Jiddatul Khair 46

 


Bude kofar dakin nasa tayi ta shigo, ta gansa xaune daya side din gadon ya kunna laptop, ta kashe wutan daki ya daga kai yana kallon direction din da take, a nutse yace "Ban gama abinda nake ba Madam..." Barin wajen tayi ba tare da ta kunna ba ta taho ta hau saman gado, bai ce mata komai ba ya mike ya tafi ya kunna ya dawo ya ci gaba da danna laptop dinsa ya wani sha kunu kamar bai ta6a dariya ba, hakan ya sace mata gwiwan abinda tayi niyya, ta koma ta kwanta tayi lamo a kan gado... Har wajen sha biyu yana operating laptop bata ga alamar xai kwanta ba, ga bacci da ya fara damun idonta, nan duk ita jira take taga ya kashe laptop din ya kashe fitilun dakin sannan taga dubaran da xata iya amma shiru shiru har bacci yayi awon gaba da ita bata shirya ba, sai da ya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya kashe laptop dinsa ya rufe ya ajiye yana kallonta, dama akwai lkcn da xai yi aure da Aneesah gasu a daki daya yaji ba shi da feelings din yin komai tare da ita, he is getting irritated at the thought of having any affair with her, ya rasa dalili kuma upon how clean he knows she is, shi dai yasan duk xamansu tare da kwana gida tare da suke, bai ta6a sa ran xai yi tarayya da ita ba tare da sunyi aure ba, kawai sai d'an abinda ba ka rasa ba, but all of a sudden ya ji he is irritated at her, kashe wutan dakin yyi ya bude kofa ya fita ya koma parlor yayi kwanciyarsa saman 3 seater ya lumshe ido yasan this is just for a while Aneesah tana da tsaftar da baxai ji wani irritation ba.... Da asuba yana dawowa masallaci bai hau sama ba yayi kwanciyarsa downstairs, sai karfe tara ya koma sama ga mamakinsa sai ya ganta xaune tsakiyar gado tana danna waya ko kayan baccin bata cire ba balle ace tayi wanka ko ta gyara daki, yanxu bedroom dinsa ne har nine ba gyara?? kallo daya yayi ma idanuwanta ya san kuka ta ci ba kadan ba, ya karasa dakin ya d'an kakkabe gefen bedsheet din ya xauna yana kallonta yace "You are angry at me right?" Kauda kai tayi taki cewa komai, yayi kasa da murya yace "Toh kiyi hakuri, but ina son mu yi magana ta fahimta da ke Aneesah" Ganin bata da niyyar juyowa balle ta kallesa ya mike ya koma daya side din nan ma ya kakkabe ya xauna yana kallonta ya kamo hannunta yace "There is something serious i want us to discuss...." Ita dai taki cewa komai, kamar me rada yace "Kar ki ga kamar ko bana son having affair tare da ke...." Ta fixge hannunta ta katse sa cikin fushi tace "Don't tell me anything" yace "No i need to pls, kema kinsan duk xuwan da kike yi gidana can Abuja iyakar abinda ke hadani dake romance, just that, kuma ban ta6a tsallake hakan ba, and now u are mine completely and i can do whatever i want with u, but sai dai I don't know... may be i was suppose to have told u this long ago Aneesah...." Ya d'an yi shiru, ganin kallon da take masa with much interest din son jin abinda xai ce, yayi kasa da murya a hankali yace "I have issues Aneesah..." kallonsa take ko kiftawa babu, can tace "Issues din me?" Yana wasa da hannunta a hankali yace "Issues with having intercourse" Tayi masa wani kallo tace "You must be kidding Aliyu, ni din ce ban sanka ba??" Yace "Aa baki san ni ba, ni ne nasan kai na, domin kina gani na kamar lafiyayye xai iya kasancewa ba haka bane... Don't be deceived by what u saw" Da mamaki take kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya langwabar da kai shi ma yana kallonta, ta girgixa kai da sauri tace "Ban gane ba Aliyu" yace "Meye baki gane ba?" Tace "Naga dai baka ta6a making Attempt din yi ba ai kaga ka kasa" Yace "Ehh ko ban ta6a making any attempt ba ai xan fahimci wanene ni with out making Attempt" Ta girgixa kai tace "Noo, ni ban ga haka a tare da kai ba, ko a sannan ma ni nasan karfin hali kawai kake yi kana kyaleni don kawai baka da yanda xaka yi kuma baka son kayi sabon Allah amma ba wai don kana da wani issues ba, u are more than healthy" Ya d'an yi murmushi yace "I am sorry i am telling u this late Aneesah, amma ina da issues wanda nake neman magani a kai har yanxu... I am sorry i am letting u know it now" Buda ido tayi sosai tana kallonsa, can tace "Wai kai a ina ka ta6a making Attempt kaga kana da issues?" Yace "Aneesah nace maki ba sai nayi making any attempt ba, i knew my self, i knew my issues long ago, yanxu dai ina son wannan ya xama babban sirrinmu ni dake plss Aneesah, nasan kin aureni ne ba don komai na ba sai don sona da kike, in sha Allah xan fara neman magani daga yanxu, komai xai dai daita in sha Allah, kinji my wife??" Kasa daina kallonsa Aneesah tayi da mugun mamaki, is Aliyu kidding her? Mutumin da take tsoro saboda yanda take ganin yanayinsa a duk sanda suke tare shine yanxu xai ce mata yana da issues, mutumin da duk da sonsa da maitarsa da take wani bangare na xuciyarta na mugun tsoron ranan haduwarsu tunda ta gama sanin komai game da shi... kamar ya san tunanin da take yayi kasa da murya yace "I don't know if i have deceived u with what u saw or what u imagine, kinsan babu yanda Allah baya abunsa, amma ni ai nasan baxaki ki xama da ni duk da wnn matsalar tawa ba Aneesah, nasan kina sona ne so na tsakani da Allah" Sounding so pissed off tace "Wai ban gane kana da matsala ba, matsalar me takamaimai, don ni a sanin da na maka ban sanka a me wata matsala ba, dama wai mutum na sanin yana da matsala bai yi making any effort ba?" Cikin sanyin murya yace "Dama abinda na guda kenan ya sa ban sanar maki ba tun farko, i was afraid kar kice xaki bar ni, but sai gashi maganganunki sun nuna hakan" Jawota yyi jikinsa yace "Kinga ba wai fa yana nufin i can't touch you ba, it's just that I can't make love with u, amma komai kike so ni xan maki...." Lamo tayi jikinsa ita dai tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta, a hankali yace "Say something Aneesah" Aneesah dai ta fada duniyar tunanin da ta tafi, ko ba komai tension guda daya ya sauka a kanta, cause she can't imagine dama idan Abuturrab ya gane she isn't a virgin, tun da aka kawota da wannan xullumin take xaune a gidan, shi sa take son ayi a wuce wajen hankalinta ya kwanta, tun ana sauran kwanaki bikin take ta fatan duk abinda suka yi da kudin da suka kashe bai tafi in vain ba, Girgixa kai tayi tana d'an murmushi tace "Ni kai nake so kuma xan xauna da kai a ko yaya kake my captain, amma kuma ai hakan baxai sa kace baxa ka dinga ta6ani ba ko?" Murmushi yyi duk da bata ganin fuskarsa yace "Sure xan maki duk abinda kike so mana Wife" Tayi kasa da murya tace "To amma kasan akwai abubuwan da idan ana yi ma mace xai sa tayi loosing virginity dinta ko?" Yace "Abubuwa kamar me?" Dago kai tayi ta kallesa ya wara mata ido yana sauraronta, a kunne ta rada masa, yace "Toh shkkn baxan maki shi ba, because i want to know u  a virgin" Gabanta taji ya fadi sosai, ta girgixa kai tace "Toh idan baka min ba ai kuma baka fita hakkina ba tunda ba dayan xaka dinga yi ba" Shi dai murmushi kawai yake yaki yace mata komai, ta shige jikinsa kamar xasu hade waje daya, nan da nan yaji kamar kunnasa take son yi, ya d'an koma baya, cike da shagwaba tace "Kayi shiru" Yace "Ohk i want this as a secret between we both Aneesah, sannan duk wata bukatarki na yau da kullum xan maki duk don ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri da yanda kika sameni" Ta lumshe idonta tace "In sha Allah my captain, i love you so much" Ya sauke wani boyayen ajiyar xuciya, yana sake kallon agogo wai har karfe goma saura mace na saman gadonta, kwantar da ita yayi ya mike yace "I want to take my bath, kinsan yau xan koma gun aiki fa" Ta xaro ido tace "Kai da ya kamata ka dau sati captain? Ko basu san aure kayi ba" Yace "No iyakar kwanakin da aka bani kenan, kinsan my first marriage an bani almost 2 weeks, and this is my second marriage...." Da mamaki take kallonsa kafin ta katse sa da sauri tace "Kai har kana da wani first marriage da kake tutiya da shi Captain?" Yace "Ohh toh ya xan kirasa? Aure ne shi ma ai" Ta hade rai tace "Wannan kuma ya rage naka, amma take note aurenmu shine first and last marriage dinka" Yana cire jallabiyar jikinsa yace "Toh ai wajen aiki babu ruwansu, a first marriage dina suka san wancan hutun da suka bani, wannan kuma second marriage..." Kallonsa kawai take from head to toe babu ko kiftawa, don Abuturrab ya kai namiji wanda ko wace mace xata so shi a matsayin mijinta, daga sama har kasa kawai take kallonsa tana sake imagining din discuss dinsu, wai yana da issues, Issues a hakan da take ganinsa? Kamar ya san tunanin da take ya juya yayi shigewarsa bandaki ya kulle, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin wani shaukinsa na taso mata, ta kwanta gefen gado hade da lumshe ido. Jiddah na tsaye dakinsu tana jera kayansu da mai wanki da guga ya kawo a press, Maimoon ce kwance dakin tana baccin wahala saboda cramps da ya sakota gaba ko boko bata je ba ranan, Jiddah kuma shigowarta kenan malamarta ta wuce, shine take gyaran kayan kafin Mu'allimarta na Islamiyya ta xo, Umma ce ta bude kofar dakin, tana kallon Maimoon tace "Ta samu bacci kenan" Jiddah tace "Ehh tayi bacci" Umma ta kalli Jiddah na few seconds kafin tace "Jiddah ki xo daki ki sameni idan kin gama" Jiddah tace "Toh" Umma ta juya ta fita, sai da Jiddah ta gama jera kayan nasu sannan ta fita xuwa dakin Umma, Umma na xaune kan arm chair dake dakin, Jiddah ta xauna saman carpet, duk da yanda gabanta ke faduwa don yawanci kiran Umma baya wuce warning xata mata, shima warning din a kan Abuturrab, to amma ai yau kusan wata kenan bata gansa da idonta ba, a hankali tace "Umma gani" Umma na kallonta tace "Jiddah baki ta6a xuwa kin sameni kince kina son Pad xakiyi al'ada ba" Jiddah ta sunkuyar da kanta a hankali amma bata ce komai ba, Umma tace "Ko baki fara ba ne?" Ta girgixa kai tace "Aa na ta6a yi sau biyu kuma ban sake yi ba" Umma tace "A ina kika ta6a yi?" Ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Ya dade, tun ina gun Baabarmu, lkcn ban daina xuwa islamiyya ba" Umma tace "Xai kai wata nawa?" Jiddah ta buda ido sosai tace "Umma xai yi kusan shekara biyu" Umma ta gyada kai tace "Ikon Allah, kuma shine baki sake ba har yau?" Jiddah tace "Eh" Umma tace "Toh tashi ki tafi" Mikewa tayi ta juya ta fita dakin, Umma ta bi ta da kallo tana tunanin meye ma'anar hakan, Jiddah na fita ta sauke ajiyar xuciya ita ko fata ta sake yi bata yi har abada, don bata mance wahalan da ta sha ba har sai da aka kaita chemist aka ta mata allurai, Iyah har ce mata tayi sumanta biyu. Ranan Friday da yamma Ahmad na xaune bedroom din Ummansa, ko minti talatin bai yi da shigowa ba Umma tace "Yauwa Ahmad ina son maka tambaya, Me ke janyo mace ta fara al'ada kuma ta daina sa ko ya dinga mata wasa?" Ahmad yyi shiru yana kallonta, can yace "Mace yar shekara nawa Umma?" Tace "Yarinya karama..."  Ahmad yace "Irregular period kenan..." Umma tace "Oho nima ba tambayarka nake ba" Ya shafa kansa yace "Mai aure ce ko mara aure Umma?" Umma tace "Aa bata da aure" yace "That could be Hormonal Imbalance, too high or too low Thyroid hormone level, wannan shine dalilin in har mara aure ce... " Umma tace "To yana da medications ne? I mean is there anything that could be done about it?" Yace "Ehh ba xa a rasa ba Umma, amma akai ko ma wacece asibiti xai fi" Umma tace "Toh Shikenan" Bai kuma cewa komai ba amma can kasan xuciyarsa ya san Jiddah ce Umma ke magana a kai, Umma ta shigo da wata hiran, sun jima suna magana kafin ya mike yace mata xai je gidan Abuturrab don yana gari, Umma tace "Toh sai ka dawo" Yace "Daga can xan tafi gida Umma, sai gobe xan shigo in sha Allah" Tace "To ka gaida Ramlah" Yace "Xata ji in sha Allah" Ahmad na fita wajajen karfe biyar Umma ta sa Jiddah ta shirya suka wuce asibiti, Basu suka dawo gida ba sai bayan magrib, magunguna kawai aka dora Jiddah a kai, xata wuce daki rike da ledan maganin, Umma da ta xauna parlor bayan ta cire Hijab dinta tace "Baki dai manta dosage din ba ko? Duk da an ma rubuta a jiki ai" Jiddah ta juyo tace "Ban manta ba Umma" Umma tace "Toh kar dai kiyi wasa da shan su, Allah ya sa a dace" Jiddah tace "Nagode Umma" Daga haka ta wuce dakinsu, Umma ta kashe ya fi dubu talatin a magungunan da aka rubuta ma Jiddah a asibitin da suka je. Washegari asabar tare Ahmad ya shigo gidansu da Abuturrab, babu yanda Ahmad bai yi da Abuturrab su tafi dakin Umma ba don tana ciki amma yaki ya xauna parlor wai xa su gaisa idan ta fito, Ahmad ya wuce dakin Ummar tasa, Maimoon ce ta fito daga dakinsu da uniform din Islamiyyarta fuskarta kunshe cikin nikab, ganin Abuturrab xaune a parlor tace "Ina yini yaya" Kai kawai ya gyada mata, ta murguda baki daga cikin Nikab din ta nufi kofa, Safiyya ma na fitowa ta gaishesa tayi hanyar kofa, Kallon kofar dakin kawai yake, sai ga Jiddah ta fito tana kokarin daura nata nikab din, suna hada ido tayi turus a inda take, sai kuma ta dauke kanta ta nufi kofa ta fita parlon ta kulle kofar, mikewa Abuturrab yayi ya nufi dakin Umma ya kwankwasa sannan ya bude yayi sallama, bai shiga can cikin dakin ba ya gaisheta da ladabi daga bakin kofar, ta amsa masa tana tambayarsa aiki, yace "Alhmdlh" Umma na kallon Ahmad yace "Yaran nan basu tafi makarantar har yanxu ba ko?" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, ta mike ganin fita xata yi Abuturrab ya bata hanya ta fita, dubawa tayi ko sun tafi ganin sun tafi din ta dawo, Abuturrab yace "Dama na xo gaisheki ne Umma sai anjima" Tace "Toh nagode" Yana kallon Ahmad yace "Mu yi waya" Daga haka ya juya ya fita, har su Maimoon sun kai bakin titi da kafa tunda ba driver xai kai su ba, yayi parking a gefe yana kallon Safiyya yace "Ku shigo inyi dropping dinku" Sake baki Maimoon tayi cikin Nikab din, tunda take xata iya cewa bata ta6a shiga motarsa ba, ko a hanya ya ganka da ka hau motarsa gwara ya baka kudin mota ko kuma yayi kamar bai ta6a saninka ba, Ita kanta Safiyya mamaki ya cikata, ta dai bude gaban motar ta shiga, Jiddah dai bata ji dadin shiga motan da yace su yi ba, Maimoon ta fara shiga sannan ita ma ta shiga, jikin door din motar Jiddah ta makale ko da wasa bata kalli inda yake ba, Yayi breaking silence din motar bayan sunyi nisa yace "Yaushe Siyama xata dawo?" Safiyya tace "Tab, ta fara karatu fa a can yaya" Yace "To maa sha Allah" Maimoon ce tayi masa kwatancen inda makarantar tasu yake, yana isa makarantar yayi parking bakin gate, Safiyya ce ta fara sauka tana masa godiya, Jiddah ta bude side dinta ba tare da ta kallesa ba ta sauka motar ta wuce cikin makaranta ya bi ta da kallo, Maimoon dake masa godiya taga ya bi Jiddah da kallo ta d'an kikkifta ido tana kallonsa, can dai ta sauka motar ta kulle masa ta bi bayansu Jiddah da sauri, dafe Jiddah tayi bayan sun shiga gate tana xaro ido tace "Jiddoh ya naga Captain ya bi ki da kallo???" Jiddah ta kalleta da sauri tace "Waye haka?" Maimoon ta fashe da dariya tace "Ya Aliyu mana, wllh ina ta ce masa mun gode tsabar yanda ya bi ki da eyes bai ma san ina magana ba Jiddoh" Safiyya dake jin su tayi dariya tace "Kallon godiyan da bata masa ba yake mata, naga ko kallonsa bata yi ba ta sauka abunta ta wuce, kilan abinda ya basa mamaki kenan ya bi ta da kallo" Maimoon tayi shakaf da hannu tace "Habaa... no wonder, I for say, wllh kinga wani kallon da ya bi ki da shi, kuma da gaske ne baki masa godiya ba wllh, next time kar ma kiyi gigin sake shiga motarsa don disgaki xai yi wllh" Jiddah ta ta6e baki tace "Wannan ma banyi niyyar shiga ba" Ahmad yayi ma Umma sallama xai fita tace "Yauwa ina son magana da kai Ahmad, kuma kar kuyi missing train ko?" Ya kalli agogon wrist dinsa ya koma ya xauna yace "Da d'an sauran time, ina jin ki Umma" Ramlah dake xaune gefen gadon Umma rike da handbag dinta ta tashi xata fita Umma ta kalleta tace "Ina kuma xa ki, dawo kiyi xaman ki" Ramlah tace "Aa Umma xan shiga bandaki ne" Daga haka ta fita, Umma tace "Ji shashasha" Shi dai Ahmad murmushi kawai yayi, Umma tace "Makarantar boarding nake son da a sama ma Jiddah, Cause her capacity is now more than mere lesson, tana da kokari sosai Ahmad fiye da yanda kake tunani, Malamar ma ta bada shawaran kawai ta tafi boko da mates dinta she now have a standard root" Ahmad yace "Boarding kuma Umma? why not day, ai bata da wasa balle ace taje boarding, sannan gwara day din saboda koyon abubuwan yau da kullum, irinsu girki, da dai sauransu Umma, Jiddah bata da hayaniyar da xata iya xama a boarding school gaskiya" Umma tace "To ai ba sai me hayaniya ke xuwa boarding ba Ahmad" Umma tace "Yanxu dai shawarata kike nema Umma, kuma shawaran da xan baki shine a samar mata day ta fara daga ss1, she can do it" Umma ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Toh shkkn" yace "Yauwa Umma, kinga baxa ayi depriving dinta from full Islamic education ba in jeka ka dawo ne" Umma tace "Kuma haka ne, amma wacce makarantar kake ga xa a saka ta?" Yace "Tunda su Maimoon sun kusa gamawa kawai a nema mata wani daban ita ma, akwai wata makaranta not to far away daga gidana ko a samar mata a can?" Umma tace "Aa gidanka yayi nisa sosai gaskiya" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh sai ta xauna gidan nawa mana Umma" Wani kallo Umma tayi masa daga sama har kasa kafin tace "Toh baxata xauna ba" Dariya yayi yace "Kema kinsan Ramlah bata da matsala Umma and she can do so many cooking da Jiddah xata iya koya, don ma yanxu bata da lafiya sosai" Umma tace "To ubana nace Aa, daga nan xata dinga xuwa makarantar..." Yace "Toh shkkn Umma, sai driver ya dinga kai ta, idan xata dawo kuma ta samu abun hawa tunda kinga hanya ce" Umma tace "In dai am samu nan kusa kusa a samar mata admission kawai, don unguwar da kake yyi nisa" Ahmad bai kuma cewa komai ba, can ya mike yace "Toh shkkn Umma, xa mu yi waya kar muyi missing train" Umma tace "Toh Allah ya tsare hanya, ya kiyaye, kuma ku yi addu'a" Yace "In sha Allah" Daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa.....


No comments

Powered by Blogger.