da Malam Sanda.


Batada zabi ko qwarin gwiwar hanawa Aqeel dinta abinda yakeso Dan haka ta amince Bayan tashiga tsoro da fargaban abinda zai biyo baya sosai.


Kafin ta amince sharadin sai idan mahaifiyarsa ta amince tukuna zatai auren idan Haj maryamah Bata amince bazataiba.


Baibi takan shawartar Haj maryamah ba Kai tsaye yayiwa malam Sanda tayin auren Mamin tasa tareda rokonsa akan amincewarsa bawai Dan komaiba sai Dan kamar Yana rokonsa ne ya zama gatan Maminsa alokacinda baya Nan.


Malam Sanda yasa Aqeel matashi ne Mai nutsuwa da hangen nesa tareda tunani na masu ilimi Dan haka baiyi wani dogon Jan lokaciba yace idan Zainab din ta Aminta da aurensa shikenan Allah yabasu hakuri da zaman lafiya.


Take ya sanar masa ta Aminta Dan haka a washe gari ya karbi sadakin Maminsa a hannun baba Malam Sanda ya shigo dasu sai alokacin ya tunkari Haj maryamah da zancen sbd kamar aikin Gama ya riga ya Gama 

Dan Idan ba Hakan yayiba tun farko ya tunkareta bazata aminceba da wuri zatai watsi da zancen.


Malam Sanda kuwa da baisan cewar Zainab din qanwar Haj maryamah bace baiyi tunanin Zainab nada dangiba Dan kuwa Dama kusan kowa sanin marainiya Mai Aiki ake Mata wadda aka dauko tun Tana yarinya har girman yanzu shiyasa ma ya amince da auren Dan shima ya bada tasa gudunmawar gurin inganta rayuwarta.



***

Tsit palon Haj maryamah ya dauka sbd wutar da itama ta Dan dauke ta wucin gadi,


Kudin sadakin Zainab da Aqeel din yake nuna Mata take kallon agabanta zuciyarta na neman toshewa da rashin iska na zallan mamaki da firgici.


Maida kallonta tayi kan Aqeel ahankali Tana nazarin yanda yariga yayi nisa aduk wani lamarin daya shafi Zainab baya shakkar kowa bare tsoron bacin ranta.


Daqyar ta iya bude bakinta tace"


Zainab tasan ta zancen??


"Tasani Amma nine na tilasa Mata amincewar......


Sbd Kaine ka haifeta ko?


To meye amfanin samuna da zancen yanzu Bayan kun riga kunyi shawara har Kai ubanta ka karba sadakinta. 


Dan rintse idanuwa yayi ahankali Yana sauke Kai daga kallonta Dan a kala manta Yana iya jiyo tsananin fushinta da bacin ranta.


Kasa cewa komai tayi ta miqe ta shige bedroom dinta tabarsa a palon sbd wani tiriri da zafi zuciyarta ta dauka.


Sosai taji zuciyarta tayi zafi da Zainab,


Tafara gajiya da yanda take baa matsayin kowaba agurin Dan data dauka cikinsa ta haifa akan Zainab,


Ya maidata kwata kwata a Bayan Zainab,

Zainab itace first priority dinsa kafin ita,

To meye amfanin Zainab a rayuwarsa da zata fi Masa uwar data haifesa.


Sbd yanda ranta yayi tsananin baci daga shi har Zainab Babu Wanda takuma magana dashi ta dauki fushi Sosai.


Zainab kuwa batasan meyake faruwa ba Dan batamasan cewa harya karba sadakinba.


A bangaren Aqeel kuwa ganin yanda Haj maryamah tadauki zafi matuqa akan zancen yasashi sanarda Baba malam Sanda a daura auren zuwa jumaa Tunda saura kwana biyar juma'ar tayi.


Sai alokacin ya sanarda Mamin tasa yakuma Bata sadakinta a hannunta.


Shiru tayi tsawon mintuna tareda shiga tunani kafin ta tambayasa Haj maryamah Bata kirata tayi Mata maganar ba Bayan Dole saida izininsu da saka hannunsu zaayi duk wani lamarin.


Haka ya share zancenta Dan yasan Maminsa bazata amincewa aurenba kamar yanda yasan bazata taba aurar da ita dinba 

Shikuwa bazai iya barin rayuwarta ta qare a Hakan ba tinda ba baiwarsu bace itama uwarsa ce,


Idan a baya batada gata ayanzu daya San Kansa shine zai zama gatanta daga Nan har lokacinda zai bar duniya inshallah.




Hankalin Haj maryamah bai Gama tashina da tsananin bacin rai saida Malam Sanda da Kansa yayi magana da ita ya sanar Mata yanda sukai da Aqeel tareda Bata tabbacin jumaa zaa daura auren.


Kudi ya fidda ya ajiye Mata daidai qarfinsa akan asiyawa Zainab din sitira.


Haj maryamah harsuka Gama magana ya tafi batasan haqiqanin me take cewaba Dan kuwa Aqeel yagama kasheta da mamaki wato har dangin mahaifinsa yasa malam Sanda yayi magana dasu akan auren Zainab din acan akai neman aure na manya aka sake bawa Aqeel qwarin gwiwar wannan aikin alkhairin daya hada tareda saka Masa albarka.



Kasa danne tsananin bacin ranta tai Dan bazata iyaba,

Duk wani rashin mahimmancinta ga danta ya nunawa duniya Tunda ya yanke wanan hukuncin shi kadai ya zartar.


Umma takira Tana hawayen qunci ta sanar Mata komai Tana jaddada laifin akan Zainab da zata iya yarda da buqatar Aqeel ta aure batareda saninsu ba.



Ita kanta umma mamaki Mai girma tashiga Jin Zainab dince zatai aure bada saninsuba,


Kenan duk kokarin dasukeyi akanta Bata ganiba shine ta zabi 'dan da aka Haifa a gabanta ya aurar da ita ga tafaffen malaminsa da baa San asalinsaba,baasan danginsaba baida kowa.


Wannan karon ummar da kanta ta Kira Zainab tayi Mata fadanda Bata taba yimata irinsaba...


Sai alokacin Zainab tasan da basusan da zancenba ashe


Hankalinta tashi yayi da fadan umma Dan kuwa maganganu marasa dadi da raunana zuciya ta fada Mata Wanda yasata kuka sosai.


Haj maryamah ta nufa dan Bata hakuri akan lamarin Amma Kuma bacin ran Haj maryamah din yafi na Umma Dan kuwa Kai tsaye ko wannan karon tabata zabi akan idan hartayi auren Wanda baasan asalinsaba Babu ruwansu da ita sun rabu kenan har abada.


Hankalin Zainab ya tashi Dan haka Bata tsaya shawara ko tunaniba tace ta hakura da auren ta fasa.


Hakan ya daki ran Aqeel sosai tareda Jin bacin rai da kunyar halayen mahaifiyarsa...


Daga umma har Haj maryamah Babu Wanda yayiwa Zainab sassaucin bayyanarda bacin ransa Dan haka tashiga wani mummanan Hali na damuwa da qunci tareda 'dacin zuciya Mai tsanani.


Halinda tashiga yasa Aqeel akaro na farko tsayawa da raayinsa akan na ummansa da ummarta.


Dukkanin harkar tafiyarsa karatu ya sokesu da Kansa tareda sanarda mahaifiyarsa ya fasa tafiya koina.


Babbar sabuwar rigima lamarin ya koma Wanda ya haddasa bacin rayuka tareda koke kokenda yawanci Zainab ce tafi Yi Dan ita aka yabawa laifin wannan karon har dangin mahaifin Aqeel din ita suka dorawa aka ringa tofa Mata maganganun gori marasa dadi.


Karshe dai da rigima taqi qarewa har saida umma tazo da nata bacin ran hakama haj Maryamah har gadon asibiti sbd jininta daya hau sosai Dan kuwa tashin hankalin da bacin ran Aqeel babu wanda bai ganiba qarshe dai kusan Zainab din yakeda niyar zaba akan kowa Dan haka tashin hankalin Zainab da baqin jininta saiya qaru.


Dangin mahaifin Aqeel dinma sai suka maida zancen Kuma akan Haj maryamah suna sukar tarbiyarta da wadda tabawa Aqeel din tako Ina duk sai komai ya qara lalacewa.



A ranarda taga yanda Haj maryamah ke zubda hawaye akan Aqeel zai jikinta yayi sanyi Dan kuwa tasan zubar hawayen uwa ga danta fitinace garesa Dan haka ta yanke shawarar  dakatar da duka tashin hankalin dayake gudana....Dan haka ta amince da auren Malam Sanda tabar gidan har abada kamar yanda Haj maryamah tace..

Amincewarta zata sakata nesa da Aqeel Wanda Hakan zai basa damar jituwa da shakuwar kauna da mahaifiyarsa dake ganin itace ta zama sanadin da Babu kauna Mai tsanani tsakaninta da danta.

##MAMUH#

#DR SHAYKH AQEEL ASAD

#AMAL IDON NERA

#LOVE/ROMANCE

#LIFE#SISTERS




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥

Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥

Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥

Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥

Safiya huguma


*KI KULANI*🔥

Miss xoxo


Littafi daya---400

Biyu---600

Uku----800

Hudu-----1k

Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171

Maryam sani

Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪

*Ina yan uwa 'yan nijer?*

*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA

biyu---650CFA

uku----850CFA

hudu----1050 CFA

Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*Thanks for choosing us*🔥

No comments

Powered by Blogger.