nihaad 19
At first tsayawa yayi kamar bazai bi ta ba amma ganin ta kulle kofar kitchen din yayi saurin bin bayanta, Tsaye ya ganta ta dau table knife tana kuka sosai facing the knife towards her stomach, ya kalleta daga sama har kasa, sae kuma ya shiga cikin kitchen din ya dau asalin wuka ya karasa har gabanta ya mika mata yace "In da gaske kike" runtse ido tayi tana kuka iya karfinta, ya kamo hannunta ya saka wukar a ciki sannan ya koma bakin kofa ya jingina da wall din wajen ya rungume hannunsa yana kallonta da wani scorned expression, ta bude ido a hankali ta jefar da wukar ta sulale kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wayyo na shiga uku na lalace" sai kuma ta daura hannu a ka ta kurma uban ihu tana kallonsa, juyawa yayi ya bata waje, Ko sanda aka yi leaking Video dinta bata tunanin tashin hankalinta ya kai wanda take ciki yanxu, she is still yet to believe who she is seeing, wani ihun tashin hankali ta kuma kurmawa lkci daya kuma tayi shiru, to ko dai aiko sa aka yi gidan, tunanin hakan ya sa ta hau share idonta gabanta na bugawa da sauri, lkci daya tayi assuring kanta kawai aikosa aka yi gidan shine ya shigo masu har ciki, da kyar ta mike tsaye kamar me tsoron taka kasa ta karasa kofar kitchen din ta leko parlon a hankali with throbbing heart, zaune ta gansa saman kujera, suna hada ido ta wani hade rai har sannan gabanta na faduwa tayi karfin halin cewa "Malam idan aikoka aka yi sai ka shigo ma mutane har cikin nan? Wannan wani irin samun waje ne? Duk tsakar gida bai isheka ba sai ka shigo har nan" Kallonta kawai yake da wani stern look a fuskarsa, ta wani kara shan kunu tace "ko shi mai gidan ne ya baka damar shigo mana har cikin nan?" Ba abinda yace mata still, kuma babu alamar xai ce mata komai sai ma dauke idonsa da yayi, ta dake ta fito daga kitchen din gaba daya, tace "Wai baka jin ina maka magana ne ko nan din ma rashin kunyan xaka min?" Yace "Ok" Yana fadin haka ya mike ya juya yayi hanyar kofar fita daga parlon, wani irin kwanciya hankalinta yayi, taji ta samu relieve da nutsuwa, sulalewa kan kujera tayi ta jinginar da kanta da kujerar tare da sauke wani dogon ajiyar xuciya, haba ita dama ta san aikosa gidan aka yi shine xai shigo ma mutane har parlor saboda samun waje, shi kam yana fita ya kulle kofar parlon, Nihad ta share hawayen idonta a hankali tana tunanin to ina wanda aka aura mata din, har yanxu fa bata gansa ba, mikewa tayi ta nufi hanyar dakuna ta bude wani daki a hankali ta leka ciki taga babu komai dakin banda katifa, ta kulle ta sake bude wani taga shi ma katifar ce kawai, toh where is the so called husband, a hankali ta juya ta koma dakin da ta kwana ta xauna gefen gado, she is just imagining ace abinda tayi tunani daxu a kitchen gaskiya ne ai da kawai da gaske kashe kan nata xata yi kowa ma ya huta, but why will she even think that way at the first place, it is something that is neva and neva going to happen, agogon dake dakin ta kalla taga karfe goma sha daya saura, har lokacin bata ji tana jin yunwa ba, ita ta ma mance rabonta da cin abinci a cikinta, tana ta xaune dakin with different thought and imagination a ranta, can kuma ta mike duk jiki ba kwari tana tafiya a hankali ta koma parlor, windown dake kusa da kofar parlon ta tafi tana leka compound din, karamin compound ne da xai iya cin mota uku, ga mamakinta sai ta gansa xaune kan wani dakali a tsakar gidan ya rike kansa, wani faduwar gaba taji ya dirar mata, but seriously what is this man doing in this house for God sake, me yake har yanxu bai tafi ba, to ko dai mai gidan ne yace ya jirasa, this time around ta ma rasa wani takamaiman tunanin xata yi, duk sai ta birkice taji jikinta na rawa.... amma taki barin ƙwaƙwalwarta ya fassara mata abinda xuciyarta ke raya mata a lokacin, noooo it can't and will never be, tasan aikosa gidan kawai aka yi wallahi...... _Har a lokacin da ya gama hada takalman idon Abba na kansa, ganin xai fita parlon Abba yace "Ibrahim" Juyowa yayi yana kallon Abba, Abba ya nuna masa waje alamar ya xauna, komawa yayi ya xauna a hankali yana kallon Abban, Abba ya nisa yace "Kana da mata ne Ibrahim?" Khalil ya ɗan yi jim, amma ganin yanda Abba ya kafe sa da ido yayi saurin girgiza kai yace "Aa" Abba yayi kasa da murya yace "Ohk! Kana da wani dalilin da yasa baka yi auren ba har ynxu ko kawai ra'ayinka ne?" Khalil ya sunkuyar da kai yace "Dama da kaka aka ce xan yi auren idan Allah ya yarda" Abba yace "Kana da yarinyar da xaka aura ne Ibrahim?" Khalil ya dago ya kalli Abba dake ta kallonsa, sai kuma ya sake sunkuyar da kai a hankali yace "Aa ban samu ba dai tukun" Abba yayi shiru yana kallonsa as if thinking of where to start from, kallonsa kawai Abba yake daga sama har kasa duk da a xaune yake, kamar jikinsa ya basa Abban na kallonsa, sai duk ya tsargu, upside down ya juya palm dinsa a hankali not wanting to disclose the ring he is putting on, muryar Abba yaji yace "Ina son xan maka aure, xan kuma yi maka komai na auren sannan in baka gida ku xauna don na ya6a da nutsuwa da hankalin ka, bana jin ina da fargaba a kanka Ibrahim.... amma baxan yi hakan ba tare da yardar ka ba, da kuma yardar iyayenka, ina rokan wannan alfarman a wajenka Ibrahim" Khalil ya ji komai ya tsaya masa na kusan 10 seconds, lkci daya ya ji he is feeling heat all over, ya dai yi karfin halin dago kai ya kalli Abba, ganin yanda Abba ke kallonsa wanda in dai ka san Abba to xaka fahimci yana cikin damuwa wanda baya iya boyuwa ko min pretence din mutum, Khalil ya kirkiri fara'a a fuskarsa yace "Amma nagode sosai Alhaji, Allah ya kara girma, Allah ya saka da alkhairi, Nagode Alhaji" Abba yaji dadin reaction dinsa sosai cause he neva expect that, ya xata xai ce Aa ko kuma ya kawo wani excuse din, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Ameen Ibrahim, sai mu je can gun iyayenka yau mu yi magana da su ko? Su ma kuma ina fatan Allah xai sa su amince" Khalil ya hadiye abu da kyar yace "To ba damuwa Alhaji" Abba yace "Ka shirya nan da awa biyu mu tafi" Yace "Toh Alhaji" Abba yace "Nagode, amma sai dai baka tambayeni da warce xan hada ka ba" Khalil kallon Abba kawai yake, Abba yace "Yar cikina ce ba wata ba, saboda na yaba da komai naka ya sa nake son hada zuri'a da kai, ni kadai na yanke shawarar nan, kuma idan Allah ya yarda ban yi abun da xai cutar da kai a gaba ba Ibrahim, xaka yi farin ciki da hadin nan wataran, kawai tun yanxu ina neman alfarman ka koyi hakuri da ita don yarinya ce, kuma ita ma nasan watarana xata yi alfahari da xabin da nayi mata, fatana kawai Allah ya dora ni kan iyayenka" Khalil kam yayi nisa tunanin da yake don bai ma assimilating maganganun Abba, thousands of thought ne suka yi crossing mind dinsa a moment din nan, why him of all people, this means disappointing every of his relative, ko Abba bai fada masa wacece cikin yaran nasa ba ya san wacece, no!!! they are not and will neva be compatible, how will that even be? Muryar Abba ya tsinta a tsakiyar kansa ya a ce masa "Xaka iya tafiya, Allah yayi maka albarka" Ko Ameen din khalil bai iya ya amsa ba ya mike ya kwashi takalman Abba ya fita daga parlon, lkci daya yanayinsa ya sauya, wasu xufa suka hau keto masa, Yana fita compound ya nufi mai gadi ya dire masa takalman, Aminu ya mike da sauri yace "Lafiya na ganka a birkice haka? Me ya faru?" Khalil bai basa amsa ba ya nufi chalet, har idanuwansa sun kada .... Muryar Nihad ne ya dawo da Khalil duniyar tunanin da ya fada a tsakar gidan, ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta, a fusace tace "Wai baka ji abinda nake ce maka bane? Ka gaya min uban me ya kawo ka gidan nan?" Mikewa yayi yace "Ki kira babanki ki tambayesa, don shi ya kamata ya baki wannan amsan" Kasake tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo, severely yace "Sannan ina me baki shawaran kada ki sake daga min murya, ko kuma ki sake min wasu tambayoyi a gidan nan" Daga haka ya bar ta wajen tsaye ya koma cikin gidan walking fast, shikenan abinda take ta hana ƙwaƙwalwarta fassara mata ya tabbata, shikenan tsoronta da fargabanta ya tabbata, ta fashe da wani matsanancin kuka me ban tausayi ta sulale kasa ta daura hannu a ka ta kurma wani uban ihu tace "Na shiga uku na lalace, na banu na lalace, Me nayi ma Abbana xai min haka, me yasa Abbana xai min haka, me nayi ma yan gidanmu suka min haka, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka take sosai kamar ranta xai fita, ta fi minti ashirin xaune kasan interlock ta kasa tashi, she is more than shock, why her?? Ganin abun ma take kamar a mafarki, Nihad ta ci kuka ta gode Allah a zaune wajen, daga karshe ta kalli gate din gidan sai kuma ta mike da sauri ta nufi gate din amma tana kokarin budewa taji key aka sa, sulalewa wajen tayi tana ci gaba da kuka tana girgiza kanta, nan ma tafi min sha biyar, bata ta66atar da gaske an tsaneta a gidansu ba sai yanxu, sosai kanta ya fara mata ciwo, jin strength dinta ya fara karewa saboda kukan da take tayi karfin halin tashi tana layi ta koma cikin gidan, kitchen ta shiga tana kallon wukar da ya bata ta wurgar daxu, karasawa tayi ta dau wukar hawaye me xafi na sauka idonta, jingina tayi da cabinet tana kuka a hankali, to ai in tayi hakan wuta kawai xata, jefar da wukar tayi daga karshe ta fito parlon tana bin ko ina da kallo hawaye na bin idonta, karamar wayarsa ta gani saman kujera ta karasa da sauri saman kujeran ta dau wayar ta shige dakin da ta kwana, xaunawa tayi gefen gado hawaye wasu na bin wani a idonta tayi dialing number Nihal, tana sa wa sunan Nihal ya fito baro baro, ta kai kunne, yana fara ring ba a wani dau lkci ba Nihal ta daga, kasa cewa komai Nihad tayi tana kuka a hankali ta runtse idonta, jin shiru ba ace komai ba cikin sanyin murya Nihal tace "Hello" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Na shiga uku Nihal, kinga abinda su Abba suka min ko, dama ashe har Abba baya so na, dama haka aka tsaneni a gidan nan ban sani ba? wayyo Nihal wllh da Allah baxai jefani wuta ba yau da na kashe kaina kowa ma ya huta, zuciyata kamar xata fashe nake ji yanxu, i can't take this any longer, me yasa su Abba xa su min haka, sun san ma meye aure kuwa?" Kuka take kamar ranta xai fita, Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba, Nihad na shessheka tace "Pls ki turo min number Husnah yanxu ta nan, nasan kina da shi send it now plss i need it...." Tana gama fadin haka ta katse wayar ta fada kan gado tana rera sabon kuka, ko minti daya ba ayi ba Nihad taji shigowar message a wayar, ta mike xaune da sauri taga number Husnah ne Nihal ta turo mata, da sauri ta hau kiran number, yana fara ring Husnah ta daga tace "Hello" Nihad ta rushe mata da kuka tace "Husnah tawa ta kare, Abba na ya tsaneni baya so na, Husnah kila ma ba su suka haifeni ba wallahi" Da sauri Husnah ta rage volume din Mp da suka cika a daki tace "Calm down Nihad, kar ki je ki sa ma kanki wani ciwon mu shiga uku, wllh tsoron xuwa gidan nan naku nake saboda yayanki, babu ta inda kuma xan san halin da kike ciki tunda bani da number kowa a gidan, Nihal da nake da number ta tana school da na kirata tace min haka" Nihad tayi karfin halin cewa "Husnah kin san wa Abbana ya aura min?" Husnah ta gyara xama tana gwale ido tace "Aa waye?" Nihad ta kwanta gefen gado hawaye me xafi na sauka idonta tace "Husnah of all people wai drivern gidanmu Abba ya aura min" Husnah dake xaune sai da ta mike tsaye tace "Whattt???" Bude kofar dakin aka yi Nihad ta mike xaune da sauri lkci daya ta hade rai, yana mata wani kallo ya karasa cikin dakin fuska daure yace "Kar ki sake ta6a min waya a gidan nan" Wani matsiyacin kallo tayi masa ta wurgar da wayar tana ta6e baki tace "Wannan gwangwanin kake kira waya?" Kallonta kawai khalil yake babu ko kiftawa trying his possible best to calm himself, Nihad ta ja tsaki ta tashi ta koma can karshen gado ta xauna fuska daure tace "Wai waya, kai baka ma ji kunyan kiran wannan waya ba" Gyada kai yayi ya juya ya durkusa ya dau wayar da batur dinsa da yayi gefe daya ya mayar sannan ya mike ya nufi kofa ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta saki tace "Wayyo Allah na." Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad da har ta gaji da kukan da take ta ji ana kwankwasa gate din gidan, kamar tana expecting hakan ta mike da sauri tana share idonta ta fice daga dakin, dai dai fitowarsa shi ma daga dakin da yake, ta wani hade rai, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita, wani mugun tsanarsa da tafi ta ko yaushe take ji a ranta, even with joke baxata ta6a kiran wannan mutumin wai mijinta ba, mijinta ta ina? Shi har ya isa ya xama mijinta? This is even weird to imagine, bakin kofar parlon ta tafi ta tsaya fuska daure, yana bude gate din Umma ta shigo, har kasa ya durkusa yace "Barka da xuwa Hajiya, ina yini" Wani kallo Umma tayi masa sae kuma ta kyabe baki ta wuce ta bar sa durkushe a wajen, Nihad na ganin Umma ta taho da gudu ta Rungumeta ta sakar mata kuka da karfi tace "Umma na shiga uku, me yasa Abba xae min haka, me yasa Abba xae lalata min rayuwa, Umma ashe duk ba sona ake a gidanmu ba ban sani ba" Umma ta rungumeta cike da damuwa tace "Yi shiru mu shiga ciki Nihad, yi shiru" A haka Umma ta ja xuwa parlor, khalil da ya bi su da ido ya tafi kan dakalin da ya xauna daxu ya xauna, Umma na rungume da Nihad bayan ta zauna kan kujera tace "Wai ba nace kiyi shiru ba ko in tashe in tafi ne?" Nihad ta girgiza kai tana shessheka a hankali tana goge idonta, Umma tace "Ke yanxu kin yarda an aurar da ke kenan?" Nihad ta daga kai tana kallon Umma da kumburarran idonta, ba idonta ba har fuskarta ya koma ja, Umma tace "Ohh kin yarda kenan an daura maki aure da Driver?" Nihad ta girgiza kai disgustingly tace "Allah ya kiyaye wllh" Umma tace "Toh Alhamdulillah, yanda ko wace budurwa take rayuwarta haka xaki ci gaba babu batun auren kowa a kanki, kar ki kuskura ki amince wai kina da wani wai shi miji, a nan din ma bai wuce ɗan aiken ki ba kuma drivern ki, ki sa a ranki kema budurwa ce da xata iya shiga duk inda take so ta fito, ki ci gaba da rayuwarki yanda kika saba, sannan kar ki kuskura ki raga masa balle ya ga fuskar kawo maki raini, ba kowa bane shi facce drivern gidanku kuma har a yanxu dreban ne, kuma ɗan aike" Nihad tace "Toh Umma yanxu a gida daya xa mu xauna da shi kenan? Wallahi i just can't imagine that, ta yaya xa ace muna gida daya da shi?" Umma tace "Ka ji ki, Toh ina ruwanki da shi? Meye hadin ki da shi? Rayuwarki kawai xaki dinga yi kamar kina gidan ubanki, kar ki yarda ko kallon kirki ya hada ku da shi, har yau shi din ma'aikacin gidanku ne don haka a karkashin ki yake" A hankali Nihad tace "Toh, amma Umma shikenan baxan ci gaba da karatuna ba kenan" Umma tace "A saboda me? Ai kwantar da hankalin ki, yanxu daga nan gidan Alhaji Abubakar xan nufa tunda dai sun aurar da ke sai su bari kuma ki ci gaba da karatun ki" Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace "Nagode Umma" Umma tace "Kar ki yarda ki kara xubar da hawayenki a banza a hofi, ke da ma kika samu freedom din kanki yanxu, da kin tashi fita kawai fitar ki xa ki yi kanki tsaye babu neman izinin ko wani shege, sanda kika ga dama kuma xa ki dawo babu me tuhumarki" Nihad da ta ji hankalinta ya kwanta sosai tace "Haka ne Ummana" Umma tace "Toh ko ke fa, sannan duk kawayenki xa su iya xuwa nan su dinga kwana kuna yini tare, kuyi duk wani sabgarku a nan babu me cewa don me" Nihad tace "Gaskiya ne Umma, amma ni damuwata kawai ganinsa da xan dinga yi a gidan, baxai yiwu ya koma can gidan ba kawai gaba daya ni kadai in zauna a nan, wllh i hate the sight of him, na tsani ganinsa, na tsanesa" Umma tace "Aa ke kuma, ai xai ci gaba da aikinsa na tuki, kinga duk safiya xai dinga xuwa can gidan kilan kuma sai ya dawo da Abbanku daga office sannan ace xai dawo nan gidan" Nihad ta yatsina fuska, Umma tace "Ke ma abinda idan kika fita kilan sai daren xa ki dinga dawowa gida" Nihad tace "Dama mana, yanxu kawai xance su Husnah da Naf su kwaso kayansu su dawo nan mu zauna" Umma tace "Shikenan kuwa" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve, Umma tace "Kin ci abinci kuwa?" Girgiza kai Nihad tayi, Umma tace "Me yasa? To tashi ki tafi kitchen ko indomie ne ki dafa" Nihad tace "Toh" Mikewa tayi cike da energy ta wuce kitchen, sosai ta samu nutsuwa bayan abubuwan da Umma ta gaya mata, ta dafa indomie sannan ta fito, Umma tace "Bari in xo in tafi don in samu Alhaji Abubakar a gida" Nihad tace "Umma bani da waya wllh" Umma tace "Akwai nokia din yayanku bari ko Amina xan ba ta kawo maki anjima" Nihad tayi Murmushi tace "To Umma Nagode" sai da ta gama cin indomie sannan Umma tace ta taso ta rakata, Nihad ta mike suka fito compound da Umma, har sannan khalil na xaune inda yake, Ya mike yana kallon Umma yace "Sai anjima Hajiya" Umma ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki ta ci gaba da tafiyarta Nihad ta hade rai tana biye da ita a gefenta, Komawa yayi ya zauna ya bi su da kallo, suna isa gate Umma tace "Toh sai kin ji ni, idan Amina ta kawo maki wayar sai ki kirani don xan sa a siyo maki sim ayi register sai ta taho maki da shi" Nihad tace "Toh Umma" Umma tace "Maza tafi kiyi sallah ga azahar yayi, sai ki kwanta ki huta" daga haka tayi mata sallama ta wuce, Nihad ta kulle gate din, fuska daure ta nufi cikin gidan. Har bayan magrib Nihad na ta jiran Amina ta kawo mata waya amma shiru, gashi babu yanda xata yi ta kira Umma duk da tana da numberta a kai, wannan ne yasa ta kara shiga wani damuwa, karfe takwas da rabi ta mike a hankali ta fito daga dakinta, dai dai nan Khalil ma ya fito... sosai gabanta ya fadi ta ɗan koma baya, sai kuma ta daure fuska, ko kallonta bai yi ba ya shiga parlor, ta bi sa da kallo taga kamar fita zai yi, tuni turarensa ya gauraye duk parlon, ko burgeta kamshin nan nasa baya yi, ta kasa kunne taji ko fita gate xai yi, ai ko taji ya bude gate, da sauri ta shige dakinsa ta kulle kofar, banda kamshi babu abinda dakin ma yake, ta tafi gefen gado ta dau karamar wayarsa da ta gani ta hau dialing din number Umma sharp sharp, yana fara ringing Umma ta daga hade da sallama, Nihad ta marairaice tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Nihad, Number waye haka duk zero zalla" Nihad tace "Wayar yaron nan ne Umma, ya fita yanxu shine na dauka da sauri na kiraki kafin ya dawo" Umma tace "Kin ji shiru ko, wllh ba a samu anyi rijistan layin yau ba sai gobe wai, don haka gobe da kaina xanje ayi, ita kuma Amina tana dawowa islamiyya xan bata ta kawo maki kin ji" Nihad tace "Toh shkkn Umma, Allah ya kai mu goben" Umma tace "Toh Ameen, sai da safe daughter" Daga haka ta katse wayar, Nihad na duba call logs don ta kira Husnah tunda daxu ta saka numberta a wayar amma bata gani ba alamar ya goge number, instead sai number Nihal ta gani wanda ko awa daya ba ayi ba da suka yi wayan da ita, ta dinga kallon number babu kiftawa, bude kofar dakin aka yi, Nihad ta zaro ido hade da kurma ihu a tsorace ta saki wayar hannunta jikinta na rawa, tsaye yayi bakin kofa yana kallonta da wani Strict expression, lkci daya ta wani sha kunu ita ma, can dai ta tafi can jikin bango har sannan gabanta na faduwa amma bata nuna hakan a fuskarta ba, ya karaso cikin dakin ta hadiye wani abu da ya tokareta a makogwaro da kyar xuciyarta sai bugawa yake tana kara shigewa jikin bango, yana dukawa zai dau wayar ta yi hanyar kofa a mugun guje, da hannu daya yayi hanzarin fixgota ta fasa ihu tana kokarin kwace kanta tace "Wallahi xan cijeka idan baka sakeni ba, ni me xanyi da gwangwanin wayarka"
*Da kun kai hannunku xa ku danna wajen fowarding littafin nan xuwa groups ku dubi girman Allah, ku dubi darajan annabi S.A.W, da kuma son da ku ke ma iyayenku ku tuna da cewar nace don girman Allah ayi hakuri kar a min sharing to groups with over thousand members, plss i am begging sincerely ba da fada ba ko gadara, ayi hakuri a min wannan alfarman, masu siya kawai don su tura groups su yi hakuri domin Allah kar su yi haka, And if u should come across this book roaming in any group kayi kokari kayi subscribing before reading saboda ba free book bane, ur conscience shouldn't allow u to read my dear, ko yaya ne try and give something, ina kuma alfahari da duk wa enda suka yi patronizing dina, ina kuma maku fatan alkhairi...*
Nihad is just....
500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
And u show ur evidence via 07087865788
Leave a Comment