Jiddatul Khair 44
Juyawa yayi ya koma cikin dakin, ta karasa ta ajiye tray din a saman carpet din dakin, sannan ta mike tana kallonsa tace "Ina kwana?" Dauke idonsa yyi ya koma ya xauna gefen gado, ta juya ta fita ta kullo masa dakin, ya kai hannu ya dafa kansa hade da lumshe ido. Karfe sha daya Jiddah ta fito dakinsu bayan tayi wanka ta shirya, Umma dake xaune parlor tare da Aunty Nafisah ta kalleta tace "Ke kin karya kuwa Jiddah?" Jiddah ta karaso ta duka kasa kusa da kujera tace "Eh Umma" Aunty Nafisah dai sai kallonta take, ita dai kawai taji tana son Jiddah ganin bata da wani alama na hayaniya sannan tana da respect, Umma tace "Toh tafi ki daura shinkafa... yanxu xaki ga ranan tayi" Jiddah tace "Toh" sannan ta mike ta nufi kitchen, Aunty Nafisah ta bi ta da kallo har ta shiga sannan ta kalli Umma tace "Tun da ta dawo nan bata koma gidansu ba amma?" Umma tace "Aa bata je ba, to me xata je tayi, her parents are late, kishiyar mamarta ce a gidan ai, and I don't think she knows any of her relative gaskiya" Aunty Nafisah ta buda ido sosai tace "Amma kuma da mamaki ace dangin iyayenta basu nemeta ba har yanxu ai ko, Ummi tace min kusan 2 nd half months kenan fa, ae baxa ace bata da wasu dangi ba..." Umma tace "Wannan kuma ae a gun Aliyu xa a samu information din nan, tunda mu ko gidan nasu ma bamu sani ba har yau balle wani nata, and i don't even think it's necessary for now nan gaba duk xata nemesu idan Allah ya yrda wannan dole ne, yanxu dai i want her to get educated first, hakan kadai ne gatan da xa a iya yi mata" Aunty Nafisah tace "Haka ne kuma, amma da na xo naga yarinyar ban so Aliyu ya saketa ba wllh, yarinya ce me hankali da natsuwa sosai, kin ga ai da Ummi tayi dacen surka ta gari, amma wannan mata da aka kai jiya banga alamar abun arxiki ba, don naga alamar idonta a tsakiyar kanta yake, snn na ga kamar suna da wani alaka da ban san na meye ba da Aunty kuma ban ji dadin hakan ba, idan ma don yana son auren wannan ne ya sa ya saki Jiddar ai da sai ya hadasu su biyun tunda Allah ya hore masa...." Umma ta ta6e baki tace "Wannan kuma shi ya jiyo, Jiddah dai tayi masa nisa sai hange daga nesa yanxu, dama Allah ya hadasu ne don ya fiddota daga kangin rayuwar da take ciki a gun kishiyar uwarta, mu kuma mu riketa, indan ta ni ce kada ma ya nuna ya ta6a saninta har abada" Aunty Nafisah ta girgixa kai tace "Aa kar ki ce haka Hajiya Ramlah, ai kuwa har gobe bata da kamarsa don shine silar duk wani abun alkhairi da xai sameta a rayuwa ko kuma ince yake kan samunta a rayuwa, ni da xai nutsu yasan inda ke masa ciwo ya maida hankalinsa ma yace xai maidata...." Umma ta kalleta da sauri tace "Ya maida ta ina?" Aunty Nafisah tace "Ya maidata dakinta suyi xaman aure, ai saki daya yayi mata ko??" Umma tayi wani dariya tace "Xancen kike so Nafisah, Ai Aliyu ya makara, ke kinga walakanci da cin kashin da ya dinga ma yarinyar nan? Wllh kare baxai ci ba, Ai shi da auren Jiddah kuma sai kilan ko a lahira idan ana auren, amma dai a nan duniya kam ya gama aurenta, babu wani abu da xai sake hadata da shi, yaje can ya rungumi matarsa da ya auro jiya" Aunty Nafisah tace "Aa kar kice haka Hajiya baki san ikon Allah ba..." Umma tace "Wllh wllh kinji rantsuwar musulmi ko Nafisah? Aliyu have nothing to do with this girl again, Allah xai fiddo mata da dai dai ita wanda xai ga mutuncinta ba wanda xai dinga da na sanin aurenta ba yana cusguna mata sbda wasu dalilansa mara tushe" Aunty Nafisah tace "Ai bata yi kama da warce aka cusguna ma ba Hajiya... Dama can shiru shiru ce yarinyar" Umma tace "Da kika xo kika ganta da kyan gani ba, karewa ma tun ranan da suka tare ya saketa, sakin walakanci, sannan ya ajiyeta a gidan sbda shi isasshe ne, yayi ta wahal da yar mutane kamar wani ya aikesa ya aurota tun farko, kawai ki bari Nafisah amma babu wani abu da xai sake hadata da Aliyu da izinin Allah, ba dai wajena take ba" Tsit Umma tayi duk suna kallon Abuturrab da ya fito daga dakin Ahmad... kananun kaya ne jikinsa hannunsa rike da phones dinsa, ya karaso cikin parlon ya xauna kafin yace komai Umma tace "Waye wannan???" Ya d'an kalleta sai kuma yyi murmushi yace "Ina kwana Umma" Kin amsawa tayi tana kallonsa with surprise, ya kalli Aunty Nafisah ita ma ya gaisheta, da mamaki tace "Yaushe ka shigo gidan nan Aliyu??" Yace "Daxu..." Umma tace "Ita kuma Amaryar fa?" Yace "Suna can da kawayenta" Umma tace "Da sassafe ka baro gidan kenan??" Yace "Ehh" Aunty Nafisah tace "Ikon Allah, to amma har yanxu ana yayin kawayen amarya su kwana gidan amarya ni Nafisah?? na xata an daina wannan jahilcin tuntuni ai..." Umma tace "Atoh nima shi na gani, da nayi magana Hafsah kirjin bikin ce min tayi ai Amaryar sun yi magana da Aliyun kuma ya amince kawayenta su kwana tun ma ba a kawota ba, dalilin da yasa na kama bakina nayi shiru kenan bana son tashin hankali, shi yasa da su Maimoon suka ce xasu kwana gidan nima bance komai ba, a raina nace kowa ma ya kwana tunda haka ne" Abuturrab dai kallon Umma kawai yake don basu yi haka da Aneesah ba, Aunty Nafisah tace "Aa gaskiya wannan ba yi bane kuma bai kamata ba, Allah kuma ya kyauta" Umma tace "Ameen dai, kayi breakfast dai koh?" Yace "Eh nayi..." tace "A can gidan aka kai maku?" Yace "Aa a nan nayi" Umma ta kalli kitchen sannan ta kallesa da mamaki tace "A ina ka ga breakfast din, mu yan gidan ma yanxu muka tashi ai" Ya shafa kansa yace "Aa ta kawo min..." Aunty Nafisah da Umma duk suka kalli kitchen din, dai dai nan Jiddah ta fito, Aunty Nafisah tace "Jiddar ce ta kawo maka kenan" Yace "Ehh" Umma dai bata sake cewa komai ba ta ci gaba da kallon tv abunta. Ana kiran azahar Jiddah na kitchen tana gyara kayan miya da xata yi blending tayi stew, Aunty Nafisah da Umma kuma na can daki aka bude kofar kitchen din, da sauri ta juya ya shigo ciki ya kulle kofar, jikin cabinet ya jingina ya rungume hannunsa yana kallonta, Tana ci gaba da gyara kayan miyan da take tace "Akwai abinda xa a baka ne?" Yace "Aa.." Ta d'an kallesa sannan ta ci gaba da aikinta yace "Ajiye aikin nan ki saurari maganar da xan maki" Ba musu ta ajiye wukar hannunta ta wanke hannunta a sink sannan ta juyo tana kallonsa, bai yarda sun hada ido ba, yace "Instructions uku xuwa hudu xan baki" Ita dai bata ce komai ba tana ta kallonsa, yace "Na farko cikin instructions din shine ni bana son kina gaisheni a duk inda xaki gan ni... na biyu kuma duk sanda kike da bukatan wani abu ko wani iri ne ki dau wayar Maimoon kiyi min text ba sai kin gaya ma Umma ko wani ba, that is my responsibility, na uku kuma duk sanda su Umma xa su je can gidan mu you look for excuse da xai sa baxa ki bi su ba, kafin in baki instruction din karshe ina son ki fara gaya min shekarunki" Jin tayi shiru ya hade rai yace "Magana nake maki, shekarunki nawa??" a hankali tace "Baabarmu tace sha bakwai" Yace "Ohk, akwai wani da yace maki kin isa ki dinga xama kin hira da maxa ne?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "To instruction din karshe kenan babu ruwanki da wani namiji koma waye shi, idan kuma aure kike so sai ki gaya min in ji, i will settle that" Tace "To amma kuma ae kace min kar in sake nuna ma na sanka, kuma yanxu gashi kana...." Katse ta yayi yace "Ae shi yasa nace ki daina gaisheni, kinga ae wanda baka sani bane baka gaishesa" tace "To kuma ai baxa ka so ka tambayi wanda baka sani ba yayi maka wani abun kuma..." Kallonta ya dinga yi da mamaki, tace "Tunda ban sanka ba ni baxan tambayeka ka min komai ba" yace "Amma ai ban sanki ba a lkcn da na taimakeki a hayin rigasa, why didn't u turn down d offer" ta d'an yi murmushi tace "Aa ka san ni mana, ai awara nake yi sannan kuma kana xuwa siya, kaga ai ka san ni..." Yace "To bari ki ji in gaya maki abinda baki sani ba, duk wani responsibilities dinki har gobe a kaina yake sbda wani dalili da ban...." Bude kofar kitchen din aka yi duk suka juya, ya fasa karasa abinda xai fada, Umma ta shigo kitchen din, ko kallonsu bata yi ba ta dau abinda xata dauka ta fita, Abuturrab ya kalli Jiddah yace "Na gama gaya maki abinda xan gaya maki" Daga haka ya juya ya fice daga kitchen din ta bi sa da kallo. Makullin motarsa ya dauka a dakin Ahmad ya fita ya bar gidan bai sallami kowa ba... Umma ce xaune daki inda take shiga ba nan take fita ba tana kallon Jiddah dake durkushe saman carpet ta sunkuyar da kanta ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, Umma tace "To idan har baxan dinga gaya maki ki ji ba to xa a fara jin kanmu wllh, ina ruwanki da shi da har xaki ma tsaya ki sauraresa daga farko? Meye hadin ki da shi??" Cikin sanyin murya tace "Umma kiyi hakuri baxan sake ba in sha Allah" Ita dai Aunty Nafisah na tsaye jikin mirror tana kallonsu, Umma tace "Ke duk cin mutuncin da ya maki har kin mance da xaki sauraresa idan ba wauta da rashin sanin ciwon kai irin naki ba??" Jiddah ta girgixa mata kai kawai, Umma tace "Toh tashi ki fita, shi kuma xan ga uban da xai sake dawowa da shi gidan nan ai..." Mikewa Jiddah tayi ta fita, sai da ta kulle kofar Aunty Nafisah tace "Hajiya ni ban ga wani aibu ba don yayi magana da ita, ba fa rabuwar tijara ko rashin mutunci suka yi ba,, assuming he meant any harm toward her da tun farko bai shiga rayuwarta da xummar taimaka mata ba har ma iyayensa su santa, kawai dai abubuwa sun faru ne yanda Allah ya tsara amma kar kice xaki raba xumuncinsu...." Umma tace "Ni fa bance ta masa rashin kunya ko taki girmama sa ba Nafisah, kawai so nake ta rike maraicinta tayi abinda ke gabanta wato karatu, ganin cewar ita ba class dinsa bane yasa yayi mata duk abinda ya mata ba wani abu ba, ba gashi dai yanxu ya auri class din tasa ba, to a kan me xa ta ci gaba da sauraronsa?" Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta" Umma tace "Ameen" Aneesah na xaune parlor tare da kawayenta uku dake ta shirye shiryen tafiya, duk sun cika parlon da surutu ita dai bin su kawai take da um um, amma tayi nisa tunanin da take, duk da how moody she is throughout d day bata yarda kawayenta sun lura ba, bude kofar parlon aka yi duk suka daga kai, Abuturrab ya shigo da sallama da shi kadai yaji kayansa, kallonsa Aneesah ta dinga yi babu ko kiftawa, ya karasa cikin parlon yana kallonsu Fauziyya with smile on his face yace "Kun yini lafiya" Fauziyya tace "Lafiya lau ango, jiya kuma sai muka ji ku shiru shiru kai da abokanka..." Abuturrab yace "Ohh yeah, toh kun ki bar min mata ku tafi, and all my frnds that are suppose to escort me sun koma saboda aiki, shi yasa nace to bari dai nasan xuwa yau xa ku tafi ku bar min amaryata, na daga kafa jiya, amma ashe i am mistaken kuna nan dai" Dariya duk suka yi banda Aneesah da ta kauda kanta imagining how to punish him, Fauziyya tace "Da ka kwantar da hankalinka ma yanxu shiryawa muke xa mu wuce in sha Allahu" Yyi murmushi yace "Toh ba sai na haura sama ba kenan bari in jira ku a mota, sai in ajiye ku train station...." Naja tace "Mun ko gode Captain" Ya d'an saci kallon Aneesah suka hada ido ya kashe mata one eye, ta wani sha kunu, ya juya ya fita parlon, har bakin motarsa ta raka kawayen nata da jakunkunan kayansu, a kan kafada ta yafa gyalen yyi mata kallo daya ya kauda kai duk kawayenta suka shiga motar suka sallami juna sannan ya kalleta sai na dawo, bata tanka sa ba ta shige gate din gidan, ya ja motarsa ya wuce. Aneesah na komawa ciki ta haura sama ta shiga parlonsa ta dau wayarta ta kira Aunty, aunty na dagawa tace "Ya dawo?" Tace "Ehh yanxu ya shigo, amma ya tafi kai su Fauziyya tashan jirgin kasa" Aunty tace "Toh kar ki wani nuna masa komai, kiyi kamar abinda yayi jiya bai baki haushi ba kinji, kiyi hakuri... Sannan ki kula duk yanda Safara'u ta ce maki haka xaki yi anjima kada ki yarda mistake ya shiga..." Aneesah tayi kasa da murya tace "Amma Aunty he is so smart kin sani" Aunty tace "Smart din banxa, ke dai kiyi abinda aka ce maki kawai" tace "Toh shkkn" Aunty tace "Yanxu dai kawai muyi waya gobe" Aneesah tace "Allah ya kai mu" Daga haka ta katse wayar, shiru tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi murmushi ta mike ta shiga daki. Abuturrab na ajiye su a train station din rigasa ya ciro dubu ashirin din da yayi withdraw kafin ya je gida ya mika masu, nan kuma yayi masu sallama yayi wucewarsa ba tare da ya damu yasan ko akwai jirgin ko babu ba, a ransa yace idan ma babu sai su wuce park, a hankali yake driving ya shiga d'an layin wanda ke shimfide da kwalta, dai dai layin gidan mai anguwa ya samu waje yayi parking sannan ya sauka ya karasa layin da kafarsa, saman tabarman dake kofar gidan ya xauna bayan ya gaisa da dattijan da suka wayesa a wajen, yana jiran mai anguwan da aka ce masa ya shiga gida ya fito yanxu, wani dattijo yace "Ya iyalin naka?" Abuturrab yace "Lafiya lau Alhmdlh" Dattijon yace "Madallah, Allah ya maka albarka" Abuturrab ya sunkui da kansa yace "Ameen" ba a dau lkci ba mai anguwan ya fito, ganin Abuturrab yace "Ikon Allah, sannu da xuwa Malam Ali" Abuturrab ya gaishesa da ladabi bayan ya xauna, mai anguwa yace "Ya kaje gida ranan? Nayi ta kiran layinka baya shiga kuwa" Abuturrab yace "Allah sarki, Ina jin na kashe wayar ne" Mai anguwa yace "Toh madallah, ya aiki fa...." Abuturrab yace "Aiki Alhmdlh, Dama na xo tasha ne shine nace bari in karaso mu gaisa" Mai anguwa yace "Ai ko mun gode Malam Ali, ya iyalin taka dai?" Yace "Lafiya lau" Mai anguwa yace "Toh Allah ya kauda fitina, ya ci gaba sa baku xaman lafiya" Abuturrab ya amsa da "Ameen" sannan ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye nan gabansa yace "Toh xan koma in sha Allah, sai kuma wani lkcn" Mai anguwa ya rike ha6a yace "Baka gajiya Malam Ali??"
Leave a Comment