Makauniyar Kaddara 60

 


Page 60*


...........Fitowa tai da sanɗa kanta a ƙasa saboda tunani da kunyar su Granny da take zaton har yanzu suna gidan. Yayinda AK dake zaune a falon shi kaɗai yana latsa waya mayataccen ƙamshin haɗin khumrah ɗinta ya samu nasarar kaiwa ga hancinsa. A hankali ya ɗago yana kallon sashen ƙofar bedroom ɗin nasa zuciyarsa na wani motsawa a cikin ƙirji.

       A kan laɓɓansa ya ambaci kalmar “Mash ALLAH” yana wani lumshe idanunsa. Ganin tana nufar hanyar fita da sanɗar da takeyi ya ɗan murmusa, sai da ta ɗan gotashi yace, “Nan zaki zo ai”.

         Ina ƙasa Zinneerah ta shige dan kunya, har mamakinsa take ganin shi ko'a jikinsa tamkar bai aikata wani aika-aika ba. 

      “Kona taso?”.

Taji ya sake ambata. Kafinma ya gama rufe baki ta nufosa dan shi ba abin wasanta bane, abinda ya shiga tsakaninsu kuma bai rage masa kimarsa da girmansa a idanuntaba sai ma ƙaruwa da yayi. Ta ɗanji sanyin ganin babu su Granny, dan haka taso kaiwa tsugunne gabansa.

          Bai motsa daga kishin giɗar da yay a kujera yana mata kallon ƙasan ido ba, ya kamo hannunta ganin zata tsugunna. A saman cinyarsa yay mata masauki. Hakan ya sata saurin kallonsa. Da wannan damar yay amfani wajen riƙe idanunta cikin nasa. Duk yanda taso ta janye ta gagara. Sai neman kashe mata jiki yake da wani sakaltaccen kalo dake tada mata tsigar jiki. Babu shiri idanunta suka fara tara hawaye.

       Karan farko tun shigowarta falon guntun murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya lumshe ido ya buɗe a kanta yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa. “Miyasa ke raguwane?.”

      Cikin suɓutar baki tace, “Tsoro kallon yake bani”.

      Harga ALLAH ta bashi dariya, duk yanda yaso danneta kar yayi kuma hakan bai yuwuba, sai gashi da sakin murmushin da har haƙwaransa na bayyana. Shagala tai da kallonsa dan tabbas murmushi na masa ƙyau musamman wanda ke bayyana haƙwaransa irin wannan. Nisan da tai a nazari yasa harya iso da fuskarsa gab da tata bama ta saniba. Sai jin saukar laɓɓansa kawai tayi akan nata. Duk yanda taso ta nuna zamewa hakan ya gagara. Dan wani irin sallo da tunda uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata shiba yake sarrafa lips ɗinta.

        Luf tayi tana amsar rikitaccen karatun na babban yaya data fara haddacewa daga safiyar jiya zuwa yau. Sai da ya tabbatar ya ida zubar da ɗan sauran ƙarfin data samu sannan ya barta yana rungumeta a jikinsa gaba ɗayanta. Yanda yaken sauke numfashinsa mai sanyi da nutsuwa a cikin kunnenta yasata sake lafe masa a jiki tana rumtse idanu. A ranata ko rayawa take, ‘Yayanmu zaka kasheni da wannan salon naka da yafi ƙarfin shekaruna’.

       Sun kai kusan mintuna uku a haka kafin ya ɗagota yana kallon fuskarta, duk yanda yaso su haɗa ido yanzun kam taƙi yarda. Yatsunsa biyu ya sa ya ɗago haɓarta, bai damu daƙin yarda su haɗa ido da taiba. 

        Tana bashi dariya da ƙara birgesa da wannan sanyin nata, dan haka yay wani munafukin murmushi da kamata ya miƙar.

        Dining suka nufa yana riƙe da hannunta, sai da ya zaunar da ita sannan shima ya zauna. Da kanta ta miƙe ta haɗa masa abincin yanata faman binta da fitinannen kallon nan nasa dake sakata dabircewa komin jarumtar da taso nunawa.

     Shiko fahimtar da yay kallon nasa na mata tasiri tunma suna can gidan yake sakashi kasheta da su. Bata zuba nataba, bai kumayi maganaba, sai da ta gama ta koma ta zauna ta ɗan dubesa. Ganin shima dai kallon nata yake ya sata janye nata idanun gefe.

       Komai baice mataba ya fara cin abincin, sai da yay nisa da ci sannan yay magana batare daya kalletaba. “Juyo nan”. 

      Juyowar tai tana fuskantarsa, sai kawai yay mata alamar ta buɗe bakinta. Ganin yanda fuskar tasa take ya sata buɗewar. Daga haka ya cigaba da ciyar da ita yana ci shima har suka cinye. Godiya yayma UBANGIJI yana miƙewa ya barta a wajen. Hakan ya sata miƙewa itama ta tattare kayan a basket ɗin da aka kawo, sam batajin daɗin jikinta, a yanzu haka tafi buƙatar ta samu waje ta kwanta. Sashen ta bari baki ɗaya zuwa nata, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya da nufar kitchen. 

      Tana cikin wanke kwanikan ya shigo kitchen ɗin, waiwayowa tai ta dubesa. Ya canja kayansa zuwa shadda fara tas da tai masa tsananin ƙyau, ga mayataccen ƙamshinsa mai cika hancin mai shaƙa da bashi nutsuwa. Ya ɗan janye idanunsa daga kanta yana kallon agogon hannunsa. “Bara na gaishe da su Mammah kina buƙatar wani abu ne?”.

          Duk da tayi mamakin jin zancen Mammah sai batace komaiba taɗan girgiza masa kanta. 

     Takowa yay gabanta yana ɗago fuskarta suka kalli juna. “Baza'amin addu'a ba?.” ya faɗa a wani irin sanyin murya.

        Tana mamakin a yanda ya iya sarrafa yanayinsa a salo daban-daban, kuma duk cikin kame kansa babu wani rawan kai ko gaggawa tattare da shi. Idan badan ita da take ganin true color ɗinsa a tsakanin jiya zuwa yau ba babu wanda za'a faɗama haka yake ya yarda, dan ko'ita idan yay abu ya basar sai take ganin tamkar ba shine ya aikataba. Ya barta da kunya shiko ko'a jikinsa.......

       “ALLAH ya tsare ya dawo da kai lafiya Yayanmu”.

     Haɓarta ya saki da tura duka hannayensa a aljihunsa yana kallonta,  “Har yanzu matsayin Yayan kawai gareni?”. Ya faɗa yana tsatstsare ta da idanunsa masu kaifi a gareta.

        Ɗan ɗago idanu tai ta kallesa, ya wani juya mata nasa manyan idanun yana ƙara tsuke fuska.

      “Yanzu ni waye a wajenki?” 

  Ya faɗa cikin muryarnan tasa ta rashin sakewa.

     Mamaki tambayar tasa ta bata, da ɗan rawar murya da kunyarsa ta haifar mata tace, “Yayanmu!”.

      “Daga nan fa?”.

    Duk da ta fahimci abinda yake son jin sai ta noƙe dan itama ɗin dai gwanace a miskilancin. 

      “Zaki magantune”. Ya faɗa yana sake kallon agogonsa da juyawa zai fita. Jitai duk babu daɗi, 

      “Kayi haƙuri idan na ɓata maka rai Yayanmu”.

        “Ba haka matata ke bani haƙuri ba, dan haka sai ki shirya ta yanda nafi buƙata kafin na dawo”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya waiwayota ba.

         Kallo ta bisa da shi zuciyarta na maimaito mata karatun hajiya Falmata daki-daki. Ganin tunanin bazai kaita ko inaba ta cigaba da aikinta cikin dauriya dan wani sabon zazzaɓi ke neman saukar mata, ga wajen itakam har yanzu zafi yake mata kaɗan-kaɗan. Duk da yanda take jin nata haka tai juriyar gyara gidan har sashensa, sauƙintama ba wani datti bane. Turaren wuta ta saka har General falo da ƴar barandar waje. Ta bi kuma da fresheners masu daɗi. Sosai nutsuwa ta ƙara saukar mata jin ko'ina ya ɗauka ƙamshi kamar yanda take buƙata. Daga haka ta taƙarƙara ta koma bedroom ta kwanta kozata samu barci ya ɗauketa kafin sallar la'asar.

      Tana kwanciya ana fara knocking, dole ta miƙe kamar zatai kuka. Hijjab ta saka sannan ta fito ta buɗe. Ganin su maman halima yasa fara'arta bayyana tana jera musu sannu da zuwa. Suma cike da kulawa suke amsa mata suna shiga da kayayyakin da sukazo dashi. Akwatinanta ne na lefe da tarkacen ƴan kayayyaki. Sai kayan gara da suka bata mamaki. 

      Naziru daya kawosu ne yace ta buɗe ƙofar kitchen ta baya a saka tacan zaifi sauƙi. Dan yasan hanyar tunda da shi aka kawo furnitures ɗinta. Cike da girmamawa ta karɓa masa. Taje ta buɗe ƙofar shi da maigadi suka dinga jigilar shiga dasu su Sakina na tayasu da wanda zasu iya. Hardasu kayan cin-cin. Jitai ƙwalla ya cika mata ido najin daɗi da tausayin su baba. Iyaye dabanne, duk da sunsan babu abin AK ɗin ya rasa a rayuwarsa sunyi hoɓɓasa ɗin ganin sun cika mata darajarta akan abinda al'ada ta tanadar. Dan dai gara al'adace da ƙyautatawar iyaye ga miji bawai wajib bace kamar yanda samarin yanzu suke kallo, harma suke samun damar yarfa mace in ba'ai mataba saboda son zuciya.

       Sai da aka gama shiga da komai sannan ta kawo musu ruwa da lemo sukai zaman gaisawa. Sakina sai kalle-kalle take da jinjina wannan gida a ranta, duk da da ita aka kawo amarya yau dai tafi kallon komai yanda ya kamata dan shiyyasama ta nace sai tazo. Aiko sai gashi ƙiri-ƙiri tana nuna hassadanta a fili dan sai wani yamutse-yamutsen fuska take ita da uwarta dake ji kamar ta fidda Zinneerah ɗin ta kawo sakina ciki.

      Ita dai Zinneerah bama bi takansu taiba, dan akwai sauran ƴan ɗan musa da sukazo tare su uku sai maƙwaftansu mmn sadiq ɗin abokan arziƙinta suma su uku, sai ƴaƴan mmn halima da ita, da matar Naziru.

       Kasancewar su mmn halima tsaffin mata ya sasu fahimtar yanayin Zinneerah ɗin, sai mamaki ya kama irinsu mmn sakina da matar Naziru da ita kanta mmn Haliman dan sudai sunsan Zinneerah ba wannan ne aurenta na farko ba, tunda gata harda little. To amma yanayin nata yayi kama da na wadda namiji ya fara taɓawa. Sauran kam dai har ransu gani suke Zinneerah ta kawo mutuncinta, musamman ma ƴan dan musa da babu wanda yasan ƙaddarar data afku ga Zinneerah ɗin har yanzu. Duk da kuwa Inna Asabe ta saki maganganu da sukaje danya sai duk suka kallesu matsayin hassada kawai da sharrin baƙin kishinta da bai ɓoyuwa harga ƴaƴa. Sai da suka shiga ko ina suna mai yabawa da jera addu'oin fatan alkairi.


★★★


       Koda Mahma ta koma gida bata yarda ta nunama su Mammah komaiba, hasalima dama basusan inda tajeba. Da sukace zasuzo gidan AK ɗin kuma cikin dabara ta hanasu akan su bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai a maida Farah baki ɗaya dan ya kamata takoma ɗakin mijinta tunda ta samu sauƙi.

     Da farko Zakiyya ta tubure akan Farah bazata komaba har sai AK ya saki Zinneerah, zuwa lokacin Farahn ta haihu. Kallonta kawai Mahma tai tana gitgiza kai da sake yarda da zancen AK. Kamar zatai magana akan cikin Farah ɗin sai tai musu shiru kawai. Dan ita Farah ɗince da kanta tace zata koma gidanta saboda tunowa da zafafan gargaɗin AK. Ba aunty Zakiyya da Mammah ba hatta Mahma sai da tai mamakin furicin na Farah, amma sai batace komaiba tai murmushi kawai.

     Aunty Zakiyya kuwa wani shegen harara ta watsa mata da faɗin “Saiki koma ballagaza kawai mayyar miji”.

     Kaucewa dukan nata tayi tana kumbura baki, dan ita dai wlhy shawarar Adilah da sukai waya jiya da daddare zatabi, gara ta koma koma mi za'ayi ayisa acan.


★★★


     Hajiya iya kuwa data koma duk da tana fushi da Uncle Ahmad har yanzu taƙi saurarensa dan ta dage sai ya ƙara aure ya ajiye matar a Nigeria koda zata barsa ya koma. Kokuma ya bar iyalansa anan. Wannan shine zaɓin data bashi kawai ta tsuke bakinta.

      Zaunar dasu tai shida Baffah da Mommy ta sanar musu komai daya faru. Baffah dai yasha mamaki wannan al'amari, Uncle Ahmad kuwa da dama gaba ɗaya hasashensa da nazarinsa ya tafi kacokan a wajen ne tunda Baffah ya bashi labarin abinda ya faru da tarihin Zinneerah sai baiji komai ba sai takaici da tausayin Zinneerah ɗin.

        Cikin zafinsa yace, “Aiko indai ta tabbata sune suka aikata yanda sukai wasa da rayuwar yarinyarnan suma tasu saita shiga garari wlhy, dan bazamu barsuba sai inda ƙarfinmu ya ƙare. Gatan da suka kalleta da tashinsa a farko har suka aikata mata wannan ta'asar zasu tabbatar da tunaninau gurɓatacce ne kuwa”.

       Ɗari bisa ɗari duk suka bashi goyon baya. Suna cikin tattauna yanda zasu ɓulloma al'amarin Khalipha ya shigo gidan, shine ya musu ƙarin bayani akan kamo hajiya lanti da sukai a yanzu haka kuma tana hannun hukuma, Alhmdllh kuma ta bada haɗin kai akan cewar zata sadasu da hajiyar data kaima su Zinneerah dan itama saboda ita taje katsina. Amma sai ta tarar tana saudia dan can ta koma da zama. dama can sana'arta kai yara saudia aikatau, duniyace tai mata gwatson ƙyanwa tunda aka cimimiyota ta dawo kuɗin komawa ya gagareta. To yanzu dai Alhmdllh akwai bikin yaronta da akai a wannan satin rana ɗayama da nasu Zinneerah, itama jira take a gama bikin dama ta sameta dan tazo Nigeria. 

       Sunji daɗin jin hakan, a take suka yanke zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama a damƙota kawai kafin ta sake tafiya, suma kuma su Mammah karsu bar ƙasar.

        A wannan tattaunawar AK da yazo gidan gaishesu ya samesu. Zama yay suka ɗan ƙara tattauna zancen sannan ya shiga ya gaida matan gidan. Daga haka ya ɗauka little daya maƙale masa suka wuce gida dan sai da ya fara zuwa ya gaishe dasu Mammah. Acan ɗinma bai nuna musu komaiba, dan koda Farah tace zata koma gida gobe a taƙaice yace mata, “Ƙofa abuɗe take”  daga haka yaja bakinsa ya tsuke. Bai kuma bi takantaba harya baro gidan. Aunty Zakiyya kam bata tanka masaba shima bai tanka mataba dan idan taurin kai ne gidan ta taras.


______________________


      *_DANYA_*


    Ƴan biki sun dawo gida lafiya, yayinda kowa ya fara ƙoƙarin fesar da maganar daya gumtso akan auren na Zinneerah da daular duniyar da ALLAH ya kaita ciki. Ga miji ɗan gaske acewarsu (🤣ba bily ba😂). Wasuma da biyu suke ƙara kambama zancen dan baƙanta ran Inna data haukace musu da bala'in su fice mata a gida.

           Ko'a jikinsu, dan da suka fitanma gaba suka ƙara wajen isar da labarai kala-kala harda waɗanda ba'ayiba ma. Gasu Yaya Gajeje kuwa ga labarin a ransu ga tsoron tunkarar Inna da batun abinda suke hasashe tattare da Tinene, dan tunda suka shigo gidan ɗaki ta shige ta ƙudundune a zani tana rawar sanyi.

      Da ƙyar Yaya Gajeje taja ƙafafunta ta nufi gidan saboda yara data bari, gashi yamma nayi tunda tana ƙauyen gaba dasune duk da babu nisa.

     Duk da takaici da zafin da inna keji a ranta da labarin ɗaukakar da Zinneerah ta samu hakan bai hanata zaman jin labari a bakinsu Atine dakeyi suna gatsine-gatsine ba kishi fal ransu. Abinda kuma sukazo dashi sai faman ci suke har Inna ɗin dan tace raba mugu da makami ibada ne..   (😂🤣gaskiya kam aunty Asabe)

      Shi Baba ma da amaryarsa dake jiyosu daga ƙofar ɗaki dariya suka basu, musamman Inna da baba yasan shegen kwaɗayinta bazai barta ta kasa cin abinda akazo da shi dinba koda kuwa tanaci tana kuka ne.


     Washe gari da safe jikin Tinene ya ƙara tsananta, tun dare taketa kwara amai har safiya ta tashi a galabaice. Baba ya ce ta shirya suje asibi maybe dai typhoid ne ke damunta, dan itace kesa zazzaɓi mai zafi haka da naci. Amaryar baba ba sanin ciki tai ba sosai, Inna kuma idanunta ya rufe da damuwar ɗaukakar Zinneerah sam taƙi fahimtar halin da Tinene ke ciki. Su kuma su Karima tsoron faɗar abinda ransu ke raya musu inna ta hau tsinarsu sukeyi.

     Ana haka sai ga Gwaggo Laritu tazo domin ai zaman raba alkairin da AK ya basu, bata jima da zama ba Yaya Gajeje ta iso itama. Cikinsu babu wanda yay magana akan shirin kai Tinene asibiti da baba ke shirin yi. Sai da Gwaggo Laritu tai wani tunani sannan tai magana.

       “Niko Yaya nakega kai Tinene asibiti bazai jawo komai a garin nanba sai kace nace. Musamman ma daya kasance asibitin garin nan zakuje”.

     Da mamaki baba yace, “Kace nace kuma Laritu, akan ciwon?”.

     “Tabbas kuwa Yaya, dan banga amfanin aita ɓoye-ɓoye ba akan abinda kowa yasan dama wajib ne. Dan shi dai sharri ɗan aike ne dama shiyyasa ake nusar damu illarsa ga aikama kowa. Asabe tama Zinneerah fata kuma ALLAH ya karɓa mata, sai dai kuma ga sakamakon nan ya dawo ga Tinene. Dan babu wani taifot dake damunta ciki ne jikin wannan yarinyar wlhy”.

    Ba baba da amaryarsaba hatta da Inna dake jiran Gwaggo Laritu takai ƙarshe ta sauke mata kwandunan bala'in da take Tattarowa a take ta saki robar ruwan wankan ƴar Karima data ɗauka zata sako ruwan zafi, ALLAH yasotama bata kai ga zubawarba.

      Wani irin shuuu taji abu ya gitta mata cikin idanu da ƙwaƙwalwa saboda tsabar razani. Cikin rawar baki tace, “Munahika annamimiya, Laritu kirasa wanda zakima wannan sherin sai ɗiyar zumunki. To wlhy sai dai kiga ciki a jikin jikokinki, ALLAH ya isa kuma sherin da kikaima yarinyata”.

     Murmushi kawai Gwaggo Laritu tayi. amma uffan bata sake cewa ba. sai Yaya Gajeje ce tace, “Inna ya kamata ki fahimci zancen Gwaggo, ku kuma nutsu wajen karantar Tinene wlhy cikine da yarinyar nan da gaske”.

        Baki sake tabi Gajeje da kallo, sai jitai Atine tace, “Wlhy Inna da gaske ne, ki kalla Tinene da ƙyau zaki tabbatar”.

         Tsitt gidan yayi saboda kakarin aman Tinene, Inna ta fashe da kuka jikinta na wani irin rawa lokacin da idonta ya sauka akan Tinene da har ciki ya fara tasawa sama kaɗan, da alama ma ya wuce watannin da suke hasashensa. Baba kansa baya yay sai da amaryarsa ta riƙosa jikinta na rawa itama dan batason damuwa sam, musamman ma yanzu data samu cikin nan. Kafin wani ya samu damar sake cewa uffan sukaji ana rangaɗa sallama daga waje. Da ƙyar baba ya iya amsawa da nufar hanyar ƙofar gidan domin duba wanene. Da Laminu ƙanin Babawo yaci karo, Laminu ya gaishesa da girmamawa yana miƙa masa takardar hannunsa da nuna masa kayan daya sauke a mashin ƙasa. “Baba Sule gashi inji Yayana Babawo, yace a bama Karima tare da waɗan nan kayan. Yace a sanar mata ta tuna yau saura sati biyu wa'adin da kotu ta bata na kai kuɗin sarƙar hajiyar data satamawa ya cika”.

     Cikin rashin fahimta baba yace, “Laminu ban fahimcekaba nikam sam, amma kaga shigo daga ciki kai bayani agaban Karimar”.

    Babu musu kuwa yabi baba ciki, bayanin daya zayyana masa shiya sake maimaitawa Karima.

    Gani kawai sukai ta saki ƴar sai da Atine tai azamar tarota tana ambaton, “Na shiga uku Karima baki da hankaline?”.

    Ina Karima ba saurarenta takeba, dan atakema gani sukai ta yanke jiki ta faɗi, Inna ma da tun fara bayanin garin ke juya mata da wata irin hajijiya sai tabi bayan Karima ta zube ƙasa.

     Ƙarar da Atine da Sa'a suka ƙwalla na firgici ya saka amaryar baba dafe bango saboda wani irin murɗawa da mararta tayi alamar tahowar naƙuda.........


____________________


    *_KANO_*


  Bayan wucewar su mmn Halima

salla kawai Zinneerah ta samu tayi ta la'asar. Duk yanda taso daurewa da zazzaɓin daya rufeta kasawa tai, dole ta rrrafa saman gado ta kwanta dajan bargo ta lulluɓe tana rawar ɗari. 

      Cikin barcin daya ɗan fara figarta little ya faɗo mata a jiki yana faɗin, “Aunty!” cike da farin cikin ganinta. Buɗe idanu tayi da ƙyar tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar yaron mai tsananin kama da mahaifinsa. Ta ɗan lumshe ta buɗe da ciro hannunta a bargon da ƙyar ta shafa kansa. 

        “Kaga ka tadani daga ɗan barcin dana fara sweetheart, waye ya kawoka?”.

       “Abbana”. 

Ya bata amsa kansa tsaye yana ƙara daka tsalle akanta.

       “Wai ALLAH little karka ƙarasani dan ALLAH, ka tausaya mani”. Ta faɗa tana yunƙurin miƙewa zaune. Idontane suka sauka akan AK dake bakin ƙifa tsaye kawai yana binsu da kallo tamkar ya samu television.

      “Barka da dawowa” tai maganar da maida idonta ƙasa. Batare daya amsaba ya tako ciki sosai, a kusa da ita ya zauna da kamo little dake ɗane mata wuya...........✍

     

       

         *_Na gode da addu'oinku, na samu sauki Alhmdllh. Asha hutun weekend lafiya😘😍😍_*


No comments

Powered by Blogger.