Jiddatul Khair 2

 


2.....


Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace "Look... I don't want to say anything about that.... idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa" Matashin na taunar apple yace "It's

already late, tayi bacci..." Abuturrab yace "It's late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?" El-Basheer yace "Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan" Abuturrab yace "In dai Friday ne ina nan in sha Allah" El-Basheer ya daga kafada yace "Ohk then" Abuturrab yace "Let me pick a call, sai da safe" El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace "The lady u don't want to talk about?" Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa "How u babe?"

 Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano.... Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja... Tsayinta matsakaici ne.... ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace "Why ain't you picking my call Captain?" Ya gyara xamansa yace "It wasn't long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?" A hankali tace "I'm fine, ya gajiya?" Yace "Alhmdllh, where are u coming from?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Home... kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito" ya shafa beard dinsa yace "Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks" Ta langwabar da kai tace "Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow...." Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace "To ina jin ki yanxu, I'm sorry i forgot about that" Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Ina jin ki Aneesah" Tayi kasa da murya tace "Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?" Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace "To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan" Ta girgixa kai tace "Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don't u love me ne Aliyu?" Abuturrab ya xaro ido yace "Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki.... kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo..." Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace "Aa ni da motana na fito don't worry" Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace "I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba" Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace "Thank you my Captain" ya kashe mata ido yace "C'mon babe.... Nikab din kuma na meye yau kika sa?" Tace "I just felt like" ya daga kafada yace "Alright sai mun yi waya" ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace "Aa Abuturrab sannu da xuwa" ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace "Ka dawo weekend kenan" yace "Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?" Tace "Alhmdllh na ji sauki yanxu" yace "Allah ya kara lfya" tace "Ameen" ledan hannunsa ya ajiye yace "Ahmad yace in taho maki da wannan" Tace "Kun hadu a Abujan kenan" Yace "Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka" Amira tayi 'yar dariya tace "Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa" Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace "Ni dai Allah ya tsare min shi" a hankali  yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace "Ameen Umma" Tace "Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko" Abuturrab ya d'an buda ido, sae kuma da sauri yace "Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai" Tace "Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae" Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace "Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa" Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace "Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated" tace "Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance" Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace "Ko kana da inda xaka je ne?" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Aa, bari in je in dawo" tace "To Allah yyi maka albarka" da kyar ya amsa da "Ameeen" snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace "Kee" bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace "Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne" Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana'arta, Yarinyar daxu tace "Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara" Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace "Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?" Tace "Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida...." Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace "Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d'an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba...." daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d'an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace "Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba...." Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam... Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace "Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu" Sai a sannan ta kallesa tace "Toh ai sai an soya ko baka ganin danye ne? Idan kuma danyen kake so ai magana xaka yi" Dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya rungume hannu daga xaunen da yake cikin mota yana kallonta da mamaki yana sake apprehending abinda ta fada masa, sai bayan minti goma ta kallesa bayan ta kwashe awaran da ya soyu tace "To na nawa kake so?" Ya mata wani kallo yace "Me kika ce min daxu? Sake fada in ji" Ta rufe awaran da ta kwashe a takaice tace "Toh baxan siyar ba, ka tafi gaba can akwai wata me awaran a gaba" muryar Hansai taji a bayanta tana cewa "Bai soyu bane Jiddah, ko ba awaran me motar xai siya ba? Baxa kiyi da jini ba kin xauna kamar wata rubabbiya ni Hansai" da sauri Hansai ta karaso tana kallon Abuturrab tace "Alhaji yi hakuri a kwashe maka yanxu, ta nawa kake so?" Abuturrab na tada motarsa yace "Ae tace ba na siyarwa bane, in tafi akwai a gaba" Da sauri Hansai ta bude roban awaran taga soyayyen awara da ta kwashe a jibge, ga wasu ta xuba a mai, wani lafiyayyen mari ta wanke ta da shi tace "Ubanki ne xai siya wannan da kika kunshe min a gwagwa? Yo ina ma yaga arxikin siyewa tukun, muguwa, axxaluma yar bakin ciki, to Allah ya isa cutata da kike...." Wani marin ta sake wanka mata a mugun fusace ta hankadata, Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace "Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji.... wllh akwai na nawa kake so?" Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace "Toh har ya kai ki mareta haka??" Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace "Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh" cikin tsawa tace "Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?" Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace "Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema" Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace "Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai,  na nawa kake son awaran?" Yace "Dubu daya" da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk 'yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace "Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?" Aunty tace "Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?" Ummi tace "Gashi ai naji a bakin ki yau" Aunty na kallon Abuturrab tace "Kai ka ji fa Aliyu.... Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu...." Abuturrab ya d'an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign.... Sai kuma ya dago kai a bayyana yace "To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty" Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace "That's the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take...." Aunty tace "Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?" Ummi tace "Toh Allah ya baku sa'a, idan walakanta d'an Adam abun yi ne, ku ci gaba" Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace "Ina xa ka Captain?" Yace "Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york...." Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da 'yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it's very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace "Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?" Tayi fari da ido tana kallonsa tace "Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba" Yace "Ohk, ita warce take soyawan tana ina??" Ta wani yatsine fuska tace "Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje" yace "Ohkk, sai anjima" Tana murmushi tace "Toh sunana Bibalo kai fa?" Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace "Wani gida ne ake awara a layin nan?" Yaron yace "Gidansu Bibalo ne" Ya sauko motar ya kulle sannan yace "Toh kai ni gidan" Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace "Shiga ka kira min me awaran" Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace "A xaton ki an mareki jiya sbda ni?" Kauda kai tayi, ya hade rai yace "Ki juyo ki kalleni ina maki magana" Ba tare da ta juyo ba tace "Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba" kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace "Nace maka babu awara yau" Yace "Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?" Ta wani xare ido tace "Ni nace maka banyi wanka ba??" Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace "Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu" Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.


No comments

Powered by Blogger.