Makauniyar Kaddara 64
Page 64*
............Cikin dakiya Baffah yace, “Wannan hukunci naka yayi dai-dai kuma na gamsu dashi nima wlhy, dan haka nima ga nawa hukuncin akan ƴaƴana da Hindatu. Duk da ni bazan rabaki dasu ba amma tabbas zan
nesanta rayuwarsu da taki. Daga yau Abdul-Mutallab zai dawo rayuwa a Nigeria, idan har kikaga ƙafarsa a london sai dai harkar kasuwarsa amma bada rayuwaba. Hukunci na biyu anan gurin nakeson a ɗaura auren Huzaifa da Adilah itama ta baro can har abada sai dai taje domin gaisheki ita da mijinta. Hukunci na ƙarshe karna sake ganin ƙafar Hindatu a gidana har abada, idan kuma ta sake shigowa nima zanyi ƙararta........”Katsesa Abba yayi (mijin mmn sadiq) “A'a dan ALLAH ayi haƙuri Alhaji Kabeer, ai ko babu komai ALLAH ya haɗa tunda gashi har an fara ajiye jikoki bama ƴaƴa ba. Hukuncin dawowar yara dai yayi amma ita kar ace bazata zo nan ba dan ba'asan mi rayuwa zatai nan gaba ba”.
Wambai yace, “Maganarka gaskiyane Alhaji Abubakar, a daiyi haƙuri Alhaji kabeer a tsaya kan yaran kawai domin ALLAH. Babu yanda za'ai tunda zuminci ya sarƙa a tsakani, koba komai darajar shi Abdul-Mutallab ɗin da biyayyarsa a ɗagama Hindatu ƙafa. Mai afkuwa ta afku, kamar yanda kuma Malam Sulaiman yay bayani ALLAH ya bama kowa sakamakonsa tun a duniya tunda mainakon nasara duk faɗuwa sukai batare da sun ci nasarar burinsu ba. Koba komai ita wannan yarinya MAKAUNIYAR ƘADDARA ta zame mata BUƊAƊƊEN HASKE, ta mallaki ɗa, ta mallaki uban ɗa, sarƙin dake tsakanin iyayenta ya buɗe, sai muyita mata fatan gamawa da rayuwa mai albarka har ƙarshen numfashinta. Su kuma nema gafararta dan alhakinta bazai barsu cigaba da rayuwa cikin salamaba. Suma kuma waɗanda suka sakema ta'asar a nemesu aji ta bakinsu, idan kuma da amincewarsu ne shikenan ai. Sai a tattara a barma UBANGIJI ikonsa. Koda hukuncin mai martaba aka barsu ya ishi rayuwarsu izina. Masu shirin aikata wanan taɓargazar ko ma suka aikata suma sufa sani sakamakonsu naga ALLAH, dan shine kaɗai yasan hukuncin daya dace ga mutane irinsu. Ina amfanin abinda yahudu da nasara suka ƙirƙira da har zai birgeku wajen aikatawa bayan kuna al'ummar musulmai? Koba komai ka nuna rauninka kenan ga jarabawar da UBANGIJI yay maka domin gwada imaninka. Sannan zata iya yuwa shi wannan ɗan ya girma ma ya gallabi rayuwarka, ƙilama yay sanadin hallakaka ko shigarka wuta. Dan ƴaƴa da yawa sune zasu kai iyayensu wuta. Dan haka ya kamata mu kiyaye, dan kana neman haihuwa bai kamata kabi ta kowacce hanya domin samu ba. Hakan son zuciyace da rashin godiyar ALLAH. Domin idan zaka nutsu ga ni'imominsa ya maka ta hanyoyi da dama ba sai ta haihuwa ba, ko musulinci da yayika aciki da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W) daya dasa maka a zuciya kawai aka barka ya maka babban ɗaukaka da rahama. Balle wanima zakaga bayan wannan akwai wasu tanade-tanade da UBANGIJIN yayma rayuwarsa waɗanda shi kansa baima san yawan adadinsu ba. Amma saboda kawai ya jarabcesa da rashin samun ƴaƴa sai ya ruɗe ya fita hayyacinsa. Kaiconmu da wannan shiriritar, nasan rashi ƴaƴa nada zafi a rai da damuwa. Amma duk abinda ka ɗaukesa mai sauƙi sai UBANGIJI ya sake sauƙaƙa makashi kai ma a zuciyarka da ayyukanka. Idan kuma ka dage sai ka samu to lallai San zuciya kuwa ai ɓacintane ga duk mai sha'awa ko buri. Duk wanda basu haihu ba ya ALLAH ka azurtasu da zuri'a masu albarka a garesu, idan ba alkairi bane ALLAH ka sakanka musu da abinda yafi alkairi, ka yalwatasu da tarin haƙuri da juriya a zukatansu”.
Da amin duk suka shiga amsawa, kuma kowa ya gansu da bayanin waziri, saurama suka shiga tofa albarkacin bakinsu. Sai da duk mazan suka gama kace nace Mahma da tun ɗazun al'ajabin su Zakiyya ya hanata tofa komai ta duba su Zakiyyan. “Wannan shine abinda naketa nusar daku amma kuka kasa fahimta, bansan miyasa a mafi yawan lokuta gatan rayuwa da tagomashin arziƙi dake zuwa cikin hannayenmu ke dulmiyar da zukatajen jin muna sama da kowa ba. Zamu iya zartar da hukunci ga kowa, zamu iya taka kowa dan ko anje an dawo babu yanda zaiyi damu. Duk da dai anata maimaita magana ɗaya amma dolene a faɗa. Kun zalunci yarinya saboda kuna mata kallon mai ƙarancin gata, sai gashi UBANGIJI ya biyo muku ta inda bakuyi zatoba ya ruftaku a ramin da kuka tanadi sakata ku kuka afka. Shi kansa Abdul-Mutallab kun cutar dashi ai, gara ace fitowa kukai kuka shaida masa ƙudurinku, idan ya amince fine, idan bai aminceba sai ku bi duk hanyar data dace wajen ganin kun lallaɓasa ya yardan koku haƙura har ALLAH ya kawo mata iyakar da zata samu. To yanzu dai dukma abinda zai faru ya faru. kun aikata a ɓoye ALLAH ya buɗa kowa ya gani, kunyi danku tsare mutuncinku gashi ya zube a idanun kowa. Kunyi don samun haihuwa, gashi an haihu ɗan yafi ƙarfinku dan nima ina bada goyon bayan hukuncin Abdul-Hakim (Mai martaba), kunyi dan gudun kishiya, ga kishiyar nan mai daraja ma kuwa da inhar Abdul-Mutallab ya wulaƙantata koda na second guda bazamu yafe masaba, dan ta cancanci a kula da ita a riritata. Kunyi dan kar Abdul-Mutallab ya suɓuce muku, gashi ya suɓuce mukun ya dawo inda baƙwaso ya rayu dagashi har ƴar uwarsa. Da wannan kawai aka barku ya isheku, dan nidai banga ribar da kukaciba anan sai asarar kuɗaɗenku dana lokacinku da kukayi a banza a wofi, idan kuma wannan baiwa da waɗan can ma basu yafe mukuba to yanzu aka fara wasan. Koda sun yafe muku sai kuma ku jira hukuncin UBANGIJI a gareku dan shi ne yafimu sanin abinda ya cancanta da mutane masu hali irin naku. Hindatu kinfi kowa ganganci matsayinki na uwa, duk da kuwa Zakiyya ce tai amfani da abinda ke damuwarki ta sarrafaki cikin sauƙi kika afka, amma ba komai ya jawo hakanba sai gurɓataccen tunaninki da son zuciyarki. Wanda inada tabbacin son Kabeer ne ɗawainiya dake ba komaiba, girman kai ya hanaki nutsuwa ki nema sulhu da shi sai kike huce komai akan yaronsa da baijiba bai gani ba. Gashi nan ai kin rasa Kabeer ɗin da Abdul-Mutallab ɗin duka harma da Adilah. ALLAH UBANGIJI ya rabamu da son zuciyoyinmu, ya yalwatamu da haƙurin ibadarka. Daga ƙarshe dan ALLAH ina roƙama ƴan uwana gafara a gareku iyayen Zinneerah, ku yafe musu, karkuyi dubi da halayensu da cutar da sukaima ƴarku. Dan tunkan aje ko ina ALLAH ya saka mata. Dan ALLAH ku gafarcesu ko zasu sami sassauci daga raɗaɗin da za'a bar rayuwarsu da shi. Keko Zinneerah bazance ki yafe musu ba, idan zaki iya yafe musu Alhmdllh, idan kinga bazaki iyaba ki barsu da ALLAH zai cigaba da saka miki ta hanyoyi daban-daban kamar yanda ya fara tun yanzu anan duniya. Kabeer da Hajiya Mama (Hajiya iya) kuma dan ALLAH ku yafe musu badan halinsu ba, kodan darajar Abdul-Mutallab dake a tsakani, dan ya can-can-cin yabo yaron nan ta fannoni daban-daban. Duk da kun sakashi a tsakiya game da wannan al'amari a koda yaushe burinsa yaga ya saka farin ciki a zukatan kowannenku koda kuwa shi zai ƙuntata tashi zuciyar. Dan ALLAH muyi haƙuri mu yafi juna kodan shima yay farin cikin da yaketa fata akan kwanciyar hankalinmu”.
Baba ne ya fara jinjina kansa bayan kammalawar Mahma. Yace, “Kinyi bayani mai ƙyau hajiya, kuma nidai ta ɓangarena na yafe musu wlhy, dan koba komai abinda suka aikata ɗin ya zama tsanin nasara ga gudan jinina. Shiyyasa akace idan kaga UBANGIJI ya jarabceka da wani al'amari ka nutsu wajen kwatanta haƙuri dan zata iya yuwuwa wani tsanin zuwa ga nasara ne. Na yafe musu. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”.
A take aka shiga amsawa da amin duk cikin farin ciki. Maman sadiq da batace komaiba tun zamanta a wajen, tace, “Tabbas abubuwa da yawa sun faru an maimaita wasu anan amma wasu bazasu maimaituba. Ni shaidace daga wahalhalun cikin nan da yarinyarnan tasha wanda da da ƙarar kwana ranar haihuwarsa da ta bar duniya. Amma Alhmdllh, nagodama UBANGIJIN daya rayata, ya kuma kaimu ga ganin wannan ranar tunda gata a ɗakin mijinta cikin mutinci, kuma gaskiya ta buɗe a garemu ALLAH ya wanketa tun anan dunuya. Da yaso sai ya barmu muyita kallonta da laifin har ranar tashin alƙiyama. Nima na yafe muku domin ALLAH da wasu dalilai da Gwaggo ce silarsu (Hajiya iya) ALLAH ya yafe mana baki ɗaya ya kuma kiyaye na gaba”.
Itama godiya suka shiga mata da amsawa da amin. Kafin Hajiya iya ta fara magana.
“Tabbas dolene nima nace a yafemin ɗin bisa wani dalili, dan ƙila daban matsama Moddibo da ƙara aure ba da tunaninsu bai karkata ga hakan ba. Ni kuma ba komaine ya sani damuwarba sai ganin yanda matarsa bata ɗaukemi da darajaba. Hakama Hindatu. dan duk da Kabeer ya fita ƙarfin faɗa aji akan yarannan tana nuna masa iko a kansu, ko zancen auren yarinyarnan bamusan komai ba saida yazo gab. Koda yake duk ta wani tone-tone ya wuce, Moddibo ka yafemin kai da matarka dan zan iya saka kaina matsayin silar faruwar komai”.
“Bake bace sila Granny, dan koda kikace na ƙara aure baki tursasaniba, sannan tsarin da sukazo muku dashi ya sakaki wannan tunanin kema. Dan haka nikam kima daina neman gafarata bakimin komaiba why”. AK ne ya faɗa cikin dauriyar abinda yakeji game da jikinsa.
Mammah ta karɓe da faɗin, “Tabbar Inna ba laifinki bane, nice da wannan laifin, dan daban zurfafa da yawaba akan yaran nan da Zakiyya bataci galaba a kainaba har nakai ga bata goyon bayaba, dan ALLAH Adnan ka yafe min kaji, ajizancine na ɗan adam da son zuciya da tsoron rasaku tamkar yanda gangancina ya kaini ga rasa kabeer. Kishi ba hauka bane, kuma halas ne. Amma irin namu yayi muni da yawa dan muna zafafawa, da nayi haƙuri da hukuncinsa a wancan lokacin da duk haka bata faruba na tabbata. Dan ALLAH ku gafarceni baki ɗaya. Ɗiyata Zinneerah kema dan ALLAH ki yafemin kinji, wlhy bazan ɓoye mukuba tun randa na diro ƙasarnan naga yaron nan da kika haifa ƙaunarki data yaron ta kamani, duk abinda kukaga inayi borin kunyane kawai, amma har cikin raina son ɗanki dake kanki ya shigeni, koda nake cewa kar Adnan ya taɓaki ya sakeki inason na gwada yanda yake sonkine kawai ba wani abuba, kuma koda ya gama tsarani bawai ban fahimci tsaranin yayba. Sarai na san bazai iya sakinkiba wlhy, nima kuma bama zan yarda yay wannan taɓargazarba. Ki yafemin na ƙara roƙonki......”
Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza mata kai, “Mammah dan ALLAH ki daina roƙona. Wlhy ni bakimin komaiba sai tarin alkairi kodan zama mahaifiya ga Yayanmu da kikayi. Kuma ni kallon uwa nake miki daman, har abada kuma zan cigaba da kallonki da wannan kimar da darajar. Dan haka ki ɗauka bakimin komaiba. Idanma kinmin na yafe miki wlhy”.
Tasowa Mammah tayi ta rungume zinneerah tana saka mata albarka. Kamar yanda zancen nata ya saka kowa dake falon murmushi, duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata baiwar shirya lafuza masu taushi ga nagaba da ita duk da kuwa ko ba'a faɗa da gaske an tauye mata haƙinta.
Farah da Zakiyya dai babu wanda ya roƙa gafarar Zinneerah, babu kuma wanda yace dasu ƙala akan hakan, kai kowama basu roƙaba sai kuka da sukeyi kawai. Dan haka mai martaba ya umarci AK da mijin Aunty Zakiyya da shima yana a wajen akan su basu saki. Babu wanda yace komai a falon, sai AK ne ya miƙa hannu ya amshi takarda da biro daga hanun Baba Wambai. Haka shima mijin aunty Zakiyya.
Gani kawai sukai Zinneerah ta tashi da sauri taje gaban AK ta durƙusa. Biron daya dasa akan takardar ta riƙe da fashe masa da kuka tana girgiza kai. Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonta. “Yayanmu dan ALLAH karka aikata, na roƙeka karka saketa. Kuma koba hakaba ka tausaya mata ba laifinta bane itama tursata akayi”. Tai saurin juyawa ga mai martaba dake mata kallon mamaki hakama sauran jama'ar falon. “Abbah dan girmana ALLAH kayi haƙuri ka janye wannan hukuncin naka koda kuwa sauran zasu tabbata. Gara komi za'a musu ai musu da igiyar aurensu kar'a rabasu da iyalansu na roƙeka Abbah. Dan ALLAH kodan maraicinsu ai musu afuwa, wlhy na tsani naga an saki mace inajin ciwo. Granny, Baffah, Mahma, Babana dan ALLAH kusa baki, Abba dan ALLAH ku bama Abbah haƙuri dasu Yayanmu karsu aikata”.
Yanda take kuka kamar ranta zai fita sai duk hankulansu suka tashi. Dan har suƙewa takeyi, ƙoƙarin son fisge pen ɗin AK yayi yana harararta ta sake damƙesa da fashe masa da kuka. “Yayanmu dan ALLAH, kodan ƙyautar little da ALLAH ya azurtaka da shi ka taimaka karkayi, idan ka saketa ALLAH nima bazan zauna da kai ba, zan ɗauke little na tafi inda bazaka sake ganinmuba wlhy”.
Kansa dake sara masa ya dafe, da wannan damar ta samu amshe takardar da biron, ta koma gaban Mai martaba ta gurfana tana cigaba da roƙonsa shi da su baba wambai da su waziri. Sosai ta basu tausayi ta kuma sake birge kowa. dan haka hajiya iya tai ɗan murmushi da duban mai martaba ɗin da shi kansa yakejin wani irin ƙaunar Zinneerah na shigarsa. Dan koda ƴaƴansa suka kasance masu laifi bazaiso mutuwar aurensuba ai. Sai dai kuma dolene ya yanke musu hukunci domin yin gargaɗi.
“Inaga a amsa kukan Zinneerah dan ALLAH, za'a iyama su Farah hukunci bawai sai an katsa igiyoyin aurensu ba, dan koda abinda duk ya faru aka barsu ya ishesu tunawa da ishara har ƙarshen rayuwa. Ayi haƙuri dan ALLAH”.
Ƙasa kawai mai martaba yayi da kansa dan yana ganin girman tsohuwar ainun, yanda yayi ɗin ne ya saka sauran ƴan falonma fara roƙonsa harma dasu AK kansu. Ganin sun masa taron dangi ya sashi jan numfashi da dafa kan Zinneerah ya shiga jera mata addu'oi masu daraja da ake jifan mutum mai daraja dasu. Sai da ya gama ana amsawa da amin sannan yace, “Shikenan zan janye maganar saki, amma kuma dolene sai sunje masarauta sunyi wancan zaman wlhy, sauran hukuncin kuma tsakanina da sune. ALLAH yay miki albarka ke kuma, daga yau kema kin zama cikin jerin ƴaƴana”.
Kabbara aka ɗauka a take. Kowa na nuna jin daɗinsa da farin ciki. Daga haka Hajiya iya tai musu nasiha. Hakama baba wambai yayi musu sannan shima maimartaba ya ɗaura tashi, daga ƙarshe aka rufe taro da addu'a saboda lokacin sallar zuhur yayi.
★★★
Ana idar da sallar azhar aka gabatar da ɗaurin auren Huzaifa da Adilah bisa alƙawarin Baffah, dan dama sun gama magana da mahaifin Huzaifa tun daren jiya, ya kumace ya bashi wuƙa da nama dan zaman Huzaifa hakan ya ishesa dama. Shima dan baya Nigeria ne da dashi za'ai komai a yau.
Koda suka dawo cikin gida tuni labari yaje kunen kowa. Zokaga murna wajen ango da amarya dan dama sun folama juna tuni. Daga haka sukai zaman cin abincin da matan Baffah suka shirya musu, suka kuma sake tattaunawa a tsakaninsu na maza. Kamar yanda anan cikin gida suma su Granny basu gaji da sake tattauna zantukanba a tsakaninsu. Mahma taja su Zakiyya gefe tana musu faɗa akan ƙin neman gafarar kowa da sukayi. Ta zazzagesu tas tai gaba ta barsu batare da kowa ya sani ba.
AK kam bayajin daɗin jikinsa, dauriya kawai yakeyi, hakama Zinneerah tana gadon Granny ƙudunsune dan zazzaɓi na neman dawo mata sabo ga ciwon kai na kukan data sha. Tanason zuwa ta gaisa da Baba ma ta kasa.
Zuwa la'asar su maimartaba suka fara tafiya bayan ya tasa su Farah dake faman kuka gaba ya wuce dasu masarauta, harda Baba dan yanason ya shiga har ƙauyen Danya yayma baba rakkiya ya kuma gana da dagacin garin danya ta silar baba. Hakan yama Zinneerah data fito suka gaisa da ƙyar daɗi, yau ga babanta ga maimartaba wata hikima sai UBANGIJI. Shima kansa AK hakan da maimartaba yayi ya masa daɗi sosai.
Bayan wucewarsu suma su mmn sadiq suka wuce, suma hajji Lanti tafiya sukai bayan sun sake gurfana neman gafara ga Zinneerah da AK dama su Hajiya iya baki ɗaya.
Da wannan damar Mammah ta samu suka sake zama ita da Mahma dasu Baffah ta ƙara neman gafararsu da sake tattauna duk abinda ya faru. AK dai bai zaunaba ɗakinsa ma ya shige yay kwanciyarsa dan bayajin daɗi, ya tabbatar yau jininsa yayi ƙololuwar hawa tabbas.
Hajiya iya ce ta hana su Mammah komawa gidan mijin Zakiyya. Tace Khalipha zaije ya ɗakko musu kayansu suyi zamansu anan har randa za'aje ga yarinyar datake rainon cikin a Morocco.
Zinneerah ma dai magani Granny ta bata tasha ta kwanta.
________________________
*_DANYA_*
Su baba sun iso danya da tawagar maimartaba. Inda tsabar ruɗewar da maigari yayi kai kace zai kife ƙasa. Maimartaba da kansa yau a ƙauyensa, bayan ko'a labari bai taɓa jin ko kusada wajen hakimi yaje ba sai dai ya aiko wakili idanma wani abune ya taso. Ai baima san ya gurfana yana kwasar gaisuwa ba. Hakama garin danya cikin ƙanƙanin lokaci labarin zuwan maimartaba da baba a tare ya shiga kunnen kowa harsu Inna da ke kwance rijib cikin ciwo. Dan tun zancen cikin Tinene dajin uwar sata da Karima ta kima na sarƙar zinarin wata hajiya da har yay silar Babawo yimata dukan mutuwa ya korota gida ta yanke jiki ta faɗi aketa fama har yanzun. Dan saki uku Babawo yayma Karima. Ga kuma aike daga kotu cewar Karima zata biya naira dubu ɗari huɗu na sarƙar mata bayan tara kuma da zaman kaso na wata shidda bayan ta yaye ɗiyarta. Ga zancen cikin Tinene ya baje ko ina na garin danya da kewaye har ƴammata sun dasa mata waƙar dandali. Matan aure kuwa da biyu suke zuwa barkar ƴan biyun amaryar baba dansu sake tabbatar da zancen ciki da halin da Inna ke ciki na samun ciwon ɓarin jiki a silar faɗuwar da tayi.
Ga ƴan uwan amaryar baba sun cika gida daga jiya zuwa yau dan ana haihuwa baba ya kirasu ya sanar musu. A safiyar jiya saiga kusan mutane shidda sunzo, sauran kuwa sai daren suna. Duk abinda ke faruwa kuwa akan idonsune sai mamaki sukeyi kamar almara ko hikayoyin marubuta.
Cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan maigari ya cika taf da jama'ar gari saboda kiranye da aka saka sanƙira yayi musu. Ciki kuwa har dasu Sa'a a ƴan kallon zuwa ganin maimartaba. Sai da guri ya nutsa sannan maimartaba ya fito. A take waje ya ruɗe yau gasu ga maimartaba. Farin ciki duk ya bayyana a fuskokinsu kamar shima yanda yaji daɗin yanda suka amshesa duk da basu da wani cigaban kirki a garin, zaima iya cewa baisan da zamansuba saita wannan silar. Sai yaji zuciyarsa ta ƙara rauni da karaya akan nauyin al'umma dake kansa.
Bayan Matawalle ya isar da saƙon gaisuwar sarki a garesu ya gabatar da hajji lanti a gabansu tai bayani akan silar ɗaukar Zinneerah zuwa birnin katsina. Itama Hajiya Haule tayi bayani kamar yanda tayi a kano. Kafin Zakiyya ma da takejin tamjar ranta zai fashe tai nata bayanin akan gaskiyar dasama Zinneerah ciki da sukai ba ta hanyar iskanci ta samosa ba.
Take gurin ya ƙara ruɗewa da al'ajab da mamaki. Ɗunbin tausayi da nadamar cin kashin da suka dinga ma yarinya ya ringa dawo musu a rai harda masu kuka. Kafin wani dogon lokaci labari ya ƙara kaiwa ga mata dake cikin gida da jama'ar sauran ƙauyukan gefensu da duk sukasan da labarin cikin na Zinneerah. Abinka kuma da ƙananun gari babu wanda ya manta musamman daya kasance ba'a jima da zuwa akai bikin Zinneerah ɗin ba. Bakajin komai sai ALLAH wadarai ga Inna asabe dasu Zakiyya. Dan su maimartaba kan sun tafi sunbar abin faɗa ga mutane. Musamman daya kasance yanzu ALLAH ya bama Zinneerah cigaban rayuwa. Ga kuma samakon nan a jikin Tinene da ita kanta Innar dake kwance rijif ita ba gawaba ba kuma rayayya ba.
Ita kanta da labarin yaje mata sai gata tana hawaye zuciyarta na ƙara hauhawar zafi. Daga ƙarshe jikintane ya ruɗe sai da aka kwasheta zuwa asibitin cikin kusada..............✍
Leave a Comment