Noorul Hayart Complete Hausa Novel
✨ *Noor-Al-Hayat*✨
Kaleesat Haiydar_📚✍🏻
*All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance and privilege to start this book*
1.....
Muryar dattijuwar macen da baxata haura shekaru hamsin a duniya ba ne ya cika dakin, hankali tashe take jijjiga matashin saurayin da shekarunsa ashirin da takwas, kwance yake kan makeken gadon dakin, ta dinga cewa "Are you okay son, open ur eyes, Aliyuuuu ka bude idonka, What's ur problem..... Wani irin mafarki ne wannan ni fatima" sai a snn ya bude idanuwansa a firgice ya mike xaune yana bin dakin da kallo kirjinsa na heaving, lkci daya ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa dake kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Motherrr...."
ta kamo hannunsa damuwa karara fuskarta tace "What's ur problem Aliyu? Meye matsalar ka ka gaya min, are you sick?" ya buda idanuwansa yana kallonta murya can kasa yace "Ki taya ni addu'a mum... I don't knw, I just can't have rest of mind, may be....."Sai kuma yyi shiru hawaye ya taru lumsassun idonsa, tace "Ni mahaifiyar ka ce Aliyu, kana da warce xaka fadi ma damuwar ka duk fadin duniyar nn banda ni, tell me where you've gone wrong, what wrong have u done, ka gaya min Aliyu" ya share xufar goshinsa ya daura kai bisa kafadunta a hankali yace "Ki taya ni da addu'a kawai ummata" dago Kansa tayi tace "Wato dai baxa ka fada min ba koh?" Shiru yyi yana kallonta da manyan idanuwansa, can ya lumshe su a hankali ya bude yace "I will continue praying mum, it's not even worth saying kema ki taya ni...." Sake sa tayi ta mike tsam ta nufi kofa ya bi ta da ido kafin ta fita a hankali yace "Ur prayers plss mum..." Bata tankasa ba ta yi ficewarta, ya kalli agogo karfe biyun dare ya mike jiki a sanyaye ya shiga bathroom.
*5years later*
A hanxarce ta karasa dauraye cup da spoon da ta wanke ta fito kitchen din ta kashe electronics dake a kunne parlor ta dau jakarta dake kan kujera ta sakale a kafada ta nufi kofar fita tana kallon agogon wrist dinta, doguwar riga ce yar kanti Sea green a jikinta sae karamin mayafi ja da flat shoe shi ma ja, don ita din ba gwanar sa hill bace tsabar tsayinta, jakar hannunta ma dai jan ne, bbu komai fuskarta banda powder da eye pencil sai chapette da ta goga a lips dinta, amma ba lallai ka yrda cewar bata shafa pink lipstick ba tsabar pinkness din lips din dake dauke da xagayen baki, ita kanta tasan her lips are Unique, but who cares?? D'an tsaki ta ja ta bude kofa ta fito rike da makullin da xata rufe kofar Apartment dinta, tsaye taga wani matashi bakin kofar dake kusa da apartment dinta shi ma fitowarsa kenan da alama xai kulle kofa, dogo ne sosai domin kuwa irinsu ake kira da gentlemen, kuma duk tsayinta sai ta ganta karama kusa da shi, ya fi kama da mutan Egypt ko Ethiopia duba da kalan haskensa da irin gashin kansa, bakar shade ce a idonsa da ya fito da ainahin tsayin hancinsa, fuskar nan tasa a tamke bbu annuri, a hankali ta sauka ta bar masa gun, yana gama rufe kofarsa ya juya ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce parking space, bin sa tayi da kallo ta rasa gane ko mancewa yyi bai gyara belt dinsa ba, ko kuwa ass down yyi, sakin baki tayi ganin of course ass down din fa yyi, ta dauke kai cike da takaicin xama a compound daya da xa su yi da shi. Shine sabon tenant din apartment din dake kusa da nata bayan tashin makwabciyarta mai kirki Nancy, tun tashinta dama take ta addu'ar Allah yasa ba namiji bane xai kama flat din sai ga shi kuwa namijin ne, bata kuma sani ba sai a yanxu don tafi sati uku bata kasar tun bayan da suka yi hutu dawowarta kenan jiya da yamma, jiki ba kwari ta karasa rufe kofar ta fita don samun taxi da xai kai ta makaranta wato University of Cambridge dake kasar. Karfe biyu da 'yan mintuna suka fito school tare da kawarta Vanessa, tun shekararta ta farko suke tare gashi har sun doshi shekara ta uku kenan tunda saura masu yan watanni ne kawai, sai da vanessa ta jira kawartata ta hau taxi bayan ta sanar da shi Bridge street xai kai ta kafin ta daga mata hannu tace "See yah pretty" ta sakar mata murmushi tana daga mata hannu daga cikin taxi din tace "Alryt love" har suka isa gida hankalinta bai tare da ita tayi nisa cikin tunanin da take yi, har sai da muryar Ba'indiyen dake jan taxi din ya dawo da ita duniyar tunanin da ta shiga, ta fito ta mika masa kudinsa sannan ta shiga gida, da sauri ta shige apartment dinta bayan ta bude, duk da bata ga alamar yana gidan ba don babu motarsa a ma'ajiyar sa. Wanka ta fara yi tayi sllh snn ta shiga kitchen don girka abinda xata ci, Noodles kadai ya rage gidan, don haka ta daura ruwa ta shiga hada wa, kafin ya dahu ta kwashe dustbin dake kitchen ta bude kofa ta fita da tsintsiya, kasake tayi tana kallon uban kayan gym da ya jibge daga gefen flat dinsa, tun dawowarta sai a lkcn ta fito backyard din flat dinta, ta tabe baki ta dau tsintsiya ta hau share gun, har part dinsa sai da ta share tayi disposing bolar a basket ta koma ciki ta rufe kofarta, tana gama cin indomie ta wuce daki ta kwanta, ta jawo wayarta don duba agogo taga karfe uku saura minti biyar, ajiye wayar tayi don wa enda take da niyar kira tasan suna makaranta ynxu, ta lumshe ido. Ba ita ta tashi daga baccin da ya dauketa ba sai hudu da quarter, ta shiga bayi da sauri don dauro alwala tana idar da sllh kuma ta dau material din karatunta ta hau yi.
*Nigeria*
Zaune yake kan dining idanuwansa a kan system dinsa dake gabansa yana kallon kwallo, hango mahaifiyarsa da yyi tana sakkowa daga saman bene yasa shi saurin dauke plate din abincin dake gaban sa ya tura karkashin dinning din ya dau lemon dake cup ya sha kusan rabi sannan ya ajiye ya goge bakinsa da handkerchief ya ci gaba da kallonsa keenly, har ta karaso dining din idonta na gun da yake xaune, ta jingina da pillar din dake wajajen dining din tace "Ina abincin?" Dago kai yayi ya kalleta yace "Mum, ban ma yi noticing naki ba ae, na ci" tace "The plate?" Ya nuna mata hanyar kitchen yace "Har na wanke" girgixa kai tayi ta juya ta koma parlor, ya saci kallon abincin da ya ajiye kasar dining yyi saurin dauke ido ya ci gaba da kallonsa, lkci daya ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujerar dinning din, ya fi minti goma a haka yaji ance "Ya Aliyu...." Ya bude ido da sauri, kyakkyawar yarinyar dake tsaye gaban sa ta sakar masa murmushi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau... Hanan" ta buda idanuwanta sosai tace "Kai ka ajiye abinci a kasan nan?" Ta fadi tana nuna masa inda ya tura abinci, ya kalli direction din parlor da sauri yaga mumy bata nan, dukawa yyi ya fiddo yace "Gashi ki ci na koshi" ta tabe baki tana kallon hadadden jollof rice din dake dauke da kayan yanke yanke a kai da kusan quarter din kaza a gefe da plantain, kallonta yake yaga tayi murmushi tace "Kai me yasa baka ci ba?" A kara jinginar da kansa da kujera a takaice yace "I am nt hungry, idan baxa ki ci ba kema ki kai ma masu gadi yanxu" dauka tayi ta nufi kofar fita parlorn, ya bita da ido kafin ya mike ya kashe system dinsa don bai son ta dawo ta samesa a gun ya haura sama da sauri.
Misalin Karfe tara na dare tana kitchen tana dafa ruwan Lipton kamar yanda ta saba kafin ta kwanta, sai a sannan ta dinga jin kewan Nancy, don da yanxu ta ganta a dai dai wannan lkcn tana xaune kan resting chair tana shan coffee tana chatting, duk da ita ba gwanar xama a waje bace amma so tari saboda Nancyn haka nan ita ma xata bude kofa ta fita ta sameta ta xauna, sun yi ta hira kenan har kusan sha daya kafin kowa ya shiga ciki sai kuma gobe, Kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da wannan mutumin na daxu da safe daga shi sai singlet da 3 qtr waya na kare kunnensa, daya hannunsa kuma na rike da kwalba, sosai gabanta ya fadi tayi saurin kallon kofar kitchen dinta don ta tabbatar a kulle yake, ta sake satan kallonsa taga ya dakatar da wayar da yake yana kallonta ta cikin window ita kanta ta kasa fassara irin kallon, a hankali ta kai hannu ta kashe gas dinta sannan ta kashe wutan kitchen din gaba daya ta fita parlor da sauri don ta hakura da ruwan Lipton din.
Leave a Comment