Jiddatul Khair 43
Jiddah ta sauke idonta daga kallonsa tana sake nanata sunansa a xuciyarta, Aliyu kenan yake nufi, Ali shi ma ai Aliyu ne... muryarsa ya katse tunaninta, taji yace "Wani anguwan xa ki?" Sake kallonsa tayi sannan tace "Malali...." tana fadin haka ta bude jakar hannunta da sauri jin waya na vibrate, sai a sannan ta tuna ai wayar Maimoon na wajenta tun daxu da Yousuf ya kira suka yi magana, ta fiddo wayar tana kallon screen din taga Ya Aliyu... Ta d'an kallesa tace "Nayi mantuwa na taho da wayar yar uwata xan mayar mata cikin gida yanxu" Yace "Ohh ohk, take ur time, bari in ajiye ki bakin gate and i will wait u there okay?" Dai dai gate din gidan Aliyu ya tsaya ta bude motar ta sauka sannan ta shiga compound din tana tafiya a hankali, wayar har ya katse ya sake kira, kafin ta shiga parlor ya sake katsewa, a nan gabanta ya hau faduwa tana tsoron kada ta sake ganin Aunty, da sauri ta wuce sama ta bude dakin da su Maimoon suke, duk suka juya suna kallonta, Maimoon tace "Kin fasa tafiyar kenan" karasawa tayi tace "Na mance na tafi da wayarki ashe a jakata, kuma ana ta kiranki amma dai ya katse.." Maimoon ta xaro ido tana kallon wayar da Jiddah ke mika mata tace "Lahh ashe wayar na gun ki na xata yana caji, wa ke kira?" Lkci daya mood din Maimoon ya canxa ganin me kiranta, cike da damuwa tace "Ni dai na shiga uku, wai ya Aliyu ke kirana, to me yasa?" Dagawa tayi ta kai kunne fuska daure, Kafin tace komai yace "Kuna ina?" Ta turo baki tace "Aa muna nan gidan amarya yaya..." Yace "Ke da wa da wa?" Tace "Ni, Aunty Safiyya, Aunty Ramlah, Nafisah, Aisha da Yusra, sai Jiddah amma ita xata wuce gida ynxu, mu kuma muna son mu kwana ne" murya can kasa tace suna son su kwanan don bata san me xai ce ba, instead sai taji yace "Wacece xata tafi?" Ta kalli Jiddah da har ta nufi kofa ta fita, tace "Jiddah" Yace "Xata tafi ina?" Maimoon tace "Wai gida, tace ita baxata kwana ba" yace "Gidan da babu kowa?" Maimoon tace "Nima dai haka na gani... Amma Ummi na nan ai" Yace "Bata wayar" ta mike da sauri tace "Toh bari in kai mata ta fita yanxu" Yace "Do that quickly" cikin hanxari Maimoon ta fita dai dai second stairs taga Jiddah a tsaye tana kallon parlor, Jiddah da bata ma san Maimoon ta fito daki ba, ta sauke idonta daga kallon da take ma 3 seater din parlon, ta ci gaba da sauka downstairs a hankali, Maimoon ta kwalo mata kira tace "Yaya xai maki magana" Daga haka ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar, amsa Jiddah tayi tana kallon screen din sannan ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "Ina xa ki?" Tace "Gida" yace "Toh kar ki kuskura ki fita daga gidan nan ba tare da su Maimoon ba" shiru tayi ta ma rasa abinda xata ce, a takaice yace "Bata wayar" Ta mika ma Maimoon wayar, daga daya bangaren yace "Nafisah dama xan yi ma magana kai mata wayar yanxu" Maimoon tace "Toh" daga haka ta juya ta tafi kai ma Nafisah waya a daki ranta fari tass bai ce su wuce gida ba duk da ta sanar da shi xa su kwana, Gaba daya mood din Jiddah ya canxa, ta ci gaba da sauka a hankali ta nufi kofar parlon ta fita, har sannan Ali na jiranta bakin gate, ta karasa kusa da motar don glass a sauke yake, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri don Allah brother dinmu yace mu kwana a nan kawai" Yace "Ohh really, to shkkn Jiddah, can i get ur digit plss?" Tace "Bana rike waya ae" ya xaro ido yana kallonta, yace "Saboda me?" Sincerely tace "Karatu nake yanxu" kallonta yake yi da kyau, but come to think of her age kamar ynda ya kiyasta a ransa sae ya yrda da abinda tace, ya shafa lallausan gashin kansa yace "Then how will i be contacting u?" Tayi shiru, yace "Amma yar uwarki na da waya ita ai" Tace "Ehh ai ta girmeni" Yace "Ohh ok, gobe da karfe nawa xa ku bar nan?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Toh xanyi sallama da safe hope it's okay?" Ta xaro ido tace "Aa idan yayanmu na nan fa" yace "Ohk sai yayi maki fada?" Ta gyada masa kai, shiru yayi, can yace "Okay then xan turo kanwata Khaleesat, she is just ur mate i guess, and kuna yanayi da ita sosai, ranan farko da na ganki a balcony daga nesa sai na ga kamar ita but i know i was mistaken coz tana boarding schl... She is available now sun yi hutu, and i want u two to be frnds..." Tayi murmushin karfin hali tace "Toh" Yace "Let me not keep u standing in sha Allah xata shigo da safe sai ta baki waya mu yi magana okay?" a hankali tace "Allah ya kai mu" murmushinsa me kyau yyi mata ta juya ta shiga compound din gidan, a parlor ta ci karo da Aunty da kawayen Aneesah rike da warmer din abinci iri iri sun fito daga kitchen, Da mamaki Aunty ta tsaya tana kallon Jiddah, can ta ajiye babban warmer din hannunta tana kallon hanyar stairs ta nufota, Jiddah ta fara komawa baya gabanta na faduwa, Aunty na nunata da yatsa tace "Wai ke wacce irin natattciya ce mayya? Ban koreki daga gidan nan ba kika kara dawowa don ubanki, kin ga wani bare a nan banda ke? Duk fa babu bare a gidan nan wllh, Me kika sake dawowa yi banda rashin xuciya don Allah, idan muna abu na family me yasa xaki dinga cusa kanki, wllh tunda nake ban ta6a ganin me naci mara xuciya irinki ba.. ke a wa xaki biyo jama'a xuwa gidan nan idan ba kin yada xuciyarki kare ya lashe ba, bamu hada komai dake ba fa, babu dangin iya balle na baba, yar talakawa dake ma idan ba kaddara ba da kuma Aliyu da ya ja mana wannan masifa da fitina me xai shigo dake irin wannan family din, ke kin ma samu waje ko waiwayon kauyanku baki yi kin shigo birni ko..." Jiddah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, duk kawayen Aneesah na tsaye parlon suna kallonsu da alamar abun ya masu dadi, Aunty ta bude kofa ta hankadata waje a fusace tace "Fita ki bar gidan nan don uwarki, wllh kika sake dawowa sai na kwara maki tafasasshen ruwan xafi sai dai duk abinda xai faru ya faru" Juyawa Jiddah tayi ta fara tafiya, taji xuciyarta yayi mata rauni sosai, tun da aka fara shirin kai amarya dama tace ita baxata ba amma Hajja tayi ta fada wai ita ma xata fara koyon mugun hali irin nasu Aisha da Maimoon, xata fara yi ma mutane musu da taurin kai, haka ne yasa bata sake cewa komai ba aka shirya da ita aka tafi kai Aneesah, banda wannan bata tashi da intention din bin yan kai amarya ba don karatu ma tayi niyyar yi idan an tafi, da gefen hannunta ta share hawayen da ya gangaro fuskarta me xafi, tana fitowa kofar gida ta nufi titi da kafa, ta fi minti goma a tsaye tana jiran adaidaita sahu kafin ta samu daga karshe, har suka isa gida hankalinta baya jikinta, ta sauka ta basa kudi, snn ta juya xata shiga gate dai dai fitowar Aliyu daga gate din rike da makullin motarsa, kana ganin fuskarta kasan tayi kuka duk da ba me yawa ba, daga sama har kasa yake kallonta, yace "Tafi wajen motata ki jirani" cikin sanyin murya tace "Me xanyi a can? Don Allah ka barni in shiga gida" Yace "Are u questioning me?" Juyawa tayi ta nufi motar walking slowly, har ta isa gun motar ta tsaya, sai a sannan ya nufi motar ya bude back seat yana kallonta, hawaye ya kawo idonta tana kokarin ganin bai xubo ba cikin rawan murya tace "Don Allah ni baxan shiga ba, ka barni in je inyi sallah" Ya dinga kallonta, sai kuma ta juya masa baya ta fara kukan dake cin ta, sai a lkcn maganganun Aunty ke mata xafi sosai a xuciyarta, taji she really wants to go back to Hansai, don ita kadai ce idan tayi mata bata kuka kuma bata Jin xafi a ranta tunda a ko da yaushe kallon mahaifiyarta take mata, ita ta taso ta gani a matsayin baabarta, kuma ita take ma kallon baabarta, Kallonta Abuturrab ya dinga yi cause kana jin yanda take kukan kasan she is hurt, bin wajen yayi da kallo sannan ya kama hannunta ya shigar da ita motar, ta hade kanta da gwiwa tana rera kuka, ya xauna gefenta ya kulle motar yana kallonta yace "Jiddah" kin dagowa tayi, ya dago kanta yace "Me aka maki?" Girgixa masa kai kawai tayi, yace "Aunty ko?" Nan ma ta girgixa masa kai kawai, Tsawa yayi mata yace "Baxa ki bude baki ki min magana ba" ta kuma rushe masa da kuka, ya kamo hannunta yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace "Clean of those tears..." Bata masa musu ba ta amsa amma bata goge idon ba, ya karbe a hannunta ya fara share mata idon yace "Me Auntyn ta maki?" Taki ce masa komai, bayan few seconds yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" Kamar jiran jin hakan take ta hade kai da gwiwa ta fara sabon kuka, ya dagota ya hade rai yace "Ba nace kiyi hakuri ba?" Cikin shessheka tace "Dama nace ma Hajja baxan je ba shine ta sa sai naje..." Bai ce mata komai ba sai kallonta yake but he is boiling from inside, mota ce tayi parking dai dai kofar gate aka bude motar Aunty ta sakko da wasu kawayenta suna ta labari, ya dinga kallonsu har suka shige cikin gida, Jiddah taji hankalinta ya tashi ganin Aunty ta dawo gidan, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah ko xaka kai ni gidan Umma kilan ta koma gida..." Bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido ya shiga driver seat ya tada motar ya bar layin, a hanya aka yi ta kiran wayarsa, ya daga daga karshe, calmly yace "Kun ga Ahmad ni ba yaro bane da xa a wani jera dani kafin in shiga gidana, this isn't my first marriage, my first marriage ma babu wanda yayi min haka, i went home my self, don haka duk sanda nayi niyyar shiga gida xan shiga, yanxu ina wani sabgar ne..." Ahmad yace "Ohh really?" Abuturrab yace "Yes Ahmad, bana anguwan ma ni" Ahmad yace "To idan kaje gidan sai ka sallami kawayenta..." Abuturrab yace "Sun wahala in dai sallamata suke jira... xa mu yi magana good night" daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gidan Umma yayi parking ya kashe motar, Jiddah da taji wani relieve ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace "Sai da safe" Daga haka ta shiga gate din gidan ya bi ta da kallo. Gidansa ya wuce daga nan, Aneesah da kawayenta na daki banda complain babu abinda take, Fauziyya tace "Nima ban ta6a ganin haka ba wai kannin ango su wani xo gidan amarya suce xa su kwana ranan da aka kawota, wllh sai kinyi da gaske wajen tattaro hankalin mijinki gaba daya gareki ya share kowa ya daina ganin kowa sai ke, don wnn dangin nasa baxa su bari kiji dadin rayuwar aurenku ba" Aneesah tace "Baxa su bari in ji dadin rayuwar aurena ba??" Wani dariya tayi tace "Lokacin da shigowa gidan nan xae fara gagaransu xan kira in sanar maku, ni fa Captain da ku ke gani nawa ne ni kadai wllh, haka plan din yake dama" Naja tace "Atoh, dama wa xai xauna ya xuba ido, barin ma miji irin naki, wllh kar kiyi sanya Aneesah... Kowa tashi tsaye yake" Aneesah tace "Ni nasan bani da matsala da yan mata tunda nasan wanene captain, nasan root din matsalata a aurenmu kuma magancesa ba wani big deal bane wllh" Jin an bude kofar parlon duk suka yi tsit, Maimoon ta shigo cikin dakin tana wani cika tana batsewa tana kallonsu Fauziyya tace "Ya Aliyu yace idan kun gama xaman ku fito xa a maida ku can gida" Aneesah ta cire gyalen kanta da sauri tace "A maida su gida?? Budar kan fa??" Maimoon bata ko kalleta ba ta juya ta fice, Mikewa Aneesah tayi ta fice daga dakin bayan ta daura mayafi a kanta ta sauko downstairs, tsaye ta gansa a parlor, da mamaki tace "My Captain kace xa a maida su Fauziyya gida? As in how?" Yace "Ehh" ta daure fuska tace "Toh wai budan kan fa?" Calmly yace "Duk budewar nan da kika yi ma kan bai yi ba sai wani special one kike jira" Da mamaki take kallonsa, yace "Pls Aneesah I'm tired and i need rest now... idan xa su sakko in ajiyesu tare da su Maimoon su sakko, or i leave the house duk sanda suka tafi in dawo" Kallonsa kawai Aneesah take, sai ga su Maimoon da Aisha da Nafisa ko warce da jakarta a hannu tana cika tana batsewa suka sakko suka ma Aneesah sai da safe suka fita waje, juyawa yayi ya bi bayansu, ya fi minti goma xaune a mota yana jiran fitowar kawayen Aneesah uku amma shiru shiru, su Maimoon dai na xaune bayan mota, daga karshe ya tada motar ya maida su gida, ko sai da safen kirki Maimoon bata yi masa ba ta shige gate tare da su Aisha, sai a sannan tace "Da nace masa xamu kwana fa daxu bai ce komai ba don har cewa yayi in kai ma Jiddah wayar ita ma ta dawo ta kwana I don't know what made him Change his mind all of a sudden" Aisha dai sai ta6a bake take tace "To ba gashi dai mun dawo gidan ubanmu ba" Direct hotel Abuturrab ya wuce yyi lodging daki, sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kashe wayarsa. Har karfe biyun dare Aneesah bata yi bacci ba, bata ta6a xaton haka nata first night din xai kasance ba, yanxu duk abubuwan da aka ce tayi a wannan daren baxata yi ba kenan ya tashi a banxa, gashi tayi ta kiran layukansa duk a kashe, dama rashin mutuncin Aliyu ya kai haka bata sani ba, lallai kamar yanda aka ce mata xama ba nata bane, xaman kuwa ba nata bane, she needs to bring down Aliyu to d level she wants him to be for her, kawayenta uku na kwance saman gadon sun yi bacci abunsu hankali kwance, mikewa xaune tayi daga karshe ta fita parlor ta xauna tayi tagumi, duk irin burikan da ta ci ma daren nan ya tashi a banxa kenan?? a takaice sai wajen karfe hudu bacci barawo ya sace Aneesah, Washegari da safe aka kawo abinci daga can gidansu Abuturrab, Fauziyya ce ta bude kofar parlon ta amshi abincin a hannun su Safiyya ta kai masu can sama, bayan sun hada shayi me kauri ga uban kwai da dankali a gabansu Fauziyya tace "Wllh ki nuna ma Captain din nan bacin ranki, wacce amarya ce aka ta6a yi ma wnn walakancin da yayi maki, ni ko a tarihi wllh ban ta6a jin haka ba, kar ki kuskura ki amince masa duk dadin bakinsa sai kin gwara kansa shi ma kin rama... Wannan ai walakanci ne wllh, duk wani ango na xumudi a ranan da aka kai masa amarya amma banda naki angon...." Aneesah dai bata cewa komai amma gaba daya ranta a dagule yake, daga karshe ta mike ta dau wayarta ta fita, wani dakin ta shiga ta kulle ta yi dialing number Aunty, yana fara ringing Aunty ta daga tace "Amarya bakya laifi, har kun tashi? Fatan dai komai normal?" Aneesah ta fashe da kuka, Aunty ta xaro ido ta mike tsaye ta fita daga dakinta don akwai wasu baki, murya can kasa tace "Lafiya Aneesah me ya faru? Da matsala ne?" Cikin kuka Aneesah ta shiga ba Aunty labarin abinda Abuturrab yayi jiya, Aunty ta saki baki har Aneesah ta kai aya, can tace "Abinda ya maku kenan Aliyun?" Cikin kuka Aneesah tace "Wllh kuwa Aunty, ni da babu kawayena ma da baxan ji wnn kunyan da nake ji ba ynxu, duk fa sun san komai kar suje su yada ni a Abuja, har cewa suke ko a tarihi basu ta6a jin amaryar da aka yi ma wnn rashin mutuncin ba" Aunty da ranta ya dau tafarfasa tace "Shikenan, share hawayenki Aneesah, xan kiraki nan da anjima kadan, kiyi hakuri ko su Mumy kar ki sanar ma kinji!" Aneesah na shessheka tace "Toh" daga haka Aunty ta katse wayar tana wani huci ta hau dialing number Abuturrab taji a katse, rike baki tayi tana naxarin walakancin da xata masa, can tayi wani murmushi hade da kwafa ta koma daki xuciyarta na ci gaba da 6ararraka.... Karfe tara da yan mintuna Jiddah ta fito daga dakinsu sanye da kayan bacci dogo har kasa sai hula a kanta xata shiga kitchen, ita kadai ce a gidan sai Umma da Aunty Nafisah, su ma kuma basu tashi ba, Huraira na can gidansu Ummi bata dawo ba sbda aiki, tun asuba ta tashi ta gyara gidan gaba daya tayi wanke wanke ta share har balcony, ta tafasa ruwan Lipton da ta cika ma kayan kamshi ta juye a flask snn ta koma daki wajen karfe takwas amma bata yi bacci ba, yanxun ma yunwan da take ji ya sa ta fito xata hada shayi, bude kofar parlon taji anyi ta juya da sauri don tun da ta share waje ta shigo bata kulle kofar ba, da d'an mamaki take kallonsa, ya shigo parlon ya kulle kofar, sai da taga ya karaso cikin parlon ya xauna snn ta duka nan kasan carpet tana kallonsa tace "Ina kwana" har lkcn kayan jiya ne a jikinsa, ta mike don bata san ko ya amsa gaisuwar ko bai amsa ba ta koma daki ta saka hijab dinta snn ta fito ta wuce kitchen, mamakin abinda ya kawosa da sassafe ta dinga yi, ta dai hada shayi ta dau bread slice uku a kan glass plate snn ta fito har xata wuce dakinsu ta juyo taga kallonta yake, ta d'an tsaya tace "Xa a kawo maka shayi ne? Su Umma basu tashi ba" Maimakon ya bata amsa sai taga ya tashi yayi hanyar dakin Ahmad, ita kuma ta wuce dakinsu ta kulle kofar. Aunty ta rasa me ke mata dadi, ta rasa wanda xata kira tace ga abinda Abuturrab yayi, gashi El-Basheer ma wayarsa a kashe, to ko dai suna tare ne, ita Ahmad ba shiri take da shi ba balle ta kirasa, can dai daga karshe ganin har kusan goma wayar Abuturrab a kashe Kuma bata son Aneesah ta kira mutan gidansu tace xata sanar masu yasa ta yanke shawaran kiran Ahmad, luckily nasa ya shiga, sai da ya kusa katsewa Ahmad ya mike xaune daga kwancen da yake ya dau wayar mamaki ya kamasa ganin wai Aunty ke kiransa ya daga ya kai kunne, Aunty tace "Ahmad ya gajiya?" Yace "Ina kwana?" Tace "Lafiya lau, Aliyu fa?" Ahmad yace "Aliyu kuma? Ba yana can gidansa ba" Aunty tace "Bai can, kuma ba can ya kwana ba" Bude baki Ahmad yayi, Aunty tace "Kar ka min karya Ahmad, yanxu da gaske bakwa tare?" Ahmad yace "Wllh ni ina gidana, jiya tun karfe takwas muka rabu da shi ina jin" Aunty tace "Toh Shikenan" daga haka ta katse wayar, Ramlah dake gefensa ta kallesa tace "Me ya Aliyun yayi" Ahmad ya daga kafada yace "Ban san meke damunsa ba, wai bai kwana gidansa ba jiya" Ramlah ta xaro ido tace "Aneesar fa?" Ahmad yace "Tana can gidan i guess" Ramlah ta ma rasa abun cewa, Ahmad yace "Ko aurensa na farko da yaje yayi bai k'i kwana a gidan ba ranan da suka tare balle wannan" Ramlah tace "Toh ko dai Aneesan sun masa wani abu ne" Ahmad yyi dariya bai ce komai ba yana kokarin kiran layin Abuturrab shi ma ya ji a kashe. Karfe goma Jiddah ta fito ta ajiye cup da ta sha shayi a kitchen sannan ta dau wani cup din ta hada wani shayin, ta ajiye kan tray, kwai kwara uku ta soya da albasa shi ma ta daura a tray din, ta dau ledan slice bread din ta ajiye saman tray, sannan ta dau tray din ta fito, a hankali take tafiya xuwa dakin Ahmad, ta fi minti daya tsaye bakin kofar kamar me contemplating kafin tayi knocking a hankali, jin shiru ta sake kwankwasawa gently, bude kofar dakin aka yi ta koma baya tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta.....
Leave a Comment