Jiddatul Khair 51
Makulli Aneesah ta sa a kofar bandakin bayan ta shiga gabanta na faduwa, ta ajiye towel din a karamin bucket ta tara ruwa ta dau sabulu ta fara wanke hannunta ba ji ba gani... Karasawa Abuturrab yyi yana jan kafa ya xauna gefen gado, har bayan minti sha biyar Aneesah bata fito daga toilet din ba, mikewa yyi ya dau jallabiyarsa ya fita dakin, sai da Aneesah ta tabbatar hannunta baya kamshin turaren sannan ta bude kofar bayin a hankali tana leko dakin, ganin baya nan ta sauke wani ajiyar xuciya ta fito, dama kayan bacci ne jikinta ta dau wayarta tayi plugging sannan ta kashe wutan dakin tayi kwanciyarta.... Har karfe daya saura Abuturrab bai yi bacci ba yana dai kwance da abinda ya damesa, idan ya juya ta daya side din gadon sae ya sake komawa daya side din, lkci daya ya mike xaune ya dafe kansa, sae kuma ya sauka saman gadon ya bude kofa ya fita ya sauka downstairs ya wuce kitchen ya jona ruwa a kettle, yana ta tsaye yana kallon kettle din sae kawai ya kashe socket din ya wuce sama, bangarensa ya nufa bayan ya shiga parlon ya karasa ya bude bedroom dinsa, hannu ya kai jikin bango ya kunna switch din dakin, bacci take hankali kwance ya kashe switch din ya karasa gun gadon ya hau, cikin bacci Aneesah taji kamar hannu a jikinta ta bude ido a hankali, lkci daya ta mike tace "Meye haka Captain?" Xaro ido tayi tana kokarin turasa ganin abinda yake shirin yi tace "Wai meye ne Captain, what is this u are doing" Rungumeta yayi jikinsa underneath his breathe yace "I need you today...." Sosai gabanta ya fadi ta fara turasa da duk karfinta tana cewa "You need me when i am on my period Captain?" Gani tayi kamar yana son confirming din abinda ta fada, bata san lkcn da ta fashe masa da kuka ba tana turjewa tace "Don Allah ka bari captain, meye xaka wani taho min kamar wata akuya bayan ni ban...." Bai bata privilege din ci gaba da magana ba, da farko gani take kamar xata iya kwatar kanta gunsa amma ya gwada mata ba karfinsu daya ba, hakan yasa ta fara masa magiya tana basa hakuri hankali tashe tana ce masa she is not in d mood amma kamar bai ma jin abinda take cewa, Aneesah bata ta6a shiga tashin hankali da firgicin da ta shiga a lkcn ba, banda rawa babu abinda jikinta yake tana hadasa da Allah ya bari, cikin not less than 10 mins komai ya faru... Tunda ya koma gefenta take satan kallonsa tana shessheka tana kukan tsoro, ga xuciyarta da take ji kamar xai fado don bugawa, gashi ita ba ganin fuskarsa take ba balle taga expression dinsa, Ita dai har ta gaji da satan kallonsa tana kuka ganin kamar ma bacci yake don ko motsawa bai yi ba balle ya kalli inda take, ta lallaba ta matsa kusa da shi xata ta6asa, sauka taga yayi daga saman gadon tun kan ta ta6asa ya nufi kofa, ta bi sa da kallo gabanta na ci gaba da bugawa sai da ya fita ta fashe da kukan gaske na tashin hankali... Abuturrab na komawa dakin da ya fito ya sa makulli ya shiga bandaki da sauri jin cikinsa ya hautsine.... Har kusan asuba Abuturrab bai yi bacci ba duk da sallah da ya dau lkci yana yi, after subhi prayer yana xaune parlor deeply in thought, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number Ahmad, Ahmad ya shigo daki kenan dawowarsa daga masallaci ya nufi wayarsa da mamakin wanda ke kiransa by this time, ganin Abuturrab ne ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren Abuturrab yace "Good morning" Ahmad yace "Morning..." Abuturrab ya d'an shafa kansa yace "Dama ina son maka tambaya ne" Ahmad yace "Alright i am all ears" Abuturrab yace "I want to know more about Virginity, what it is, and how it is" Buda ido Ahmad yayi sosai yace "Tohhh" sai kuma ya kalli Ramlah dake xaune saman darduma, kofa ya nufa yace "Ban gane tambayar ka ba" Abuturrab yace "Meye baka gane ba a ciki?" Ahmad na fitowa parlor ya nemi kujera ya xauna, Abuturrab yace "I'm serious Ahmad, ka bani amsar tambayata don Allah" Ahmad yace "No ina mamakin hadin Pilot da tambayar ne... But anyway virginity da Hausa shi ake ce ma budurci, kuma idan aka ce Virgin ana nufin wanda bai ta6a intercourse ba, weather a male or a female..." Abuturrab yace "To ya ake gane someone that is a virgin?" Ahmad yace "Mace ko namiji?" Abuturrab yace "Both" Murmushi Ahmad yyi yace "Ita mace akwai wani thin membrane lining da ake kira da hymen a jikinta, and it will seem a bit difficult to penetrate in her, don dole sai anyi breaking hymen din, and in some cases they will be shedding of a little blood, mind u in some cases nace, wasu matan kuma ba sai ta hanyar intercourse kadai hymen dinsu ke breaking ba, d'aga abu me karfi, tsalle tsalle, hawan bishiya ko keke, and many stuffs like that, yana sa suyi loosing hymen dinsu, but duk da haka ba wai xa a ji su kamar sun ta6a samun affairs bane idan an kusance su, don't quote me wrong... sae dai kawai baxa su yi shedding blood din nan ba, infact masu hymen din ma ba ko wacce ne ke fitar da jini ba...." Katse sa Abuturrab yayi yace "Amma kuma ya ake gane warce ta sa6a sex da warce bata ta6a ba?" Ahmad yace "That's so easy, warce bata ta6a ba u neva find it easy to penetrate in, they are alot of struggles, and u ur self will know u just need to be extra gentle on her...." Katse sa Abuturrab yyi yace "Alright thank you, sai anjima" Ahmad yace "But why all this questions?" Abuturrab yace "Karin ilimi" D'an murmushi Ahmad yyi yace "Ohk that's great" Abuturrab yace "Sai anjima" daga haka ya katse wayar, ya jefar a gefensa ya jinginar da kansa da kujera. Sae kusan karfe shidda ya tashi ya wuce dakin da ya kwana yyi wanka, xaune yyi gefen gado thinking of how to get his cloth from his room without seeing Aneesah, ganin lkci na ta wucewa kuma driving xae yi xuwa kano ya mike ya wuce can bangarensa kawai, Aneesah na kwance kan gado ta dunkunkune cikin bargo tunani iri iri a ranta, bata san ya encounter dinta da Abuturrab xai kasance ba yau, ko wani hukuncin xai dauka a kanta oho, to amma taya ma xai gane ita ba virgin bace bayan tana da tabbacin bai ta6a sex ba balle ace yayi da wata har ya banbance, sannan ma duk da rashin virginity din nata sai da taji axabarsa, kenan dai a matsen take, kuma ba lallai ya ma gane ba virgin bace ita, ita dai kadai take ta tunani kala kala, kana ganinta kasan she is so tense and disturb, duk irin burin da ta ci na yanda haduwarta da shi xai kasance ya wargaje, ko armashi abun babu banda axaba, tsoro da tashin hankalin me xai biyo baya, to amma duk da haka ita tasan tana da taste dinta kamar yanda ake yawan gaya mata, shi dai kawai ba ya gamsu ba ina ruwansa da yanda ya sameta, kilan ma bai gane komai ba ita ce ke ta damun kanta, ta ina xai wani san virgin da warce ba virgin ba abinda bai ta6a yi ba, Abuturrab bai ko kalli saman gadon da take ba ya wuce gun kayansa, ta bisa da ido tana tunanin abinda ma xata ce masa, lkci daya ta fara shesshekan kuka, ya dau kayansa da jakar laptop dinsa ba tare da ya kalleta ba still, ganin xai fita cikin rawar murya tace "Naka tukuicin kenan after deflowering ur wife Captain?" Tsayawa yyi ya juya ya kalleta yace "Did u say deflower?" Shiru tayi gabanta na mugun bugawa tana kallonsa daga kwancen da take kamar er mage, yayi wani murmushi yace "I wished so Aneesah, but my trust got betrayed by u, i regret doing what i did yesterday...." Cike da karfin hali ta mike xaune ta dake tace "Ur trust got betrayed?? How Captain?? Wannan wani irin magana ne?" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta girgixa kai tace "Amma ka bani mamaki, yanxu so kake kace min maxa nake bi ko me?? Dama ashe baka fi kowa sanin halina ba Captain? Bayan kai ka ga alamar akwai wani wanda nake kulawa har muka yi aure?" Sai kuma ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Tunda nake ban ta6a zina da wani d'a namiji ba Allah shaida, idan ina yi kai ma da ka sani ai don irin wannan abun baxai boyu ba, bani da wanda nake kulawa da ya wuce kai, me na maka xaka saka min da haka a ranan da ka kusance ni..." Abuturrab bai ce mata komai ba ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da kallo tana hadiye abu da kyar. Bayan ya shirya ko sallama bai mata ba ya fice daga gidan cikin motarsa, yana driving ya kara dialing number Ahmad, bayan Ahmad ya daga yace "Ahmad i still have more questions" Ahmad yace "Alright go on" Abuturrab yace "Kace not everyone ke shedding blood due to reasons u listed.... haka ko?" Ahmad yace "Yes" Abuturrab yace "But how about if u just find ur self in without any stress, me hakan ke nufi, or ana samun irin wannan cases din gun warce bata ta6a sex ba?" Ahmad yace "Noo!! if u should go in freely, to ko ma wacece ta ta6a sex wllh, continuously ma kuwa, and probably for long take abunta shi sa ma kayi noticing hakan lkci daya...." Abuturrab dai yayi shiru yana sauraronsa, Ahmad yace "And let me tell u something, in dai mace ta sa6a sex before marriage to memory din wanda ta sa6a da shi din will remain in her brain, da kyar ta iya rabuwa da shi duk da fa ga mijinta, yawancinsu basa iya tsayawa a matrimonial home dinsu without following men outside, it's just like a curse, ko da sun dau vow din repenting to ina gaya maka na yan shekaru ne... xa su koma idan ba Allah ne ya so su da Rahama ba" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba, Ahmad yace "Are u okay now?" Abuturrab yace "Sure nagode, i am on my way to kano, thank you... Sai anjima" Ahmad yace "Alright safe trip" Katse wayar yayi ya ci gaba da tukinsa. Tun da Aneesah taji fitar motarsa a gidan ta hau kiran Aunty, Aunty na dagawa ta fashe da kuka tace "Aunty na shiga uku..." Aunty dake kwance kan gadonta ta mike xaune da sauri tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Wllh kawai daren jiya Aliyu ya far min, duk yanda nayi kokarin stopping dinsa hakan bai yiwu ba har sae da yayi" Aunty ta bude baki tace "Yayi?? To sai aka yi yaya ynxu?" Tana kuka tace "Tun jiyan ya ki kulani bai ma kwana dakin ba, sae yau da safe ya xo daukan kaya yake ce min i betrayed his trust, kinga wllh ynxu ma haka ya tafi kano ko sallama bai min ba" Aunty ta saki salati tace "To garin yaya hakan ya faru, garin yaya kika yarda kinsan halin da kike ciki Aneesah?" Kuka kawai take tace "Wllh he forced him self in me Aunty, nayi kokarin preventing hakan amma ni ba karfinmu daya ba" Aunty tace "Tabdi, to ni yanxu me xance??" Aneesah ta dinga goge idonta ko da wasa bata ce ma Aunty turaren da ta bata ne ya fashe ba, Aunty tace "Toh abinda xai faru duk inda xaki nemo kudi ki nemo a samu a rufe bakinsa kawai" Aneesah tace "Sai in dau zinarina in siyar, I can't imagine Aliyu yace xai rabu dani sabida haka, wllh ina sonsa sosai Aunty" Aunty tace "Ya rabu da ke?? Ji wani mugun alkaba'i, ke fata kike ya rabu dake ma kenan? Akan wannan d'an abun xai rabu dake kamar warce ta kashe mutum? Mata nawa ne aka aurar bbu budurcinsu kuma suna xaune qlau da mazajensu? Rabu da d'an iska xai ma sakko ne, ke dai kawai ki siyar da zinarin ki turo min kudin a tura benue" Aneesah tace "Toh Aunty, ynxu xan fita kasuwa in siyar sae in tura maki kudin" Aunty tace "To yi maxa, kar ki wani damu abunki, ubansa ma yayi hakuri da hakan balle shi gantalalle, shaff mancewa xai yi idan na sa ayi aikin..." Aneesah tace "Toh nagode Aunty, bari inje, xan kiraki" Aunty tace "To yi maxa" daga haka ta katse wayar, ko wanka Aneesah bata yi ba tun daren jiyan balle aje ga sallah, ta saka doguwar rigar atamfa ta xumbula hijab dinta sannan ta saka zinarin a jaka ta fita daga gidan. A ranan Ahmad ya kai Jiddah makaranta kamar yanda ya ce da Umma, Tunda yyi duk registration din da komai ya tafi ya barta kawai ta fara karatu Monday din... Da yamma karfe hudu da kansa yaje daukota daga school din, amma sanin halin Ummarsa sae ya wuce da ita can gida kawai, Umma tayi farin cikin fara makarantar Jiddah sosai, ita dai Jiddah na xaune kasa kan carpet tana murmushi, Umma tace "Toh tashi kiyi sallah ki ci abinci" mikewa tayi ta wuce dakinsu, Ahmad ya kalli Umma yace "Kince daga nan xata dinga tafiya ko Umma?" Umma tace "Eh xata dinga xuwa daga nan" Yyi murmushi yace "Ga dai sauki amma ke baki so Umma" Umma tace "Saukin me?" Yace "Kashe transport" Umma tace "Kai yanxu ka bada shawarar a bar kamarta da Ramlah a gida kai kana can gun aiki, to wa xai dinga gaya masu gaskiya ko ya sa su kan hanya, shiririta kenan kawai" Yace "Kema dai kinsan Ramlah bata da shiririta Umma, sannan Jiddah ma na da hankali da nutsuwa sosai, kinga from monday to Friday idan taje schl sae ta xo nan Friday din da yamma ta maki weekend, ina ga xae fi wllh" Umma tace "Shkkn kuma babu me sa mata ido kan karatun?" Yace "A nan ma kinsan bbu me sa mata ido amma take yin karatunta wholeheartedly" Umma ta ta6e baki tace "Toh ae shkkn, sae ta tafi can din, amma friday ta dawo nan tayi weekend" Yace "In sha Allah Umma" Sae kusan biyar da rabi suka bar gidan suka koma gidan Ahmad, a hanya yake bata hakuri kan gidan Iya da bai kai ta ba tunda ta koma schl, Jiddah tayi murmushi kawai tace "Toh Allah ya kai mu wani lkcn" Ranan friday Abuturrab na shigowa garin kaduna gidan Umma ya nufa direct, yana parking a kofar gida ya shiga cikin gidan, Umma ce xaune parlor suna hira da Huraira, yayi sallama ya shiga parlorn, sanye yake da fararen shadda da suka amshesa sosai, sae da Huraira ta gaishesa sannan ta bar parlon, Ya xauna saman kujera yana kallon Umma yace "Ina yini" Umma na kallonsa tace "Lafiya lau, daga ina haka?" Yace "Daga gida" Tace "Madallah, ya kwana biyu?" Yace "Alhmdlh..." Sallama aka yi bakin kofar Umma ta daga kai tare da amsa sallaman, ta shigo parlon sanye da hijab dinta gogagge har kasa da jakarta a hannu, ta gefen ido yake kallonta har ta karaso cikin parlon ta nufi Umma ta durkusa nan kasa kusa da ita a hankali tace "Umma ina yini" Umma tayi murmushi tace "Lafiya lau Jiddah ya karatun?" Ta sunkuyar da kanta tace "Alhmdlh Umma" Abuturrab dai kallonta kawai yake, Umma tace "Ya su Ramlar" Jiddah na wasa da fingers dinta tace "Tana gaisheku..." Umma tace "Ahmad din ya shigo ne?" Jiddah ta girgixa mata kai tace "Aa" tunda ta lura da cewar Abuturrab ne xaune parlon duk da ba wai kallonsa tayi ba taki yarda ta dago kanta gaba daya, Umma tace "Toh yayi kyau, kije ki xuba abinci ki ci" Tace "Umma na ci abinci" Umma tace "Ohk to kice ma Huraira ta kawo ma Aliyu ruwa" Mikewa Jiddah tayi still bata yarda ta kalli direction din da yake ba ta wuce kitchen din, satan kallonta yake har ta shiga kitchen din, sai kuma ya kalli Umma yaga wani kallo da take masa...
Leave a Comment