Najma 1-2
👄👄👄👄👄👄
*Najma*
💋💋💋💋💋💋
_By maman nurul hudah_
*Tsokaci*
_Kirkirarren labari ne banyi shi dan cin zarafin kowa ba in yayi dai'dai da rayuwarka/ki akasi aka samu and please don't take it personal...._
~Warning~
*Ban yarda wani ko wata ya juya min labari ta ko wace siga ba,ba tare da izinina ba,in kunne yaji jiki ya tsira*
🅿️1️⃣💋2️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kauyen makunkule dake Niger state
Bacci take a saman yamutsatsen katifarta karama Wanda kana Masa kallo d'aya zaka gan da ita da bahu duk daya juyi take kamar inda Yara suke cikin dare mussaman in sun Sha Wasa da rana,duk miyau ya wanke Mata fuska,mafalki take Wai gata a gidin bishiya inda kakanta me anguwa ke Zama a kujeransa tana sulhu kamar inda ta saba,mikewa tayi still tana bacci Dan tana da dabiar sleeping talking and walking....I mean irin nasu bacci suna tafiya suna surutai
Tafiya take harta fito waje Ido a rufe tana fad'in Kai Mani zaka biyasa wayarsa in kaki za ayi maka bulala ashir......."
Bata karasa ba taji saukar ruwan me shegen sanyi a jikinta a firgice ta zabura ta bude Ido ta Kai hanun fuskarta ta Shafo ruwan Dake gangara sai ta gan haske tar idanunta ga umma tsaye a kanta tana huci
Wani kallo tayiwa umma nata ranta in sunyi dubu Toh duk sun b'aci wani numfashi ta ja kafin ta saki wani razananne Kara me rikitarwa sanan ta Fadi kasa timmm
Tsaki umma tayi ta bar wurin rike da rubber a hanun tana jiyo iya na cewa uwani meke faruwa
Jin muryar iya ta Kuma sakin wani mahaukacin Kara cikin make murya a Dole aljanu tayi tace"iska na hau"
(Hohoho watoh mutumin daya hau iska Yana fadin ya hau iska )
Iya ta fito tana sakin ashar,tana cewa uban waye ya tab'ota har yasa ta tada aljanu"
Umma ko shigewa d'aki tayi ta kulle tana jinjina wanan matsifa da d'aurin gindin da uwani ke samu a gun su iya da Abbu
Iya Rai b'ace ta karaso ta duka da k'yar tana rike kwankwaso ta d'ago kanta ta Dora a cinyarta tana jijjigata tana cewa"su waye ku me za a Baku "
Cikin kifkifta Ido da jan numfashi tace"mune mazuzu shekarun dubu uku da goma,iya ya ma Kika ce ana Kiran uku da goma a hausace
Iya Kamar wata sakarya tace"saba'in "
Uwani tace" toh dai shekarunmu dubu saba'in abinda muke so Kuma daraza "
Iya tace"miye Kuma daraza Ni uwani a Ina za a sameshi "
Uwani ta dan bude Ido daya tace" ai nasan ke din a duhu kike toh larabci nayi Miki kaza ake Kira daraza
Umma Bata San lokacin da dariya ya kufce Mata ba tace"uwani ohoho Ni saude na gan abinda ya girmeni watoh dajajan ne daraza hmmm laillah yariyar nan ta maidamu garori"
Ji tayi iya tace"toh karku damu yanzu za a yanka ayi muku miyarta Ina shikenan dai"
Sake sakin ihu uwani tayi tace"ba shikenan ba muna son a siya Mana juns(juice)mu kora da darazar "
Iya tace"Ni Ina nasan wani jins shima larabci ne?"
Uwani ta saki mika ta d'aga hanun ta bigewa iya hab'a iya ta saki ihu.........uwani ta leka fuskarta sai ta Fara fisge fisge tana cewa"a yanka Mana zakara ko Kuma mutum mafi tsufa a gidan Nan ya mutu "
Iya ta Kai hanun ta toshe Baki tace"ah'ah ku daina Kiran mutuwa "
Uwani da dariya ya so subuce Mata ta matse da k'yar tasan inda iya ta tsani Jin kalmar mutuwa ta Kuma fisgewa tace,ya mazuzu ya madudu ya kal daraza kazar gida katuwar zakara wa in Anki a kashe tsohuwar gid......"
Ai Bata Gama ba iya ta kwalawa umma Kira tana cewa
Bari dai in leka fans dina🤣😭
Please share
Maman Nur
Leave a Comment