Makauniyar Kaddara 35
Page 35*
............“Babangida duk ka rikitar dani wlhy, gani na dawo ɗaki ni kaɗaice yanzu mike faruwa ne?”. Hajiya iya dake zama a bakin gado ta faɗa.
Numfashi Baffah ya furzar daga can. Cikin nutsuwa yace, “Inna yanzu muka rabu da mijin Hauwa'u, kamar yanda na sanar miki dama munyi dashi yau zaizo yanada muhimmiyar magana”.
“Eh ƙwarai anyi haka”.
“Yauwa to Inna, maganar zancen yaron nan ne dai daya tsayamin arai mukayi dashi, ashe yaron ɗan wajen Zinneerah ne”.
“Uhm ban fahimcekaba dai babangida. Wace Zinneerah kake magana? Inno wai?”.
“Tabbas ita kuwa”.
Sosai zancen ya daki zuciyar Inno. Har sai da ta janye wayar daga kunnenta ta kalla, ta dai tabbatar da ɗan nata take waya ba wani dabanba dan haka ta mayar. “Babangida tayaya hakan ta faru? Dama Zinneerah ta taɓa aure ne?”.
“Bata taɓaba Inna. Ƙaddarar rayuwa ce takaita ga haihuwarsa....... (Anutse ya shiga yimata bayani dalla-dalla kamar yanda Abba ya sanar masa). Sai ga hajiya iya na hawaye shaɓe-shaɓe na tausayi. Dan har cikin ranta tanaji Zinneerah bazata aikata hakan da ganganci ba, dole akwai abinda ya faru dai......
Baffah ya katse tunaninta da cewar, “Inna harga ALLAH ta ɓoye-ɓoye ya ƙare, shin baƙya wani tunani game da kamannin yaron nan da Adnan kuwa? Adnan ba kama yake da yaran gidannan ba mahaifiyarsa ya biyo komai a kamanni balle muce ƙarfin jini yakai yaron Zinneerah da ɗakko kamannin yaran gidan nan. Shin kodai akwai abinda Adnan ke ɓoye mana ne?. Dan kwanaki sau biyu ana sanarmin shigowarsa Nigeria baizo inda mukeba. Nayi shirune kawai na ƙyalesa dan karna tayar miki da hankali”.
Babu shiri Hajiya iya ta miƙe tsaye tana ambaton, “Shi Moddibon da kansa?”.
“Wlhy kuwa Inna, ko lokacin da Khalipha yazo hutu tare sukazo”.
A take kan hajiya iya ya sake kullewa. Kamar yanda shima Baffah kan nasa yake a kulle. Dan sudai sunyi imani da cewar yanda yaron ya shiga ran kowa a gidan akwai wata a ƙasa. Sannan kamannin kam sunyi yawa, sai dai idan acan kuma dangin hindatu tushen matsalar take ba abinda zukatansu ke karkatar dasu akai bane.
Hajiya iya da takardar wajen mmn sadiq ta faɗo mata a rai tai masa sallama akan zuwa anjima zasuyi waya bara ta kashe wata wutar.
Tana katse kiran takardar ta ɗakko a inda ta ɓoyeta, ta sake komawa inda take zaune da ta warware.
*_Assalamu alaiki_*
*Alkairin ALLAH da samuwar lafiya mai ɗorewa su tabbata a gareki Gwaggo. ALLAH ya dawo mana dake gida lafiya*
_Gwaggo zan fara da baki haƙuri akan wani abu da muka ɓoye miki game da Zinneerah, munyi hakanne saboda ba abune mai daɗi ba ko farin ciki. Duk da dama dai munyi niyyar sanar daku ɗin harga ALLAH. Akwai ƙaddarar data faɗama Zinneerah wadda itace tai sanadin dawowarta zama a wajena, dan da tana can wajen mahaifinta da muka rabu...................._ _(Ta bada labarin tun aurenta da baban Zinneerah har bayyanarta da ciki a garesu da haihuwarsa kaf bata rage komaiba. Daga karshe ta ɗora da faɗin___). Yaro da mukazo dashi ranar da yara sukace ƙaninsune shine yaron, sunansa Abdul-Mutallab. Dan ALLAH ku gafarcemu da rashin sanar muku wannan labarin tun farko, bamun ɓoye bane dan bamu yarda dakuba. ALLAH ya hukunta sai yanzune zaku sani kawai. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai albarka da amfani._
Sosai Hajiya iya taja wani irin dogon numfashi mai tafiya a sarƙe. Ko kaɗan bataga laifin mmn sadiq akan ɓoyewarba. Domin ko itace zata iya ɓoyewar bisa dalilai masu yawan gaske. Abinda kawai yake neman jefa zuciyarta a ruɗani irin wanda Baffaah ya shiga anan uku ne zuwa biyu. Shigowar sunan Khalipha a labarin da taimakon da yay ma Zinneerah a Shira hospital, Kamanin yaron da Abdul-Mutallab, dan wannan kamanni yakai ai zaman dogon nazari akansa.
Sannan har cikin ranta kuma tausayin Zinneerah da ƙarajin ƙaunar yarinyar ya ƙara faɗi a zuciyarta. Yarinya ƙarama kamar wannan ta fuskanci irin waɗan nan manya-manyan jarabawoyi na rayuwa. Amma abin mamaki ko'a labari bata taɓa nunama waniba, hakan na nufin itaɗin yarinyace mai yawan kamun kai da riƙe sirri, insha ALLAH kuwa zatayi wani abu, sai ta ƙwato mata haƙƙinta, dan har cikin ranta son yarinyar takeyi tamkar nata jikokin........
★
Daga ɓangaren Farah da kiran Mammah ya shigoma a waya. Wani ɗan karan daɗine ya tsarga mata. Tai saurin ɗagawa tana kai wayar kunnenta, dan har cikin ranta tana son Mammah kamar yanda itama take nuna mata soyayya.
Tana ɗagawa ta fashe mata da kuka, a rikice Mammah tace. “Auta lafiya kuwa? Miya faru da kuka haka ni hindatu?”.
“Babu lafiya Mammah, ina cikin damuwa da tashin hankali. Naje gidan jiya kawai na tarar bakyanan sai Mahma kaɗai, yau kuma sai ga tashin hankalin da yafi na jiyan ya riskeni”.
Hankali tashe Mammah tace, “Am so sorry baby na. Ai bazan jimaba zan dawo kodan saboda halin da ake ciki. dan yanzu hakama na kammala tura kaya Morocco. Na Nigeria suka rage kawai insha ALLAH. Amma mi kikajeyi gida? Wane kuma irin tashin hankali kike a ciki?”.
“Ƙannen Yah Abdull ne suka zo jiya, harda yarinyarnan mara kunya data jimin ciwo a ƙafa. Mammah duk bama wannan ba. Wlhy Yah Mutallab ya haifi yaro da wata a waje kokuma yayi aure a ɓoye bada saninmuba”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Farah wane irin maganane wannan? Ya haifi ɗa da watafa? Ke waya faɗa miki? Wacece ita wadda ta haifi ɗan kuma?” Mammah ta faɗa itama cikin tashin hankali.
“Mammah wlhy nima ban sanba. Yanzun nan naga yarinyarnan tana waya da yaron da Moos'ab, shine Moos'ab ɗin ya sanarmin yaron na Abdul-Mutallab ne, kinga kuwa indai ba'a waje wata ta haifa masa shiba wlhy aure yayi a ɓoye bamu saniba. Indai hakan ta faru mutuwa zanyi Mammah
“Kai ina!! Duk rintsi bazan bari hakan ta faruba Farah, dan wlhy har abada bazanyi sakacin da Kabeer zai ƙwacemin Abdul-Mutallab ba. Nayi alƙawarin tarkon da suke ganin zasu ɗana masa ya faɗa bazan bari yayi tasiri ba, dan haihuwarki itace kawai raba gardama a tsakaninmu. Kinga kuwa hakan na nufin babu wata mace data isa zuwa ta haihu da Abdul-Mutallab a ɓoyema ban saniba. ki kwantar da hankalinki yau ɗin nan zan baro china kuwa, dan bani da wata nutsuwar zaman yin abinda nazo yi ɗin”. daga haka ta yanke wayar.
Faɗawa Farah tai saman gadonta tare da fashewa da kuka mai cin rai, ji take tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta, dan inhar wannan ɗan ya tabbata na Abdul-Mutallab tasan ita kam rayuwarta tazo ƙarshe. Kenan bayan ita ya taɓa sanin wata mace a duniya? Ya taɓa dai-daita farin cikin da yake bata da wata mace? ‘Kai ina wlhy hakan bazai yuwuba’ ta faɗa a fili tana fashewa da matsanancin kuka ta miƙe ta fito daga ɗakin.
Ficewa tai daga gidan dan ta rantse bazata sake kwana ba sai Mammah ta dawo sunji daga ina aka samo little. Ko kallon su Zinneerah dake falo zaune Farah batayiba ta nufi hanyar fita abinta.
Da kallo suka bita a tsorace. Cikin damuwa Jamal yace, “Gaskiya Yah Moos'ab baiyi tunaniba, miyasa shima ya faɗi cewar ɗan Yayanmu ne bayan yasan halin Aunty Farah da kishi. Gashi nan wannan maganar dashi yake gani yayi akan wasa gashi tana neman zama babba”.
Wasu hawaye ne masu zafi suka sake silaloma Zinneerah, dan ita a yanzu damuwarta daban da tasu, bataga laifin Farah ba, dan ko ita data haifi little har yanzu ta kasa fita daga ruɗanin kamannin da yakeyi da Yah Adnan. Balle ita dataga komai sama taka yau, ai komi tayi bai kamata aga laifinta ba.
Tunda ta haifi little yau shine karon farko data tsinci kanta a matsanancin tashin hankali tun bayan barowarta Danya.
Acan kuwa wajen su Hajiya iya an kira Moos'ab dan yayma Farah bayani akan wasa yake mata, Hajiya iya da Khalipha sun fito dan a bata wayar amma suka samu ta fice. Cikin damuwa suka sake shiga, dan ba ita kaɗaiba harsu Hajiya iya ganin kamannin yaron da AK ɗin sukai sosai fiye da kullum a yau.
Hajiya iya ta dubi Khalipha daya yanke kiran tace, “Ina Moddibon yake harya bari ta fita?”.
Kansa ya girgiza mata alamar bai sani ba. Sai su Bahijja ne suka sanar mata sungafa kamar ya fita.
“Fita kuma? To lafiya?”.
Hajiya iya ta faɗa. Khalipha da zuciyarsa ta bashi inda Yayan nasu yake yace, “Granny ina zuwa. Inaga yana baya, kinsan shi idan ransa ya ɓaci yafi bukatar ya killace kansa inda babu hayaniyar komai.
Batare da ya jira amsartaba ya fita shima. Kamar yanda yayi hasashe acan bayan ya samesa yanata kaikawo hannayensa goye a baya.
Harya karaso gab dashi baisan da zuwan Khaliphan ba, dan harga ALLAH kamanin yaron da shi ƙara gigitashi sukeyi, zai iya rantsewa tunda yaga yaron nan bai ƙara barci mai daɗi babu mafarkinsa ba. Dauriya kawai yake aɗan tsakanin nan har Hajiya iya ta samu lafiya. Amma da tuni ya koma Nigeria dan kawai yaga asalin mahaifin yaron nan shikam. Sai dai kuma abinda ya faru a yau ya ƙara tada masa tsumin ƙwaɗayin son zuwa Nigeria. Ko ita Farah jin gaskiyar zancen ya sakashi yimata uziri, dan inhar shi da yaron ke kama dashi zai iya rikicewa dolene ita yaga fiye da haka a gareta. Musamman daya santa da shegen zafin kishin tsiya, a yanzu babuma abinda zuciyarta bazata hasaso mataba game da yaron kamar yanda shi kansa duk da ance yaron ɗan Gwaggonsu ne zuciyarsa taƙi samun nutsuwa.
“Yayanmu”.
Khalipha ya kirashi cike da damuwa. Juyowa yay ya kallesa sai dai baiyi magana ba. Khalipha ya ƙarasa takowa garesa, kansa ya ɗan risinar ƙasa saboda abinda zai faɗa.
“Yayanmu kayi haƙuri, kar abinda aunty Farah keyi ya dameka. Dan ALLAH kumata uziri dolone ta shiga ruɗani kamar yanda muma ɗin muke a cikinsa tun ganin yaron da mukai a Nigeria, kawai dai ita matsalarta bata da nutsuwar zama ta fahimci abune”.
Karon farko AK ya saki murmushin ƙarfin hali, hannunsa ya ɗora bisa kafaɗar Khalipha ɗin. “Hakane bestie, Farah ta cancanci uziri a wajenmu, sai dai minene dalilin Moos'ab na cewa yaron nawane?”.
“Wlhy tsokanarta kawai yake Yayanmu, kasanshi duk da baida yawan magana yanada son wasa. Kuma inaga ya manta bataga yaronba a waccan ranar”.
Kai AK ya shiga jinjinawa yana sauke nannauyan numfashi, ya sauke hannunsa daga kafaɗar Khalipha yana maidasu bayansa ya harɗe. Taku biyu yayi batare daya juyo ya kalli Khalipha ba yace, “Bestie mi zuciyarka ke baka akan kamannina da yaron nan?”.
Babu shiri Khalipha ya kalli bayan nasa da sauri, haka kawai yaji gabansa ya faɗi, dan inhar gaskiya zai fito ya faɗa to komaima zuciyarsa na bashi musamman idan tunanin Zinneerah ce mahaifiyar yaron yazo masa arai kamar yanda yake zargi. Baki ya buɗe da ƙyar zaiyi magana Hajiya iya data biyo bayansu ta katsesa.......
“Wai tsayuwar mi kukeyi anan? Yarinyarnan fa bata gidan nan”.
Atare suka juyo suna kallonta. Takowa AK yay cikin tafiyarsa da babu gareje zuwa inda take, bai kawo wa take nufi ba dan haka yace, “Wace yarinya Granny?”.
“Matarka mana”.
Ɓoyayyen numfashi yaɗan sauke, a ransa yace ‘da sauƙi’ tunda yasan dai Farah ƴar garice bazata je wani wajeba sai gidan Mammah.
“Karki damu Granny babu inda zataje sai wajen su Mammah. Ya kamata mujema kisha maganinki”.
Daga haka ya kama hannunta suka nufi ciki Khalipha biye dasu. Basu sami su Zinneerah a falonba, sai mai aikinsu dake ƙara gyarawa. Har ɗaki ya raka Hajiya iya, ganin Zinneerah kwance a gado su Bahijja zaune jigum-jigum yasa Hajiya iya tambayarsu ko lafiya?.............✍
Leave a Comment