Makauniyar Kaddara 7

 


Page 7*


...........Tafiya take batare da tasan ina take dosaba. Gashi babu alamar gajiyawa tattare da ita, duk da mai kallo a kallo ɗaya zai iya fahimtar lallai tana tare da gajiyar, amma ita kasancewar bata cikin hayyacinta bata

saniba. Babban burinta kawai tai nesa da garin Danya baki ɗayansa. Bata damu da yunwa da ƙishirwar dake damunta ba, balle ta tuna bayan ita akwai wata halitta a jikinta dake buƙata idan ita bata buƙata.

            Kusan dai-dai ketowar alfijir ta iso bakin titin da batasan kona wane gari bane. Batai kuma tunanin son ta sani ɗinba ta zube a ƙofar wani shago ta kwanta cike da gushewar hankali dana tunani. Wani irin nannauyan barcine ya ƙwasheta kuwa, kafin wani dogon lokaci ta fara sauke numfashi......


★★★★


         Tsabar gajiyar da suka kwasone a yinin yau ya saka Gwaggo Laritu barci mai nauyi sosai, har takai da sai da babban ɗanta ya leƙo sashen domin tada ita da asuba. Dan da kullum itace mai tashinsu, amma sai gashi yau sun rigata su. Rashin jin motsinta kuma ya tabbatar masa da makara tayi kenan.

       Tashi tai da ƙyar tana mamakin barcin da tai haka mai nauyi. ga ƙofartata buɗe alamar Zinneerah bata rufe musu ba. Kallon saman gado tayi inda ta bar mata ta kwanta dan ita dama bata iya kwanciya a gado sai ƙasa. Ganin babu kowa a gadon tai tunanin ko Zinneerah bayi ta shiga ita ta tashi ne.

     Bata damuba ta fito gabatar da alwala. Saboda tunanin Zinneerah na bayin ya sata zuwa can wajen dabbobinsu tayo fitsari tazo tai alwala kar makarar tai yawa. Hankalin Gwaggo Laritu bai sake tashi ba sai da taga harta idar da salla gari yay ɗan shaaaa babu motsin Zinneerah. Ajiye carbin da take ja tayi ta fito tsakar gidan. Ganin babu alamarta ya sata nufar ƙofar bayi tai gyaran murya. Shiru. ta sakeyi, nanma shiru. Sai kawai ta danna kai. Gabanta ya faɗi ganin babu alamar anyi amfani da bayin ma. A rikice ta fito, hakan yay dai-dai da dawowar Awwal babban ɗanta daga masallaci, shi Safiyanu yana Lagos neman kuɗi.

      “Mama lafiya kuwa? Mi kike nema?.”

       A rikice tace, “Zinneerah wannan yaron (bata faɗar sunansa saboda ɗan fari). Ban gantaba”.

      Da mamaki shima yace, “Dama anan ta kwana? Ko zuwa tai yanzu da sahe?”.

        “Anan ta kwana mana. tare da ita muka taho nan saboda gidan nasu kasan akwai mutane bazai yuwu zama gareta ba ai ko?”.

      “Hakane Mama”. Ya faɗa yana cigaba da lalleƙa ko'ina na sashen nata. Har takaisa ga fita nasu sasssan. Har sashen ƙaninsa Safiyanu ya tambayi matar tace bataga Zinneerah ba itakam. Bama tasan anan ta kwanaba, dan sanda su Gwaggo Laritu suka dawo gidan tayi barci kasancewar tanada tsohon ciki dama.

     Wani tunani ne yazoma Awwal a rai, dan idan bai mantaba dazai fita salla a buɗe yaba ƙofar zaure. Ya dawo sashen Gwaggo yana faɗin, “Lallai Mama akwai matsala. ALLAH yasa yarinyar-nan ba guduwa tai ba, dan wlhy a buɗe naga ƙofar soro yau, kuma na tabbatar bazaki kwanta baki rihe ba”.

        “Hazbunallah! Wlhy na rihe wannan yaron, ni kuma takaici da damuwar da suka haɗu sukaimin yawa ya sani shigewa na barta anan zaune akan idan ta gaji da zaman zata shigo ɗaki ta kwanta. Aiko zama bai ganniba bara muga ko tana gidan nasu”.

       “A'a mama yi zamanki ni bara inje”.

      “Kai dai barsa naje. Ai ba fasa zancen za'aiba cikin hikina za'a dubata. Dan dama dole naje gidan saboda aiki tunda yau ne ɗaurin auren Karima ”.

      Badan hakan ya masaba ya haƙura. Dan har ransa yana son Zinneerah da tausayinta matsayinsa na ɗan-uwanta.


       Koda Inna taje gidan bata shigaba. Dan dama batazo danta shiga ɗinba. Tayi alƙawarin har agama wannan bikin bazata leƙa gidanba. Sunbar Inna da ƴaƴanta kamar yanda tafi buƙata. Yaro ta samu ta aika ya kira mata Sa'a anan maƙauftansu da yace sun kwana ita da su Karima.. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito tana mutstsukar ido alamar yanzu ta tashi. Ko gaisuwarta Gwaggo Laritu bata tsaya amsawaba tace, “Sa'a shiga gidan nan naku cikin hikima ki dubamin Zinneerah ”.

        “Gwaggo Zinni kuma? Ba'a gidanki ta kwanaba dama?”.

      “Nidai ba surutu na tambayeki ba, jeki fara dubawa”.

      Kai Sa'a ta kaɗa tana nufar cikin gidan da ƴar hayaniyar waɗanda suka tashi ta fara kaurewa. Babu wanda ta tambaya ta shiga neman Zinneerah a gidan. Sai dai babu mai ko alamarta. A rikice ta dawo ta sanarma Gwaggo Laritu. Itama sai ta sake ruɗewa......


★★★★


         A ɓangaren Zinneerah kuwa barci tasha sosai a ƙofar wannan shago har fitowar rana. Sai da mai shagon ya fitone ya tadata domin buɗewa. Tashi tai kawai ta matsa gefe batare data tanka masa ba. Shima ɗin bai tanka ba dan kallon mahaukaciya kawai yake mata duk da babu alamar datti a jikinta. Saɓanin kwanciyar yanzu kam zama tai tana kallon motsin mutane dana wucewar motoci. Babu abinda take fahimta dan ƙwalwarta ba aiki take irin na mutane ba. Ga yunwa mai tsanani na cinta. Dan haka ta ƙurama mutane dake a runfar mai-shayi dake acan tsallaken titi idanu sunasha suna kwasar hira da dariya da gaddamar siyasa. A hirar tasunema takejin sunan garin da take a yanzu mai suna Tsanyawa.

       Mai shagon ne ya lura hankalinta na ga masu shan shayi, haka kawai yaji tausayinta, dan haka ya fito zuwa tsallaken ya siyo mata shayin da biredi harda indomie.

       Wajenta ya dawo yana murmushi, “Baiwar ALLAH kina son kici ko?”. Ya faɗa yana kallonta. Batace komaiba tai ƙasa da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. Murmushi ya sakeyi shima ya ajiye mata filet ɗin indomie ɗin da kofin shayin da aka ɗora biredi a sama. “Gashi to kici”. Kanta ta rausaya masa kawai taja filet ɗin nanma batai magana ba. Batai ko tunani wanke hannu ba balle yin sallar asuba. Tasa hannu ta hau cin abincin a nutse kamar yanda nutsuwa ta kasance jinin jikinta dama can. Citai ta ƙoshi tai gyatsa. Batare da wanke hannunba ma a yanzu ta zame ta sake kwanciya sai barci.

       Sosai tausayinta ya sake cika zuciyar mai-shagon nan. Yazo ya kwashe kayan data gama cin abincin batare da yayi magana ba. 


       Yanzu ma barci sosai Zinneerah tasha a wajen, dan bata farkaba sai gabanin la'asar. Zama tai tana kallon mutanen garin daketa faman kaiwa da komawa, dan wajen ya sake cika fiye da ɗazu da safe. Ga titin motoci nata kai kawo suma. Mai-shagon nan ne dai ya fito salar la'asar ya ganta zaune ta tashi. Cike da tausayinta yace, “Baiwar ALLAH kin tashi ashe?”.

     Bata tanka masaba yanzu ma. Tadai ɗago kai tai masa kallo guda ta maida kanta ƙasa. Yanzuma kamar ɗazun murmushi yayi, ya nufi inda masu abinci suke ya siya mata yazo ya bata. Kamar ɗazu bata tankaba bakuma ta wanke hannu ba tahau ci, tare da ɗaukar ledan ruwan ta fasa tasha ta ƙoshi tana lumshe idanu. Tamkar ɗazun sai ta sake zamewa a wajen ta kwanta sai barci.

     Mai shagon ya dawo sallar la'asar ya ganta ta koma barci, mamaki ya kamashi sosai ganin barci bai mata wahala. Yama fahimci yunwarce ke tadata kenan. Barcin kuma shine salon nata lalurar.

     Har lokacin tashinsa yayi kusan ƙarfe takwas na dare bata tashiba. Ya sai abinci ya ajiye mata bayan ya rufe shagon ya wuce gida. 

         Zinneerah bata farka ba sai kusan sha biyun dare. Yanda ta tashi tana riƙe ciki da matse fuska zai baka tabbacin yunwace. Idonta na sauka akan roba rufe da leda tai saurin jawowa kuwa. Ganin abinci jikinta har rawa yake ta hau ci. Sai da ta cinye tas tasha ruwa sannan ta miƙe tamkar an tsikareta. Jakkar kayanta ta ɗauka ta fara tafiya tamkar daren jiya dan jitai gaba ɗaya nanma ta tsanesa. Burinta kawai ta ƙara gaba tai nesa da garin na Tsanyawa.

        Tafiya take cikin gushewar hankali da tunani tamkar daren jiya. Gashi abin tashin hankalin yau a kan titi ne. Sauƙinma darene babu yawan mitoci sai jefi-jefi. Haka dai ta cigaba da nausa kanta cikin kariyar UBANGIJI a wannan dare ma.....


★★★


           Hankalin kowa ya tashi na rashin ganin Zinneerah ɗin, dan Gwaggo Laritu kasa haƙurin ɓoye rashin ganin nata tai sai da ta fasa. A take aka shiga nemanta lungu da saƙo na garin, sai dai ganin har wani daren ya sake rufawa kowa ya fahimci dai da gaske Zinneerah ta sake guduwa kamar yanda Inna ke faɗi cike da gadarar tabbatarwa tana dariya kuma.

        Kuma duk da tashin hankalin rashin ganin Zinneerah ɗin a haka aka ɗaura auren Babawo da Karima. Aka kuma kaita gidan mijinta a wanann daren. Dan zasu fara zama anan Danya kafin su wuce Kaduna kamar yanda ya faɗa.

       Washe gari an sake tashi da neman Zinneerah a ƙauyikan kusa da su har zuwa kusada ko za'aji labarin tahau mota zuwa wani waje. Babu wani labari makamancin an ganta da suka jiyo. Haka suka dawo gida cike da damuwa da tashin hankalin wannan al'amari.

        Ran Inna ya ɓaci dan ba haka tasoba. Sotai ace kowa ya dinga zagi da faɗin Zinneerah guwa ta sakeyi wajen karuwancinta. Amma sai taga saɓanin hakan kowama sai tausayinta yakeyi da damuwa da halin da zata shiga bayan wanda ta tashi a ciki. Sa'a kuwa kuka taci na tashin hankali ita da Yaya Gajeje, har takai Sa'ar da kwanciya zazzaɓi mai zafi. Duk da Atine ba damuwa tai da Zinneerah ba ita kanta saita wuni sukuku da ita, dan jini ya wuce wasa ai. Wannan yasa duk bikin na Karima yaƙi armashi kamar yanda Inna taci buri. An ɗaura aurene kawai hankalin mutane ba'a kwance ba.

       Kamar ko yaushe yanzunma Baba baice ƙalaba akan al'amarin, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar tashin hankali da damuwar dake a tattare da shi. Yana tsananin so da ƙaunar Zinneerah, musamman daya zam soyayyar da yakewa mahaifiyarta bayan barinta gidan nasa duk sai ya tattarata akan Zinneerah bayan itama wadda yake mata. Dan wannan tsantsar soyayyar Inna ta hango tattare da shi ai ta shiga ta fita ta raba tsakaninsa da ƴar tasa har bai iya cewa uffan akan al'amarinta a gidan.

      Haka wannan dare ya kasancewa duk wani masoyin Zinneerah a cikin tashin hankali da damuwa da tausayinta. Inda washe gari kuma suka sake tashi da wani sabon tashin hankali na barin baba shima garin.

    Wannan tashin hankalinne ya sake ruɗasu suka sake ƙare yinin ranar da neman Zinneerah da Baba a dukkan garuruwan dake da maƙwaftaka da su. Sai dai babu koda labarin ɗayansu. Yau kam saɓanin jiya harda Inna a wannan tashin hankalin. Dan bata taɓa tunanin Baba zai iya bin bayan Zinneerah ba. Duk haukanta da rashin tausayi tana bala'i-bala'in son mijinta uban ƴaƴanta. Dan badanma soyayyar da take masanba bazata taɓa  zuwa wannan ƙauyen ta zauna ba da sunan aure. Saboda garinsu Marabar musawa yayi ashirin din Danya yawa da komai na kayan more rayuwa. 


★★★


        Tamkar jiya yau ɗinma sai gabannin asuba Zinneerah ta yada zango a wani ƙaramin ƙauye da ke a bakin titi. Yau kam a ƙarƙashin wata bishiya ta samu ta kwanta sai barci. A haka mutanen ƙauyen suka wayi gari suka ganta. Da farko ma su tsoronta suka farayi, dan a fuska da jikinta babu mai ɗaukarta mara hankali kasancewar komanta fes yake. Haka yara suka zagayeta harma da manyan kowa ya kasa zuwa inda take. To duniyarce babu gaskiya ai. 

       Barcinta tasha sosai sai wajen sha biyu ta farka da yunwa kamar jiya. Ta shiga bin mutanen dake zagaye da ita da kallo ɗaya bayan ɗaya. Batare da tayi magana ba ta maida kanta ƙasa ta duƙar tana yamutsa fuska da dafe cikinta dan yunwa takeji sosai.

         A ɗan tsorace wani dattijo a cikinsu yace, “Mutum ce ko aljana?”. Banza Zinneerah tai bata amsaba, sai faman riƙe ciki take ita dai. Kusan min tuna biyar ta ɗago tana kallonsu hawaye na zirara mata. Cikin rawar murya tace, “Dan ALLAH ku bani abinci”.

      Kallan kallo suka shigayi a junansu batare da wani ya amsa mata ba. Cikin fisgar numfashi ta kuma faɗin, “Abinci dan ALLAH zan mutu”.

         Tausayintane ya kama wani matashin saurayi dake tsaye gefe da jikka a hannu alamar abin hawa yake jira. Ya matso kusa da ita yana faɗin, “Komi aka baki zakici dai ko?”.

     Da sauri ta kaɗa masa kanta. Fuskarsa cike da tausayinta ya zaro hamsin a aljihu ya bama mai wainar ƴar tsala ta gero a gefe yana faɗin, “Bata ta duka”.

       Amsar kuɗin mai ƴar tsala tayi ta zuba mata wainar a roba, tasa yaji a gefe ta miƙawa saurayin. shine ya ajema Zinneerah gabanta, zata saka hannu ya dakatar da ita akan ta bari ta wanke hannun. Ina bata sauraresaba ta hau cin kayanta hannu baka hannu ƙwarya. Sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta cinye tas. Ruwan da ya ajiye mata dan wanke hannu ta raruma ta kafa kai tasha sosai. Sai gata tana lumshe idanu da sakin murmushi, a fisge tace masa “Nagode”. Daga haka ta zame ta kwanta a wajen sai barci.

        Yanda tai din ya bama kowa mamaki, sai dai bayanin wani tsoho ya sakasu maida kallonsa garesu.

       “Wannan yarinyar ba mahaukaciya bace, da alama kurciya akai mata ko makamancin hakan”.

      “Baba lado miye kurciya?”.

Saurayin da ya sai mata ƴar tsala ya tambayi tsohon. Kamar tsohon bazai sake magana ba, sai kuma ya ɗan girgiza kansa yana mamular goron dake bakinsa. “Kurciya asirine mana shamsu. Akan yima mutum idan ba'a son ya zauna a waje. Akanyi asirin a jikin tsuntsuwar kurciya. Duk inda kurciyar ta nufa can mutum zai nufa shima”.

         A take jikin mutanen wajen yay sanyi, tausayin Zinneerah da batasan sunayiba ya shigesu sosai, suka shiga ambaton ALLAH ya saka mata.


         Yauma kamar jiya yunwa ce kawai ke farkar da ita. Data samu taci saita koma barci, da daddare tsohon nan ya saka aka kama masa ita zuwa gidansa da nufin zai taimaketa. Babu musu kuwa matarsa ta amsheta hannu bibbiyu dan dama ya mata bayani akan Zinneerah ɗin hasalima itace ta bada shawarar su taimaketa.

     Sai dai kuma yauma cikin daren ta farka a firgice kusan ƙarfe ɗaya. Cikin sanɗa ta silale tabar gidan dan ko katangar kirki tsoffin basu da ita. Haka ta ɗauki hanyar titi taita tafiya cikin ficewar hayyaci. Sai dai wayar gari sukai babu ita. Sun tausaya mata matuƙa. Dan basusan inda ta nufaba kuma. gashi ko jikkarta bata ɗaukaba nan ta barta a gidan nasu.


       Haka al'amari ya cigaba da kasancewa akan Zinneerah. Duk inda asuba tayi takan tsaya ta yada zango, a wani garin ta samu tallafin abinci, wani garin kuwa babu mai kallonta. Dan zuwa yanzu kamanninta sun fara canjawa saboda rashin wanka da sauran buƙatu. Ba kullum take samun damar yada zango a gariba. Watarana a daji take yada zangon, haka zata yini kuka da juye-juyen yunwa har barcin nata na ƙa'ida ya ɗauketa.

       A randa ta cika kwanaki goma sha ɗaya da baro gida ALLAH ya iso da ita cikin garin kano, inda ita batasan inane ɗinba. Sai dai taga yawan jama'a da gine-ginen nan yafi na duk garuruwan data baro a baya. Anan ɗinma ba a hayyacinta takeba. Dan kamar yanda ta saba kwanciya da tashi taita tafiya haka ta cigaba dayi, hakanne yasa taita nausa kanta cikin ƙwaryar kano sosai har batasan tanayiba. 

     Zuwa yanzu har takai kowa kallon mahaukaciya yake mata, dan yaran kan tsokaneta. Harma manyan sukan koreta idan ta ɗan laɓaɓa wani gurin zata huta ko tana neman abinci. A haka ta sake share kusan sati biyu cikin ƙwaryar kano, indan kuma an haɗa da barowarta gida tana neman ƙulla wata ɗaya. Ɗan cikinta ya fara fitowa fili kowa yana gani, duk da ba wani uban girma yayiba na azo a gani.

           Duk da yanayin da take ciki haka take kasancewa cikin laulayi, dan kusan kullum da zazzaɓi take kwana, wani abin kuma idan taci takanyi amansa dan baya zama. 

     Yau data kasance juma'a mutane nata kai kawo na zuwa masallatan juma'a a cikin garin na kano, wanda a yanzu haka Zinneerah na gab da barin garin tana neman ɗaukar hanyar jigawa dutse. Tafiya take a hankali cike da kasala saboda rashin samun inda zata raɓa ta kwanta tun ɗazun, dan tun barcin gabannin asuba data kwanta a ƙofar wata maƙaranta gari na wayewa aka korota. Shine har yanzu bata samu ta sake samun wajen kwanciyarba kuma. Ga yunwa na cin hanjinta da zazzaɓi. Tun tana tafiya tana kallon inda take saka ƙafarta har takai idanunta sun lulluɓe da duhu.


             Gudu motar takeyi sosai daga hanyar jigawa tana nufo cikin Kano. Yanda passengers ɗin cikin motar basu damu da gudun da direban keyiba zai tabbatar maka da suma son ai gudun suke dansu sami sallar juma'a cikin jam'i.

         Sam idonsa bai kula da abinda ke gabansaba sai da yazo gab. Yay ƙoƙarin taka birki yana salati kamar yanda suma fasinjoji keyi cike da tashin hankali da ruɗani, sai hakan ya gagara dan sun riga sunzo gab da ita. Gashi ita kuma sam batajin uban horn ɗin da drivern ke zabga mata da iyakar ƙarfinsa ba. 

     Ji kake wani ƙuuuuuuuu!!!!!! Motar ta bada sauti mai ban tsoro, yayinda razananniyar ƙarar da zinneerah ta ƙwalla saboda azaba ta danne ƙarar ƙugin da motar tayi.. Cikin tsananin tashin hankali kowa dake a cikin motar yake ƙoƙarin fitowa. Dan cikin amincin ALLAH babu abinda ya faru da kowa a cikinsu. Gaba ɗayansu kan Zinneerah dake kwance wanwar a ƙasa sukayi kowa na salati a rikice.............✍

     

No comments

Powered by Blogger.