My Lady Boss Hausa Novel Complete
MY LADY BOSS🕊️_*
_(Romantic and comedian)_
......1
_*Na Aunty Aisha Ango Bamalli👑*_
_*Maman teddy🧸*_
_Lagos_
A hankali take bin ilahirin wurin da aka ajeta da kallo...this is the first time da ta taɓa shiga wani Company da sunan aiki,saukar da lulun idanun ta da suke a ƙaƙƙafe na rashin kunya tayi tana duban computer n dake gaban ta...huuuuu wani gwauron numfashi ta sauke a hankali tana gyara zaman mayafin da ta yane kanta dashi, shigar suit ɗin jikin take kallo kamin ta sheƙe da wani irin wawan dariya jikake wurin ya amsa hahahaaa...Saurin kallon ta ma'aikatan gyefen ta sukayi wanda hakan yasa Sumayya ɗaure Fuska tamau kaman ba ita tayi dariyar ba,wanda dama wannan al'adarta ce , komai ta nuna bata son raini...ganin yanda ta haɗe girar sama yasa duk rawar kan ma'aikatan wannan wuri mata da maza shiga hankalin su , a zuciyoyin su suna cewa " wannan itama BOSS ce ,but aƙwai babban ta a sama zata daina wannan fuxgar ne haɗuwa ɗaya idon sukayi". Ma'aikatan ke magana kowa da abun da yake saƙawa a zuciyar shi game da Sabuwar ma'aikaciyar tasu Wato Sumayya.
Ɓangaren Sumayya kuwa juyi take a kujerar da take kai kaman wanda ta saba hawan zuciyar ta ,tafff ƙugunta da cinyoyin ta suka cike kujerar ,saboda tsaban ƙiban ta da ƙasa Allah yabata hip da manyan mazaunai ka aza ta haura shekara ashirin da biyar in kayi mata kallon sace.... Nisawa tayi tana ciko wuya a zuciyar ta cewa take" Oh Sumayya wannan anya rayuwar da kika ɗauka ma kanki mai ɓillewa ce kuwa? Mtswww ɗan tsaki tajah a hankali kamin tace " nida ba zama nazo yi ba ,naxo na saci kuɗin Company na gudu , ya za'a ajiye Ni anan wurin? Tayi maganan tana duban gyefe da gyefen ta babu alamar hanyar satan kuɗi ...taɓ wallh da sake dole na bar wurinan na koma wurin asusun kuɗi na companyn kamin su gane takardun dana taho dasu ba nawa bane , daga Ni sai takardar secondary gomma nayi komai oya oya nabar Company nan.
Rintse ido tayi nan take ta tuno da inyamurin ta mai lapo data amsa masu bashi yanxu bashi ya dameta...Wani irin buɗe idon ta tayi da sauri tana rarrabasu kamin ta ce "Ta ina zan fara? Miƙewa tayi tsaye tana kallon sama inda taga PA Wanda ya ɗauke ta aikin ya nufa...ƙallon glses ɗin wurin tayi ganin ya hasko mata komanta yanda ta sauya kaman ba itace Siman Gaye ba...Murmushi tayi a hankali tana tuno da abun da ya faru da ita da Mmn biyoda kwanaki da suka wuce....
Tafe take tana surfa bala'i haɗi da sauri zaf zaf ,yanda take masifa ka aza da wani a gyefen ta takeyi... cilla ƙafafun ta kawai takeyi tamkar wacce zata tashi sama...na gaji da wannan ƴar iskan garin ,ace bashi ya hanani sukuni , Anbi an dameni, wallahi duk wacce ta kuma zuwa mun da maganar bashin ta sai na tijara koma waye? Wannan abu haka?.. Kai innalillahi yanzu ta ina xan fara ne?". Tayi maganan tana tsayawa haɗi da kama ƙugu... matashiyar budurwa ce da ashekaru baxata haura ashirin ba take wannan banbamin tare da surutai yin su take ita kaɗai kaman zautattaciya. Daganin ta kasan fitinanniya ce lamba ɗaya... Sakin hannayen ta tayi tana cigaba da tafiya ,yanda take tafiya zaf² yasani ƙare mata kallo ina mmki.
"Wasu yaran inyamurai da yarbawa ne da suka duƙufa wasa suka hango ta can nesa wanda a yanayin sa hijabin ta an jawo shi gaban goshi na tsaban iyayi da ƙauɗi yasa su saurin miƙewa ba tare da kowa yayi mawa ɗan uwan sa magana ba".
Kai mu gudu ga Sima nan,Siman gaye!".
Kamin su rufe baki Sumayya da ta hangosu dama bata raga mawa yaran layin ko kaɗan , bare su da cikin su akwai wanda yayi mata laifi... Hakan yasa su cikin sauri ta ɗaga ƙafanta kamin su ankare har Sumayya ta iso gaban su...babbabara uban can, Ni kuke kira da Siman gaye? Ni sa'ar ubanku ne ko uwar ku?".
"Jikin yaran ne yahau rawa kar kar kar kaman wanda aka sa masu shocking kamin salihu yace" A'a ke ba sa'an mu bace, Don Allah Sima kiyi haƙuri". Kallon sama da ƙasa Sima kebin yaran dashi don so take ta fanshe hushin ta akan su ,yau ta wayi gari babu sisi , wannan yasa ta kai hannu tana damƙo Samuel da yake aikin raba ido yana neman hanyar fechewa ,don yasan irin laifin da yayi mawa Sumayya ta damƙe shi mai rabasu sai Allah".
Oh Jesus! Samuel yayi maganan yana haɗe hannayen shi biyu alamun addu'a. Wani irin dariya Sima tasa tana murtike fuska tamkar ba itace tayi dariyar ba ,kamin tace " Jesus ɗin uban ka,gama addu'a n naka tass ,yau sai ka san Allah ɗaya ne. Sima pls forgive me...Sima Sorry pls.
Wani irin gigitaccen tsawa ta daka masa wanda yasa shi yin shurin da bai shirya ba ,sai wani irin gumi da yake haɗawa kaman yayi wanka da ruwa ɗumi...Forgive ɗin ubanka ai Ni bansan meye kalmar ba tayi maganan tana ware manyan taffan hannayen ta tana zubasu a fuskar Samuel wanda jin sautin ƙarar marin tassssss kaman saukar tartatsin wuta yasa su salihu rugawa a wani irin matsiyacin gudu , suna barin Sumayya da Samuel da yake wani irin tsala ihuuuu ...aaahhhhh kawai yake cewa yana kururuwa n neman agaji,kun san arna idan iftila'i ya same su basu san Allah ba sai ihu na banza...tsala ihu agaji yake yi amma kash kowa na leƙowa yana ganin Sumayya ce sai ya juya da sauri ,don tayi ƙaurin suna wurin iya masifa da tijara". Bakayi mata ba tayi bare kuma kayi mata? Wannan yasa duk dukan da take mawa Samuel babu wanda yaje ƙwatar sa ,sai magulmata da sukayi saurin sanar da maman biyode wanda ta kasance mahaifiyar Samuel a hasale ta ƙarako inda Sima ke zaune tana ba Samuel punishment a rana ita kuma tana gyefe a inuwa . Sam bata lura da Mmn biyode ba don idon ta a rufe yake cewa take" idan ka tsaya da up and down ɗin nan wallahi sai nayi ƙasa ƙasa dakai ƴan iskan yara marasa mutunci , nice Sima wando dai dai da kugun kowa....
Ɗan ta Mmn biyode ta nufa tana tada shi tsaye kamin ta nufo Sima da itama miƙewa tayi tsaye tana kallon ikon Allah ,ta kama kugu tana shirin tijara taji Muryar Mmn biyode na mgn cike da masifa....l I have never see stupid goat like you...mene yaro na yayi maki,always fighting ³ wid people! what's wrong with you Sima? won't be agree baxan yarda ba wurin Uwar ki zanje yanxu ,Allah yasa ba hauka ne akan ta ba itace asibitin mahaukata na duniya...zan kai ku court......wani irin rintse ido Sumayya tayi tana jikin ta na kyerma hawaye na bin kuncin ta , babu abun da ya ɓata ranta irin ambaton mahaifiyar ta da Maman biyoda tayi ta zaga...har da zagin lallarurar ta na hauka". Yanda jikin ta ke tsuma kaman boss yasa Maman biyoda saurin kama hannun Ɗan ta tana shirin gudu wa...
Sumayya ne ta kai hannun ta tana miƙashi ga bishiyar darbejiyan dake kusa dasu wani tsalle tayi tana karyo reshen haɗi da daka tsalle tana biyo bayan Maman biyoda ,ihu ta hau yi tana faɗin Umma na zaki zaga ,kamin Maman biyoda ta juya taji saukar Sandar darbejiyan tauuuuu". Wani irin gigicewa Maman biyoda tayi tana riƙe Sandar ,nan suka hau kokawa da Sumayya wanda dukan mmn biyoda take tana faɗin Umma ta zaki zaga yau sai nayi ƙasaƙasa da kowa naku...
Ihun maman biyoda da Sumayya yasa mutane fitowa daƙyar aka ƙwaci mmn biyoda a hannun Sumayya da ke ihu tana faɗin Umma na zaki zaga??????....
Murmushi Sumayya tayi a hankali tace " Allah sarki Umma na , bazan bari bashin lapo su tajaramaki Ni ba , zan waxgi iya rabona mai Company kayi haƙuri nima ba'a son Raina zan saci kuɗin ku ba...astagafurullah mun astagafurullah mun tayi maganan tana hayewa wani dogon stairs , ba tare da tayi tunanin komai ba".
Idon ta ne yy wal³ ganin hasken wurin yasha ban ban dana inda take , tabbas anan dukiya take! Tayi maganan a zuciyar ta tana takawa zuwa wurin wata matashiyar budurwa da ashekaru zata kai 32 ganin an rubuta sectary yasa Sumayya nufar inda take kai tsaye".
Tsaye Sumayya tayi akan ta wanda mulki ya hanata ce mata komai wanda itama sectariya isa da mulki yasa bata kalli Sumayya ba...kujerar gyefen ta Sumayya tajah ta zauna ba uhm bare uhm'uhm. Wannan yasa Hauwa ɓaidu ɗago idon idanun ta cike da masifa tace " Malama ba'a zama mana anan.
Shiru Sumayya tayi kamin ta ɗago da dara daran idanun ta tana watsa mawa sakatariyan wani irin kallo na baki isa ba kana ta motsa laɓban ta tana cewa " Ba'a zama kuma aka aje a gurun?.
Ta ƙare maganan suna kallon kallo, fahimtar Sumayya ƴar bala'i ne kuma gashi a ƙaidar Company n kukayi faɗa korane ko cacan baki yasa Mrs Hauwa ɓaidu cije lips ɗin ta tana kwantar da murya wakike nema ko nace me kike so?". Ina son magana da mai wannan wurin ne?. Saurin kallon ta Mrs Hauwa tayi kamin ta fara tunanin Anya Sumayya nada hankali kuwa? Sir Khamal da idan aka ganshi gudu akeyi ita tazo tana wani ce mata tana son magana dashi? Mutumin da idan yayi magana da kai sau uku to na huɗun korane??....
Leave a Comment