Makauniyar Kaddara 14
Makauniyar kaddara |
Page 14*
............Tsitt gidan yay na wucin gadi kowa na duban Zinneerah da mamaki. Cikin fushin da basusan ta iyaba ta nuna Aliya idonta na cikowa da ƙwalla. “Ki kama harshenki a duk lokacin da zuciya ke ingizaki wajen kuskuren suɓucewarsa. Zaki iya mani ni baki isheni ko kalloba. Amma idan kikace ƙarancin tarbiyyarki zai cigaba da rufe idanunki wajen raina waɗannan lallai zan maidaki cikin hayyacinki!!”.
A yanda tai maganar babu tsoro ko alama a cikin idanunta ne yay matuƙar saka shakkarta a zuciyar Aliya. Dan haka ta kasa komai sai kallonta da take hannunta riƙe da kuncinta.
A fusace Luba tayo kan Zinneerah, wani wawuyan cakuma tai mata wadda tai sanadin suɓucewar zanin goyon datake goye da little. A take yaron yay baya gaba dayansa. Ita kuma Luba ta cakumi Zinneerah ɗin sukai gaba.
Kusan a tare Maman Sadiq da Maman Halima suka iso wajen daf da Little daya tsage da wani gigitaccen kuka zai kai ƙasa. Cikin amincin ALLAH ya faɗa cikin hannunsu da suka tara a tare.
A can kuwa tsakanin Luba da Zinneerah dambe ne sosai ya harƙume. A tunanin Luba zata iya dukan Zinneerah ne dan tana ganin ta fita girman jiki. Sai gashi Zinneerah ɗin na tumurmusar hancinta a ƙasan sumintin gidan. Ganin irin dukan da Zinneerah kema Luba yasa Aliya da Maman Sakina rufe Zinneerah da duka suma.
Masu iya magana sunce sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, da wannan damar suka sami galaba akan Zinneerah duk da dai ta more sosai itama akan Luba ai. Ganinfa abin zai zama hauka Maman Halima ta sakarma Maman Sadiq Little dake kuka saboda tsoratan da yayi ta nufesu tana ƙoƙarin janye Maman Sakina da Aliya amma ta kasa. Sai faman kaima Zinneerah duka suke suna ɗura mata zagi, har takai Maman Halima ɗinma na samun rabonta.
Ana cikin wannan rikici ALLAH ya kawo sallamar wata baƙuwa mai tsananin kama da Maman Sadiq. Ganin abinda ke faruwa duk da batasan wa suke duka ba ta ajiye jakka itama ta shiga cikin masu rabo. Da ƙyar suka iya yakice Zinneerah a tsakkiyar su Maman Sakina daketa zage-zage tamkar dangin maguzawan farkon ƙarni.
“Innalillahi, mike faruwa kukuwa haka a gidan naku Yaya Hauwa? Maman Halima miya kaiki shiga wannan shirmen?”. Baƙuwar ta faɗa tana duban Maman Sadiq dake jijjiga Little, sai kuma ta maida kan maman halima. Kafin ta dubi Zinneerah data nufi ɗaki abinta kamar bada ita aka gama kicimilliba yanzun.
Cikin baƙin ciki Maman Halima tace, “Sannu da zuwa Maryama. Dolene ta kaini ga hakan ai, taya zasu tararma yarinya haka bayan ta fisu gaskiya. Sam Saude batason a zauna lafiya a gidan nan wlhy Maryama”.
Ganin yanda su Maman Sakina ke ƙara hayayyaƙowa yasa baƙuwa Maryama cewa, “Kunga naga wata sabuwar fitinar ke neman tashi kuma. Maman Luba dan ALLAH kuyi haƙuri haka ya isa. Yaya shige muje, Maman Halima dan ALLAH kema shiga ɗaki kawai”.
Shawarar Maryama Maman Halima da Maman Sadiq sukabi kowa ya shige aka barsu sunata haushi kamar karnuka. Sai da suka shiga ne Maryama taga Zinneerah da ƙyau. Cikin ɗaurewar kai tace, “Wai nikam wa nake gani anan haka Yaya?”.
“Hummm Maryama bar wannan batun zauna ki huta. Sannu da zuwa kinsha hanya. Bansan kina tafeba ai”.
“Tafiyar bata shiri bace ba ai Yaya. Kuma nama nema wayarki amma sam bana samu, shiyyasa kawai nai ƙuru nace bara na biyo ɗin dai kar nai rashin hankali”.
“Tofa, ALLAH yasa badai wani abune ya faruba kuma?”. Mama ta faɗa tana mikama Zinneerah da kanta ke duƙe a ƙasa alamar kuka take little. “Ki tashi ki masa wanka a bashi abinci tunda yayi shiru”.
Sai lokacin Zinneerah ta ɗago tana share hawayenta. Ta amshi little ɗin kafin ta gaida Maryama. Amsa mata tai tana binta da kallo, hakan yasa Zinneerah miƙewa ta shige ɗaki da Little a hannu. Ajiyar zuciya Maryama ta sauke bayan shigewar Zinneerah ɗin, duk maman sadiq dake ƙoƙarin kawo mata ruwa na kallonsu. Sai da ta ajiye ruwanne ta sake maimaita mata tambayar ɗazun.
Maryama tace, “Lafiya ƙalau, sai dai lafiyar mai rauni. Inno ce jikin nata babu daɗi, dan sunce shekaran jiya da daddare kamarma bazata kwana duniya ba”.
“Innalillahi wa'inna ilairraji'un. Yanzu nan har jikin Inno yakai tsanani haka amma baza'a sanarminba Maryama, har ke dake a Minna kiji”.
“Kiyi haƙuri Yaya Hauwa, wlhy ba laifinsu bane. Buba yace tunda ciwonta ya fara motsawa a cikin satin nan suke neman wayarki data Yaya amma basa samunku. Ni kaina Baban su Atiku suka samu tunda kinsan dai ba wani muhimmanci wayata kedashi ba”.
“Eh kuma sun fini gaskiya, dan layin nawane ya samu matsala wlhy, Yaya kuwa bansan yaya akai suka gaza samun nasaba, kokuma matsalar network ne. UBANGIJI ALLAH ya ƙara mata lafiya. Jikine na tsufa sai dai Alhmdllh”.
“Wlhy jiki kam na tsufa. Dama na biyo ne idan babu matsala sai mu wuce Baucin tare mu dubata, to saima ina shirin tahowa danai waya da Buba yake sanarmin ai Hajiya Iya taje garin taga halin da take ciki ta ɗakkota suna anan kano wajenta”.
“Tofa, ita Hajiya Iya ɗin dama suna anan kano ɗin har yanzu?”.
“A'a yaya yakike wannan magana haka. Handa Hajiya Iya da iyalanta sukai ƙarfi a garin nan kina ganin zasu iya barinsa kuwa? Kenan baki cikama Inno alƙawarin da kikai mata na neman inda suke ɗinba?”.
“Humm Maryama bazaki ganeba. Ni wlhy kin ganni nan harka da masu kuɗin nan ba sonta nakeba sam. Bani ƙaunar shiga inda akafi ƙarfina a wulaƙantani”.
“Kai Yaya kenan har kin sani dariya. Aiko kinga Hajiya Iya bata da wannan, mace ce maison zuminci sosai. Danni kinga mun taɓa haɗuwa da ita kusan sau biyu kuma duk banga wani nuna ƙyama daga garetaba. Saima jana da taitayi a jiki tana min faɗa da cewar Baba ya rabamu da dangi bamusan kowaba sai Inno”.
“To kinsan abinne da wuya wlhy Maryama. ALLAH ya ƙaddara bazanje ɗinba sai ta silar zuwan Inno ɗin. Dan yanzu hakama ni nama manta yanda adireshin gidan yake”.
“Wannan mai sauƙine ai Yaya sai a kira Baban su Atiku ya kira Buba muji. Nidai na kasa haƙuri, dan ALLAH wai wacece wannan mai kamanni damu haka? Inaji a raina jininmuce yarinyarnan”.
Murmushi Maman Sadiq tai tana mata harar wasa. “Rashin haƙurinki na nan dai Maryama. to ƴarki ce ta Danya ƙaddarar rayuwa ta kawota nan”.
Da matuƙar mamaki Maryama tace, “Wai Yaya kina nufin Zinneerah?”.
Kai kawai Mama ta gyaɗa mata tana amsa sallanar Maman Halima.
Shigowar Maman Haliman ta saka Maryama yin shiru, Maman Halima ta ajiye mata kular abinci tare da zama suka gaisa cikin mutunta juna da tambayar lafiyar iyalai. ta mike zata fita Maman Sadiq ke sanar mata dalilin zuwan Maryama ɗin.
Jajanta musu Maman Halima tai cike da alhini, tare da addu'ar samun lafiya ga Inno ɗin kakarsu data haifi mahaifiyarsu. Bayan sun mata godiya ta fice. Maman sadiq kuma ta ƙwalama Zinneerah kira.
Koda Zinneerah ta fito sai Maryama dake sharar hawaye ta miƙa mata hannu tana faɗin, “Zonan ɗiyata dan ALLAH, zo naji ɗuminki”.
Babu musu Zinneerah ta nufeta duk da batasan wacece itaɗin ba. Sai dai kamaninta da mahaifiyarta ya tabbatar mata jininta ce. Haɗata tai ita da Little da yasha wanka duk ta rungume kukanta na ƙara ƙarfi. Maman sadiq ta miƙe tana ƴar dariyar ƙarfin hali da faɗin. “Oh halin naki dai bai canzuwa kenan har sai ƴar taki ta ganoki itama. Nikam bara kiga na miƙe, kema idan kin gama kukan kizo kiyi sallar la'asar kiɗan watsa ruwa sai ki zaman cin abincin ƙyafi jin daɗi”.
“Yaya dole nai kuka kodan kunya da takaicin kammu akan yarinyarnan. Zinneerah ki gafarcemu dan ALLAH, munsan bamu ƙyauta mikiba, bamuyi miki adalciba a rayuwa. Dan ALLAH ki mana afuwa”.
Zinneerah bata iya cewa komaiba. Sai murmushi kawai da take famanyi da ƙoƙarin danne nata kukan dake neman kufcewa. Sai da Maman Sadiq data sake fitowa mata maganar tazo tai wankan ne ta lallaɓeta da ƙyar ta share hawayenta da sakin Zinneerah da itama zuwa yanzun hawayen take sharewa.
★★★
Bayan Gwaggo Maryama tayi wanka da salla sukai zaman cin abincin zuminci da ƴar uwarta. Yayinda little kenan tare dasu a falo nata wasansa konace ɓarna. Zinneerah kam tuni ta shige ɗaki dan zazzaɓi nema ke neman rufe mata jiki.
Gwaggo Maryama ƙanwa ce ga Maman Sadiq. Uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sukaɗai mahaifiyarsu ta haifa a duniya ALLAH yay mata rasuwa, dan haka akwai shaƙuwa mai ƙarfi da ƙaunar juna tsakaninta da ƴar uwartata wadda ƙaddarar aure takai can Minna jihar Niger. A yanzu haka itama ta zuba iyalai acan Alhmdllh.
Kaf labarin Zinneerah da dalilin zuwanta nan wajensu da samuwar Little Maman Sadiq sai da ta zayyanema ƴar uwarta dakeshan kukan tausayin Zinneerah har cikin ranta. Tare da ɗaukar dukan laifi ta ɗora akansu suda sukai wasarere da lamarin Zinneerah ɗin bayan sunsan rashin imani irin na Asabe. Tunda har ta iya rabo Maman Sadiq da mijinta itama Zinneerah ɗin ba barinta zataiba.
Murmushi mama tayi, cikin son kwantarma da ƴar uwarta hankali ta shiga nuna mata komai ƙaddara ne. Tunda UBANGIJI ya hukunta sai Zinneerah tai irin wannan rayuwar babu wani daya isa hana hakan a cikinsu ai. Sai dai su cigaba da mata fatan alkairi kuma a rayiwarta ta gaba. Wannan kam ta rigada ta faru kuma.
“Hakane Yaya Hauwa. Amma wannan tabon bazai taɓa goguwa a zuciyar yarinyarnanba dangane da watsi da mukai da ita bayan duk munsan a inda take”.
“To yadai wuce yanzu dan ALLAH. Muci abinci koma kimtsa kafin Yaya ya shigo gidan muji yanda za'ai tafiya inda Inno take. Dan da san samune mu tafi yau duk da naga garinma dai yana haɗe fuska alamar hadari”.
Da wannan maganar ta Maman Sadiq bakin Gwaggo Maryama yayi shiru. Suka ƙarasa cin abincin da saida ta matsa mata. Daga haka suka zauna zaman hirar zuminci da jiran dawowar Abba gidan.
Kamar yanda su Maman Sadiq ke jiran dawowar Abba iyalan Maman Sakina ma zaman jiran dawowar tasa gidan suke cike da alwashin sai Zinneerah tabar gidan yau ɗin nan. Duk da sun shige ɗaki basubar zage-zage ba da aibanta Maman Sadiq da Maman Halima. Dan ko abincin rana yau sunƙi zuwa su ɗakko na ɗakinsu har yamma tayi yara suka dawo daga makarantar islamiyya.
Tunda su Abdull sukaga Gwaggo Maryama suka rikice da murna sosai. Itama taji daɗin ganinsu. Ta haɗasu a jikinta ta rungume harda Little daketa walwalar ganinsu.
Bayan an idar da Sallar Magriba Sadiq yazo yana sanarma Mama Auntynsu bata da lafiya. Kafin tace wani abu sallamar Abba ta shigo kunnuwansu alamar ya dawo gidan kenan.
Duk da suna a cikin ɗaki ba kuma nan ya shigoba kai tsaye sai da suka amsa. Su Sadiq duk suka fice yima Abban sannu da zuwa kamar yanda suka saba idan ya shigo suna gida.
Wuff Maman Sakina ta fito daga ɗakinta tunda taji sallamar mijin nasu. Kusan a tare suka shiga falonsa da ita da yaran. Sama-sama ta gaidashi, zata fara kumfar baki ya ɗaga mata hannu dan dama tun a yanayin data shigo yasan gidan babu lafiya. Ga kuma Aliyu na faɗa masa Auntynsu bata da lafiya tana ɗaki kwance.
“Salla zanyi, sannan kinsan dokata a gidan nan bana buƙatar yin maganar da duk bata shafi alkairiba a gaban yarana. Dan haka ki koma sai anjima idan na nutsu kizo miyi magana ba yanzu ba”.
Wani irin baƙin cikine ya turnuƙe zuciyar Maman Sakina. Ta fito fuuu kamar zata tashi sama. Da kallo kawai ya iya binta yana mai girgiza kansa.
A ɗaki kuma Gwaggo Maryama ce da kanta ta miƙe zuwa wajen Zinneerah da Sadiq yace bata da lafiya. Ƙudundune ta sameta cikin bargo tana rawar sanyi. Saurin ƙarasawa tai gareta tana faɗin “Subahanalillahi Zinneerah dama baki da lafiya amma kikayi shiru?”.
Kafin Zinneerah ta bata amsa Maman Sadiq ta shigo ɗakin itama. Duban inda take kwancan tayi tana bama Gwaggo Maryama amsar zancenta. “Tunda ta iya cin dambe ba dole tai zazzaɓi ba. Ki tashi kiyi wanka da ruwan zafi kici abinci kisha magani, dan wannan dai zazzaɓin bai wuce sanadin hayaniyar nan ba”.
Cike da takaici Gwaggo Maryama tai tsaki. “Shi dai yaya ya auroma kansa masifa wlhy. Ayi mace bata son zaman lafiya kamar dangin yahudawa”.
“Humm ai kaɗanma kenan Maryama, dan wannan fitinar ba mutuwa taiba rufa tai, na tabbata jiran dawowar maigidan take, bara kuma kiji zakice nina faɗa miki”.
“Fitinanniyar banza. Gashi nan duk tabi ta koyama ƴaƴa hali mara amfani, aini Zinneerah ta birgeni sosai data nuna musu ƙyalesu dama kawai take ba tsoro bane. Shi kuma yayan tunda yasan halinta dama ai kinga sai yay musu iyaka yanzun”.
“To ALLAH yasa. Dan da kike ganinta a haka son matarsa yakeyi”.
Kiran sallar magriba da aka kirane ya katse hirar tasu. Zinneerah kam dama harta shige bayi tuni.
Bayan idar da sallar magriba Gwaggo Maryama ta tsare Zinneerah taci abinci tasha magani sannan ta kwanta. Maman Halima ma ta kawoma Gwaggo Maryama nata abincin yaɗan zauna sukai hira bayan ta shiga ta duba Zinneerah data sanu barci. Kiran sallar isha'i yasata komawa nata sashen.
Alhaji da yara kam basu shigo gidanba sai da aka idar da sallar isha'i. Harda Little da yay barci. Gwaggo Maryama ta amshesa ta goya tana maijin tausayin yaron a ranta.
Sai da Maman Sadiq ta tabbatar Alhaji yaci abinci ya huta sannan suka fita ta raka ƴar uwarta danta gaidashi. Sai da sukai sallama ya amsa shi da Maman Halima dake tare da shi sannan suka shiga. Sosai fara'ar fuskarsa ta daɗu yanama Gwaggo Maryama lale da zuwa dan dama yara sun sanar masa zuwanta.
Suna kaiwa zaune sai ga Maman Sakina tamkar an jehota falon dan ko sallama basa tunanin tayi. Kallonta Alhaji yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga Gwaggo Maryama. Hakan da yayine ya saka Maman Halima da Maman Sadiq suma yin kamar basusan da shigowar tataba.
“An haɗa kai an shigo dan a ƙulla mana sheri ni da ƴaƴana. To ta ALLAH bata mutumba”.
Babu wanda ya tanka mata. Sai da Alhaji ya gama gaisuwarsa ta zuminci da Gwaggo Maryama sannan ya dubeta fuska a tsuke. “Saude yaushe ne zakisan inda ke miki ciwo ne wai kekam?”.
“Taya kuwa zansan ciwon kaina agola ta haɗani da ƴayana ta doka saboda an gina mata jiki da tuwon gero dana dawa Abban Luba”.
Kallonta kawai yake batare daya tankaba. sanin baya son jan rai a magana ya sata fara zayyane masa abinda ya faru, sai dai tanayi tana haɗowa da ƙarya da sheri. Tsam Gwaggo Maryam ta miƙe zata fice ya dakatar da ita. “Maryam kina gidan duk akai wannan?”.
“A'a gaskiya Yaya kafin nazone. Nadai iske kawai suna rikicin faɗa nashiga na taya Maman Halima rabawa”.
Komai baiceba sai kallonsa daya maida ga Maman Sadiq. “Ina Zinneerah ɗin take?”.
“Tana can kwance babu lafiya”.
“A dalilin shi wannan rikicin kenan?”. Ya tambaya yana cigaba da dubanta.
Kafin ta amsa masa Maman Sakina ta karɓe da faɗin, “Andai shirya munafunci kawai za'ace, yo inba munafun........”
“Saude!”.
Ya katseta a tsawace. Badan tasoba dole tai shiru. Yaja tsaki da faɗin, “Da safe inason ganinku dukanku har yaran”. Ya faɗa yana miƙewa ya fice.
Ganin haka ya saka su Maman Sadiq miƙewa suma duk suka fito. Sai dai a mamakinsu sai hangarsa sukai ya nufi sashenta da alama duba Zinneerah zaijeyi.
Hakan yama Gwaggo Maryama daɗi sosai, duk da dama tasan halin ɗan uwan nasu baya wasa sam da lamarin gidansa. Amma batai tunanin Zinneerah ta samu matsayi na musamman haka a garesaba.
Bayan ya shiga ya dubata tana barci dan haka ya fito falo. Batare da dubansuba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “A tada ita muje ko nan kyamis ɗin Umar ne tunda dare yayi”.
Halinsa da Maman Sadiq ta sani yasa bataja zancenba taje ta tado Zinneerah suka tafi kyamis ɗin. Itako Saude nacan tana tijara a sashenta kamar zata haɗiye haƙoranta, musamman ma dataga Alhajin ya fita tare da Zinneerah da Sadiq.
WASHE GARI
Washe gari da safe Zinneerah ta tashi Alhmdllh babu zazzaɓin dan tasha allura jiya. Bayan idar da salla suka zauna zaman hira ita da Gwaggo Maryama dake janta a jiki cikin hikima. Sai da gari yay ɗan haske suna shirin fita gaida Alhaji sai gashima ya shigo duba Zinneerah ɗin. Kanta a ƙasa ta gaidashi. Ya amsa mata da kulawa kamar yanda ya saba da tambayarta kuma jikinta.
“Alhmdllh Abba naji sauki”..
“Haka akeso ai, ALLAH ya ƙara lafiya”.
“Amin” suka amsa gaba ɗaya.
Sai da ya koma sashensa da kusan mintuna biyar sai ga Hussaina tazo kiransu. Maman Sadiq tasan Maman Sakina ce zata matsa da fitinar sai an zauna. Dan haka ta mike ita da Zinneerah ɗin suka tafi, aka bar Gwaggo Maryama na ƙarasa aikin da Zinneerah ta fara.
Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, dan haka suka sami wajen zama suma su Luba nata harar Zinneerah. Alhaji daya gama nazarin kowa a ƴan sakanni ya basu damar bayani ɗaya bayan ɗaya.
Ya ɗan murmusa yana girgiza kansa. Sai kuma ya haɗe fuska ya balbalesu da bala'i su duka. Kafin ya dawo kan Aliya da Luba da sukaima su Maman Sadiq rashin kunya harda zagi. Ganinfa reshe zai juye da mujiya Maman Sakina ta miƙe da bala'i zata taresa ya daka nata tsawa itama. Cikin jan dogon gargaɗi yace, “Wlhy daga yau ya sakejin makamancin haka akan matansa saiya musu dukan mutuwa a gidan”. Ya kuma sakasu bama su Maman Sadiq haƙuri da ita kanta Zinneerah ɗin. Sannan itama yay mata faɗa akan marin Aliya da tayi tunda yayartace. Yayi hakanne dan kawai kar ace yayi son kai dan yasan dai Zinneerah ta fisu gaskiya. Daga haka ya sallami kowa suka fito Maman Sakina da ƴaƴanta ransu fal baƙin ciki da alwashin hana Zinneerah zaman lafiya a gidan cikin hanya mai sauƙi da Abban bazai gane komaiba.
Maman Sadiq kam ko a jikinta dan bataji komai ga abinda Abban yayiba. Sai ma shirin zuwa inda Inno take suka farayi dan Abban yace su shirya sai ya kaisu da kansa idan zai wuce kasuwa shima ya dubba Innon daga nan. Hakan yasa Maman Sadiq amso wayarsa suka kira mijin Gwaggo Maryama ya turo musu lambar Buba dazai kwatanta musu gidan Hajiya Iya ɗin ko asibitin da Inno ke kwance.............✍
Leave a Comment