Najma 3-4
👄👄👄👄👄👄
*NAJMA*
💋💋💋💋💋💋
By maman noorul hudah
🅿️3️⃣👄4️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tace"saude Wai Ina kike ne kina Jin yariyar Nan ta tada aljanai sunce kaza suke son ci ki fito ki leka d'akin yusifa ya fito ya kamo a yanka"
Umma ta fito tana danne dariyarta Wanda da k'yar ta iya yin Haka ta sauke idanunta Kan iya ba abinda jikinta yakeyi in ba rawa ba kafin ta maida kallonta Kan uwani dake kwance idanunsa na had'uwa uwanin ta janye nata gudun umma ta b'ata Mata shiri,umma ta girgiza kanta ta saki wani murmushi wanan uban d'aurin gindin da uwani ke samu gun iya take sheka ayanta inda take so
Sanin halin iya da Kuma ashar da ta Fara saki tana cewa mutum Dan kaniyarsa a ce yayi abu da jiki ya tsaya Yana b'atawa mutane lokaci ko sai jinin uwanin ya Kare an fa ce da jini suke amfani
Jin Haka yasa uwani sake Mika straight ta Fara girgiza jiki tana cewa"a siya Mana Madara gwagwani pakmik(peak milk) da marina in ba hakan....
Iya ta saki wani ihu tace"ohoho saude Wai sai sun ce in Basu Raina ne zakiyi Abu da jiki a Basu su ci ko zasu tafi duk munti d'aya in Kika b,'ata fah tambaya abubuwa zasuyi tayi
Ummi ta Kara sauri ta buga kofar yusifa yana kwance Yana bacci ta buga kofar da karfi ya mike a firgice
Tace"iya Wai ka Zo ka kama zakaranta uwani ta hau aljanu Kuma sunce
Kaza suke so shine take son a Kama Mata
Rai b'ace ya kau da Kai yace"kowa fa yasan yariyar nan fa aljanun karya takeyi Amma sai ayi ta biye Mata haba umma Ina Jin dadin baccina a tashi ne Salan inyi ciwon ka....."
Sake mika uwani tayi Jin abinda ya fad'a tace"a daina karyatamu ko muyi ba daidai ba
Iya tace"wane mutum ai Babu Wanda ya Isa ya karyata .....Kai yusifa so kake in uanka ya dawo yayi maka hukunci
Mikewa yayi Yana kunkunin Yana fitowa ya kalli uwani Suka had'a Ido
Tace"wal a daka yaji wal ci da kaza yaji Maggi Fara"
Iya tace"yanzu yusifa zai daka yajin ai, uwar me yake in Banda baccin asara da Kuma zaman gulma
Cikin tsarewar gida yace"wallahi iya ban gan Wanda ya Isa ya sani in dakawa wanan yariyar yaji in banda ta maidaku gaulaye yariya tayi ta karyar aljanu Kuma ku hau Kuna biye mata"
Iya zatayi magana uwani tace"Wal karki takura Masa dan bazai daka ba Wal mu zamu daka da kanmu ai da hanun mu"
Iya tace"Kuma naku zaifi laushi kila ma ko sekan biyu bazakuyi ba ya daku Abu na jinnu Kuma"
Wanan gab'ar ko Saida umma ta kyalkyale da dariya
Iya cikin seriousness tace"kull karki kuskura ba ayiwa jinnu dariya
Cikin kankanin lokaci umma ta fara had'a miyan had'adiyar kaza sai kamshi yake irin dahuwar su ta kauye me Romo
Itako uwani tana gindi tabarya tana fama da yaji a wahalce bashi da alamar dakuwa gashi a rayuwa Bata son harka da yaji dan ko Yaya ta tab'a jikinta sai taji zafi
Iya ta kalleta ta gan idanan sunyi jajur tace"ya haka manya Baki Ina tunanin zaku Gama a cikin kankanin lokaci sai gashi har kazar ta daho ba labari
Uwani tayi wurgi da tabarya tace"Ina..... mu bamu son yaji"
Ummadai kallonta take wani lokacin tana tunanin ko uwani Bata da Kai ne oho "
Zama tayi a taburm yusifa dake zaune kofar d'akinsa rike da madubi ya saki murmushi yace"aljanai sunji maza ikon Allah
Bata kulasa ba tana zaune umma ta juyo Mata kaza a kwano ta kawo Mata daman iya ta aika Mata maltina
Natsuwa tayi tana cin kazar sai kada Kai take kamar kadargaruwa Saida tayi nak ta saki gyasa umma tace"toh zamu iya cin ragowar aljani?"
Tace"lah lah a ajiye Mana anjima zamu ci"
Iya tace"toh mu dai kamshi muka ji kenan baza a dan bamu mu maida y....."
Kallon da uwani tayi Mata ne yasa ta maida maganarta
Tana wanke hanun sai ga fareeda ta shigo da gudu tace"uwani Yana faruwa a hayi su deluwa suna can sun cakume juna suna dambe ke abin dadin kallo*
Ai ko takalmi Bata sa ba kamar giftawar aljan ta haye guntuwar katangan gidan ta tsallake a guje
Iya ta saki salati Dan ko Dan kwali Babu kanta sai Kuma ta fashe da kuka tace"ya bazatayi ta Kama aljanu ba
Tana gaba fareeda na binta a baya Kan kace me ta Isa hayin ta gan delu na maida numfashi ga malam sani gefensu alamun ya rabasu
Cikin daga murya tace"al'quran sai an sake haba dai bazanyi gudu a banza ba
Malam sani ya dubeta suna had'a Ido ta kauda Kai tace"eh dambe Nike son a sake Dan ban gan ta farko ba
Yace"Baki da kunya in rabasu ki ce su sake ke wace irin shad'aniya ce?"
Ta wani d'aure fuska cikin kunkunin tace
Please share
Maman Nur
Leave a Comment