Makauniyar Kaddara 8
Page 8*
..........Ko tsayawa fahimtar a ina taji ciwon direban baiyiba. Kasancewarsa mutum tamkar ruɗaɗɗe, abu kaɗan ke gigitashi. A yanzu hakanma jikinsa sai rawa yakeyi.
“Dan ALLAH ku taimaka a sata a mota muje asibiti karta rasa ranta”. Ya faɗa a gigice da rawar jiki saboda jinin dake zuba a jikinta da basusan ko daga ina bane.
Suma kansu yanda ya rikice ɗin sai hankalinsu ya ƙara tashi, ga yarinyar tunda tai ƙarar farko bata sake ko motsiba alamar numfashinta ya rabu da gangar jikinsa. Ga jinin dake fita a jikin natama tashin hankaline mai zaman kansa.
Wani abokinsa driver ne daya tsaya a wajen kamar yanda yaga motoci nata tsayawane ya nufesu a rikice. “Ya ilahi, Naziru Accident kukayi haka?”. Cike da tashin hankali ya bashi amsa. “Wlhy bugeta nayi Malam Abubakar, sam banga yarinyarnan ba sai da mukazo gab da ita. Nayi ƙoƙarin kauce mata kuma hakan ya gagara”.
“Hasbinallahu wani'imal wakil. Inaga to kusata a mota, wasu ƴan motar taka saisu dawo nan wajena tunda ba mutane sosai”.
Kowa yayi na'am da wannan shawaran, dan haka a take sukayi hakan kuwa. Cikin kano suka ƙarasa shiga, inda kai tsaye suka nufi wani asibin kuɗi kamar yanda wani a motar ya bada shawran, dan sunsan yanzu idan sunje na gwamnati wani sabon turancine zai tashi na maganar ƴan sanda da sauransu. Cikin amincin ALLAH suna zuwa kuwa aka amshesu kasancewar ansan shi wanda ya bada shawaran. Ashema yana taɓa aiki a asibitin. Da taimakon wannan bawan ALLAH aka shiga bama Zinneerah da batasan ina kanta yakeba taimakon gaggawa.
Alhmdllh kusan awa ɗaya da rabi saurayin nan da likitan da suka taimaketa suka fito, fuskar saurayin da murmushi yace, “Alhmdllhi kowa ya kwantar da hankalinsa komai yazo da sauƙi, cikin ikon ALLAH ma bataji wasu ciwuka masu tsauriba, sai dai cikin jikinta da ƙyar aka samu ya tsaya, saboda shi ne ma zamu riƙeta dan tana buƙatar kasancewa a ƙarƙashin kulawar likita na kamar sati biyu zuwa uku haka”.
Ajiyar zuciya drivern ya sauke. Hakama sauran fasinjojin da sukai karar biyosu duk suka shiga ambaton Alhmdllhi. Sai dai kuma hankalin drivern a wani fanin a tashe yake. Da damuwa yace, “Amma zamanta sati uku a asibitin nan zan iya shiga wani hali ɗan uwa. Kuɗin gado kansu aikine babba a gareni”.
Murmushi saurayin yayi yana dafa kafaɗarsa, yace, “Karka damu za'asan yanda za'ai insha ALLAH. Idan kuma yarinyar ta farka ai dolene musan daga ina take? A nema iyayenta da mijinta ko”.
Ajiyar zuciya ya sauke yana gyaɗa kansa. Daga haka suka fita zuwa massallacin da basu tayar da sallaba su har yanzun.
Bayan an idar da salla daga can sauran fasinjojin kowa ya kama gabansa. Da ga shi Naziru direba sai abokinsa Abubakar da saurayin nan da ya faɗa musu sunansa Khalipha suka dawo asibitin. Sun sami damar shiga dubata yanzu kam. Tana kwance an saka mata ruwa. Sai hanunta dake ɗaure da bandage alamar taji ciwo a wajen, sai gefen kanta shima da sauran gurare jefi-jefi. Kasancewar an cire mata kayan dauɗar jikinta an saka mata na asibitin kalar green sai taɗan canja kamanni kaɗan. Duk da idanunta a rufe suke sun fahimci dai ta farfaɗo barci takeyi yanzun, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu, a fili kuwa suna ambaton Alhmdllh tare da mata fatan samun lafiya. daga haka suka fita domin biyan kuɗi suma suɗanje gida kuma.
*BAYAN KWANA UKU*
Kwana uku Zinneerah na samun kulawa a asibitin da taimakon Khalipha dake tsaye akan komai. Dan koda direba Naziru ya bada iya kuɗin da ALLAH ya hore masa Khalipha ɗinne ya ƙara wasu aka biya kuɗin gado harna kwana goma, yace idan da buƙatar tafi waɗanan kwanakin sai asan abinyi. Alhmdllh jikin nata da sauƙi, dan ƙananun ciwukan harsun fara nuna alamar warkewa saboda bata da ƙan jiki, sai dai hannun natane take kuka da shi dan ta samu tsagewar ƙashi ne. Amma shima Alhmdllh yau ta tashi da sauƙi.
Abu ɗaya ke tadama su Khalipha hankali, shine da zaran dare yayi babu zaman lafiya. Tata zabura kenan akan saita fita a asibitin. A daren farko sun ɗaukama tanada taɓin hankaline, hakan yasa suka danna mata allurar barci mai ƙarfi sosai, wadda ta jata har washe gari da rana tana barci. Sai da likita yay bincike kamar yanda Khalipha ya buƙata sannan suka fahimci lafiyar ƙwaƙwalwarta ƙalau sai dai kuma wani abu daban da basu saniba.
A dare na biyu kam tana farawa wani tunani yazoma Khalipha. Kafin azo ai mata allura ya shiga tofa mata addu'oi, tun tana ɗan fisge-fisgen kaɗan da faɗin ita a barta ta tafi har ta fara lafawa, sai kuma gashi kafinma ayi allurar barci mai nauyi yay gaba da ita. A ranar haka Khalipha ya kwana da abin nan a rai, dan ji yake a ransa tamkar ya santa ko yanada alaƙa da ita. Dare na uku ma tana farawa ya fara mata addu'oin nanma sai gashi ta lafa. To a yau Alhmdllh bayan an cire mata ruwan da aka saka mata Khalipha ya saka wata Nurse ta taimaka mata aka goge mata jiki da duk abinda zai taimaka mata.
Kusan ƙarfe bakwai sai ga Naziru direba da abincin karyawa kamar yanda ya jura kawowa kullum, da rana kuma almajiri yake kawo mata. Idan kuma ya dawo aiki yakan zo asibiti yay kamar awa guda sanann ya wuce gida. Hakan da yake yi nama Khalipha daɗi, shiyyasa baijin ƙyashin taimaka masa akan jinyar yarinyar dako sunanta har yanzun basu sani ba.
Sai da aka gama kimtsata sannan suka shigo ɗakin. Fuskar Naziru washe da fara'ar jin daɗin ganin jikin nata yaketa ambaton, “Alhmdllhi, Alhmdllhi. Kai naji daɗin ganinta haka Malam Khalipha, ALLAH ya saka maka da alkairi, nagode-nagode”.
Murmushi Khalipha yayi idanunsa akan Zinneerah shima yace, “Ai ƙoƙarin ka ne da adalcinka ya kaimu ga wannan nasarar Malam Naziru. Da ace guduwa kayi bayan kawota nan muma bazamu sami ƙwarin gwiwar taimakonta ba, dan direbobi da yawa idan irin haka ta faru guduwa suke subar majinyaci a asibiti koda kuwa ya zama gawa. Yanzu inaga jikin nata Alhmdllh gaskiya, ya kamata musan sunanta da inda ta fito dan mu nema iyayenta da mijinta kodan abinda ke a cikinta”.
Cikin washe haƙora Naziru yace, “Wannan gaskiya ne Malam Khalipha”.
Duk wannan magana dake fita tsakanin Khalipha da Naziru Zinneerah na zaune ne a gadon kanta a ƙasa tana saurarensu. amma ko sau ɗaya bata ɗago ta kallesu ba tanata faman wasa da yatsun hannunta ne kawai kamar bata a wajen ma.
Nurse ɗin dake a gefenta ta ƙarasa gyara mata abinda ya rage ta fice ta barsu. Sai a lokacin su Khalipha suka ƙarasa inda take suna mata sannu. Yanzunma bata ɗago ta kallesu ba. Sai dai cikin rawar murya tace, “Ina yini”. Daga haka tai tsit.
Wannan shine karon farko da sukaji muryarta tana cikin hayyacinta, dan haka sukaji daɗi har cikin ransu. Khalipha yace, “Masha ALLAH, yau dai naji muryar ƙanwata”.
Batace komaiba, kamar yanda bata ɗagoba. Bai damuba, dan ya fahimci akwai damuwa tattare da ita. Zama yay a bakin gadon daga can ƙarshe, dan haka tai saurin janye ƙafafunta data miƙe ta naɗesu. Baice komaiba, sai ma Naziru ne yaja kujerar roba shima ya zauna a kusa da shi. Su dukansu idanunsu a kanta suna kallonta cike da tausayi, dan shekarunta sunyi ƙanƙanta da fuskantar lalurar ciki irin haka a ganinsu.
“Ƙanwata!”.
Khalipha ya kirata cike da kulawa..
A karon farko ta ɗago taɗan kallesu, sai kuma tai azamar maida kanta ta duƙar batare data amsa masaba. Ya ɗan murmusa da sake faɗin, “Ki saki jikinki munan duk yayunkine kinji, munason miki wasu tambayoyine, ko zaki taimakemu da amsa?”.
Kanta a ƙasa har yanzu ta gyaɗa masa kanta. Shima kan nasa ya gyaɗa cike dajin daɗin tana fahimtarsu. Ya cigaba da faɗin, “Minene sunanki?”. Shiru bata amsaba. Fahimtar bazata faɗaba ya sashi sake cewa, “A wane anguwa kike anan kano?”. Yanzu kam kanta ta girgiza masa.
Cikin rashin fahimta yace, “baki san anguwarba ko ba'a nan kikeba?”.
Kanta ta ɗaga masa.
Naziru ya amshe da sake faɗin, “Ba'a nan kike ba?”.
Kanta yanzu ma ta kaɗa musu.
Kallon junansu sukai da mamaki, kafin Khalipha yace, “A wane gari kike to?”.
“Nima ban saniba, na manta komai”.
Ta basu amsa a fisge tana ƙara ƙasa da kanta alamar gajiyawa. Nanma kallon juna sukai cike da mamaki da fargaba. Naziru zai sake magana Khalipha ya girgiza masa kai alamar su barta kawai.
Badan Naziru yasoba yay shiru, Khalipha ya miƙe yana faɗin, “Yauwa to bara na turo sister Salima ta baki abincin kici, dan nasan kina bukatarsa”. Daga haka ya kama hannun Naziru suka fice batare da ya jira amsawarta ba.
Bayansu tabi da kallo har suka fice, ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tana lumshe ido. haka kawai take shiga takura da shiga wani yanayin da batasan dalilinsa ba a duk sanda Khalipha ya kasance a ɗakin.
“Malam Khalipha akwai matsala kenanfa idan yarinyarnan batasan wacece ita ba, gata da ciki” Naziru ya faɗa cike da damuwa sanda suke fitowa.
Ajiyar zuciya Khalipha ya sauke yana furzar da iska. Yace, “Tabbas akwai matsala, amma ni tun daren farko da aka kawota na fahimci akwai wani ɓoyayyen al'amari tattare da ita. Dan yanda take zabura cikin dare da faɗin abarta ta tafi, da safe kuma taita barci yasa nake ganin kamar tana a wani hali. So yanzu dai sai munyi haƙuri munbi a hankali zamu kamo bakin zaren insha ALLAH”.
Numfashi Naziru ya sauke shima. ransa da damuwa yace, “Ni kuma yarinyar kama ma takemin da amaryar Yayana wlhy, sannan maganar ɗawainiyar asibin wani abune mai zaman kansa Khalipha, badan ka taimaka min ba ai bansan yaya zanyiba nikam”.
Murmushi kawai Khalipha yayi, cikin kauda maganar ƙarshe yace, “Kana nufin tana kamani da wadda kasani?”.
“Sosaima kuwa, tun jiya da aka ɗan goge mata jiki naga kamaninta da Maman Sadiq sosai wlhy. Amma dai yau zan kawo matata da yamma dan ina komawa gida da wuri irin yau ɗin, kasan mata sun fimu lura. Kaga sai muji abinda zatace itama”.
“Wannan shawaran yayi Malam Naziru, ALLAH ya jishemu alkairi”.
“Amin ya rabbi, bara nazo na wuce dan na samu damar dawowa da wuri, yau katsina zan nufa insha ALLAH. Kuma sahu ɗaya zanyi na dawo gida”.
“ALLAH ya bada nasara. Ya kuma maido mana daku lafiya”.
Godiya Naziru yayma Khalipha ya wuce. Shima Khalipha sai ya wuce nasa uzirin acikin asibitin.
★★★
Misalin ƙarfe huɗu na yamma Zinneerah na zaune a gadon jinyarta, idanunta tsaye ƙyam akan matashin cikinta, wanda yau ne karan farko data iya zaman masa wannan kallon. A duba guda da zakai mata zaka iya fahimtar ta lula duniyar tunanine. Dan har Naziru direba da matarsa sukai sallama biyu a ɗakin babu amsa.
Kallon juna sukai shi da matarsa, kafin su sake maida idanunsu ga Zinneerah wadda da'alama har yanzu batasan da shigowar tasu ba. Takowa matar Naziru tayi har inda take, ta kai hannu akan kafaɗarta tana sake rangaɗa wata sallamar. Zabura Zinneerah tayi dan kamar daga sama taji sallamar tata. Ganin Naziru tsaye a ƙofa ya saka sauke ajiyar zuciya. Ta janye hanunta data ɗora saman cikin nata tana maida dubanta ga matar Nazirun da tai tsaye ƙyam tana duban Zinneerah ɗin da alamun mamaki a fuskarta.
Kafin Zinneerah tai magana tai saurin faɗin, “Ikon ALLAH, Abban Nasiba kaga kuwa abinda nake gani?”.
Cikin nuna tamkar bai fahimceta ba yace, “Mi kika gani?”.
Ganin kallon da Zinneerah ke musu ne na alamar tsoro ya sakata wayancewa ta zauna kusa da Zinneerah ɗin tana faɗin, “Gani nai ƙanwar tawa ta lula tunani batama san da zuwan namu ba”.
A hankali Zinneerah ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da sake maida kanta ta duƙar a ƙasa.
Yayinda shi kuma Nasiru ya kasa ko motsi dan yayi zaton abinda ransa ke raya masa na kamannin yarinyar da Maman Sadiq matar tasa zata faɗa. Sai kuma yaji saɓanin hakan. Jin Zinneerah da matar tasa na gaisawa ne ya sakashi shima ƙarasowa gaban gadon ya ajiye ledan hannunsa yana dubanta da kulawa.
Itama batare data sake ɗagowa ta kallesaba ta shiga gaishesa kamar yanda ta saba. Da kulawa ya amsa mata da sake tambayarta ƙarfin jikinta. Tace taji sauƙi.
Sun jima a ɗakin tare da ita, sai dai su kaɗai suke ƴar hirarsu jefi-jefi. Zinneerah na zaune shiru tana saurarensu kanta a ƙasa. Sai da Naziru ya tambayeta ko Khalipha ya shigo? Ne ta girgiza masa akai alamar a'a kawai batare da tayi magana ba.
Fara kiraye-kirayen sallar magriba da akai ne yasa sukai mata sallama suka fito.
Suna fita ta sauke ajiyar zuciya, tare da zamewa a gadon ta kwanta ta lumshe idanunta da sake maida hannunta akan cikinta kamar ɗazun. Batasan wane tunani zatai akan wannan cikinba a rayuwarta. Dan yazo mata a yanayin MAKAUNIYAR ƘADDARA. shin tayaya wai aka samar da shi ne? Wanene ubansa? Kodai dama cikin basai mutum yayi aure ko ya aikata iskanci ba yake samunsa?.
Wannan tunanin shine a ranta. Dan harga ALLAH ita dai tasan duk masu haihuwar garinsu sai sunyi aure. sannan idan akaga wadda batai aureba da ciki akance mata ƴar iskace mai bin maza. A yanda kuma takejin ma'anar kalmar mai-bin maza a abaki manya shine mace mai zuwa ta aikata abu mara ƙyau da namiji. To amma ita yau gashi bata a cikin duk waɗancan kason mutanen amma gata da ciki. Bata taɓa aure ba. Bakuma ta taɓa iskanci irin na waɗancan matanba. To kenan bayan waɗanan dalilan mace zata iya samun ciki ta wata sigar kenan kamar yanda itama a yanzu take tsamanin ta hakan ta sameshi?.
Lokacin da Zinneerah ke wancan tunani a waje tsakanin Naziru da natarsa kam tattaunawa sukeyi suma akan abin al'ajabin da suka gani. Dan suna fitowa Matar tasa ke faɗin, “Abban Nasiba wlhy ɗazunfa waskewa nayi dan naga yarinyar nan ta tsorata. Kasan kuwa mina gani tattare da yarinyar nan?”.
Kansa ya girgiza mata kawai batare da yace komaiba. Itama batare data damu da hakan da yayinba tace, “Wai shin kai bakaga kamarta da Maman Sadiq ɗin gidan babban yaya bane?”.
A yanzu kam gaba ɗaya ya tattara hankakinsa gareta. Cike da zumuɗi yace, “Wannan dalilin yasa na kawoki nan Faɗima. Dan inata kokwanto, kinsan akan hakan jiya har gidan Yaya naje na sake ganin Maman Sadiq kuwa?”.
“Ikon ALLAH, to amma ita yanzu ai kaga yan uwanta ko?”.
“Inafa, bata iya faɗa mana komai akantaba wlhy, da alama akwai saka hannu a al'amarinta gaskiya, dan kamar bata da isashshiyar kafiya, kamar kuma mai tare da sammu ko jinnu. Amma ni yanzu kinsan wane tunani nayi?”.
Kanta ta girgiza masa.
Ya sauke numfashi yana bin Khalipha dake fitowa daga wata baƙar mota data faka a kusa dasu da ido. Tinted glass ɗin motar yasa basuga wanda ke zaune matsayin driver ba. Sai Khalipha ɗin daketa faman ɗaga masa hannu yana murmushi har motar ta sake ficewa a harabar asibitin.
Inda su Nazirun suke ya ƙaraso yana faɗin, “A'a malam Naziru kune anan haka?”.
Cike da kallon alamar tambaya da Nazirun ke masa ya gyaɗa kansa. Dan mamakin wannan babbar motar da aka saukesa a ciki yakeyi. fahimtar hakan da Khalipha yasoyi ya sakashi yin murmushi da juyawa yana kallon motar da har ta gama ficewa a gate ɗin asibitin ta hau titi. Sake maido dubansa yay ga Naziru da shima motar ya koma kallo yanzun cike da basarwa.
“Yaya dai malam Nazir?”.
Murmushi Naziru yayi a karon farko ƙasan zuciyarsa fal saƙe-sake akan tunanin da alama Khalipha ɗan masu da shi ne. Dan shi tunma randa suka ɗakkosa a Jigawa yaso fahimtar hakan. Amma shi Khalipha kamar bayason nuna shiɗin wanine.......
Gyaran muryar da Khalipha yayine ya katse tunaninsa. Shi kuma Khalipha ya maida dubansa ga matar Nazirun suka fara gaisawa. Bayan sun gama gaisawarne Naziru yay masa bayanin itama abinda matar tasa ta faɗa game da kamannin yarinyar da matar yayan nasa.
Khalipha yace, “To inaga mafita ɗayace damu kamar akan wannan tunain naku, mizai hana kubi hanyar data dace ita matar yayan naka tazo asibitin nan ko zamu sami wani bakin zaren, idan kuma babu damar yin hakan mu haƙura har yarinyar ta samu sauƙi sosai sai mu kaita gidan yayan naka mu da kanmu”.
“Lallai wannan shawaran taka yayi Khalipha, kuma na gamsu da shi. Insha ALLAH zanyi iya duk ƙoƙarina zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu Maman Sadiq tazo asibitin nan kafin yarinyar nan ta kammala kwanakinta inaga kamar zaifi sauƙi”.
Daga Khalipha har matarsa sun gamsu da hakan, dan haka sukai sallama yay cikin asibitin su kuma suka fito don tafiya gida.
__________________★
A haka kwanaki suka cigaba da tafiya, Zinneerah na cigaba da jiyya da samun kulawa ga Khalipha, Naziru ma yana iya bakin ƙoƙarinsa ganin yazo dubata koda hidimar Khalipha ɗin da baya gajiyawa.
Sosai ta samu sauƙi, dan yanzu Alhmdllh ko zaburan daren nan nason a barta ta fita batayi saboda Khalipha bai barin asibitin da wuri saboda ita kawai. Kasancewar suna sakata barci da wuri dan ta sami hutu sosai yakan zauna yayta mata addu'oi yana tofa mata, itako bama tasan yanayiba dan tuni tayi barcinta.
Yawan kulawa da samun abinci mai inganci da takeyi yanzu ya sakata canjawa a zaman asibitin tamkar bamai zaman jinyaba. Tayi wani fresh da ita ga cikin nata nata sake nuna kansa. A duk sanda ta dubi cikin takan zauna taita kuka maiban tausayi. Dan takan rasa wane irin kalar tunani zatayi akan wannan MAKAUNIYAR ƘADDARA data riski rayuwarta?. Gaka da ciki amma bakasan ta hanyar daka samosaba balle ai tunanin wanene ubansa kuma. Ita yanzu ma da'an sallameta daga asibitin nan batasan indama ta dosaba kuma. Dan koda sha'awa bata son tunawa da Danya a ranta ma balle ai tunanin komawarta can.
Har yanzu su Khalipha basusan sunantaba, tun kuma waccan ranar basu sake neman jin wacece itaba. Tamaƙi yarda ta saki jiki dasu gaba ɗaya.
Yauma kamar kullum tana zaune a ɗakin da tab ɗin Khalipha dakan bata wai tayi game ko kallo haka danta rage kaɗaici. Game ɗin takeyi fuskarta na fidda murmushi mai ƙayatarwa, a kallo ɗaya zaka fahimci tana cikin nishaɗi, shiyyasa shi kansa Khaliphan yake ɗaukar Tab ɗin ya bata dazaran ya shigo cikin asibitin. Shekaran jiyama a wajenta ta kwana.
Ɗan harbawar da zuciyarta yayi yasata dakatawa dayin game ɗin, haka yau ta tashi da wannan tsinkewar zuciya da batasan dalili ba, jin abin na ƙara ƙarfi ne ya sakata ajiye tab ɗin ta Khalipha gefe ta zame ta kwanta tana ambaton ‘hazbunallahu wani'imal wakil’ a ranta ko zataji ɗan daɗi............✍
Leave a Comment