nihaad 21

 


A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take kwance da kallo, a daki take saman gado, ta mike xaune da kyar tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo ga wani sanyi da ke shigarta duk da fankan dakin a kashe yake, ta kalli agogon dakin taga karfe biyu dai dai, window ta kalla ganin duhu yasa ta fahimci biyu na dare ne, hade kai tayi da gwiwa bayan tayi recalling duk abubuwan da suka faru, she couldn't stop tears from rolling down her eyes, ta dinga shessheka a hankali, tunawa da tayi bata yi sallan magrib ba balle Isha'i ya sa ta dago kanta tana goge idonta da ya kumbura, tayi kokarin sauka daga saman gadon amma taji baxata iya ba, ko ina ciwo take ji yake mata a jikinta, hakan ya sa ta koma ta kwanta a hankali, Hijab dinta dake gefenta ta jawo ta lullube da shi ta takure waje daya sbda sanyin da take ji sosai, amma bai taimaka mata da komai ba sai rawan dari take, bayan kusan minti talatin ta ji an bude kofar dakin, ita dai tana takure inda take ta rufe har kanta da Hijab, tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallonta, dama ya zo dubawa ne ya ga ko ta tashi or she is still unconscious cause he isn't as bad as she is, he have human conscience in him unlike her, har xai juya ya fita sae kuma ya karasa cikin dakin ganin kamar she is shivering, ya isa kusa da gadon yana kallonta xai cire Hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta riko hijab din a fusace cike da tsiwa tace  "Baka da hankali ne?? Uban meye xaka shigo min daki cikin daren nan?" Sake Hijab din yayi ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara sai kuma ta ja tsaki ta koma ta kwanta jikinta na rawan sanyi sosai. Har aka yi asuba Nihad ta kasa motsawa daga exact spot din da take a kan gadon tun cikin dare, she is so sick and weak, tayi yunkurin tashi ya fi a kirga amma kamar an danneta saman gadon take ji, duk da babu wani abun da ta ci tun jiya amma haka ta dinga jin amai yana damunta kamar xai taho mata, ga ciwon kai me tsanani da ya addabeta, wajen karfe takwas taji aman ya taho mata, bata san sanda wani strength ya xo mata ba ta sauka daga kan gadon tana layi ta bude kofar bandaki, nan ta durkusa ta dinga kakarin amai amma ba abinda ya fito, Khalil na kwance parlor yana jin ta amma ko motsawa bai yi ba daga saman kujeran da yake, a nan tsakar dakin Nihad ta kwanta tana maida numfashi hawaye me xafi na sauka idonta, tana nan a haka har kusan karfe sha daya na safe, zuwa lkcn kuma xaxxabin ya ci karfinta, Duk yanda ya so fita harkarta a gidan kasawa yayi, cause he wasn't raised to be mean, ya kuma san bata ci abinci ba throughout jiya don shi ya fito da indomie da ta bari a daki bata ta6a ba, karfe sha biyu saura ya mike yayi hanyar dakin after soothing himself to do so, kwata kwata ba don ranshi ya so ba ko don tayi deserving ba yayi hakan kawai dai shi din me tausayi ne, yana bude kofar dakin ya ganta nan tsakiyar dakin a kwance, ya fi minti daya tsaye bakin kofar yana kallonta kafin ya karasa cikin bedroom din, ya duka a gabanta ya cire hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta bude idonta da yayi jajir amma babu strength din rashin kunya ko tsiwa, bai kai hannu jikinta ba but yana jin hucin zafi a jikinta, ya mike ya fita daga dakin ya dau wayarsa, bayan ya gama kiran da xai yi ya shiga kitchen, ruwan gora ya juye a kettle ya daura saman gas, bayan ruwan yayi xafi ya hada shayi a cup ya fito, dakin ya koma ya ajiye mata shayin, amma ya kasa ce mata ta tashi ta sha, har cikin ransa bai son ko magana ya hada shi da wannan yarinyar, kawai daga karshe ya fice daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, bayan kusan awa daya ya fita kofar gida ya shigo da wani likita, wani asibiti dake home service ya kira suka turo masa likitan, bayan sun gaisa ya kai sa har dakinta, likitan ya ajiye abubuwan da ya taho da su yana kallon Nihad, Khalil ya juya ya basu waje yayi zamansa a parlor, bayan likitan ya dubata ya tilastata ta dan sha shayi, sai da yayi yakin kusan minti sha biyar kafin ya samu da kyar yayi mata allurai, ya kuma bata magunguna ta sha, da tace masa sanyi take ji ya dauko wani zanin gado da ya gani a leda ya bude sannan ya bata ta rufa da shi, yace "Allah ya sauwake, Anjima da daddare xa a dawo yi maki allura" Ita dai bata ce komai ba don bacci taji yana hauro mata har ya fita daga dakin, yayi ma khalil sallama sannan ya bar gidan..... Tashi khalil yayi wajajen karfe uku ta dalilin gate da ake kwankwasawa ya fita zuwa gate din ya bude, Aunty Jamila ya gani bakin kofar, sosai take kama da Mummy, ya mata sannu da xuwa sannan ya bata hanya ta shigo gidan, sai da suka shiga parlor ya xauna kasa ya gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ya sabon waje" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh madallah, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya" Bayan few seconds ta sake kallonsa tace "Ina Nihad din?" Ya dan kalli hanyar daki yace "Tana ciki" Aunty Jamila tace "Toh sanar mata na zo" Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin sai kuma ya dawo yace "Aunty bata jin dadi ne tun jiya daxu likita ya zo dubata, ki karasa cikin dakin" Aunty Jamila ta mike ta bi bayansa zuwa dakin, kofar kawai ya bude mata ya koma gefe, ta shiga dakin da sallama ya juya yayi komawarsa parlor, don tunda likitan ma ya bar gidan shi bai shiga dakin ba. A hankali Nihad ta mike xaune tana kallon Aunt dinta, Aunty Jamila ma kallonta kawai take don ba karamin rama tayi ba, Aunty Jamila ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Ya jikin" kamar jira Nihad take ta fashe mata da kuka tace "Aunty don Allah ku yafe min, wallahi ban san daga inda video din nan yake ba, ni ban ta6a video haka ba, kuma ban ta6a bari a min video haka ba, i don't know how everything happened" Aunty Jamila ta ma rasa abinda xata ce mata, Kuka kawai Nihad take ta hade kanta da gado, Aunty Jamila ta dagota tace "Ya isa haka, ba kuka na zo ki min ba, abinda ya faru kuma ya riga ya faru babu me ja da Ubangiji" Nihad dai goge hawayen da ya ki tsaya mata kawai take, Aunty Jamila ta girgiza kai tace "Da kina jin maganar uwarki duk haka da bai faru dake ba Nihad, ke ce tara kawaye, ke ce gantali, ke ce shiga kamar ba yar musulmai ba, kina ganin yanda yar uwarki ke rayuwarta gwanin sha'awa ita da ma ba gaban iyayenku take karatu ba, kin bata wayonki Nihad, kin kuma yi ma kanki damage din da baxai ta6a goguwa ba a doron kasa ba, ina ne wannan Video din naki bai je ba a internet?" Nihad dai kuka take kamar ranta xai fita, Aunty Jamila tace "Da kika je can kebbi din kinyi kawaye ne?" Nihad ta girgiza mata kai kawai, Aunty Jamila tace "Ta yaya ma xa ki ce ke baki san daga inda video din nan ya fito ba? Ba fa daura fuskarki aka yi ba ko wani abu, ke din ce a video din, ko Inner wear din ma ai ni na siyo maki su a Lagos ba a dade ba" Nihad ta ma rasa abun cewa, Aunty Jamila tace "Idan kin je makarantar baki zama a hostel ne?" Nihad ta sunkuyar da kanta, Aunty Jamila tace "Buda baki xa kiyi ki min magana" Cikin rawar murya tace "Aa" Wani shegen kallo Aunty jamila ta mata tace "Ba kin ce min kawayenki a hostel su ke ba?" Nihad ta gyada kai tace "Ehh amma a aji muke haduwa da su" Aunty Jamila tace "Baxa ki daina min karya ba?" Nihad ta hadiye abu da kyar tace "Da gaske Aunty" Aunty Jamila tace "Toh ke kika sani, ki rike gaskiyarki a ciki, xan ga ta yanda xa ayi a gano ta ina video din ya fito idan kin ma mutane karya" Nihad dai tayi shiru gabanta sai faduwa yake, ta yaya ma xata fara ce ma Aunty Jamila babu wani kebbi da suka je da Aunty Kamila hostel ta koma da zama, cab ai rufeta kawai xata yi da duka a nan, sannan ko jiya da suka je gida sai da Umma ta bata shawaran ko da wasa kar ta ce ma wani ai bata je kebbi ba hostel ta koma, ko da xa a cika ta da tambayoyi, balle ita tasan Husnah da Naf da Zully, enemies dinsu ma basu ma video ba balle ita, idan ma Zully na video suna daki tunda ita mayyar video ce Husnah tayi ta masifa kenan tunda su dama sun saba xama daga su sai lingerie, Aunty Jamila ta katse mata tunaninta tace "Don uwarki wataran da kanki xaki bude baki ki fadi ta inda video ya fito, dena wani tunane tunane, yanxu dai ki gama nuku nukunki da karyarki aikin gama ya riga ya gama tunda ga ki a gidan mijin ki" Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace "Wallahi ni ba mijina bane shi Aunty, kuma baxai ta6a xama mijina ba, shi drivern ne zai zama mijina? Wllh baxan ta6a yarda ba" Aunty Jamila tace "Gaskiya kam, tunda xa ki iya daukan takarda ki rubuta masa saki ki sake sa... Kinga karshen rashin yarda kenan" Nihad ta kara rushewa da kukan takaici, ita fa da taji ance khalil mijinta sai taji kamar an dau duniyar gaba daya an aza mata a kai, da dai a dinga furta mata wannan kalmar gwara a nuna mata bindiga kawai a harbeta, Aunty Jamila bata damu da kukanta ba ta bude cup din da ta gani a rufe ta ga shayi ne a ciki, tace "Me kika ci yau?" Ta girgiza mata kai hawaye caba caba a fuskarta tace "Ban ci komai ba" Aunty Jamila ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta fada kan gado tana rera kuka, Khalil na ganin Aunty Jamila ya mike yace "Za a dauko maki wani abun ne Aunty?" Aunty Jamila tace "Aa, so nake ko shinkafa da miya ne a samu a dafa, inji akwai kayan miya a gidan?" Yace "Aa xan fita in siyo yanxu" Aunty jamila tace "Toh shkkn" Daga haka ta shiga kitchen don daura ruwan shinkafa, Nihad ta hadiye kukan da take ta jawo jakar Aunty Jamila ta zuge zip din,  Wayarta ta ciro tayi dialing number din Nihal, sai ga number ya fito da suna, aika kiran tayi ta kai kunne, Nihal na dagawa tayi sallama hade da cewa "Ina yini Aunty?" Nihad ta wani kyabe baki tace "To ni ce nan ba ita ba" bata jira Nihal ta saurari Nihal ba tace "Kin ga Number Husnah xa ki turo min ta nan yanxun nan ba wani magana na kira ki min ba" Nihal tace "Ke me xa ki yi da number Husnar nan ne?" Nihad tace "Wannan bai shafe ki ba, kawai ki turo min abinda na tambaye ki" Magana Nihal take amma Nihad ta katse wayar kawai, ba a wani dau lkci ba sai ga number Husnah ya shigo wayar Aunty Jamila, Nihad ta mike da sauri ta tafi gun jakarta ta bude ta dauko biro da jotter, A hankali ta dawo ta zauna sbda har sannan bata gama dawowa dai dai ba tana dan jin jiri, bayan ta kwashe number ta tura takardan cikin pillow case dinta, sannan tayi dialing number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga, Nihad tace "Ni ce Husnah" Husnah dake cikin kasuwa ta nemi wani shago ta shiga da sauri ta zauna tace "Nihad ina ta kiran wancan layin da kika kirani da shi jiya naji kamar anyi blocking, line busy kawai yake sa min, har dare ina trying wllh, to ni kuma na rasa ta inda xan sameki" Nihad tace "Ai wayar wancan wawan yaron ne, wato blocking din ki yayi ko?" Husnah tace "Wallahi kuwa, wai yanxu kina nufin daga ke sai shi a gida daya?" Nihad ta fashe da kuka tace "Wallahi the thought of this na sa inji kamar in kashe kaina Husnah" Husnah tace "Ki kashe kanki a kan wa?? Aa wallahi turo min address din gidan yanxu" Nihad tace "Toh ai ban san ko ina ne nan din ba, amma bari in kira Umma in tambayeta" Husnah tace "Toh maza kirata ko ki turo min numberta ni in kira" Nihad tace "Toh" Katse wayar tayi ta hau kiran Umma, yana fara ring Umma ta daga, Nihad tace "Umma ni ce" Umma tace "Aa Jamilan na can kenan yau?" Nihad tace "Ehh" Umma tace "Toh anjima Amina na nan xuwa maki da wayar anyi rijistan layin" Nihad tace "Toh, Umma su Husnah ne ke son xuwa kuma ni ban san address din nan ba" Umma tace "Gaskiya baxa ki sani ba, kinsan me xai faru?" Nihad tace "Aa" Umma tace "Kice kawai su taho nan gida sai su biyo Amina tunda ita ta san gidan" Nihad tace "Toh Umma" daga haka Nihad tayi mata sallama ta katse wayar, ta kira Husnah ta sanar mata yanda suka yi da Umma, Husnah tace "Hakan ma yafi sauki wllh, turo min number Aminar" Nihad tace "Toh, amma kar ki kira layin nan na kanwar Mumy ce" Husnah tace "Toh shkkn, kawai sai mun zo anjiman" Nihad tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tayi deleting duk calls din da tayi ta goge message da tayi ma Husnah na number Amina, sannan ta mayar da wayar cikin jakar. Bayan la'asar Aunty Jamila ta gama girka shinkafa da miyan, A plate ta xubo ma Nihad ta fito parlor tana kallon khalil tace "Ga can abincin an gama" Yace "Toh sannu da aiki Aunty, Mun gode" Dakin Nihad ta wuce ta ajiye abincin a kasa, Nihad ta fito daga bandaki daure da towel, ta xauna gefen gado tana kallon Aunty Jamila tace "Sannu da aiki Aunty" Aunty Jamila tace "Yauwa sannu, kiyi maza ki ci abincin" Nihad tace "Toh nagode" nan ko ta rasa ta yanda xata tambayeta yaushe xata tafi don bata son su Husnah su zo tana gidan nan, ganin bata da niyyar tashi Aunty Jamila tace "Toh tashi ki fiddo kayan da xa ki sa mana" Nihad ta mike ta bude jakar ta dauko riga da skirt, bayan ta shafa mai ta sa turare sannan ta sa kayan, Aunty Jamila ta dauko abincin ta mika mata, amsa tayi ta fara ci, gaba daya taji bakinta babu dadi tura abincin kawai take, Aunty Jamila ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idar da sallah tace "Aunty ke baxa ki ci abincin ba?" Aunty Jamila tace "Aa na ci abinci kan in fito gida" Nihad bata kuma cewa komai ba, Aunty Jamila tace "Toh ni xan tafi Nihad" Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve don abinda take ta jiran ji kenan ganin hudu da rabi yayi tasan kilan ma su Husnah na hanya yanxu, Aunty jamila tace "Ki bude kunnenki ki saurare abubuwan da xan gaya maki da kyau" Nihad ta sauke idonta a hankali tace "Ina ji Aunty" Aunty Jamila tace "Ki nutsu ki dawo hankalinki, kinga wancan mutumin dake parlor??" Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya har hawaye ya cika idonta tun bata ji abinda xata ce ba, Aunty Jamila tace "Toh mijinki ne shi yanzu...." Nihad ta rushe da kuka tace "Don Allah Aunty ki daina cewa haka, wayyo ni a daina ce min haka gaskiya" Aunty jamila tace "Ba shakka, to rufeni da duka sai in daina ce maki haka, ke ba taimakonki yayi ba da ya rufa maki asiri ya aureki?" Kuka kawai Nihad take, Aunty Jamila tace "Toh wllh idan ba fushin Ubangiji kike son ja ma kanki ba ki bi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna lafiya a duniya, naga kamar baki saduda ba har yanzu baki dau darasi daga abinda ya sameki ba, ni iyakar abinda xan gaya maki kenan idan kin ji yayi maki amfani idan kika yi watsi da shi kuwa kuka bai kare maki ba a duniya" Daga haka Aunty Jamila ta mike ta dau mayafinta ta yafa, ta dau handbag dinta, kuka kawai Nihad take ganin ta nufi kofa sai kuma ta mike ta bi bayanta cikin rawar murya tace "Toh Aunty karatuna fa?" Aunty Jamila ta juyo ta kalleta tace "Wannan kuma sai ki tuntubi mijinki ki ji, mu kam ai bamu da iko da wannan, in ya amince sai ki ci gaba" Nihad na girgiza kai tace "Aunty don Allah kice masa ran monda xan tafi makaranta ni dai" Aunty Jamila tace "Ohk ni ce ma xan gaya masa, ashe shkkn iyakar karatunki kenan a duniya in har ni xan gaya masa" Fita Aunty Jamila tayi daga dakin tayi ma Khalil sallama a parlor, ya mike yace "Aunty har za ki koma" Tace "Ehh wllh na bar yara a gida" Yace "Toh bari in ajiye ki" Tace "Aa da kayi zamanka kawai Nagode, ina fita xan samu adaidaita sahu" Yace "Aa bakomai, xan ajiye ki yanxu" daga haka ya dau makullin mota ya fita, sai taji dadin yanda ya karramata sosai, kuma ko ba komai xata samu enough chance tayi masa magana a mota a kan Nihad, Nihad ta bi sa da wani harara, Aunty Jamila ta kalleta bayan ya fita tace "Wa kike harara Nihad?" Kin cewa komai Nihad tayi, Aunty jamila tace "To ki sani yau shine ganina na karshe da xaki yi a gidanki, indai baxa ki kwantar da kai ki zauna lafiya da mijinki ba" Nihad ta fashe da kuka har da bubbuga kafa tace "Ni Aunty ki daina ce masa mijina don Allah, wayyo Allahna na shiga uku" Kofa Aunty jamila ta nufa ta fice daga parlon, sai da suka fita daga gidan Nihad ta koma dakinta tana share idonta, Allah ya kiyaye wannan ya zama personal driver dinta balle kuma wai miji, suna fita ko minti goma ba ayi ba taji ana kwankwasa gate, da sauri ta mike ta fice daga dakin ta tafi compound don ta san su Husnah ne suka iso, tana isa gate din taji muryarsu kuwa, sosai wani farin ciki ya lullubeta amma kuma lkci daya fara'ar fuskarta ya bace da ta ji ta kasa bude gate din, kuma kamar ta waje aka kulle, Naf tace "Gate din ya ki buduwa ne kin bar mu tsaye cikin rana?" Nihad tayi narai narai da ido tace "Wllh kamar ta waje ya kulle" Husnah ta bude baki haka Zully, Naf tace "Amma dai wannan a yan iskan ma A ne shi, ta waje ya kulle gate? To a saboda me? Akuyarsa ya ajiye a gidan yake tsoron kar ta gudu da xai kulle ki cikin gida?" Nihad bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba shkkn da gaske kulleta yayi, Husnah tace "Ke kuma matsalarki kenan, to meye na wani kuka" Amina dai na tsaye rike da ledan waya a hannu, Naf tace "Toh wai ina yaje?" Nihad tace "Wai fa Auntyna ya kai gida shine sabida bashi da hankali ya kulle min gate ta waje kamar gidan ubansa" Husnah tace "Kuma wllh makulli ya sa, ni ko har na kagu in ga wannan me ido da kwallin" Nihad ta goge idonta tace "Kawai ku ɗan jira a nan yanxu xa ku ga ya dawo" Haka suka yi ta jira a bakin gate din, ita kuma ta zauna kan dakalin dakin da aka tanadar don mai gadi a compound din, tun daga nesa khalil ke kallonsu a bakin gate din, yayi parking ɗan nesa da gidan, Amina tace "Yauwa gashi can, motar gidanmu ce wannan" Su Naf duk suka kafe motar da ido ana jiran aga fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace "Ji gantalalle ya ki saukowa a motar" Zully tace "Shi ne ai nake kallon ikon Allah" Naf ta kalli Amina tace "Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali, uban wa zai bari tsaye cikin rana" Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta cikin motar tace "Ka bamu makullin gidan" Yace "Su waye bakin gate din?" Amina tace "Kawayen Aunty Nihad" Yace "Ohk, ke kika kawo su kenan?" Tace "Ehh Umma ta bani sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba" Ya mika hannu yace "Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin wancan ya fadi" Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan hannunta yace "Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?" Amina ta daure fuska tace "Ni ai a motarsu muka zo" Yace "Toh koma motar tasu" Daga haka ya ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin.....


*Kiyi subscription ki karanta hankalinki kwance yar uwa*




*Nihaad* is 500 via Fcmb Hauwa Bello Jiddah


Then u show ur evidence via👇🏻

07087865788

No comments

Powered by Blogger.