Jiddatul Khair 25
Abuturrab ya dau throw pillow dake gefensa ya jefa ma El-Basheer da ya bi Jiddah da ido, sae a sannan El-Basheer ya dauke idonsa, sai kuma ya daga kafada as if counting his words yace "Ita ce.... Ex-wife din taka?" Abuturrab na kallonsa da wani expression yace "Does that warrant u to stare at her that way??" El-Basheer yyi shiru yana danna wayarsa kamar baxai ce masa komai ba, sai kuma ya kallesa yace "Naga kamar ganinta ya fi jin ta ne, ita ce yar hayin rigasar?" Abuturrab ya masa wani kallo ya dau remote yana canxa channel, El-Basheer yace "Ko dai a gidanka ne ta samu transformation din nan, she's got a beautiful shape" Abuturrab ya mike, sounding fed up yace "Stop this plss El-Basheer... U r sounding lousy" El-Basheer yana shafa gashinsa yace "Lousy? Ohk sorry about that" Abuturrab ya dinga kallonsa da wani expression that is expressing how really angry he is, ya koma ya xauna yana canje canjen channel, El-Basheer ya bi parlor din da kallo yace "I need something cold to take now, haka kake treating visitors?" Mikewa Abuturrab yyi ya wuce kitchen, El-Basheer ya bi sa da kallo, fridge ya bude ya dau bottle water daya sannan ya fito, sama ya wuce yana cewa "In dai ni xan kawo maka ruwa xaka dade baka sha ba" El-Basheer ya bi sa da kallo yana d'an murmushi, can ya girgixa kai, bude kofar dakin Jiddah Abuturrab yayi ya shiga.... xaune ya ganta ta takure waje daya, tana ganinsa ta gyara xamanta tayi narai narai da ido tana kallonsa, ya ajiye ruwan gaban mirror ya juyo fuska a tamke yace "Me nace maki daxu?" Shiru tayi, yace "Ba ce maki nayi kar ki fito ba all through?" Hawaye ya cika idonta tace "Ruwa ai naje in dauka, ba ce min kayi in daina shan na bandaki ba" Yace "Me ya hanaki dauka daxu da kika sakko" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Xo ki dauka" mikewa tayi ta tafi gun madubin ta dau goran ruwa, yana kallonta yace "Sannan ba nace kada ki sake sa irin kayan nan a gidan nan ba?" Ta kallesa tace "Ai daxu ka gaya min, ina ce daga yau kace.." Bai kuma cewa komai ba ta koma inda take ta bude ruwan, sai da ta sha ruwan sannan ya juya ya fita dakin, tsaye ya ga El-Basheer a parlor hannunsa rike da kwalin lemon chivita yana sha, Abuturrab ya xauna yace "What will u be taking for lunch?" Xaunawa El-Basheer yayi yace "Naaah... I'm full, i just need rest" Abuturrab yace "Okay mu je sama" Mikewa yayi ya fara tafiya sama, El-Basheer ya mike ya bi bayansa rike da lemonsa, Abuturrab ya kai sa part dinsa, xaunawa El-Basheer yayi gefen gado cikin bedroom din bayan ya rufe lemon hannunsa ya ajiye yace "Tsarin gidan yayi sosai, the Architecture is really good" yana fadin haka ya kwanta, Abuturrab dai na tsaye gaban madubi yana kallonsa ta madubin, can dai yace "Xan je in dawo yanxu!!!" El-Basheer ya dago yace "Ina xa ka?" Yace "To get lunch" daga haka ya nufi kofa ya fita, yana isa kofar Jiddah ya bude, ya d'an hade rai yace "Dauko Jilbab dinki, ki sameni waje" Daga haka ya wuce, yana cikin mota Jiddah ta fito da Hijab har kasa, sai da ta shiga gaban motar sannan yayi horn, mai gadi ya hau bude gate din, jan motar yayi suka fita gidan, wani babban eatry ya tafi, ya siya ma shi da El-Basheer fried rice and chicken, Jiddah dae na xaune kan kujeran da ya nuna mata cikin eatry din, sai bin mutanen wajen take da kallo, baka ta6a cewa tare suke da Abuturrab don bai ko sake kallon inda take ba, wani mutumi ne ta ga ya ja daya daga kujeran table din da take ya xauna, ya daga face cap dinsa yana kallonta, ta saci kallon Abuturrab da ke xaune wani table can yana jiran order din da yayi, ta sake kallon mutumin, ya sakar mata murmushinsa me kyau, ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Hello, how are u doing, are u waiting for ur order?" Ta saci kallon Abuturrab taga kallon direction dinsu yake ko kiftawa babu, sosai gabanta ya fadi, cikin rawan murya tace "Yayana na nan fa" Mutumin ya bi eatry din da kallo, kawai gani yayi Abuturrab ya nufosu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Abuturrab na isowa yana kallon mutumin babu yabo babu fallasa yace "Didn't she tell u she is married?" Mutumin ya mike yace "Ooh i am sorry plss" Abuturrab bai tankasa ba ya ja wani kujeran ya xauna facing her directly, mutumin ya kara basa hakuri, nan ma yaki amsawa har mutumin ya bar wajen, Jiddah ta saci kallonsa suka hada ido, ya jefa mata wani kallo yace "Ko tausayin rayuwarki baki ji har xaki fara kula maxa ko?" A hankali tace "Ni bani na kirasa ba kawai xuwa yayi" Yace "Toh bari kiji har sai kin gama jami'a kin fara aiki, kafin ki kalli ko wani namiji balle har ki kulasa" Ta gyada masa kai kawai, ya ci gaba da danna wayarsa har aka kawo masa order da yyi a takeaway, without looking at her yace "Me xa ki ci?" ta sunkuyar da kanta tace "Ko meye" tsaki yyi ya mike ya bar wajen, jollof rice yayi mata order da kazar ita ma sannan suka bar eatry din, tana rike da ledan nata ta wuce dakinta bayan sun isa gida, Abuturrab na shiga bedroom dinsa ya tadda El-Basheer a kwance yanda ya bar sa idonsa lumshe, parlonsa ya koma ya xauna.
Bayan la'asar Abuturrab ya sauko downstairs ya samu El-Basheer dake xaune yana jiransa, El-Basheer yace "Plss idan baxa kaje ba ni in tafi mana, i have many places to go yau din nan, i will be leaving probably tomorrow in sha Allah" Abuturrab ya mika masa wayar hannunsa yace "Aneesah..." amsar wayar El-Basheer yyi ya kai kunne, Abuturrab ya ajiye makullin motarsa sannan ya koma sama, El-Basheer ya amsa gaisuwar Aneesah yace "Ya kwana biyu?" Aneesah tace "Alhmdlh, he is just telling me kuna tare yanxu" El-Basheer ya d'an yi murmushi yace "Yea daxu na shigo kaduna and am at his resident now" tace "Oh ohk, ya su Ummi?" Yace "Ban je ba" Aneesah tace "Ayya, to ya garin?" El-Basheer yace "Cool, i have a question for you Aneesah, nasan baxa ki boye min ba" kafin ta ce komai yace "Tell me.... is Aliyu saying the truth na cewar ya saki yarinyar nan??" Aneesah ta yi shiru da fari, can kuma cike da confusion tace "Yarinya? Wacce yarinyar? Kuma sakin me?" Shiru El-Basheer yyi, can yace "Ohk then, i will pick a call right away...." Daga haka ya katse wayar ganin from all indication she knows nothing about what he is saying now, sake kira tayi ya ajiye wayar gefensa ya jingina da kujera, Abuturrab na tsaye dakin Jiddah dake rakube jikin gado, yana kallonta strictly yake cewa "In har muka shigo gidan nan kika wani sakko wai xaki dau wani abu xaki sha mamaki na, duk abinda xa kiyi kiyi ki gama yanxu kafin mu dawo" ta gyada masa kai kawai, kamar wanda ya tuna abu ya juya da sauri yana kallon kofa, lkci daya ya fice daga dakin ya sauka downstairs yana kallon El-Basheer da manyan idanuwansa yace "Hope... Hope you didn't say anything apart from greeting to Aneesah???" El-Basheer yace "Of course baka ce min haka ba, na tambayeta ko gaskiya ne ka saki yarinyar nan kamar yanda ka fada, and from d way she sounds, bata san komai kan maganar ba ma" Abuturrab ya xaro ido yace "Ohh my God... Me yasa xaka yi mata wannan maganan El-Basheer?? We are still hiding it from her" Mikewa El-Basheer yyi ya dau makullin motar Abuturrab yace "Ni kace min bata sani bane, ga ta nan tana ta kira, pick and find what to say to her" daga haka ya nufi kofa ya fita, Abuturrab ya bi sa da kallo xuciyarsa na tafarfasa. Daukar wayarsa yyi yaga calls din Aneesah har biyar yayi silencing wayar ya bi bayan El-Basheer.... Bangaren Aunty suka fara shiga suka gaisheta bayan sun isa gidan, Aunty na kallon El-Basheer tace "Har ka iya xuwa wai gidansa El-Basheer, ni fa na tattare lamarin Abuturrab na watsar a gefe, i see no reason da xai dinga boye boyen cewar ya saki yarinyar nan, ko meye fa'idan xama gida daya da ita bayan ya saketa, who is he deceiving?? To wllh I've made up my mind cewar Abbansa na dawowa sati me xuwa xan sanar masa komai, wannan ae iskanci ne, to ko minti biyar ba ayi da muka gama waya da mahaifiyar Aneesah ba, labari ya je masu, kana tunanin xaka iya ci gaba da boye masu ne dama?? Wllh yanxu haka duk hankalina a tashe yake, nayi kokarin fahimtar da su ba auren amma ya faskara...." Kallonta kawai Abuturrab yake yi, shi na Aneesan ma bai damesa ba kamar na Abba da tace xata sanar ma ya saki Jiddah kuma yana xaune tare da ita, gaba daya yaji hankalinsa yyi mugun tashi, Waje ya nema ya xauna jin har kansa ya fara juya masa, El-Basheer yace "Ni banga abun boye boye a nan ba, let this be known to everyone that she is no longer ur wife, kana xaune gida daya da macen da ba muharramarka ba, who does that??" Abuturrab ya kalli Aunty da ta ci gaba da abinda take bbu fara'a fuskarta, yyi kasa da murya yace "Amma Aunty kinsan Abba won't be happy idan yaji na saketa, he will be highly disappointed at me, kuma ni sbda bana son bacin ranki ya sa na saketa wllh, idan kika gaya ma Abba cewar nayi hakan yanxu he won't take it likely with me, i am just confuse Aunty" Aunty ta juyo a fusace tace "Ni kuma dole in sanar masa duk abinda xae faru ya faru ba, are u this happy being with the girl da yasa ka daina dawowa weekend gidan nan sae dai ka sauka gidanka ka karashi weekend dinka ka wuce, haka xaman naka da ita yayi dadi duk da ba matarka bace ashe?? To kuwa xaka sha mamakina kuwa wllh" Ya girgixa kai yace "Aunty ni weekend din ma gaba daya na daina dawowa fa, Jiya ne kawai na dawo sbda El-Basheer yace min yana hanya" Aunty tace "Wato ita kadae ke yanda ta so a katon gidan? Ka sakar mata babban gida haka ta ci karenta ba babbaka, to baxai yiwu ba ne wllh" Shiru yyi bai ce komai ba, Aunty tace "Don kuwa da ta ci gaba da xaman gidan nan naka gwara ka dawo da ita nan, dama mai aiki xata tafi garinsu jibi, kaga ba wani xai ce ta bar nan gidan ba wataran..." Kallonta kawai Abuturrab ke yi gabansa na bugawa, tayi masa tsawa tace "Kallon ne amsan ka? Ko baxa kayi abinda nace bane??" Ya girgixa kai yace "Aunty can din ma ina assuring dinki ba sae wani yace ta tafi ba xata tafi, wllh ita kadai ce bbu kowa" Aunty ta kara masa wani tsawa tace "Nace ka dawo da ita gidan nan, ko ban isa ba??" Ya sunkuyar da kansa lkci daya jikinsa yyi sanyi, can ya kalleta cikin sanyi yace "Toh" Sannan ya mike ya nufi kofa ta bi sa da harara tana huci, El-Basheer ya d'an yi murmushi yace "But how can a normal human being do what Abuturrab did?" Cike da bacin rai Aunty tace "Atoh... Isn't this irritating Bash?? Wllh da lamarin nan nake kwana nake tashi a raina, ya ce ya saketa quite alright he did that, na sani, to kuma xaman me suke tare idan anyi magana yace Abbansa, ance masa da Abban nasa ya san ya saketa xae barsa ya ci gaba da xama gida daya da ita, ga yarinyar ido a bude, to xaman iskanci yake son fara yi da ita ko me, don dai shi ma ba saiti garesa ba kuma ba jin magana yake ba, ka sani, na sani, shi yasa bai dauki xaman da yake under same roof with her wani abu ba" El-Basheer ya mike yace "Allah ya kyauta" daga haka ya fita. Ko bangaren Ummi Abuturrab bai shiga ba ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya jinginar da kansa da kujera yana jiran El-Basheer, dalilin da yasa bai son xuwa gidan kenan idan ya dawo weekend, ganin har bayan minti sha biyar El-Basheer bai fito ba Abuturrab yyi dialing numbersa, El-Basheer na dagawa, a fusace yace "Inyi tafiyata ne?" El-Basheer yyi murmushi ya katse wayar, kallon wayar Abuturrab ya dinga yi, sai ga text ya shigo masa, bude content din yyi, "C'mon wani irin gaisuwa kake son inyi ma Ummi, gaisuwan minti goma? Tunda kai kaki shigowa gaisheta ni baxan iya ba" Abuturrab ya mayar masa reply yace "Ka sameni a gida then" daga haka ya ajiye wayar ya tada motarsa ya bar anguwar. Yana parking ya shiga parlor ya xauna kujera ya jinginar da kansa ya lumshe ido yana jin ransa ba dadi, text ne ya shigo wayarsa ya bude ido a hankali ganin Aneesah ce tayi text din ya bude content din, "Abinda ka min was the least i expected from you Aliyu, ban yi xaton haka ko a mafarki ba, amma ka sani ka cuceni, ka ci amanata, ka yaudareni, ka ruguza min rayuwa, i gave u all my trust but u ended up betraying me, why Aliyu, did i deserve this harsh treatment from you?" Ko gama karanta text din bai yi ba yayi mata reply kamar haka "Since you never expect this from me... Then u consider me... Aure kuma sai idan kece kika ce baxa kiyi da ni ba, as for me you will be my first and last wife in sha Allah.... i will call u in 5 hours time in sha Allah" daga haka ya tura mata text din ya ajiye wayar ya mike ya wuce sama. Har bayan Magrib El-Basheer bai shigo gidan ba, hakan ya sa Abuturrab yyi dialing number sa, yana fara ring El-Basheer ya daga yace "Gobe xan shigo before leaving, Ummi tace i should spend the night here" Abuturrab yace "Ohk" daga haka ya katse wayar. Mikewa yyi ya wuce sama ya bude kofar dakin Jiddah, tun da ya dawo ko motsinta bai ji ba, tana xaune gaban mirror tana ma gashinta kitson kalaba, ganinsa ta dau hulanta ta saka, yana tsaye bakin kofa yace "Meye hakan kike yi?" Tace "Aa ina kitson gashin ne, yana karyewa idan ban yi kitso ba" Yace "Sai anyi kitson ne baxai karye ba?" Ta gyada masa kai, yace "Toh kwance wannan abinda kika yi, tunda a garinku ne aka ce maki xai karye idan ba ayi kitso ba, a tsefe xaki bar gashin, haka nake so" Ta kallesa da sauri, that was when he realized what he just said, lkci daya ya hade rai yace "Ko kina ganin kitso a gashin su Ramlah, mu a nan ba a kitso" Cikin sanyin murya tace "Toh" ta fara tsife dogon gashin nata da ta kitsa, har ta gama tsefe daya bata ji ya tafi ba, hakan yasa ta leko sa ta cikin gashinta da ya rufe mata fuskarta gaba daya, suna hada ido ya juya ya fita dakin. Ana kiran isha ta gama parking din dogon gashin nata ta kitse jelan sannan ta sa hularta. Karfe tara saura wayar da Abuturrab ya bata ya fara ring a gaban madubi, karasawa tayi ta dauka tana kallon number jikin screen din sannan tayi picking ta kai kunne, muryarsa taji yace "Ina jiranki a parlor" Daga haka ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta sa Hijab dinta ta fita, shi kadae ne xaune parlon ta durkusa jikin kujera a hankali tace "Gani" Yace "Me kika ci?" Ta sunkuyar da kanta tace "Taliya na dafa" ya nuna mata ledan dake gefensa yace "dauka" mikewa tayi ta isa kusa da shi ta duka ta dau ledan, ya rike numfashinsa sbda wani kamshi na daban da ya doki hancinsa, ganin kwalin lemo a cikin ledan ta cire xata ajiye, ya saki breath dinsa ya hade rai yace "Har da shi xa ki tafi" Innocently tace "Ban iya sha ba" Yace "Haka xa ki je ki koyi sha yau, tunda ke yar kauye ce" Bata ce komai ba ta mayar da kwalin cikin ledan sannan ta mike ta nufi stairs, bin ta yyi da kallo tana isa stairs ta juyo suka hada ido, da sauri ya dauke idonsa, tace "Nagode" sannan ta wuce sama, jinginar da kansa yayi a hankali da kujera yana jin damuwa iri iri a ransa, gasasshiyar kaza ce da yaji Jiddah ta bude a dakinta, sai kamshi kazan yake, ta kalli kwalin hollandia din sannan ta bude ta d'an sha kadan, ji tayi yayi mata dadi a baki sbda gardinsa, ta lumshe ido ta kara sha sannan ta ajiye ta fara cin naman a hankali, lkci daya rayuwar da tayi a gidansu ya fado mata, tura kazan tayi tuna Babarsu da tayi.
Abuturrab na kwance wajajen sha daya a parlor, waya na kare kunnensa, he felt relieved bayan yayi convincing Aneesah a kan kaddara ce ya sa shi auren jiddah sannan kuma bashi da aurenta a kansa yanxu, daga daya bangaren cikin sanyin murya tace "Amma why is she still at ur resident My captain??" Yace "Ina kike son in kai ta yanxu?" Tace "Ni ko gidanmu ma ka kawota su Mummy baxa su ce Aa ba wllh, ni nasan karyar da xan masu, ka barta ta dawo gidanmu plss" Bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, a hankali yace "Koh?" Ta marairaice tace "Sure dear" yace "I will think about that, xuwa nan da short period of time" tace "Do so fast plss Captain" daga kai yyi jin footstep a stairs, lkci daya yace "I call you in some minutes time" bai jira cewarta ba ya katse wayar, yayi kasa da idonsa kamar me bacci, A hankali Jiddah ke tafiya duk xatonta bacci yake hannunta rike da ledan kazan da ko yanka uku bata ci ba, to bata saba da shi ba shi yasa bata iya ci sosai ba, drink din ne ma ta d'an sha ba laifi, kitchen ta tafi ta ajiye ledan kazan a fridge ta ajiye lemon ma sannan ta fito, a hankali take tafiyar ta nufi stairs ya bi ta da kallo, nighty ne jikinta wanda ya wuce kneels dinta da hularta a kanta, sai da ta isa stairs ta juyo ta kallesa suka hada ido, sosai ta tsorata, yyi saurin mikewa xaune pretending to be awake at that moment yace "Me kike yi a nan" ta nuna masa kitchen tace "Na kai abu na ajiye" yace "Je ki dauko abinda kika ajiye" Tayi narai narai da ido ta ki motsawa daga inda take, ya hade rai yace "Baki ji abinda nace ba?" Da gudu ta wuce sama, ya mike tsaye da mamaki yana bin ta da kallo, har ta shige dakinta.
Leave a Comment