Sanadin Zane 11-12
ππππππ _*SANADIN ZANE*_
ππππππ
By maman noorul
Hudah
Paid book
π Ώ️1️⃣1️⃣π1️⃣2️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhaji Usman Mai Riga ya kasance d'an kasuwa inda yake sana'ar Saida kayan gwari ba wani Mai kudi bane Amma Yana da rufin asiri da wadatan zuci yana da mata d'aya watoh Rabi da ya'yanta uku Maryam itace babban yar'sa sai me bi Mata Kabir(kawu) sai Kuma autarsu Fatima sun taso ne cikin gata dukda malam Usman ba wani me kudi bane Yana kokarin faranta kusu
Maryam (ummi) nada shekara 18 Allah yayiwa malam Usman rasuwa mutuwar ta bala'in girgizasu domin kuwa Basu San kowa nasa ba tun Yana Raye ba irin fama da ba a Sha dashi ba Amma yaki abin mamaki itama Rabin Bata da wani Yan uwa sun daiSan Yar nijar ce a cewarta yaki akayi a kauyensu ta tsinci kanta anan duk ba wani girma ne dasu ba Amma Maryam sai taji Bata yarda da labarinta ba ,shiko babansu in kana so ka gan b'acin ransa ka Masa maganar asalinsa sai ya zazzage maka matsifa hakan yasa kullum suna cikin fad'a da yarshi Maryam Dan kamar tasan zai mutu sai ta sashi gaba tace ya fada musu asalinsa Amma har ya mutu ko da Wasa yaki fad'a musu daga inda ya fito
Fatima kurma ce saidai ba Haka aka haifeta ba tana da shekara takwais tayi rashin lafiya sankarau ya kamata wanan shine sanadin kurmacewarta Wanda anyi magani Amma ba a dace ba
Malam Usman na rasuwa kamar had'in baki ranan addu'ar uku sai mahaifiyarsu ta rasu baxan iya fad'a muku tashin hankali da suka shiga ba mussaman ma data kasance ba wani dogon rashin lafiya sukeyi ba shi malam ciwon Kai itako mama daga baccin Rana Wanda k'yar aka ce Mata ta Shiga tayi Dan jininta yayi mugun Hawa shikenan Bata sake tashi ba
Maraici Suka shiga sosai Dan Basu da Mai tallafa musu kabir a karanci shekarunsa ya Fara zuwa kasuwa a rumfar mahaifinsa saidai ganinshi yaro domin a lokacin Yana da shekara Sha biyar ganinshi yaro yasa ake cutarsa wajen kudi Kuma Babu wani kasuwa Dan duk Rabin kayan ma asararsa akayi sun lalace sai jalin ta lalace,Maryam ce ke Fadi tashi wajen ciyar dasu tana aikatah wankau duk wani aiki yi takeyi ita da fatima ana Haka a gidan da take zuwa aiki wwani alhajin mato ya so aurenta taki har makota an bata shawarar ta amince Taki a cewarta tana da wanda take so Hamza duk inda aka so ta aureshi ki tayi kawu Kamar yayi hauka Dan sosai yake son suyi kudi Amma ummi taki amincewa har ta auri Hamza ba abinda ke Shiga tsakaninsu da kawu sai habaici dan kallon matsiyaci yake Masa saidai fa baya fad'a a gabansa sai bayansa kasancewar Allah yayi sa Mai fusaka biyu saidai Baya zalunci Kuma Baya so a zalunci wani nasa
Koda ummi tayi aure sai ta bar kawu shi kadai a gidan mahaifinsu Wanda yake d'aki biyune kacal sai bayi ta Kara da inda suka kebe da buhu suna girki
Ummi ta tafi da Yar kurma watoh Fatima Wanda mijinta yayi iya kokarinsa wajen Bata tarbiyya da Kuma kulawa Nan ta samu tayi school Amma a primary ta tsaya
Tana da shekara Sha bakwai Yar kurma kyakyawa ce sosai Dan Fara ce irin ta mu ta nigeria Amma ba can din Nan ba Amma duk tafi su haske saidai fah mahaifinsu ne fari sol,irin farin Nan da zaka gan mutum ya koma jazur bature dukda wahalal da yake Yana shiga Rana besa farinsa ya dusashe ba mahaifiyarsu ce baka
Kurma nada shekara bakwai ta auri wani d'an cirani aliyu suna ce me ali
Ali Nima ya kawosa Nigeria inda yake sana'ar Saida su fruit Ali mutumin kirki ne sosai ga kokarin Nima Bai tab'a Bari Fatima ta nimi wani Abu ta rasa ba Kuma be damu da lalurarta ba ko kadan sai ma faranta Mata yake ba ruwansa
Tana Jin dadin Zama dashi Dan ba ita kadai yake dawainiya da ita ba harda su ummi da kawu komai Ali ya samu zaice na kurma ne hakan na faranta Mata Rai
Tana da tsohon ciki,cikinta nada wata bakwai maifinsa ya kirasa ya dawo gida Cameroon ya so ya jira sai ta haihu but it was ugent Dole ya tafi tare suka je sosai iyayensa suka karbi kurma hanun biyu biyu ba kyama
Ashe Wai maihaifinsa bashi da lafiya ne he was diagnosed with cancer hakane yasa mahaifin ya bashi umurni ya dawo gida da Zama dan ba lallai ya rayu ba Kuma shine kadai d'ansa namiji ga mahaifiyarsa bata fita kowa gudunta yake a cewarta tana da kambun baka,Dan wasu ma lakanin da sukayiwa gidansu dashi kenan
Badan Ali yaso ba bΓ yan sati biyu ya dawo Nigeria shi kadai domin tattara muhimin abubuwansa
A lokacin daya sanar da ummi taci kuka sosai sai cewa take Ali bamuyi Haka da Kai ba Ali wallahi da nasan ba nan zaku dawwama ba wallahi Ali da an hakura da auren ta tafi ba sallama haba Ali cewa fah kayi zaku dawo yanzu kana fad'a min zaka bar Nigeria haba
Jikinsa yayi sanyi yace"kiyi hakuri yah Maryam wallahi bani da niyyar kuntata muku Amma umurnin iyayene ba inda zanyi kiyi hakuri zatayi ta zuwa tana duba ku,Kuma akwai waya a hanunta
Ummi share hawaye tayi tace"ai wayar Bata da amfani tunda ba Kira za ayi aji muryarta ba"
Yace"tana text yaya Maryam
Ummi dai ba Haka taso ba Haka ya baiwa kawu shagonsa ya tafi Rai ba dadi Dan yaji dadin zaman Nan din harda gida garesa anan din room and palour uku
Koda ya koma ya tarar mahainsa ya rasu Haka yaci kuka akayi zaman makoki sai bΓ yan sadakar uku aka fad'a Masa wasiyar da mahaifinsa ya Bari na ya maye gurbinsa a wurin aiki....mahaifinsa Yana aikin a masarauta shine Mai bawa flower ruwa tun Yana saurayi yake wanan aikin har ya tsufa duk Wanda ke Shiga gidan yasan da zamansa an shaidesa da hakuri,juriya rokon Amana
Haka ya d'auki Fatima Suka Koma gidan da zama ita tana sashen masu aiki itama gudun karta Zama asarariya sai kawai ta yanke hukunci Fara aiki tunda in ka nuna muradi ana samu tana so tayi ta samun kudi tana taimakawa Yan uwanta
Aiko ta samu an kaita sashin uwargidan sarki Mata Mai karamci da sanin ya kamata d'an daya gareta a lokacin Yana da ten years sosai yake son fatima kullum yana nanike da ita Dan tana girka me abincinsu ta Nigeria Wanda yake cewa abinci Mai dadi,Mami watoh sarauniya lubnah Bata damu ba dukda ana ta zugata akan ta bar yarima Yana muamula da talakawa itadai ba abinda ya dameta farin ciki da take gani a fuskar d'anta ya fiye Mata komai
Haka dai suke ta rayuwa har Fatima ta
Maman Nur
Leave a Comment