Jiddatul Khair 34
Bayan sati biyu Jiddah na xaune dinning area ita kadai bayan magrib, Hijab ne har kasa jikinta, Huraira kuma na kitchen tana wanke wanke, gaba daya hankalinta na kan takardan gabanta taji an danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, ta koma baya tana kallonsa tace "Ina yini" Da murmushi yace "Lafiya lau Jiddah" ta juya ta koma parlon ya karaso ya xauna, tace "Ya Aunty Ramlah?" Yace "Tana gaisheku, Umma na daki ne?" Tace "Ehh" yace "Tou xauna mana" d'an murmushi tayi ta xauna edge din kujera yace "Kin fara karatu koh?" Tace "Eh" yace "Amma ki fada min gaskiya, kina ganewa?" Ta gyada masa kai, yace "Aa bude baki ki min magana" Sunkuyar da kai tayi har sannan tana murmushi tace "Ina ganewa" Yace "Toh wani rana da wani rana ku ke karatun?" Tace "Ranan litinin xuwa juma'ah" Yace "Asabar da lahadi fa?" Tace "Islamiyya muke xuwa tare da su Maimuna" Yace "Toh me da me ake koya maki litinin xuwa Juma'ahn?" Tace "Karfe tara na safiya take xuwa mu yi boko xuwa karfe biyu, sai kuma Islamiyya karfe uku xuwa shidda" Yace "Duk ita ke maki bokon da Islamiyya?" Ta girgixa kai tace "Aa wata ce daban take xuwa karfe uku" Yace "Maa sha Allah, kawo takardun naki in ga" Mikewa tayi ta nufi dining ya bi ta da kallo ta dauko jakar da duk litattafanta ke ciki ta dau har da na kan dining table sannan ta kai masa, ya amsa yana dubu abubuwan da suka yi na sati biyu, ita dai tana xaune tana wasa da fingers dinta, ya daga kai ya kalleta yace "Anya ke da kanki kike aikin nan da malama ke baki?" Tayi murmushi tace "Ni ce nake yi ka tambayi Maimuna" Yace "Maa sha Allah, ki dinga maida hankali haka kinji?" Tace "Toh" Ya dau wayarsa dake ring, ta jira har ya gama wayar ya ajiye sannan tace "Aliyu fa?" Daga kai yayi ya kalleta, ta sauke idonta yace "Waye Aliyu?" Jin bata ce komai ba yace "Ohh captain wai?" Still bata ce komai ba, yace "Yana kano, mun yi sati biyu bamu hadu ba, kuma bana jin ya xo weekend" Tace "Toh" Umma ce ta shigo parlon ganin Ahmad tace "Yaushe ka shigo?" Yace "Not too long" Ta karaso ta xauna yace "Ina yini Umma" Tace "Lafiya lau, yau ma baka xo da Ramlan ba?" Yace "Ehh na barta da su Aisha ne sun je can gidan" Umma tace "Ohk" kallon Jiddah tayi tace "Har kin gama karatun?" Tace "Aa ina kan yi" Tana fadin haka ta mike ta isa gun Ahmad ta kwashi duk takardunta ta wuce daki, Ahmad yace "Cewa nayi ta kawo in ga performance dinta and naga she is really trying" Umma tace "Gaskiya kam, she isn't dull kawai dai karatun ne bata samu ba, amma in sha Allah nan da few months a yanda naga take da hazaka she might catch up with her mate, tana da kwakwalwa kam maa sha Allah" Ahmad yace "Toh Allah ya sa hakan, sai ayi enrolling dinta jss3 ko?" Umma tace "Ehh" Ya shafa kansa yace "Umma daxu Yousuf ya kirani..." Umma tace "Ya aka yi?" Ahmad ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Wai a kan Jiddah..." Murmushi Umma tayi tace "Ni dai nasan ba haka nan yake xuwa gidan nan frequently ba da dalili, toh maa sha Allah..." Ahmad yace "But Umma ai bata bukatar wannan yanxu, she need to concentrate fully on her studies" Umma tace "Toh ai sai ka jira in gama magana ko... ni baxan hanasa alaka da ita ba, sai dai shigo da batun soyayya gareta yanxu isn't necessary, he should wait a little...." Ahmad dai bai ce komai ba. Aunty ce xaune gefen gadonta waya kare kunnenta tayi shiru fuskar nan nata a daure, can ta mike tace "Haka yace maki?" Daga daya bangaren Aneesah tace "Wlh Aunty" Aunty tace "Toh kyaleni da d'an iskan, nasan maganinsa...." Aneesah tace "Ni fa wllh Aunty yau kusan wata daya kenan na ma kasa gane kan relationship din nan namu" Aunty tace "Daina kiranki yayi?" Tace "Toh ai dama tun farko ba kira yake ba sai in ni na kira ya bi miss call, yanxu kuma ko na kira din ma sai sanda ya ga dama yake kira, sai yace aiki yayi yawa..." Aunty tayi shiru tana sauraronta, sai kuma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Amma kuna dai maganan still koh?" Tace "Aa muna magana, kawai sabon miskilanci da jiji da kai ya karo... Sai yayi ta cewa shi baya son damuwa, shi baya jin dadi, shi he want to sort somethings bothering him, shi yana son break, shi he wants to be alone for sometimes, haka dai wllh... Kamar baya son magana da ni" Aunty dake ta jin ta, tace "Amma ya siya maki abinda nace kice ya siya maki ko bai siya ba?" Tace "Aa ya tura min kudin har da kari ma" Aunty tace "Toh shkkn, xan kiraki xuwa anjima, ki kwantar da hankalinki" Tana kai wa nan ta katse wayar tayi dialing number Abuturrab, sai da ya kusa yankewa ya daga, yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Wani laifin muka maka Aliyu yau kusan sati uku babu kai babu labarin ka?" Yace "Aa aiki ne yayi yawa yanxu..." tace "An sake employing dinka a wani airline din ne bayan wanda kake aiki?" D'an murmushi kawai yyi bai bata amsa ba, tace "Atoh gwara ai in ji, kuma ai kana shigowa kadunan, xuwa gida ne kawai baka yi" yace "Aa bana shigowa, amma xan shigo friday din nan in sha Allah" Tace "Toh ina saurarenka" Daga haka ta katse wayar. Hijab Jiddah ta dauka xata saka bayan ta gama shiryawa Maimoon ta hade rai tace "Meye hka kuma, ba ga mayafi na ajiye maki ba" Jiddah ta xaro ido tace "To ae an hanani" Maimoon tace "Wa ya hanaki?" Ta sake xaro ido sae kuma tace "Tou bari in sa" daukan mayafin tayi ta yafa, Maimoon ta washe baki tace "Waoww kinga yanda kika yi kyau kuwa" Murmushi kawai Jiddah tayi, suka fita xuwa dakin Umma, Umma tace "Kuna kai sakon ku dawo, ba sai na gaya maku kuna da Islamiyya karfe biyu ba" Maimoon ta marairaice tace "Yau dai kawai Umma, Sis Ramlah fa na can gidan" Umma tace "Toh ku bani xan ba Driver ya kai idan ya dawo" Maimoon ta xaro ido tace "Aa wllh ynxu xa mu dawo Umma" Kudin mota ta basu suka fita gidan, Jiddah na rike da ledan sakon da Umma ta bada su kai ma Hajja, karfe sha daya da rabi suka isa gidan, Maimoon tayi sallama bakin kofa tayi knocking sannan ta tura, Jiddah ta bi bayanta, babu kowa a parlon suka nufi part din Ummi, Ummi ta fito daga bedroom dinta jin sallama, ganinsu tace "Aa sannunku da xuwa" duk suka xauna suka gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ku kadai?" Maimoon tace "Eh Umma ce ta aiko mu gun Hajja" Ummi tace "Ohk, ya karatu Jiddah" Jiddah ta kalleta ta d'an yi murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Maimoon tace "Ramlah ta koma ne Ummi?" Ummi tace "Aa tana ciki tana bacci" Maimoon tace "Toh bari mu kai ma Hajja mu dawo" Ummi tace "Ohk" mikewa tayi jiddah ma ta tashi suka fita daga parlon, dakin da Hajja ke sauka idan tana garin Maimoon ta nufa Jiddah na biye da ita, Maimoon tayi sallama bakin kofar sannan ta bude, Hajja ta daga kai tana amsa sallaman, karasawa ciki Maimoon tayi ta duka tace "Ina kwana Hajja" bata jira ta amsa ba ta kalli Abuturrab dake xaune dakin yana kallonsu daga sama har kasa ta cikin glass din idonsa, ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana yaya?" Yace "Me yasa baki ajiye mayafin a gida kin fito haka ba?" Maimoon ta hau gyara mayafin jikinta tana murmushi, Jiddah dai kanta na kasa ta durkusa ita ma ta gaida Hajja, sannan ta d'an kallesa taga wayarsa yake dannawa tace "Ina kwana" Ya kara wayar a kunne ya mike ya nufi kofa, Hajja ta saki baki tana kallonsa har ya fita, can ta kalli Jiddah tace "Ji ruba66e, toh ke idan ba dai neman wajen xama kike ba meye na gaishesa bayan iyayensa sun sa ya sakeki babu ko dar ya cike takarda ya mika maki, ai babu abinda kika hada da shi kuma yanxu, toh ga dai shi ya gwaleki, tun jiya fa na samu labarin dawowar almurin amma kun ga sai yanxu ya shigo gaidani yana shan kamshi ya wani sha uban gilashi kamar sabon makaho, Aa bak'in halinsa ya fi karfinsa gaskiya, alhalin sbda shi nake xaune har yau a gidan nan ban koma masar ba, to Hafsah ta ce min sati me xuwa xa a kai kudi gidan yarinyar da yake so da aure amma in ja bakina inyi shiru tunda ba a gaya min ba tukun, shine yasa nake ta xaune nan Allah" Maimoon dai sai murmushi take, Hajja tace "Toh aiko ku Ramlan tayi?" Maimoon ta ajiye mata ledan kusa da ita tace "Ehh tace mu kawo maki wannan" Hajja ta leka cikin ledan tace "Ahh da kyau, baiwar Allah nace mata gobe xan tafi shine ta bada tsaraba a kawo min, to tafiya ai ta lalace tunda auren Aliyu ya tunkaro, yanxu shigowarsa nake tambayarsa shi ma ya tabbatar min da haka ne" Jiddah dai sai kallon Hajja take, Maimoon tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Hajja tace "Ameen, ita ma Ramlah gata can ta xo tun shekaranjiya, kilan mijin baya nan, amma da kyar idan ba ciki ne da ita ba, kai cikin ne ma wllh, sai wani salalo salalo take" Maimoon ta kalli wayarta dake ring ta mike tace "Xa mu koma Hajja, sbda muna da Islamiyya karfe biyu" Hajja tace "Toh ai shkkn, anjima xan sa Aliyu ya kawoni in mata godiya idan ya ga dama kenan, kabu kabu fa yake amma jin kansa yake kamar me wani sana'ar arxiki baya ganin kowa da gashi, ga d'an banxan girman kai, ba ga masu kabu kabun ba muna ganinsu a tashar mota, ga yan acaba suma ai duk kabu kabun ce, to kuma waye shi Allah na tuba" Su dai basu ce mata komai ba suka fita dakin, sai a snn Maimoon ta mika ma Jiddah wayar tace "Yousuf" Jiddah ta amsa ta daga sannan ta kai kunne, murya kasa kasa Maimoon tace "Don Allah kice ya xo ya daukemu basu da nisa sosai daga nan" Tana fadin haka ta wuce bangaren Ummi, Jiddah ta nufi parlor, cikin sanyin muryarta tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, me Maimoon take rada maki?" Murmushi tayi ta xauna saman kujera tace "Aa babu komai, ya ciwon kan yayi sauki?" Yace "Alhmdlh, ya su Umma?" Tace "Umma tana gida" Yace "Ku kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gidansu Aunty Ramlah" Yace "Ohk, yaushe xaku koma gida?" Tace "Karfe biyu xa mu tafi Islamiyya" Yace "Baxa ku dade ba kenan?" Tace "Eh" yace "Toh in xo in maidaku gida?" Ta d'an yi shiru, yace "Kin fa ce kin daina taurin kai" D'an murmushin tayi ta kwantar da kanta jikin kujera dai dai nan suka yi ido hudu da Abuturrab dake xaune dinning area din parlon da laptop gabansa, wani faduwa taji gabanta yayi, Yousuf yace "Kinyi shiru" Ta dago kanta tace "Toh sai ka xo" Yace "Good, in few minutes time xan iso yanxu in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh" Katse wayar yayi, ta dinga kallon screen din, can ta saci kallon Abuturrab taga laptop dinsa yake dannawa, ta mike ta wuce part din Ummi, ya bi ta da ido. Karfe daya saura Yousuf ya iso kofar gidansu Abuturrab, ganin xa a tada sallah ya sauka ya shiga masallacin kofar gidan, bayan an idar ya kira number Maimoon, Maimoon ta mika ma Jiddah, Jiddah na kai wa kunne yace "Ina waje ku fito" Jiddah tace "Toh" Katse wayar yayi, suka yi ma Ummi sallama a bedroom dinta sannan suka fita, gaban Maimoon ya fadi ganin Abuturrab da ya fito daga masallaci, amma taki yarda su hada ido, Jiddah kam bata ma gansa ba ta kalli Maimoon tace "Ke da kike son ya xo ya daukemu ai ke xaki yi jagora" Maimoon tace "Don Allah ke dai mu je" Jiddah ta fara tafiya Maimoon na biye da ita, ta bude front seat ta shiga, Maimoon ta shiga baya, sai a sannan Jiddah ta ga Abuturrab da ya tsaya yana kallonsu, Yousuf da ya gansa shi ma yace "Ba yayan nan naku bane wancan" Maimoon ta kirki murmushin karfin hali tace "Ehh, kaje gu gaisa ya Yousuf sai kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu" Ta madubi ya kalleta ta kara kirkiran murmushi, Jiddah dai taki yarda ta sake kallon wajen motar, Yousuf ya bude motar ya sauka ya nufi gun Abuturrab da ya kara waya a kunne roaming about the gate, hannu ya mika masa hade da sallama yana kallonsa, Abuturrab yyi stretching nasa hannun, nan suka gaisa sannan yousuf ya juya ya koma gun motarsa, yana shiga motar Maimoon da duk hankalinta ya tashi tace "Kace masa Umma ce tace ka xo ka daukemu?" Yousuf yace "He don't have any business with that" Maimoon bata kuma cewa komai ba, ya tada motarsa suka bar anguwar. Hansai ce xaune da aminiyarta Zulai gaban wani katon mutumi da babu riga jikinsa, Hansai duk ta baxa kunnuwa da idanuwa tana jiran jin abinda xai ce bayan ya gama dube dubensa, Mutumin ya kalleta da idanuwansa da aka lafta ma uban kwalli yana girgixa kai cikin katon muryarsa yace "Babu wani aure a kan yarinya, amma tana can cikin kwanciyar hankali da daula... Bata da wani matsala a rayuwa, ba abinda ta rasa..." Hansai ta sharce wani bakin xufa a goshinta tace "Toh Malam babu abinda xa ayi da xai sa hankalinta ya karkato ta dawo gida, idan ya so sai a maida min Bibalo can, wllh Malam ina fama da bakar talauci yanxu, jarin babu shi babu dalilinsa kamar dai kar ta bar wajen yarinyar, ga basussukan jama'a a kaina suna min tonon asiri har na fara tunanin in siyar da d'an gidan da muke ciki in biya bashi sai mu kama haya da sauran, in sake jan wani jari, to amma gidan fa duk ya ru6e, wa xai siya da mutunci" Mutumin wanda da alama ya gaji da surutunta yace "Ki fadi abinda kike so ayi a takaice" Hansai ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Kaga Malam so nake kayi duk abinda xai dawo min da ita duk inda take, ta dawo wajena ni ban k'i ko karuwanci ma ta xo ta min ba mu samu na rufa ma kai asiri, nasan dai yanxu karya ne ace bata san maxa ba, dama gata da kyau ga farin jini wllh kasuwa xa mu yi sosai" Zulai sai gyada kai take, Mutumin yace "An gama, dubu hamsin kudin aikin ki" Zulai ta dafe kirji tace "Dubu ashirin fa Malam, ina nagansa? Bani da shi bani da dalilinsa wllh, ko dubi daya na kaina bana magani yanxu" Yace "Toh ku tashi ku tafi duk ranan da ku ka shirya ku dawo" Xata yi magana cikin tsawa yace "Ku fita nace sai kun shirya" Da sauri suka mike suka fita a d'an dakin, Hansai ta fashe da kuka tace "Yanxu ya xanyi Zulai, kema kinsan bani da ko dubu biyu na kaina wllh, duk na siyar da kayan dakina babu komai balle in dauka in siyar" Zulai tace "Daga karshe dai gidan nan kawai xaki siyar in dai bukata xai biya, in har Jiddah ta dawo ai sai kin kera wanda ya fi wannan a cikin gari, dama ba sai an 6ata ake gyarawa ba, kawai mu je a sa gida a kasuwa..." Hansai ta share idonta tace "Toh shkkn, in sha Allahu baxan ji kunya ba" Daren ranan Jiddah na karatu a dinning kamar yanda ta saba bayan magrib aka bude kofar parlon, Hajja ce ta shigo sakale da jakarta tace "Assalamu alaikum" Jiddah ta amsa sallaman tana mata sannu da xuwa, Hajja tace "Ina Ramlan take?" jiddah ta mike tace "Tana daki bari in mata magana" Hajja tace "Toh yi maxa wancan d'an daban sai ya iya tafiya ya kyaleni, kinsan dama da kyar ya kawoni sai da uban ya sa baki" Jiddah dai bata ce komai ba ta tafi dakin Umma, ba a dau lkci ba Umma ta fito sanye da Hijab da murmushi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Yauwa Ramlah daxu naga abun arxiki shine nace bari dai in taso in xo da kaina inyi godiya, don mu a Masar haka ake, Allah yayi maki albarka ya kara arxiki sai dai tafiyar ma ta lalace don wannan yaro Aliyu gobe xa a kai kudin aurensa kuma ina nan har sai anyi komai idan Allah ya yrda" Umma tace "Allah sarki, ai da kinyi waya na xo kawai Hajja ba sai kin fito da daddaren nan ba" Hajja tace "Aa barni na xo, banda me sonka wa xai tuna da kai har ya baka tsaraba haka..." Tana kai wa nan ta mike tace "Toh ni dai bari in koma ni da wancan d'an kabu kabun ne muka xo kar ya tafi ya barni in rasa tudun dafawa" Umma tace "Tare da Aliyu ku ke?" Hajja tace "Ehh wllh, sai da ma ya xageni a hanya muna tahowa daga nace masa ba jirgi fa yake figa haka ba, ni dai bakina alaikum naki biye masa ya kunyata ni a kasar mutane" Umma tace "Amma yace wani abu, shine baxai shigo ya gaisheni ba??" Hajja tace "Ahaf ai wannan mutumi dai daga d'an iska sai shi, baya ganin kowa da gashi" Umma ta kira Huraira a daki tace "Tafi kice ma Abuturrab ina kiransa a waje" Tace "Toh" sannan ta fita, Hajja ta koma ta xauna tace "Gwara dai kiyi masa soso da sabulu sannan ki hadani da d'an arxiki ya maidani gida kar kasheni a hanya" Umma dai bata ce komai ba, Maimoon ta fito tare da Safiyya suka gaidata, Hajja tace "Allah maku albarka, ya baku ilimi me amfani" Jiddah dai tuni ta koma ta ci gaba da karatunta a dining, Ba a dau lkci ba Abuturrab ya shigo parlon kansa a kasa, Ya karaso ciki ya gaida Umma da ladabi tace "Saboda ka isa yasa ka xo gidan nan ka xauna mota baka shigo gaisheni ba?" Ya ki kallonta a ido, yana kame kame yace "Aa waya nake yi a motar dama xan shigo Umma" Hajja tace "Karya yake algungumi har cewa yayi minti biyar ya bani wllh, ni dai ki hadani da me hankali ya maidani gidan d'a na don Aliyu abun tsoro ne, babu uwar da na hada dashi balle ya cuceni, gashi uwar tayi ta xuba masa ido kamar tana tsoronsa bata fada masa gaskiya, ita kuma yar Benuen can tayi kane kane a kan lamarinsa, ai ni ina ganin iftila'i tunda ja sauka gidan Usman, abubuwa suke babu tsari kamar dai gantalallu" Abuturrab dai sai kallonta yake ta gefen ido, Umma tace "Toh ka kyauta, from henceforth i don't want to see ur legs in my house again, get out" Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi kofa ya fita, Jiddah ta bi sa da kallo, Hajja ta ajiye jakanta ta cire mayafinta ta linke ta ajiye, ta gyara xama tace "Dama idan babu me mayar dani gida sai dai in kwana a nan kawai, baxan bi mutumin can ba abu ya lalace min" Maimoon ta fashe da dariya Hajja ta marairaice tace "Allah kuwa ke baki ga yanda ya wani fita kamar Zaki ba daga fadan gaskiya" Umma tace "Kiyi xamanki kawai a nan Hajja" Hajja tace "Toh a kai min kayana daki" Karfe tara da rabi Umma na dakinta tare da Jiddah dake gyara mata press din kayanta, Umma tayi dialing number yayarta, nan kuma ta sanar mata duk abinda Aliyu yayi mata daxu, Ummi tace "Kiyi hakuri Ramlah, Ni yayi ma ba ke ba, kinsan wannan xancen auren da ya kirkiro ma kansa da Hafsah kawai suke sabgarsu, ban san komai a kai ba, uban ne ma yace min gobe xa su kai kudi, wllh bai ce min komai ba shi har yanxu" Umma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya ina ta ce maki a tashi tsaye kince Aa ba komai, wllh wannan abu ba lafiya a ciki, ga dai abu kiri kiri fa" Ummi tace "Aa ki kyalesu kawai, shi ba yaro bane kuma sarai da hankalinsa, abinda kike tunani ba shi bane, shi dai ne ya xabar ma kansa haka, ai ba shi daya na haifa ba dai? Dama shi da namiji ai wasu kake haifa ma" Umma tace "Ki kyaleni da shi xan saita masa xama wllh" Sun jima sosai suna waya, Jiddah dai duk sai bata ji dadi a ranta ba, taji kuma a xuciyarta tana son yi ma Abuturrab magana, to amma a ina xata gansa??
Leave a Comment