Makauniyar Kaddara 67

 


Page 67*


.............Alhmdllhi sosai zuwan Mahma ya taimakawa Zinneerah, dan tana ɗebe mata kewa da rage wasu abubuwan. Tana kwana na huɗu ma da zuwa sai ga wata dattijuwa Hajiya iya data sa aka kawo mata daga bauchi ta iso. Nanma ya haɗu ya ƙara

taimakawa Zinneerah ɗin sosai. Dan Mama A'i mace ce mai ƙoƙari da haƙuri. Gashi bata da yawan hayaniya itama ga kuma tsafta. Hakan yasa tasu tazo ɗaya da AK. Duk da dai iyakacinta ɗan taya aikin gida Mahma ke musu girki, wani lokacin kuma Zinneerah ɗin kan shiga da kanta tayi. Hidimar Little kuwa dama ta koma hannun Mahma. Yanzu ma a ɗakinta yake kwana abinsa.

     Haka aka cigaba da turawa har ALLAH ya sauka Tinene lafiya daga danya. Ta samu ƴarta mace mai kama da ubanta sak. A randa ta haihu a ranar aka ɗaura aurenta da Lado. Bayan arba'in zata ta tare. Baba bai gayama Sa'a da Zinneerah ba sai kusan kwanaki biyar da haihuwar ma. Dukansu sun mata addu'a da fatan alkairi, suka kuma aika musu da abinda ALLAH ya hore musu tunda duk ba sana'a sukeba. Dan Sa'a ma makaranta ta koma Dr Mahmud nason ta haɗa kwalinta na secondary da shirirta da halin Inna yasata kasa haɗawa. Tunda koda ta koma bayan baro Zinneerah Danya bata kammalaba tunda komawa tai ta fara daga js1.

       Ranar tarewar ma da ƙyar AK ya yarda suka tafi ita da Sa'a. Amma ya tabbatar mata banda kwana ranar zasu dawo. dan ko little ma bai bitaba ita kaɗai ta tafi Haneef ya tafi kaisu ita da Sa'a dasu Bahijja.

       Sun sami tarba mai ƙyau, dan kowa sai ji dasu yake sun zama tamkar wasu taurari a dangi baki ɗaya. Kowa nata tausayin Zinneerah da fatan ALLAH ya sauketa kafiya. itama Sa'a ALLAH ya bata nata dan har yanzu dai babu ciki.

     Ganin yanda jikin Inna ya ƙara rincaɓewa yasa hankalin Zinneerah da Sa'a ƙara tashi, dan Karima dake gidan tana kula da ita tata ƙorafi kenan da mita. Wani lokacinma sai yaya Gajeje ta yunƙuro tazo ko matar baba tai mata wani abun Karimar na zaune taƙiyi. Kiran AK tai ta sanar masa. Bai wani ja zancenba yace ta haɗashi da Haneef dan tunma ɗazu yake nemansa ya gaza samu, itama ɗin ya nemetan yaji yaya suka sauka amma bai samuba sai yanzu data kirasa.

     Umarni ya bama Haneef ɗin akan su taho da Inna kano. Batare da Zinneerah tasani ba sai da aka idar da sallar la'asar Baba ya tunkaresu da zancen. Murmushi kawai tayi bata nuna bata saniba. A ranta kuwa tana mamakin Yayansu.

       Kowa yaji daɗin abinda AK ɗin yayi, dan haka ana gama shagali basu zauna akai amarya ɗakintaba suka tattaro zasu taho, wai kuma Karima zata biyosu Baba yace bata isa ba. Yaya gajeje zata bisu daga baya. Itako ta zauna Danya.

          Sa'a ma da nufin kwana tazo, amma jin Zinneerah bazata kwana ba kuma za'a tafi da Inna sai kawai ta shirya ta biyosu. A shira hospital suka sauke Inna, inda Dr Mahmud yasan da zuwan nasu dan sunyi nagana da AK. Anan suka bar masa Sa'a bayan sunga komai ya dai-daita na kula da Inna. Haneef ya wuce da Zinneerah gida ya fara ajiyeta sannan suka wuce gida suma dasu Meenal.

         Tun daga ranar jinyar Inna ya dawo ƙarƙashin kulawar su AK, amma Yaya Gajeje tazo daga danya tana tare da ita a asibitin. Kullum sai Zinneerah taje ta dubata kamar yanda Sa'a ma haka. Alhmdllh kuma jikin nata na ƙyau ba kamar sanda tana Danya ba. Dan magunguna masu ƙyau da tsada ake mata amfani dasu, ga kulawa ta musamman da take samu daga mazan ƴaƴan nata. Baba ma lokaci-lokaci yakanzo dubata shi da yan uwansa da amaryarsa da Karima.

         

        A haka Zinneerah ta cigaba da turawa har aka shiga kwanakin jiran tsammani na haihuwarta. Zuwa yanzu kam sosai bata da lafiya tamkar cikin little, dan dolema aka koma da ita zaman asibiti. Kwanakinta shidda a asibitin a wata safiya ta wayi gari da naƙuda. Sai dai fa tamkar cikin little jini ya ɓalle mata ga haihuwar shiru. Hankalin AK da kowama ya tashi, hakan yasa Dr Mahmud ya bada shawarar kawai ai mata cs kafin ta jigata ƙarfinta ya ƙare.

    Babu wani jayayya AK ya amince. Zuciyarsa fal tausayin halin da take ciki. Yayinda yake rayawa a ransa ko wannan tashin hankali da ta shiga a wancan karon na haihuwar little ya isa hana su Farah zaman lafiya da jin daɗi. Shikam sai yanzuma yake ganin matsalar da sukaita fuskanta na rashin jin daɗin rayuwar aurensu kullum faɗa da fitina shi da Farah ko wannan halin da suka zama sanadin jefa yarinyarnan ya isa su rasa farin cikin rayuwar aurensu ai. Dan Dr Mahmud ya tabbatar masa da haka tasha irin wannan wahalar a wancan karon ma.

      Alhmdllh an yi mata cs aka ciro ƴaƴa biyu mace da namiji. Zokaga murna wajen kowa. Shikam AK duk da yana murna da samuwar tasu hankalinsa nakan matarsa. sai da yaji tabbacin kasancewarta cikin ƙoshin lafiya sannan hankalinsa ya ɗan kwanta harya amshi jariransa ƙyawawa masu lafiya yana mai jerama UBANGIJI godiya daya bashi ƙyautarsu ta silar da ALLAH ya halatta masa bayan ya cire tsammani daga hakan.

         Inna daketa samun sauƙi  tana zaune dan yanzu takan ɗan motsa jikin aka sanar mata da haihuwar Zinneerah. Hawaye kawai su Sa'a sukaga tanayi amma batace komaiba. Hakan yasa suka gagara fahintar na minene? Na daɗine kona nadama? Kona baƙin cikin har yanzu?.

     Oho masu karfin ajin ma basusan tanai ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci Shirawa suka cika asibitin domin taya Yayansu murna da samun wannan ƙaruwa. Waɗanda basa kusa kam irinsu Khalipha da Adilah tuni hotunan babes ya isa ga wayoyunsu.

       Addu'a dai kam sun shata kamar yanda Zinneerah ma keshan tata na fatan samun lafiya. dan kowa bai gantaba itakam har AK ɗin sai da daddare. Shima ya samu tanata barci. Ya ƙureta da ido cike da tausayi da ƙauna dan dukta rame sosai fiyema da lokacin da cikin na jikinta. Sumbatar goshinta yayi da hannunta yana mai jera mata addu'ar samun lafiya.


    Sauran ƴan uwa kuwa da abokan arziƙi basu sami ganintaba sai washe gari, zuwa sannan ta farka Alhmdllhi. Kuma tana gane kowa da amsama kowa gaisuwarsa.

     Lokacin da taga ƴan jinjirayenta da farin cikin dake shinfiɗe a fuskar AK murmushi ta dinga zubawa itama. a ranta tana musu addu'a. A fili kuwa sai ta dinga nuna alkunya su Hajiya iya na mata dariya. Sai dai har cikin ransu hakan da tai ya musu daɗi, dan yaran yanzu daba kawaici garemu akan ƴaƴaba koda na farine balle na biyu.

      Sai dai kuma wata sabuwa. wannan karonma tamkar haihuwar little ruwan nono ya zamarwa yaran damuwa. Dan da sun sha cikinsu duk sai yake kumbura suyita kuka. Ga namijin da son abinci tamkar ubansa. Hankalin AK ya tashi matuƙa da hakan. Amma da Dr Mahmud ya sanar masa haka dama sukasha fama akan little sai yaɗan sami nutsuwa. Yanzuma magunguna suka haɗa mata. Amma sai Mahma tace wanann al'amari kamar bana asibiti ba. Yanada nasaba da jinnu sai an dage sosai ma Zinneerah ɗin.

    Kowa yasha mamaki, amma sanin wacece ita a wannan fanin yasa duk suka amince. Itace da kanta ta fara harhaɗama Zinneerah magungunan gargajiya ta fara amfani dasu, tace insha ALLAH komai zai daidaita.


      Kwananta takwas a asibitin aka sallameta, Alhmdllhi zuwa yau kuma yara sunsha nono kuma babu wani matsala data biyo baya. Hakan ya saka kowa farin ciki dajin daɗi. AK yaga amfanin wannan sani na Mahma da yaketa ƙorafi akansa tunda gashi ta bama matarsa magani an kuma dace.

      A randa aka sallamesun ranar Mammah ta iso Nigeria, zokaga murna wajenta datai tozali da ƴan jikokinta. Su Adilah ma an iso daga Lagos suda tawagar Mommy. hakama Gwaggo Maryama. Inna ma da aka sallamota nan AK yace a kawo ta huta sosai kafin a maidata Danya.

     Kai tsaye gidan hajiya iya aka wuce da Zinneerah, za'ai suna acan sannan su koma gidansu su cigaba da jego kuma.

     Yara sunci sunayen Hajiya Iya da Baffah. *_Ameenatu & Kabeer_* za'ake kiransu (Amaan & Anam). AK ya zata Mammah zatai fushi, sai yaji batace komaiba. Yaji daɗin hakan, dan koba komai ya yarda ta dawo hankalinta yanzu kam. 

      (An zinni sai muce ALLAH ya raya keda yayanmu angon jego).

        AK dai bason bidi'a yakeba. Dan haka aka shirya ƙwarya-ƙwaryar liyafa anan harabar gidan akaci akasha kowa ya godema ALLAH. Ƴan Danya, ƴan ɗanmusa ƴan bauchi sun cika gida dam domin taya murna. Hakama mai jego da jarirai sunsha ƙyau harsun gaji masha ALLAH.

    Kowa ka gani sai son barka. Amare ma da yawansu suna maƙale da cikkuna kanana sai fatan suma ALLAH ya saukesu lafiya.


        Kwana biyu da suna AK ya takura dole su Zinneerah suka tattaro suka dawo gidansu, aranar kuma ƴan danya da ƴan ɗanmusa suka koma. Suma ƴan bauchi washe gari suka kama gabansu sai kuna wata ta taso.

      Zinneerah tayi farin cikin kasancewar gidan cike da jama'a. Dan kuwa Ga mahma ga Mammah da suka koma sashen Farah suka zauna. Ga kuma Mama Ai, ga Yaya Gajeje da Inna. karima ma maƙalewa tai taƙi bin ƴan suna. Sai Tinene da Atine ne suka koma da amaryar baba.


      Ganin al'amura komai ya daidaita jikinta yayi sauƙi kamar ba yankata akaiba Alhmdllh yasata ƙudirin tunkarar AK da batun dawowar Farah gida. Dan itako tama fi son ta dawo hakanan tunda dai tasan zuwa yanzu ta horu. Dan su Meenal suna bata labari da sukaje da Granny kwanaki duba Farah ɗin abin gwanin ban tausayi. Duk sun fita hayyacinsu ita da Zakiyyan dan horo mai tsanani maimartaba yasa aketa musu batare da sanin kowa ba. Idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka su din bane ƴan gayu ƴan ƙwalisa masuji da naira a bankuna.


          Suna zaune a falonta na farko ita da Yaya Gajeje da Karima, Yaya Gajeje tana shirya ƴan biyu da akaima wankan safe. Zinneerah ma tayi nata dan tana cikin kwalliyarta tamkar ba jego takeba. Har Karima na tsokanarta da tacigaba da kashe ɗauri baban ƴan biyu ya lallaɓo a samo gambo kafin arba'i.

        “Ya ilahi, dan ALLAH Yaya Karima barmin baki, ina ni ina wani gambo ana zaune ƙalau”.

     Dariya suka sanya mata, suna cikin dariyarne Mama A'i ta shigo riƙe da hannun Little dake kuka wai ya faɗi. Dubansu duk suka maida garesu, Karima na kamo hannun little ɗin da faɗin, “Yaya akaine Abdul?”.

       “Faɗuwa yayi, ya shigo da gudu yaci karo da kujera”. Mama A'i ta bama Karima amsa.

       Baki Zinneerah ta taɓe tana miƙama Yaya Gajeje pampas da za'a sakama Anam. Tace, “Maganinsa kenan, shidai a rayuwarsa yayi gudu, bansan daɗin mi yakeji ba sai kace wani ɗan ƙwallo”.

      Yaya gajeje ta katseta da faɗin, “Ai tsautsayi dai baya wuce ranarsa, sannu kaji Abdul ka daina gudu wannan gidan naku dake cike da kayan santsinnan, ni kaina babba idan ina tafiya wlhy a hankali nakeyi dan ji nake kamar zan faɗi”.

     Dariya Karima da A'i sukayi, Zinneerah taɗan murmusa da zancen Yaya Gajejen tana maida hankalinta ga little. “To gudun mi kakeyi?”.

      Baki ya tura gaba yana makalewa bayan Karima. “Daddyna yace nakiraki zaije anguwa”.

       “Naji to, kace ina zuwa”.

  Sai da little ɗin ya fita ta duba Mama A'i. “Mama an gama haɗa abinda ya rage ɗinne?”.

       “Eh an gama maman Abdul, harma na miki karanbani na shirya a tray ”.

      “Kai aiko ngd aiba karanbani bane”. Zinneerah ta faɗa tana mikewa. Fita tayi domin kai masa kayan breakfast ɗinsa.


         A falo ta samesa zaune yaci gayu cikin ɗanyar shadda ash, yana zaune a dogon kujera little a kusa dashi yana duba masa ƙafarsa da yaji ciwo. Koda tai sallama bai ɗagoba har ta karaso inda suke ɗauke da tray ɗin. “Barka da hutawa”.

     “Barka” ya amsa mata yana ɗan dagowa ya dubeta. Duk yanda yaso maida idonsa ga ƙafar little ɗin kuma sai ya kasa. tai ɗan murmushi da ɗauke kanta ganin kallon da yake mata. “A ajiye nan ko dining?”.

      Lumshe idanun yayi ya ɗan buɗe a kanta, cikin kasalar data samesa yanzu yace, “Ajiye anan kawai”.

    Saman centre table ta ɗaura tray ɗin da duban ƙafar little dake cikin hannunsa. “Shi kuma wannan miya samu ƙafar tasa?”.

    Iska AK ya ɗan furzar. “Yace faɗuwa yayi ga waje harya fashe, taimakemu da man zafi ma a ɗaki”.

       Bedroom ɗin nasa ta nufa tana faɗin, “Maganin mai gudu kenan idan yana tafiya”. 

      Murmushi kawai AK dake binta da kallo yayi, dan a kwankin nan data haihu duk ramar nan ta ciki da tayi nan ɓacewa take, sai wani irin buɗewama takeyi alamar lafiya ta samu. Miƙewa yay yabi bayanta yanama Little gargaɗin ya jirasa ya dawo.


      Zinneerah na ƙoƙarin fitowa sukaci karo, baya ta koma tana faɗin, “Ouch Yayanmu zaka fasamin kai”.

         “Kokuma ni zaki fasamin ba”. Ya faɗa yana matsota. Kallonsa take da mamaki, ganin dai da gaske kanta yayo tai saurin faɗin, “Yayanmu wani abu ya farune?”.

       “Faffaruwa ma madam” Yay maganar yana kamo hannunta da jawota jikinsa. Hancinsa ya cusa cikin wuyanta yana magana raɗa-raɗa. “Ko tausayinama baƙyaji kin barni da kwana da little ke kinacan kina morewarki ko?”.

     Dariya zancen nasa ya bata, amma sai batayiba tai murmushi da ƙoƙarin ƙwace kanta. “Yayanmu ai amfanin mata biyu kenan, ni ina fama da wannan fiɗan inani ina ɗaukarka. Kawai aunty Farah ta dawo kaga ni sai nayi arba'in”.

        Gani tai ya saketa baki ɗaya yana tsuke fusaka. Ya watsa mata harara yana jan guntun tsaki, batare da ƙara cewa komaiba ya juya ya fita a ɗakin. Bayansa tabi da kallo tana murmushi, a fili tace, ‘Uhm ka gama mazuranka ne dan nasan kana son kayarka’. 

       

      Iskeshi tai yana zuba abincin da kansa. Batai maganaba ta matsar da little kusa da shi ta zauna, “Ina waje. ciwon Alhaji?”. Ta faɗa tana kamo ƙafar little. Nuna mata yayi, ta buɗe man zafin ta shafa masa yana wani shii da baki da yarfar da hannu. “Daddy kace tayi a hankali zafi”.

       “Oh ALLAH, ALLAH yaron nan saika kashe auren da babu soyayya, yanzu shafa maganinne da zafi?”.

          Zancen nata ya bama AK dariya amma sai ya gimtse bai yiba. Yadai kamo hannun little ɗin yana bata amsa a daƙile. “Dama can babu soyayyar ne ai”.

     Tasan da biyu ya faɗa, dan haka taja bakinta tai shiru. Sai dai ta cigaba da kallonsu yanacin abincin yana bama yaronsa har suka kammala.

      Bai wani jima da gamawarba ya mike yana kallon agogo. “Saifudden zai kawo muku cefane. Dan bazan dawo ba sai dare”.

     Mikewa itama Zinneerah tayi da faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi ya kara buɗi, miza'a dafa maka da daren”.

      Kallonta yay cikin ido sonta da buƙatarta na ɗawainiya da shi, yaja numfashi da duban inda little yake. Ganin hankalinsama ba'a kansu yakeba sai ya sake kallonta. “Abinda nakeso a dafamin kam ai ba bani za'aiba. Sai dai nayi manage da tuwo”.

     Murmushi tayi tana maida kanta gefe dan tasan ina ya dosa, ta hau tattara kwanikan, “Uhm ni Yayanmu ALLAH fitina kake ƙarowa kullum, na kawo mafita kuma kaji haushina”.

       “Ke dai kika sani” ya faɗa yana nufar ƙofa.

      Murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda take. Sai da ta kammala ta tisa ƙeyar little da baima lura da fitar Daddyn nasaba ta rufo sashen. A sashenta ta samesa zaune suna gaisawa dasu Yaya Gajeje ƴan biyu duka na'a jikinsa yana kallonsu zuciyarsa fes da farin ciki. Inda yake little ya nufa ita kuma ta nema waje ta zauna. Ya ɗan jima a falon suna maganar jikin Inna daya fara lekawa tana barci dasu Yaya Gajeje kafin ya basu yaran da musu sallama ya fice, bayan ya jefeta da wani kallon duk randa na kamaki. Murmushi mai sanyi kawai tai masa da rakashi da addu'a.

      Shima daga nan sashen Farah ya shiga inda ya samu su Mammah na karyawa. Sun gaisa nanma yaɗan zauna suka taɓa hira sannan yay musu sallama yabar little anan ya fice.


       ★★★


Daga ranar Zinneerah bata sake masa zancen Farah ba har ALLAH yasa sukai arba'in. A randa tai arba'in ɗin kuma su Mammah ke shirin tafiya katsina duba su Farah daga can su wuce london. 

         Gaba ɗaya Zinneerah sai ta shiga damuwa. Dan zamansu a gidan ba ƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninsu ba. Ganin shine zai kaisu katsinar ta sake daurewar masa zancen dawowar Farah sai ya balbaleta da faɗa, duk da tasan bayason wargi bata taɓa ganin fushinsa irin yau ba. Ita kuma yanda yake mata ihu akai yasata fara kuka.

      Suna haka Mammah ta shigo falon. Saurin share hawaye Zinneerah tayi tana ƙaƙaro murmushi da yima Mammah ɗin dake binsu da kallo sannu. Daga haka ta zame ta gudu ta barsu, dan tasan tunda Mammah din ta shigo nan da kanta magana zatayi da shi.

      Da kallo tabi Zinneerah harta fice kafin ta maida ga AK dake ta wani bata fuska. “Abdul-Mutallab mi kaima yarinyarnan?”.

       Guntun tsaki yaja yana murza goshinsa. “Mizan mata kuwa Mammah, itace da neman fitina kawai”. 

     Shiru Mammah tai tana kallonsa cike da nazari, sai kuma taɗan girgiza kanta da cewa, “Fitina kamar ya? Ai kowa Yasan Zinneerah bata da kwaramniya, dan nidai a zamanmu gidan nan banga wani abun ashsha daga garetaba sai dai ajizanci irin na ɗan adama kawai. Amma yarinya mai kawaici da kunya ga haƙuri. Sai dai idan kai ne da laifin tunda sarai na san halinka bawai baƙona bane. Miya haɗaku?”.. 

         “Nifa Mammah babu abinda nai mata. Kawai ta isheni da zancen Farah ne”.

      Kallonsa kawai Mammah keyi dan maganar yanayintane da faɗa sosai. Ta sauke numfashi da gyara zamanta. “Abdul-Mutallab nasan Farah mai laifine tabbas, amma karka manta harda gudunmawarmu, kuma maganarta da yarinyarnan take maka tasan kantane. Dan wannan haline irin na mutanen ƙwarai da sake tabbatar maka ita mai tarbiyyace da hangen nesa. Ni bazance dole ka dawo da Farah gidankaba, amma zan baka shawarar ka daina ƙuntata yarinyarnan akan abinda ba laifinta bane saima alkairi da takeson ɗoraka akai. Ita rayuwa komai ɗan haƙuri ne ai. idan akai haƙurin sai komai ya zama labari wataran”.

       Shi dai kansa na ƙasa baice mata komaiba harta gama zancen Farah da Zinneerah ta ɗakko abinda ya shafesu sannan ya tsoma baki.


    Duk da Zinneerah tasan su Mahma basu rasa komai na rayuwaba sai da ta shirya musu tsaraba domin girmamawa. Musamman turarurrukan khumrah dana wuta da a koda yaushe suke yaba kamshin a jikinta da gidanta. Hakan yasa tasa Hajiya Falmata ta haɗa musu na musamman akai musu packaging nashi. 

    Sai gata harda ƙwalla da zasu wuce. Bama ita ba hatta su Yaya Gajeje sunji babu daɗi. Inna ma da take ɗan magana yanzu kuma takan ɗan motsa jikinta tafiyace dai batayi sai da ta nuna alhinin tafiyar tasu, dan kullum sai sun shiga sun gaidata sau uku a rana babu fashi.

       Duk yanda Zinneerah ke share hawaye AK na kallonta ta mirror. Yay ɗan murmushi yana cizar lip ɗinsa dan yau kam yasan ango yake tunda Mahma ta ɗaure mata ƙugu sai da tai arba'in duk da ba haihuwa tayi da kanta ba. 

      Baisan Mahma ta masa wayo bane tanata gyare masa Zinneerah ɗin a ɓoye. Ga gyaran Hajiya Falmata datake ɗorata a layi, hakama Hajiya Iya kullum cikin faɗa mata dabaru takeyi. Ita kanta tasan idan taje hannun boss din nata sai ta yabama aya zaƙinta. Shiyyasa yau duk take a tsure.


   Kasancewar da little ya tafi suna wucewa mai ƙunshin da zatai mata tana isowa. Ƙunshi akai mata na gani na faɗa na jan lalle da baƙi, Yaya Karima ta yarfa mata kitso kananu da ya fiddo mata ƙyawunta sosai musamman yanzu data yi wani bulɓul da ita tamkar ba itace tasha fama da rama lokacin cikin ƴan biyu ba.

        Kasancewar basu zauna wasaba kamar wasa kafin la'asar suka kammala komai tai fes da ita. Dama tunda ta fara zaman jegon nan take dilke jikinta da kayan gyaran fata na musamman da Hajiya Falmata ta haɗa mata ga kuma na Mahma. A gurguje ta shiga gyaran sashe. AK duk da bawani ƙura yayi ba. Sai da ta tsaftace komai yay mata yanda takeso ta baje kalolin ƙamshinta masu rikitashi. Sanda ta dawo sashenta ma su Mama A'i sun gyare ko ina sai ƙamshi yake. 

       Waya tai zamanyi da AK ɗin taji kosun taho. amma yace mata yana dai shirin tahowar. Taji daɗin haka dan ta samu damar shiga kitchen kenan ta haɗa abinci da kanta. Dan tunda ta fara zaman jegon nan kullum cikin ƙorafi yake akan abinci, idan kaji baiyi maganaba Mahma ce tai girki da kanta saboda shi.

     Lafiyayyen abinci ta shirya masa da tasan zai gamsar dashi. Tare da haɗaɗen shayin barnawa daga Hajiya Falmata da kalolin kayan sha na zoɓo da kunun aya. Suna kammalawa dan da taimakon Mama A'i tayi ta bar mata idawa bayan ta ɗiba na AK takai sashensa.

      Wanka takeson shiga Amaan ya wani saka kuka shi a dole yunwa yakeji. Ɗaukarsa tai tana dungurinsa da kiransa acici like Daddynsa. Tana gama bashi a tsaitsaye itama Anam ta saka tata rigimar. Kanta ta dafe da amsarta Yaya Gajeje na dariya. “Wai yaran nan mi kuke son maidani ne halan? Ku gama naku shima yazo ya isheni da tasa rigimar”.

        “Ai daidai kenan”. Cewar Yaya Gajeje tana dariya. Murmushin jin kunya Zinneerah tayi da ajiye Anam din ta shige cikin dan watsa ruwa...........✍


No comments

Powered by Blogger.