Najma 13-14
ππ«¦ππ«¦ππ«¦
*_NAJMA_*
ππππππ
By maman noorul
Hudah
Wanan littafin na kudine regular 300 vip 600 via
2378022567
Aisha Mohammed
Zeinith bank,for more information please contact me via my watsaap number 09090112846
π Ώ️1️⃣3️⃣π«¦1️⃣4️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yace"Baki wanke hanun ba"
Tashi tayi jikina rawa ta karasa bakin rariya ta wanke hanun sanan ta dawo da wuri ta Fara cin abinci ba wani sosai take cin sakwaran ba sai naman take ci,saida ta koshi ta saki gyasa shiko kallonta yake ganin zata cire hanun yace"naman ya isheki ne naj"
Ta girgiza kai tace"cikina ya koshi bakin be koshi ba Amma in na cigaba da ci Ina gan Saida akaini gida a baro
Yace"kici in Zaki Kara "
Ta kalleshi ta gan da gaske yake sai tace"sa min a Leda toh in naje gida anjima zanci ai "
Yace ok Bari a zubamiki
Godiya ta me ta mike ta Shiga kicin din baaba ta d'auko days daga cikin ledoji da take cusawa a gun window ta kawo me
Be juye Mata instead ya rufe yace"ki tafi da kwano gobe Kya dawo Mata dashi
Tace"baka da matsala wallahi
Yayi murmushi ya mike ya fita sai gashi ya dawo da jakar da Ciro a mota ya Shiga dakin tsoho ya tube ya d'aura wani babban towel ya fito rike da sabulu da soso sai Dettol antiseptic ya zuba a ruwan wanka da baaba ta juye me a bucket ya shiga dan karamin bayin su day ake hango kansa dan da Kara akayi
Tana ganin Haka ta mike ta bar gidan da kular Miya a hanya ta gadu da Abbu zai koma gida ta bashi kular ta tafi gun fareedah
Bata gansu ba alamun dai an Gama ko ma me fareedah take son ta gani sai kawai tayi hanya gidansu
Ta tarar fareedah na wanke ta gaida mamanta sanan ta zauna jiran fareedah tana wajen akayi magrib ganin maman fareedah tasa ta gaba tayi sallah yasa itama tayi badan taso ba tana idarwa kafin maman fareedah ta fito daga d'akin Suka bar gidan
_______
Be ji Dadi ba daya fito be ganta ba ya tambayi baaba Ina take
Baaba tace"Wai ka d'au uwani na Zama gu d'aya ne makale maka da tayi ma saboda kazar ne kuma ka Bata ta tafi ba shikenan ba,gobe sai mu gan ko ni Zan Bata lokacin Yi maka Miya ka kyauta
Rungumeta yayi Lura da taji haushin abinda yayi yace"Yi hakuri matan nasan kina kishi ne Ni nayi alkawarin Zan siya Miki kaji masu yawa kinji
Jan hanjishi tayi tace"Wai Ina ummanka da abbanka
Yace"ummana tana lafiya Abba Kuma ya tafi Dubai d'aya dawo zai shigo yace Yana son a muku ginin zamani"
Cikin Jin Dadi ta Fara jerowa d'an Bata addu'a tana cewa Allah ya dawo dashi
Yace"Ina ne gidansu naj ?"
Tace"Wai son miye hadinka da yarinyar Nan ne ka nace Haka
Yayi murmushi yace"she is cut ne yariya akwai shiga Raine baaba
Bata koma cewa komai ba yace"Yi min kwatanci "
Kwatamcw tayi me ta fita Yana kamshi Yana sanye da jeans blue da bakar polodata Masa kyau
. Da tambaya ya Gane gidan me gari babu shakka komai ya shiga Yana sallama
Iya ce zaune a tsakar gidan tana ta zuba mita sai yusifa Dake zaune kofar dakinsa umma Kuma na gindin murhu abban uwani Kuma na kwance a taburma duk a gajiye yake ya dawo gona
Iya tace"kaifa umaru sai ka dage da saude Mata sai shagen son jiki a ce har tsakar dare Bata Gama girki ba salon uwani ta kwaso yunwa ta dawo ba abinda zata ci a Shiga uku dukda ragowar kazarta na Nan Amma duk mun San ba ita ke ci ba
Umma dake tuka tuwo tace"kiyi hakuri iya yanzu Zan Gama fah
Sallama yayi a Karo na biyu iya ta kalleshi Bata Sansa ba Amma ta washe hakora tana cewa bako mukayi ne?"
Ya jinjina Kai ya suka cikin Ladabi ya gaidasu Suka amsa iya ta mike ta kawo Masa kujera
Umma ko tana tuka tuwo tana amsa Masa Abba Dake kwance ya mike zaune shima ya amsa sai ga abbu ya fito a d'aki yanaganinshi shima ya washe Baki yace"saifudeen Kaine a gidan naku"
Yayi murmushi ya shafa Kai Abbu ya kalli iya yace"jikan malam dauda ne dake birni shine ya Zo
Iya tace"ayyah ayyah ayyah Ma sha Allah ya ka baro iyayen naka yace"alhamdullilah iya
Zama Abbu suna ta Hira shidai vaza Ido yake ya gan ta inda zata fito but shiru shiko abbu be ma Lura ba sai hiransa yake Masa
Tambaya yake son yayi Amma ya kasa saboda nauyi a Haka dai umma ta Gama tuwon ta kwashi
Yusufa yace kina ta fad'a Kuma ke kin San ki da Rana aka Gama tuwon Nan ba ci zatayi ba,kila ma sai ta koshi a gidan mutane zata dawo inda uwani ne kunyi a banza
Abbu na murmushi yace"bana Jin ma zata ci tuwon Nan dan ga kular miyar kazarta data hado dashi d'azu Kuma kunce na d'azu da aka yanka Mata ya rage
A maganar Abbu ya gane Bata dawo gida ba saimamaki ya lullubeshi ya kalli agogo ya gan Tara ta kusa...an kawo me tuwo be ci ba yace ya koshi ummatace"ah'ah wallahi ko kad'an ne ai ka ci "
Da k'yar tayi dashi ya Fara ci Aiko yayi me mugun Dadi sai gashi ya cidayaea sai godiya take Mata
Ganin alamun sum Fara Jin bacci Dan tuni Abba yayi bacci abbu ko tun Yana da abin fad'a har hirar ta Kare iya dai ke dakon jiran uwani ya mike yayi musu sallama badan yaso ba
Tafiya yake Yana tunanin Wai a ce yariya karama na yawu Haka Kuma a a samu ba
Haka yayi ta zagayen garin har ya cire Rai da ganim sai yaji muryarta
Cike da bala'i tace"in har mutum ya Isa ya Kuma San ya cika dan halak Dan kutumar babbanbura ubansa ya dakeni,Kuma za ayi ta duk Wanda yasan ya haihu haihuwar uwarsa da ubansa Dan Allah ya raba fad'a Nan da za ayi
Tsit kake Jin wajen ya d'auka dukda dandakin ne ba Wanda ya iya magana
Komawa baya yayi ya bi hanya da take jin maganarta Aiko ya ganta da kayandazu sai takalminsa daya Bata d'azu
Yana zuwa beyi wata wata ba ya d'auketa ya sabata a kafada ai ihu ta saki Dan Bata gansa ba tace toh fah na gan ta kaina satar mutum a cikin mutane
Suna Shiga wata lungu ya direta sai a lokacin ta ganshi
Zatayi magana kawai ya fusgota ya rungume
Shiru tayi tana tunanin Ashe dan iska ne shi ban Bata sani
Janye jikinta tayi sai ya duka tana kokarin yin magana ya
Maman Nur
Leave a Comment